Showing 18001 words to 21000 words out of 23627 words
Chapter 7 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx
ne na fahimci ina
da sabon shigar ciki, saboda kula da nayi ta
hanyar yawaita yin gwajin do it yourself da
nake yi.
Na same shi zaune yana duba takardun da
yake rubutawa na kammala karatunshi na nemi
wuri na zauna ina jiran ya gama.
Ya kalle ni, yaya dai amarya da magana ne.
Na dan yi murmushin jin suan da ya kira ni, na
ce eh amma ai zan jira ka gama tukuna ya ce,
a'a ke dai na tattara na ajiye kawai maganarki
ai tafi wannan aikin tunda don ku ake yin shi.
Matso nan ki zauna na karasa inda yake
nuna mun na zauna sai dai na kasa yi mishi
bayanin saboda zuba mun ido da yayi.
Ya dan yi murmushi ya ce, "Hauwa'u
kenan, kin san wani abu? Na dan girgiza kai ya
108
ce, Kunyarki tana bani sha'awa, tana kuma
kara mun sonki da ganin martabarki a kullum.
Don kuwa nasan kunya aba ce da Allah
yake yiwa salihan bayinshi. Cikin hikima ya
sani nayi mishi bayanin komai, don haka take
kawai.
Sai ya kira Likitan da yake mu'amalla da
shi ya ce, mu same shi a gida. Ya rubuta
gwaje-gwaje da kuma scarming ba mu dawo
gida ba sai da muka biya muka yi.
Kamar yadda aka taba yi mun bayani a
baya, wannan ma haka ne, bambanci kawai shi
ne wannan cewa yayi mahaifata bata da karfin
rike nauyi mai yawa.
Don haka idan cikin ya kai wasu watanni za
a daure bakinta, don haka zan rage ayyukan
karfi da kuma yawan Zirga-zirga har zuwa
lokacin da za a daure.
Muka dawo gida ya ce naje na kira mishi
Amina. Nayi sallama a bakin kofar na shiga
nayi mata bayanin kiran da yake mata, muka
hadu a falon yayi mata bayani a gajarce.
Sannan ya ce, Don haka yana so ta kar6ar
mun aiki har kafin na samu lafiya nayi kwari.
109
Tayi mishi wani irin kallo da ban taba ganin
tayi mishi makamancin shi ba, sannan ta ce
"Zakari kenan lallai ka same ni a yadda ka ke
so na karbeta abinci fa ka ce?
Ya ce. eh na wani dan lokaci ne kawai
saboda lalurar da ke tare da ita. Ta ce, To ba
zan iya ba ko cikinta ya zauna ko kada ya
zauna wannan matsalarku ce ba tawa ba.
A kan wannan 'yar iskar karuwar da ka.
"Ke! Ya daka mata tsawa, take kuma da ni da
ita muka zuba mishi ido.
Ni dai na dauka zai rufeta da duka ne
saboda abinda na gani a cikin idonshi, itama
kuma bata kara cewa komai ba.
Juyawa tayi ta fita. Shi kuma ya koma ya
zauna sai da na bari zuciyarshi tayi sanyi
sannan na ce ni fa idan ka yarda ma zan iya yin
girki tunda dai ba mai yawa ba ne.
Ya ce, "A'a ki bari kawai nasan abinda zan
yi."
Da daddare Amina bata yi abinci ba, kamar
yadda ta fada shi kuma yace bai yarda nayi ba,
don haka take away yayi mana har da yaran
gaba daya.
110
Washegari da safe da kanshi ya shiga kicin
ya tafasa ruwan zafi ya hada tea ya baiwa
yaranshi, sannan ya ajiye mun ya tasa ni a
gaba.
Na ce, "Da ka yarda da abinda nake gaya
maka. Zan iya kananan aikace-aikace shima
Likitan ya gaya maka jijjiga jikina ne ba zan yi
ba.
Ya ce, "Ban yarda ba, idan kuma na gane
kema ban isa na saki ko na hanaki ba zan san
irin zaman da zan yi da ke."
