Showing 9001 words to 12000 words out of 23627 words
Chapter 4 - MAI DAKI (4) Book Complete By Hafsat C Sodangi.docx
kina ganin sai na hana ki ci gaba
da karatu bayan a halin da muke ciki zaki je aji
na uku ne."
56
Na kawar da kaina gefe na ce, Kawa
ra ayina kenan, kuma ina fata maganar zata
tsaya a nan."
Nayi mishi sallama na juya na shiga gida.
Na zauna a kan katifata cikin daurewar kai.
To ban kullaci Mallam Zakariyya ba kan
abubuwan da yayi mun ba don kuwa ma sai na
ce ban san abinda yayi mun mai tsanani ba.
Tunda bai fadar da ni ba kamar yadda nayi
zato ba daidai gwargwado, kuma abinda naci
shi ya bani haka nan rashin mu'amallar shi da
dalibai ba laifi ba ne.
Don kuwa yana kare mutuncin shi ne,
daliban Jami'a wasu ko ba ka neme su ba su za
su baka kansu, don shedananci.
Ko kuma don suci sakamako mai kyau. To
amma kwata-kwata ni bana ra' ayin shi.
Ban san dalili ba yanayin shi na dakewa
yana matukar fadar mun da gaba a duk sanda
na ganshi kuma sai na tuna da Ishak saboda
daurewar fuskarshi.
Mutane ne da basa murmushi sai da wani
dalili. Sannan kuma sai kawai a ganni a aji na
zama matar Mallam Zakariyya.
57
Kai abin zai yi mun wuya tunanina daya
kawai shi ne Babana ga dukkan alama kuma ya
yarda ya amince da shi.
Ga ni kuma abinda na gaya mishi a ranar tä
nuna yarda ne da maganar.
Idan kuma har zan sallami Mallam
Zakariyya to zan yi hakan ne cikin hikimar da
wani abu ba zai shiga tsakanina da Babana ba.
Shiryawa nayi tsaf cikin kasaitacciyar
kwalliya ta leshi coffee brown mai adon zare
sky bluc da pink na yafa gyaie pink na saka
takalmi na pink na rike purse pink na yiwa
Umma sallama.
Gidan su Nasiba na tafi.
Kasancewar ko kwana hudu bamu yi da
rabuwa ba, ya bata mamakin ganina.
Tana murmushi ke kuwa wannan irin
zukckiyar kwalliya kamar sabuwar amarya?"
Na ce, "To wa ya sani ne." Na labarta mata
komai da yake faruwa, tun daga kirana da
Babana yayi har zuwan Mallam Zakariyya da
abinda na gaya mishi.
58
Ta dan yi shiru zuwa can ta ce, "To amma
idan gaskiya zan gaya miki, to banga aibin
Mallam Zakariyya ba.
Mutum ne mai mutunci wanda babu wani
mutum da ya ta6a bada labarin mummunan
abinda yayi.
Sannann dan kankanin abinda yayi miki
kuma kema laifi ki ka yi mishi a matsayinshi
na Malami.
Kuma ko kina matarshi zai iya hukunta ki a
Makaranta don kuwa matsayinki na matarshi
daban matsayinshi na Malaminki daban.
Muna cikin wannan hirar ne aka yi sallama
da Nasiba. Ta kalli Usman yaron Yayanta da
yazo mata da sakon.
Ta tambaye shi wanda yake sallama da ita
ya ce ban tambaya ba, bari na koma ya dawo
ya ce wai in ji Malaminku ne Mallamn
Zakariyya.
Muka zubawa juna ido cikin mamaki ta ce,
"Lallai abin nayi ne. Bari na bude mishi dakin
baki."
Ta mike tsaye tana yafa gyalenta, na ce "To
kada dai ki ce mishi ina nan, yauwa.
59
Bata kulani ba wucewa tayi ta fita. Ni kuwa
tashi nayi na shiga wurin Hajiya na zauna
muna hirarmu, don kuwa mata ce ma
barkwanci.
Na kusa awa guda a zaune a dakin amma a
raina ina mamakin dadewan Nasiba, sai gata ta
shigo ta kalle ni.
