Showing 15001 words to 18000 words out of 23627 words
Chapter 6 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx
/>
Tana kukanta ina rike da cokali a hannuna
na kasa komai saboda takaici, shi kuma salad
dinshi yake sha tamfar ba a yi wani abu ba.
Ya kalle ni idan ba za ki iya zuba mun
abincin ba ajiye ki bani wuri. Inda zan iya da
ajiyewa nayi na tashi, to amma ba zan iya ba.
Na zuba mishi na kammala mishi komai na
mike na tafi dakina na zauna a bakin gado.
Maganganun Amina suna dawo min ban
taba jin mutumin da yayi mun irin wannan
zagin ba.
Kala Mallam bai ce mata ba saboda bani da
mutuncin da zata zage ni ayi mata magana.
Washegari kicin na fara shiga na hada abin
karyawa na dauka zan shiga naji su suna
magana.
91
Da alama kuma ba ta dadi ba ce, na karasa
dakin na zauna a kasa na gaishe shi ya amsa a
dake.
Na hada mishi nashi na mika mishi ya zuba
mun ido, nayi gaggawar sunkuyar da kaina.
"Gargadi na karshe da zan yi miki shi ne, na
kada ki sake zuba mun abinci ki tashi ki bar ni
da shi a wurin, shashashar yarinya kawai."
Na ajiye a gefe na tashi na shiga cikin bed
room din shi don na gyara, sai dai raina a
matukar bace.
Na gana abinda zan yi na fito na same shi
yana ee mata ba za ta yi ba. Idan kinga za ki yi
girkin da zaku ci da rana shi kenan.
Idan kuma kin ga za ki iya tilasta ni sa ta yi
miki girkin da zaku ci don kawai tana amsa
sunan matata sai mu gani.
Tunda na fahimci ba kya jin maganata. Na
gama shirina na fito muka tafi.
Makaranta kowa a shirye yake don fara
jarrabawa, kuma mun fito lafiya ba tare da
matsala ba.
92
Na biyo office din Mallam ba shi da alama
zai tafi yanzu, na ce ko zan tafi ne saboda mun
gama jarrabawa.
Bai kalle ni ba nima ban kara cewa komai
ba. Ba mu dawo ba sai wajen karfe uku.
Amina bata yi girki ba na shiga dakina ina
kokarin neman abinda zan ci saboda wata irin
gigitacciyar yunwa da ta kama ni.
Shayi na hada na sha wanda take kuma ya
burge mun ciki, nayi ta kwara amai babu
kakkautawa.
Nayi wanka na saka jallabiya na shigo cikin
jikina a mace na dauko indomie na yara na
dora a wuta cikin sauri ta nuna na ci na dan ji
dadi.
Sannan na koma nayi La'asar kafin na dawo
na dora abincin dare.
Duk abinda nayi kokartawa kawai nake yi
saboda wani zazzabi da ya rufe ni. Na hada
komai na kai mishi yadda muka saba.
Na zuba mishi abinci har yaci ya gama
Amina bata zo ba, ya kalle ni.
93
"Ke ba za ki ci ba ne?" Na ce, Bana jin dadi
ne. ya ce "Allah ya sauwake, amma da kin
daure kin ci ko babu yawa."
Ban yarda na ci ba don kuwa zuciyata ba a
nutse take ba.
Wajen karfe dayan dare na tashi saboda
murdawan da cikina ya ke yi, na shiga bayan
gida wani aman ne ya sake kubuce mun, nayi
ta yi.
Motsin da naji a bayana baisa na juya ba,
don na san Mallam ne. na wanke jikina na
dawo daki na kwanta.
Ban wani jima ba na sake komawa. Tun ina
aman abubuwan da na ci da rana har sai da na
koma kakarin aman kawai nake yi.
Amma babu abinda ke fita. Nayi matukar
galabaita.
Wajen karfe hudu saura kwata, Mallam ya
dauke ni zuwa asibiti, tun kan mu isa naji ni a
jike, abinda na dauka fitsari nake yi saboda
wahalar da nayi.