Wannan magana da yayi tasa jikina yayi
sanyi, don haka ban sake yi mishi maganar ba.
Kwance kawai nake a dakina tunda yau Amina
ta karbi kicin din.
Waya muke yi da Nasiba kan batun aurenta
wata mai zuwa, tare da yi mata bayanin halin
da nake ciki.
Muna 'yar hira kan shirye-shiryen bikin.
Mallam ya shigo ya zauna a kusa da inda nasa
kaina a kan gado yana jin hirar shakiyancin da
Nasiba take yi.
Ya dan yi murmushi bayan na kashe wayar
ya ce, Kawancenku da Nasiba dai akwai
111
mamaki a ciki, don kuwa halayenku daban-
daban.
Na gyara zamana a kan gadon ya miko mun
ledar da ke rike a hannunshi tare da plate na
bude rabin kaza ce sai wata hadaddiyar shinkafa
a robar disposable.
Na mike tsaye ya ce, ina zuwa? Na ce zan
dauko abu ne a fridge. Ya ce, zauna me za ki
dauko? Na ce ruwa.
Ya isa fridge din ya miko mun robar ruwan
swan gyara zama nayi sai da na kusa cinye
abincin nan da rabin kazar sannan nasha ruwa
sannan ya fita.
Da daddare ma shigowa yayi ya ce ko zamuu
je falo ne ya ce, To idan za ki iya na dan yi
murmushi na ce, Haba dai nan da falon kuma
bayan na ce maka gar nake jina.
Ka dai yarda ne in kuma aka ce haka zamu yi
ta zama ai zaka wahala da yawa, ya ce to ya na
iya Hauwa'u?
Ina so naga dan da za ki haifo mun sannan ko
ba don ni ba kema ai kina da hakkin na kula da
ke, sannan na gamsar da kaina cewa ban kware
ki ba. Don ina da wasu 'ya'ya kefa?
112
Tausayinshi ya kama ni, lalurar da ta same ni
a gidan wani shi kuma yana ta wahala da ita.
Muka shiga falon Amina ta sha kwalliya tana
zaune ta gama abincin ta tunda girkinta ne. ban
sani ba ko ganin Malam da tayi daga wurina ne
ya 6ata mata rai?
Tunda ba ya shiga dakin wacce ba ita ce dda
girki ba, sai bisa lalura. To ita kuma bata dauke
ni a matsayin mai lalura ba. Babu wanda ya ce
wani abu a cikinmu har ita.
Na nemni wuri na zauna shi kuwa ya shiga
uwar dakinshi. Ta mike ta bishi zuwa can ya
sake fitowa tare da ita ya zauna a kan kujerar da
ya saba zama.
Ta dauki plate dinshi ta zuba mishi abinci ta
mika mishi, bai kalleta ba da remote a hannunshi
yana kokarin kamo (BBC World).
Ta gaji ta ajiye a kasa ta zuba mishi ruwan
lemo a kofi, ta debi nata taja gefe ta fara ci.
Ni dai dama a koshe nake don kuwa duk
sanda ya fita zai shigo mun da wani abu. Babu
wanda ya yi magana a cikinmu, don kuwa yanzu
bama hira da Amina.
Hirar dai da shi ne, to shi kuma yau fuskar a
daure take, don haka sai kawai na mike na dawo
113
dakina, saboda hango abubuwan da ke shirin
tashi da nake yi.
Mallam ya daina cin abincin Amina kwata-
kwata ni kuwa kullum zai kawo mun na rana da
na dare da safe kuwa hakura nake yi na sha tea
A hankali kuma yana ta neman mai aiki har
kuma an samu, sai dai aikace-aikacen gida ne
kawai ban da girki.
Babu abinda bata yi ba amma ya ki yarda ya
rinka cin abincin nata, wanda hakan ne yasa
manyansu suka zo don yi musu sulhu.