"Dan zo mana baiwar Allah."
Na mike na bita a tunanin da nake yi ma ya
tafi, sai da muka fito ta co Kin gane ko, ina
ganin ya kamata ku dan fahimci juna, don ni
banga aibun shi ba.
Sannan ma mutunne mai saukin kai ba
yadda muke yi mishi gani ba a baya."
Dan mintina talatin dinnan da kuka yi shi
ne ki ka fahimci hakan?"
Ta ce, "A'a ba haka ba ne, amma to sai a ce
boye hali yayi ya biyo ta inda ya bi don neman
aurenki. Ke kin san kenan mutun ne mai
mutuncCi.
Don kuwa da da wata manufa yake nemanki
da ya dade da nunawa. Kada ki wulakanta shi
Idan kuma kin ga hakan bai yi miki ba shi
ke nan. Yana jiranki a falo."
60
Juyawa tayi ta bar ni a tsaye a wurin ta
shige dakinta. Na shiga falon da ta sauke
Mallam.
Ban samu daman daga ido na kalle shi ba,
saboda zuba mun idanu da yayi yana kallona.
Nabi kujerar da ke daf dani na zauna. Tun
kan na gaishe shi ya ce.
"Ina fata shishshige miki da nake yi ba ya
sawa kina kara tsanata?"
Nayi hanzarin dago kaina muka hada ido.
Ya ce, "Abinda na lura da shi kenan, bakya
ra'ayina.
To amma duk da haka ina so ki bani lokaci
da zamu fahimci juna a tsakaninmu. Idan har
na gane hakan ba mai yiwuwa ba ne.
To ina tabbatar miki duk yadda na matsu da
abin zan iya hakura.
Amma a yanzu idan k1 ka ki bani hadin
kanki to ba ki yi mun adalci ba. Bai kamata na
zauna ina gaya miki halin da nake ciki game da
ke ba.
Amma ina so k1 san abin. ya kai makura ne
yasa na kasa hakuri na kai ga yın magana.
61
A yanzu dinnan da nake yi miki maganar
nan shekaru bakwai ne da aurena da matata,
amma tun bayan nan ban sake kallon wata nayi
mata makamanciyar wannan magana da nake
yi miki ba a yau.
Ba ina yi miki maganar ba ne don kiji
tausayina ba, ni ba abin tausayi ba ne don zan
ya shanyewa na hadiye na bar shi a zuci1yata.
Tunda na dade ina shanyewa ba tare da
wani ya fahimci komai a kai ba, to amma ina
so na gamsar da zuciyata.
Na san nayi mata adalci ban hanata abinda
take so ba, sai bayan da na tabbatar yafi
karfina."
Ban cewa Mallam komai ba har yayi shiru.
Ya kalli agogon hannunshi ya ce, "Yanzu
karfe uku ne, 1ina ganin gara na hanzarta don
kada lokacin sallar La'asar ya riske ni a nan.
Zan samu alfarmar sauke ki a gida?
Na ce, "A a ba yanzu zan tafi ba."
Yasa hannu a aljihu ya ajiye kudi masu dan
auki a kan hannun kujerar da nake zaune a kai.
Ya ce, "Kiyi kudin mota don Allah a kula
yin dare ba shi da kyau."
62
Ban sake yi ma Nasiba maganar Mallam ba,
1ta ma bata yi mun ba.
Wata hirar kawai muka yi har ta rako ni na
shiga mota don dawowa gida.
Tsakanina da Mallam Zakariyyya kuwa
kullum yana kirana a da safe sai dare duka
kuma gaisuwa ce kawai sai ko dan maganar
karatu.
Ba a dade ba bayan nan muka koma
makaranta. Da farko dai naji nauyin abubuwa
musamman yadda zan fuskanci Mallam a aji.
Amma shima sai na gane ya basar, don haka
nima sai na shanye. Sai kawai na dauka babu
wanda yasan zance in banda Nasiba.
Bamu fi sati biyu da komawa makaranta ba
sai kawai kwatsam Babana ya saka daurin
aurena da Mallam, abinda yayi matukar dukan
zuciyata.