Sai dai ina fitowa daga cikin motar hasken
fitilun dake harabar wurin suka haskake mana
jinin da ya wanke illahirin kayan jikina.
94
Cikin wani irin firgita nayi luuu zan yi kasa,
yayi saurin rike ni. Daukata yayi ya shigar dani
asibitin take kuma Nurses da Likita suka yo
kaina.
Gwajin farko aka tabbatar mana ciki ne,
kuma ya fita. Wankin ciki aka shigar dani, shi
kuma ya juya ya tafi, don fara kiran sallar
Asubah.
Sun so su rike ni amma naki yarda, don
haka muka dawo gida wajen karfe goma.
Jarrabawar ranar dai ta wuce ni. Abin da na
ce wa Mallam kenans ai dai bai ce mun komai
ba, tukinshi kawai yake yi.
Muna dawowa gida kuma ya sake shiryawa
ya fita don zuwa wurin aiki. Labarin da Nasiba
taji ne yasa ta zuwa bayan gama jarrabawarta.
Ta zuba mun ido cikin mamaki.
"Kinga yadda ki ka zabge kuwa yau kawai?
Gaskiya kin ji jiki Hauwa'u, sannu."
Ina kwance na amsa. Sai lokacin ne Amina
ta shigo a'a kun zo ne? Nasiba ta fara gaisheta.
Suka gama gaisawa sannan tayi mun sannu
da jiki ta fita. Sai da Mallam ya dawo Nasiba ta
tafi.
95
Har cikin dakina ya shigo ina kwance a kan
gado na saboda rashin karfin da nake dashi.
Na dan yunkura na żauna ya ce, Yaya jikin
naki. Na ce da sauki. Ba ki da matsala?ie
Na ce, Eh sai ta rashin karfi, ya ce eh ai sai
a hankali wannan kuma. Don kin zubar da jini
da yawa, ga kuma aman da ki ka kwana kina
yi.
Na dan daga tafin hannuna ina kallo, shima
ya rike yana dan latsawa.
To amma Hauwa'u me yasa kina da ciki
har kin shiga wata na uku ba ki taba gaya mun
ba? Me ki ke nufi da hakan da ki ka yi?"
Yanayin tambayar tashi tayi mun wani iri.
Na ce, "Ban san ina da shi ba. Abin da na sani
kawai shi ne, na kan tashi da zazzabi da safe,
amma baya ga haka bana jin komai.
Sai aman da nayi jiya, shi kenan. Ya ce, To
Allah ya baki lafiya, na ce amin. Muka canza
maganar zuwa can kuma sai ya sake cewa, Ina
fata kin san da cewa maganar karatun ki ba zai
shafi al'amarin aurena da ke ba ko?
Na dan kalle shi zuwa can na ce, kana
zargin wani abu ne? yayi shiru na dakiku kafin
96
ya ce, a'a bana yi. Na ce to nayi maka
alkawarin ba za ka taba ganin wani abinda
baka so ba game da maganar karatuna ba.
Yace, To na gode, yayi mun sai da safe
sannan ya fita.
Duk da rashin karfina na lallaba naje
makaranta a washegari don jarrabawata. Shima
kuma yana jirana a waje lokacin jarrabawar ina
gamawa ya dauko ni ya dawo da ni gida.
Bai ce sai ya gama ayyukanshi ba. Duk
abinda nake yi daurewa kawai nake yi saboda
yadda zuciyata take cunkushe.
Babu abinda ya tsaya mun irin ganewan da
nayi har yanzu ban rabu da matsalar mahaifar
da na samu a gidan Ahmad ba.
Yanzu me zan yi a kai? Zan sami Mallam
nayi mishi bayani ne ko kuwa yaya?
Yamma tayi, ban yi kasala ba saboda
tunane-tunanen da ke damuna gara nayi aikin
da ke gabana kawai duk da rashin karfin jikina.
Na shiga kicin saboda na dora abincin dare
na samu Amina a ciki tana yi don haka na
dawo dakina na sake kwanciya.