An kuma bata rashin gaskiya, shi kuma an
bashi hakuri tare da jaddada wa Amina kan ya
kamata ta gyara kan zamanta da mijinta shi kam
ya kafe ya ce ba zai ci abincin ba sai na wartsake
mun koma canje-canje yadda aka saba, amma
yanzu tunda ya nemi alfarmar ta a farko taki to
baya so ta rinka girkawa tana ci.
Bikin Nasiba yazo, har gida ta kawo wa
Mallam wanda zata aura suka kuma ba shi IV,
don haka shiri sosai muke yi na bikin, duk da dai
a gida nake zaune amma komai da ni ake yi a
waya.
Sanin da nayi Mallam ba zai bar ni zuwa
walima da send forth ba yasa ban ma bata lokaci
114
wajen tambaya ba, amma a yau daurin aure shiri
nayi cikin wani irin leshi mai kyan gaske.
Ga wani irin annuri da ke fita a jikina na
kwanciyar hankali da zama wuri daya, ga kuma
kyan da yaron ciki ke sawa.
Don haka ko ban ce komai ba ma an san na
hade kenan. Zama nayi a dakina ina jiran
shigowar Mallam don mu tafi tare, tunda nasan
zai halarci daurin auren, wanda za ayi karfe
goma na safiya.
Ya shigo dakin cikin babbar riga 'yar ciki da
wando na asalin yadin voil fari tas da hular shi
damanga itama fara.
Sai bakin takalmi sawu ciki da agogonshi da
ya daura rolex mai bakar fata.
Ina murmushi ina kallonshi a yau kam
annurinshi bai sa na kasa kallonshi ba dongon
mutum sosai dan siriri ba can ba baya cikin
bakake baya cikin farare.
Na sha rokonshi ya bar kasumbar shi da
kullum yake kankarewa amma sai yayi
murmushi kawai ya gyara dan gashin bakin da ta
zagaye labban bakinshi na sama. Na dai yi kyau
kenan na sake fadada murmushina na ce, ba
kadan ba, ya ce to ni zan tafi. Na mike ina gyara
115
gyalena, ya ce ina za ki? Na kalle shi na ce,
gidan bukin mana. Ya ce, a'a ni bamu yi haka da
ke ba, gabana ya fadi na ce, "Haba Mallam,
bikin Nasiba ne fa kada kayi mun haka."
Ya ce, "Zan yi miki fiye da haka don kuwa ba
zaki je ba in dauke ki na kai ki gidan biki na
ajiye ki na dawo ke hankalinki daya kuwa?
Ba kya kallon halin da ki ke ciki ne? Duk
yadda ki ke da Nasiba ba zai sa nayi gangancin
da za ki yi mun asarar wannan cikin ba, gara ki
san da haka.
Juyawa yayi ya fita ya bar ni a tsaye rike da
gyalena a hannu, kukan da nayi ranar ba na wasa
ba ne.
Ace yadda muke da Nasiba amma wai an
hana ni zuwa bikinta? Ita ya ya zata dauki abin.
Wajen sallar azahar ya dawo yana kallona, ya
ce kai Hauwa'u kenan ku ka ki ka yi? Wasu
hawayen suka zubo mun ya dan yi murmushi ya
ce, "Gaskiya ban kyauta ba yi hakuri kici
abincinki ya gyara zama ya bude abinda yazo
mun da shi.
Ya ce, Bude baki na ba ki da hannuna. Ban
kalle shi ba. Ya ce, Idan kina son na bar ki kije
116
gobe na dawo na samu kin cinye ya tashi ya fita
saboda kiran da aka yi mishi a waya.
Na dan wartsake saboda maganar da yayi
mun, don haka washegari ma da sassafe na
shirya ban tsaya jiranshi ba, bin shi falon shi
nayi na samu yana wanka.
Na shiga har cikin dakin na zauna a bakin
gadon ya fito yana kallona, kai Hauwa'u kina jin
dadi fa, wannan kwalliyar duk ni aka yi wa ita na
dan yi murmushi.