Na kasa sanin dalilin da yasa har yanzu
zuciyata ta kasa sakewa da lamarin shi,
mutumin da kowa yasan ba shi da wani aibu.
Haka nan ba ni da wani hujja na kin shi.
Wunin ranar ban iya tabuka komai ba.
63
Haka nan washegari ban tashi da niyyar
zuwa makaranta ba. Umma tana ta kallona har
ta gaji ta ce "Ni yau baku da makaranta ne
ko?
Na ce, " Muna da shi, bana dai jin dadi ne
kawai."
Waya yayi mun yana shaida min zuwanshi.
Na zurma hijabina na fita.
Kasancewar darc ne bayan sallar Isha'i a
zaune a motar shi na same shi.
Muna gaisawa ya fara tambayata dalilin da
yasa ban je makaranta ba.
Na ce haka kawai, da alama kuma amsar
bata yi mishi dadi ba. Saboda shirun da yayi na
dan wani lokaci kafin ya ce.
"Nasan anyi miki bayanin komai na game
da saka ranar aurenmu da aka yi, ina kuma fata
babu matsala ko?"
Nan ma shiru nayi ban ce komai ba, don ban
san abinda zan ce ba.
Idan ma da matsala wannan duk daga baya
ne don kuwa ba zai yiwu Babana ya zartar da
hukunci a kaina. Na nuna mishi cewa shi din
bai 1sa ba.
64
Lokacin da aka saka ba mai tsawo ba ne,
don haka ina so ki bani abubuwan da ki ke da
bukata da kuma shirye-shiryenki gaba daya.
ose Tunda ai kin san sati biyu ne ko? Na ce, ""Ni
bani da wasu shirye-shirye duk abinda aka yi
kawai ya wadatar ya ce, "To babu laifi.seo
nsm Kusan duk shirye-shiryen da ake yi na auren
Nasiba ce mai yi wanda ya dangance ni sauran
shirye-shiryen gida kuwa duk su Umma ne
suke yi.
Da alama kuma da gaske suke yi. Har kudin
bayan lefe Nasiba ya baiwa ta narko siyayya ba
na wasa ba.
Ganin irin hidimar kashe kudin da yake yi
yasa na rubuta mishi tevt a gajarce.
"Ina fata ka san nayi aure biyu a baya?"
A take kuma ya turo min da amsa.
"Na sani akwai matsala ne? "
Don haka sai kawai na rabu da shi.b ionids
A makaranta kuwa satin da maganar ta bazu
sai da naji kamar kada na sake zuwa.
65
Kowa maganar yake yi rakwacam babu tsari
wasu ma cewa suke yi dama shi ne ya daure
mun gindin cin jarrabawar da nake yi.
Duk inda na zauna kuma idan mutum yazo
mace ko namiji sai ka ji ya ce amarya
Congratulations muna taya ki murna fa wani
idan ya tsaya a nan wani sai ya kara don neman
bugun cikin yayinda wasu kuwa gaskiyarsu
suke fada taya ni murna suke yi.
Shi kuwa duk yadda yayi da ni na gaisa da
abokanshi naki yarda.
Don kuwa nasan abokan nashi ba za su
wuce Malamanmu ba.
Idan da don tani ne da ko 'yar walima ba ayi
ba, to amma Nasiba ta ki.
Gayyata sosai tayi, yan makarantarmu
kuwa sun amsa gayyata, ga kuma taron dangi
da abokan arziki. Amma komai na dangin
abinci da na sha sai da ya ragu.
Ana daura aure kuwa a washegari aka kai ni
gidan Mallam. Har a wannan lokacin kuwa da
aka watse a ka barni daga ni sai Nasiba,
Zuciyata a kuntace take.
66
"Da kin yi hakuri kin saki ranki ni fa nafi
zaton tsoro ne ya hana ki zuciyarki ta sake.
Kuma gaskiya ne a tsoracen nake don kuwa
ban san bayan auren me zai biyo baya ba, haka
nan shi wannan auren shi ne na karshe ko
kuwa shima matsala zata taso ne a sake sakina?Bayan na fara sakewa na mayar da gidan
gidan zamana? Idan da a yadda naso ne to da
zan dau lokaci ban yi wani auren ba.