97
Don haka a kwanaki biyunnan in banda
jarrabawata bana leka ko ina, ko wurin cin
abinci bana zuwa.
Shi ne dai yake shigowa ya dan yi mun hira
ya tafi saboda tunanin da yake yi na rashin
karfin jiki ke damuna.
Duk da jarrabawata ban ji kunyar shirya
lafiyayyen abinci ba, ranar da kwanana ya
zago
Nayi kwalliya mai ban sha'awa cikin yadin
material baki da pink mai rawa dinkin doguwar
riga ya kuma bi jikina ya manne saboda yaukin
yadin.
Ni kaina nasan ya matukar yi mun kyau,
don ya karawa hasken fatata kyalli. Na feshe
jikina da turare.
Sai da nayi sallah sannan na shiga falon.
A yanzu Amina ta daina yi mun shisshigin
makalkale Mallam ranar girkina, don haka ko
bana wuci sai nazo nake yi mishi abubuwan da
yake bukata.
Na shiga falon yana ganina ya dan saki
murmushin da ban san ko na meye ba a cikin
biyu, na ganin jikina yayi kwari ne ko kuma na
98
mai yaba kwalliyar dayar mu ba ne a gaban mu
ko zai yaba miki kwalliya to sai kun kebe don
gudun cin fuska.
Na karasa gaban shi ina zuba mishi abinci
na gama na zuba mishi abin sha na gyara zan
zauna ya ce ke fa?
Kamar nayi magana sai na fasa na dauki
plate ina zubawa Amina ta ce ai da ka barta
kawai kila bata jin ci ne. ka san illar bari yawa
ne da ita ballantana wanda a ka jawo shi da
karfi.
Ai ma an auna arziki da abin ya tsaya a
haka, ga yar makwabtan nan namu da suka
shigo duba ki shekaranjiya ai garin haka ita har
yanzu bata sake haihuwa ba.
Don an ce mahaifarta ta samu matsala
kawai fa akan tana Jami'a itama kamar dai
nakin nan."
Na kalli inda Mallam ke zaune yana cin
abinci sai dai fuskarshi ta canza gaba daya, na
zuba abincin na ja gabana zan fara ci.
Ta fara kokarin ci gaba da zanceen nace,
Amina ya isa haka. Ta kalle ni ta ce, au, ya isa
kuma kada nayi miki nasiha don na taimake ki?
99
Al ni 'yar uwa na dauke ki don kuwa ni ko
kishi da ke bana yi. Mallam ya ce, ta dai ce ya
isa haka ina ganin da sai kiyi shiru.
To ai shi kenan tunda dai duk bakwa son
zancen. Ita gaskiya kasan daci ne da ita
darling, amma tunda ba ka so shikenan.
Ta dan yi murmushi ta kalle shi, darling sai
da safe. Ina rike da cokali da abinci a plate ina
dan coccokalawa amma na kasa ci saboda
bacin rai.
Bana shiga harkar Amina, amma ita sai ta
shiga tawa. Har ya gama cin abincin bai sake
cewa komai ba.
Na kuma san dama tayi mishi maganar ne
don ta saka mishi damuwa a ranshi da zargi
wanda dama daga tambayar da yayi mun a
ranar da abin ya faru.
Ganin da nayi hankalinshi yana wani wuri
yasa na tattara abin da zan tattara na wuce shi
naje na kwanta.
Washegarin da muka gama jarrabawa a gida
na wuni. Ina zaune a gaban Baba Ladi don har
yanzu tana nan bata tafi ba, tana yaba mun
kyan da nayi.
100
Ta ce, "Gashi ba zama ki ke yi ba amma
kwanciyar hankali sai dai ina ga ko za a karbar
miki magani ne 'yar nan?
Na ce, A'a Baba Ladi lafiya kalau, ni kuwa
na fada mata haka ne don na san matsalata ya
kuma zamar mun dole na fuskanci Mallam
nayi mishi bayani.