Ya jawo mai zai fara shafawa ya ce, Yanzu
kinga in banda ba na son ki rinka wani motsi mai
karfi ai da sai na baki man nan ki shafa mun."
Na kalle shi na ce, Mallam yanzu man ma
motsi ne mai karti ya ce, eh mana ni inda zai
yiwu ma ai da ko numfashin nan naki da karban
miki nayi.
To amma ina ba hali, ya mike ya dauko kaya
yana sakawa, ni kuma 1na kallon agogo saboda
kaguwan da nayi shima ya kalli agogon ya ce,
"Af, kina kallon agogo zan bata miki lokaci ko.
Yi hakuri bari na dan je nan kusa na dawo sai
mu tafi. Na ce, To ko zaka sauke ni ne sai ka
wuce daga can? Ya ce, Ki dai jira ni ba wani
dadewa zan yi ba.
117
Tun ina jiran Mallam a zaune har na gaj1 na
kwanta barci ya dauke ni, ban farka ba sai wajen
azahar na dauki waya na kira shi bugu daya ya
dauka yaya amarya kin gaji da jira ko?
Kada ki damu gani nan. Ba shi ya dawo ba sai
wajen karfe hudu da rabi.
Ya shigo tamfar babu abinda ya faru, Allah
dai yasa kin yi tunanin hada tea kin sha tunda
ban samu kawo miki abinci da wuri ba.
Karo na farko da yayi magana ban kula shi ba
ya ajiye abincin.
Wani irin lafiyayyen kifi da aka bude shi aka
cire kayarshi, sannan aka gasa yayi kyau ya ajiye
a gefena tare da robar ruwa.
"Bana so kina shan zaki da yawa." Ya yago
kifin "Bude baki na baki. ". Na kalle shi takaicina
ya sake karuwa ganewan da nayi da saninshi
yayi mun abinda yayin.
Na mike zan bar wurin, ya ce zo nan. Ban
kula shi ba na ci gaba da tafiya, zo nan Hauwa'u
kada ki koyi dabi'ar da ba ta ki ba.
Dawowa nayi na zauna. Kiyi hakuri. Kuka na
kama yi saboda bacin rai, yau ne ranar karshe ta
bikin Nasiba.
118
Kuka sosai nayi yana bani hakuri. Tun jiya
nayi mata bayanin ba za ki samu halarta ba ta
kuma san ba haka kawai zan hana ki ba, ai tasan
lalurarki.
Na ce, To ai da sai ka gaya mun ba ka sa ni
na saka rai da zuwa ba, ya ce To nayi kuskure ba
kuma zan kara ba. Ya sake miko min kifin.
Yi hakuri kici, don nasan kin huce.
Cikina yayi kwari har an saka mun robar an
kuma dan rage min dokoki sai dai ba mai yawa
ba, don haka Mallam ya kai ni gidan Nasiba nayi
mata wani zur.
Gidanta ita kadai, don mijin nata bai taba
aure ba. Komai na gidan mai kyau. Na kuma kai
mata gudunmawa ta duk da sanin da nayi
Mallam ya bata.
A gida kuma na fara yin abinci tare da
taimakon Sahura mai aiki, sai dai lallabawa nake
yi komai a hankali. A lokacin ne kuma aka
kawo Abulkhairi hutu. Na gayawa Mallam ina so
naje gida ya ce, a'a a kawo shi nan yaron ya
girma sosai kamar shi daya da Babanshi sai ko
haskena da yayi. Kyauta sosai Mallamyayi
mishi wanda hakan yasa ni kara damka mishi
zuciyata dungurungum dinta.
119
Watan Azumi ya kama, Musulmi gaba daya
kowa ya bada himma wajen ganin ba a bar sh1 a
baya ba.
Matsalar dai kawai shi ne, a watanne kuma
cikina ya shiga wata bakwai, don haka lallabawa
nake yi har a yanzu saukin abin ma dai tun
shigarmu wannan zangon karatun Mallam yasa
ni dole nayi differing din shekarar gaba dayanta.