Don kuwa babu abinda naki irin a zauna
zaman kirga mun aure.
Nasiba bata tafi ba sai da Mallam ya shigo
bayan an idar da sallar Isha'i.
Da kanshi kuma ya mayar da ita gida bayan
yayi mata godiya.
Duk yadda nayi zaton abin zai zamo sai
naga ba haka ba, don kuwa cikin kankanin
lokaci sai Mallam ya sauya mun tunanina.
Don kuwa sai na gane shi mutum ne mai
wani irin rarrashi da saukin kai.
Da sassafe na tashi na dan yi abubuwan da
zan yi irin su wanka, na kuma kintsa kaina
cikin yadin shadda gizna, doguwar riga mai
laushi.
67
Nasa gyale mahadin ta na rufe jikina. A falo
na zauna ina karewa falon kallo.
Yayi kyau ba kadan ba, ba wai tsadar kayan
ba sai dai kyan tsarin da aka yi mishi ne zai
baiwa mutum sha'awa.
Komai na cikin shi kore ne mai haske.
Kama daga kan labule, kujeru, centre rug har
door mat dan sirkin ba mai yawa ba ne.
Ban dade da zama a wurin ba Mallam ya
shigo. Sanye da jallabiya fara sol a jikinshi.
Kusa dani yazo ya zauna a kan doguwar
kujerar da nake.
Na dan takura kadan saboda yanayin zaman
da muka yi. Ya ce, "Amarya an tashi lafiya?
Na fara gaishe shi yana amsawa ya ce,
"Kiyi hakuri kin tashi ba ki ganni ba na tsaya
ne a masallaci meeting na committee kan wasu
yan abubuwa da ke tasowa a unguwa.
Ina fata babu matsala dai ko? A hankali na
ce "Eh." Ya ce, "To an gode, Allah za ki zo
wurina ne mu karya gaba daya ko?"
Na ce, To. Yana gaba na bishi a baya zuwwa
inda ya kira sashenshi.
68
Tankamemen falo ne kawatacce da kujeru
masu kyau sai tibi na bango babba, sosai na
zauna akan daya daga cikin kujerun, shi kuma
ya shiga wata kofa ya dan dade kafin ya fito.
Fitowarshi babu dadewa wata mace ta shigo
doguwa ba sosai ba, yar siririya wankan
tarwada, don kuwa na fita haske sosai
Sai dai kyakkyawa ce sosai. Sannan 'yar
gaye a kallon da nayi mata da bai fi na dakiku
biyu ba.
"Sannu Hauwa'u an tashi lafiya?"
Ba sai wani ya tsaya yi mun bayanin komai
ba, take na fahimta amma duk da hakan sai
Mallam ya ce.
"Hauwa'u ga Amina nan 'yar uwarki ce."
Ta karasa kusa da shi ta dan zauna a gefe
tana mishi magana da ban san me take fada ba.
Na ji ya ce, "A abana so. Ta waiwayo ta
kalle ni.
"Ina kwana Hauwa'u, an tashi lafiya ko?"
Sannan ta sake fita sai gata da manyan kula
guda biyu take kuma ta fara zuba abinci tana
ajiyewa. Sai da ta gama zubawa sannan ta ce
nazo muci.
69
Muna zaune muna ci kowa dai da nashi, sai
dai na kasa sakewa ko kadan babu abinda nake
So kin na koma dakina su kuwa suna ta dan
hirar su.
Ya kalle ni "Yaya dai Hauwa'u, akwai
matsala ne?"
Na ce, "A'a babu." Amina ta ce, "Kila
kunyata take ji ko don dai nasan wannan
kunyar ba ta daling ba ce. Tunda ba yau aka
fara ganin juna ba."
Ni kuwa wani irin abu nake ji a zuciyata ba
6acin rai ba, haka nan ba haushi ba.
Amina ta gama cin abincinta ta mike ta fita
ta bar ni rike da plate a hannu.
"Kokarta kici abincin nan ko babu yawa.
Abinda ya fara fada mun kenan, bayan fitarta.