Sai dai ta yaya? Tunanin da nake tayi
kenan. Ban koma ba sai da na jira dawowar
Babana nayi musu sallama bayan nayi musu
alherin da na riko musu.
A yanzu zamanmu da Amina ya canza.
Kasancewar mun gama jarrabawa ni ke yin
abincina na cikakken kwanaki biyu rana da
dare.
Babu damar na fito tsakar gida zan yi wani
abu ko zan shiga kicin sai ta fara zazzaga "
maganganun habaici iri-iri.
Ni kuma ban iya irin wadannan habaice-
habaicen ba, don haka bana kulata. Abinda na
sani shi ne, bata fito baro-6aro ta ce dani take
yi ba.
Duk da nasan dani din take yi, ni kuma bana
Son rikici.
101
Rannan na kwana dakin Mallam na fito da
sasafe cikin kwalliya sosai don yin abin
karyawa. Kamar yadda muke hutu suma
Malam Jami'a hutu suke yi.
Don haka shima Mallam baya zuwa aiki
kullum, sai ya dauro. Kokarinshi na ganin ya
kammala karatun shi ne na Phd din da yake yi.
Hakan ne yasa na kuke nake shirya mishi
gara iri-iri. Na shiga kicin na fara harhada
abubuwan da zan yi amfani da su, sai ga
Amina ta shigo.
Ta tsaya tana kare mun kallo, na ce mata ina
kwana? Sai da ta tabe baki sannan ta ce, lafiya.
Wai Allah ya rufawa mutane asiri kwashen
ragowar mutane darling ya dauko in banda
haka da ban san irin sanaben da aka yi mana a
cikin gidan nan ba.
Duk da 6ata mun ran da maganar tayi
kokari nayi na shanye amma sai na juyo na
fuskanceta.
Nayi murmushi na ce, Amina kenan, ai ni
ya kwaso ni yana da cikakken sanin cewa biyu
sun aure ni kafin shi.
102
Amma duk da haka ya aura yake kuma
ganin mutuncina da darajata da ta iyayena.
To amma ke fa? Matar da ya aura a zaton
budurwa ya ganta a burme ga kuma tsaraba a
Sunke jagwalgwalon 'yan birni?
Don haka duk abinda za ki gaya mun fade
shi ba zan ji haushi ba.
Na juya na ci gaba da aikina, kirjina sai
harbawa yake yi don naji zafin maganar da
Amina tayi mun.
Ni kuma nasan na fada mata ne kawai don
ramuwa ba wai don naji ba, asali ma ni ban san
komai game da ita ba.
Baya ga 'yan uwanta da nake gani suna
zuwa. Ban san lokacin da ta bar wurin ba, na
dai juyo ne ban ganta ba.
Na gama aikina na dauko a babban tray na
shiga falo zan ajiye na sameta a falon tana
zaune tana kukan sharbe shi kuma yana wasu
bayanai da ban fahimta ba.,
"Zo nan Hauwa'u". na dawo kan doguwar
kujerar da yake na zauna na ce gani.
"Me ya hada ki da Amina ki ka gaggaya
mata maganganun da kika yi mata na kalle ta
103
yadda ta dage take fyace majina da gefen rigar
barcin ta.
Na ce, Tazo ne ta ce maka na gaya mata
bakaken maganganu amma bata yi maka
bayanin dalilin da yasa na gaya mata ba?
Ke bana son surutu, ki bani amsar
tambayata kawai.
Nayi mishi bayanan komai da ya faru tun
shigarta kicin samuna da tayi da kuma maganar
da ta gaya mun.
Shiru yayi zuwa can ya ce ni na sanki
Amina nasan kuma ba karya tayi miki ba, kin
fada mata abinda ki ka fada wane hukunci ki
ke so nayi mata bayan ke ce ki ka fara gaya
mata bakar magana.
Duk lokacin da dayarku ta tsokani wata da
magana ta rama kada mutum ya zo wurina don
ya ji zafi.