A cewarshi badi na haihu dan yayi kwari sai
na ci gaba, to ban musa ba don kuwa nima hakan
yafi mun sauki.
Raba abincin muka yi mai girki tayi abinci
soye-soye yar uwarta kuma tayi kunu da kosai
tunda shi ya ce idan bai sha kunu da kosai ba
idan ya kai azumi baya jin dadi.
Har da haduwar da muke yi gaba dayanmu a
kicin Amina bata kula ni, idan na gaisheta ma
bata amsa wa ban dai daina gaishetan ba tunda
umarnin maigidan kenan.
Habaici kuwa tunda dabi'arta ne bata daina
ba. Ni kuwa tunda na rama sau daya abin ya
zama gagarumi to na kyaleta magana ta kare, sai
tayi tayi taji dadin da take ji idan tayi.
120
Duk da zaman Sahura a gidan aikin mu kawai
take yi, bata shiga dakin Mallam, don haka mu
ke sharewa.
Kirana Umma tayi akan Babana yana rashin
lafiya, tunda naji haka kuma nasan abin ya baci,
don kuwa shi ba mai yawan ciwo ba ne, sai dai
idan zai yi ya kan yi mai zafi ne.
Cikin sauri na mike zan shiga falo saboda na
sanar da MaHam kafin ya fita don ya sauke ni a
gida.
Amina na samu tana shara har ta kawo kusa
da kofa bata yi alamar zata tsaya na wuce ba,
don haka nayi nufin rabawa ta gefenta.
Mikewar da zata yi sai kawai ta hankade ni
da hannunta na bugi bango. Ta nuno ni da
tsintsiya "Kin san Allah? Ki kiyaye ni kada kiyi
sanadin da zan saki zubad da jini a gidan nan.
Kin sanni kuwa?"
Daga bakin kofar uwar däkarshi ya tsaya ya
ce, "Me ke faruwa ne?"
"Ka dai mata kashedi kawai abinda zan iya
fada maka kenan, idan kuma ba haka ba zan yi
mata abinda da kai da ita ba za ku yi zato ba.
Idan yaso duk abinda zai biyo baya babu
damuwa."
121
"Hauwa'u!" Na ce, "Na'am, zo nan. Wuce ta
nayi na karasa inda yake tsaye ya ce, wuce ki
nemi wuri ki zauna ina zuwa.
Na ce, To. Bai sake tambayata abinda ya faru
ba, nima ban gaya mishi ba, bayanin da nayi
mishi kawai na rashin lafiyar Babana ne.
Ya ce, To na shirya muje.
A hanya nasiha yake tayi mun kan hakuri a
wata mai altarma irin Ramadan, sannan kuma a
irin halin da nake ciki bai kamata na rinka tanka
mata muna fada ba.
Zuciyata dai babu dadi kawai abinda na sani
kenan. Mun samu jikin Babana yayi sauki amma
duk da haka Mallam yasa Likita ya rinka zuwa
duba shi.
Duk da farkon azumi yayi aike sosai na kayan
abinci yau ma ya bayar da kudi ma su auki,
saboda magani da hidimar gida.
Tare muka dawo saboda aikin abincin buda
baki. Ina tsaye a kicin din ina hada abinci tunda
ni ke da girkin ranar ita kuma tana hada kunu
maganganunta take yi da z age-zage.
Ban tanka mata ba don kuwa duk da dama ba
dabi ata ba ce amsa mata a yanzu kuma tsoronta
nake ji.
122
Na gama na juye abinci a babban flask na
hada salads a gefe na dauka zan fita, ita kuma
zata shiga kicin din na kauce na bata wuri ta
shige.
Na isa falo na ajiye na tafi daki don dauro
alwala.
Muna zaune bayan sallar magriba abinci nake
kokarin zuba mishi na dauko ludayi
a cikin kunu da nufin zubawa a kofi, sai kawai
naji Amina ta ce "Lalala ki ka fantsala mun?"
Kan na san abinda zan ce mata sai kawai ta
dauki kunun gaba dayanshi ta sheka mun. Da