"Ko kuma kin fi so na ba ki da hannuna'?
Na dago ido zan kalle shi, na kasa saboda
kallon da yake yi mun. ban iya ci ba don haka
na hakura na ajiye.
Ya mike ya isa gaban fridge din dakin ya
dauko robar fresh milk da dogon kofi yazo
kusa da ni a kasa ya zauna ya tsiyaya ya dauka
ya nufi bakina zai ba ni da kanshi.
70
Na girgiza kai na karba da hannuna bai hana
ni ba sai kawai ya sake mun ya ce, "To amma
fa ki shanye duka kafin na dawo daga dauko
yara daga Islamiyya.
Kin san yau Lahadi da safe ake zuwa." Na
ce, To. Ina so na koma dakina. Ya ce, "A'a ki
zauna a nan idan kuma barci ki ke ji ga daki
nan ki shiga.
Bai fi mintina talatin ba da fita sai gashi ya
shigo, yara guda uku suna binshi a baya mza
biyu da karamarsu mace.
Dukkansu suna ba shi labarin abubuwa yazo
ya zauna ya ce, "To ba ku gaisa da Mamanku
ba?"
Gaba dayansu suka fara gaishe ni a tare
cikin fara'ata nima na amsa. Karamar ta ce,
"Baba ita ce sabuwar Mama ko?"
Ya ce, "Itama Ummulkhairi ashe kin gane ta
kenan? ta kada kanta alamar eh, ya ce "To
kuje ku huta ku cire kayan makaranta ku ci
abinci."
Suka ce, "A'a Baba mu a nan zamu ci. Ya
bude musu ido ya ce, "Kai ku tafi ku bani wuri
na ce."
71
Karamar tasa kuka, ta juya tabi yan uwanta
suka fita
Ina ganin ya kamata ki kwanta ko ban ce
mishi komai ba don kuwa ba zan iya musu da
shi ba.
Kwanana biyar a gidan Nasiba ta dawo. Na
harareta lokacin da naga shigowarta, na ce
Don wulakanci yau ne ki ka ga daman zuwa?
Ta ce, "A to ban yi kokari ba kenan, ai da
cewa nayi sai kin yi sati biyu."
Na ce, "To ai sai ki koma. Ta isa gaban
fridge din dakin ta ciro lemon kwali ta zauna
tana surkawa da ruwan sanyi saboda bata son
zaki sosai.
Amina tayi sallama. Gaba daya muka amsa
sallamar, ta nemi wuri ta zauna suka fara
gaisawa da Nasiba.
Sannan aka shiga hira gaba daya. Ta kai
mintina goma sannan ta tashi ta fita.
Nasiba ta ce da alama dai matar nan za ayi
zaman kalau da ita? Na dan yi murmushi muka
shiga wata hirar tana tambaya ta ranar da zan
koma makaranta.
72
Na ce, "Na jira ne naji ya ce mun mu tafi to
har yanzu bai ce ba."
Nasiba ta ce, "Kenan za ki jira ne sai ya ce
ki tafi, ina ce kwanaki uku yayi a dakin nan ya
fita?
Na ce, Eh mana, to da nawa ki ke so yayi?
Ta ce, "A'a ba wannan ba ne ma, ki dai sani
ne cewa ya kamata idan ku ka zauna kiyi mishi
maganar komawarki makaranta.
Kasancewar yau kwanakina biyar ne a gidan
to kuma a dakina Mallam yake.
Don haka kokarina shi ne na ganin nayi
mishi maganar Makaranta na tunda na kusa
kwanaki goma ban je ba.
Don tun kafin daurin aurenmu na daina
zuwa. Muna zaune a falo dukkanmu hira ake yi
tunda a can muke cin abincin dare gaba
dayanmu.
Sai dai ni kam duk hirar da suke yi ban iya
tsoma musu baki, idan ba saka ni a ciki aka yi
ba.
Hankalina a zahiri yana kan shirin da ake yi
ne a TV sai dai a badini ba haka ba ne.
73
Ban saba ganin mace tana yiwa namiji
abubuwa haka a gabana ba. Na