Bana so, ya ya zan auro mata ki zo kina
gaya mata irin wadannan maganganun, idan
bazawara na auro ta ina ruwanki, ina abinda ya
shafe ki?
104
Ke na aurowa ita ballantana ki ce bata y
miki ba? Ai ni ki ka zaga ba ita ba. Ya kalle n
"Tashi ki hada mun abinci.
Na hada mishi abin karyawa na mika mishi
na hada mishi ruwan lipton a wani kofin na
ajiye mishi.
Bata nuna alamar ci ba don kuwa har yanzu
zaune take tana kuka tana fyace majina.
Ya gama karyawa na mike na dawo wurina
na kwanta doon na dan samu barci sai dai
hayani ya ce ta kaure tsakaninsu bana jin
abinda yake fada ita ce dai take bayanin ya
wulakantata.
Ya tona mata asiri a wajena, don haka ita ba
zata yarda ba.
Wasa gaske karamar magana sai ta zama
babba, kafin yamma ina kicin sai ga iyayen
Amina sun iso, Goggonta da kuma yar
Aminan
Na shiga dakin Aminan inda suke na gaishe
su, sannan na kai musu abin tabawa tunda ni ce
a kicin, na dawo na ci gaba da harkokina.
Ba a jinma ba aka yi kirana a falo na shiga,
gaba daya sun hallara. Na ce mishi, Ga ni
105
tunda shi ne ya kira ni ya ce yi musu bayanin
abinda ya faru dazu da safe.
Nayi bayanin komai suna salati suna
sallallami tare da tafa hannu, ita kuwa Amina
kuka take yi.
"Alhaji ka ci amanar son da yarinyar nan
tayi maka." Ya kalle ni "Tashi ki tafi." Na
mike zan tafi, Goggon Amina ta ce, "A'a ta tafi
ina, ai gara ta zauna ayi da ita tunda ko ta tafi
ma kawar da jiki ne kawai za a labarta mata
komai.
Tunda ta kai ma sirrin dake tsakaninka da
matarka dadadde ma bai tsira ba. Ya kalle ni,
ina ce ai ki ki ke yi? Na ce, eh. Ya ce To je ki
abinki
Na dawo kicin jikina a sanyaye magana na
gayawa Amina don taji zafin ta gashi ta zama
gagarumna.
To da alama dai kenan maganar da na fada
mata gaskiya ce ko kuwa yaya? Ba su fito ba
sai sallar Magariba.
Na kai musu abincin su dakin Amina, nima
na shiga dakina don gabatar da sallahta.
106
Mallam bai nuna min komai kan maganar
tunda da ni da shi ne kawai muka san
maganar bata taba shiga tsakaninmu ba.
Nayi ta ne kawail don na rama bakar
maganar da ta yi mun, ita kuwa Amina
tsakaninsu da darling din nata ya ki dadi.
Don ta kafe akan cewa ya wulakantata a
wurina, ya tona mata asiri. Zama tsakanina da
ita kuwa abin ba a cewa komai, don a yanzu ko
na gaisheta bata amsawa.
Idan kuwa a wurin cin abinci muka gamu,
to babu mai cewa wani komai. Ya hadamnu
yayi mana magana a kan hakan ta ce ita
tsakaninta da ni babu zaman lafiya har abada.
Idan ba kwatar mata hakkinta yayi ba. Za
kuma ta tabbatar na gane kurena. Ya ce to babu
laifi, ke Hauwa'u na ce na'am, ya ce ke ce
Rarama don haka kada ki gajiya. da gaisheta da
kike yi kullum.
Don Allah baya son gaba ta wuce kwana
uku, haka nan kada ki riketa da komai a cikin
ranki kin gane ko? Na ce eh ta kalle ni taja
tsaki ta tashi ta tafi.
107
Don haka bana jin haushinta, ya'yanta
kuwa 'ya'yan mijina ne, ina da kyakkyawar
alaka da su.
Koda basa zaman gida saboda makaranta,
don lokacin da su kenan mu'amallar da ke
tsakaninmu mai kyau ce.
A daidai wannan lokacin