Showing 27001 words to 30000 words out of 33002 words

Chapter 10 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

ya kasa. Albarkacin Baba Dacta duka likitocin dake kula da shi basu dauke shi da wasa ba, kula suke
da shi sosai ba dare ba rana. Khalipha shi ya kwana da shi.
Washe gari da safe Dacta ya zo da Mami don ita kwanan asibitin ta yi, suka duba jikin nasa
yana samun sauki ba laifi ba kamar jiya ba.
Har ya yiwa Khalipha murmushi, Khalipha ya matsa gare shi shima ya yi murmushin.
Ya ce, “Sannu Baba, Allah zai baka lafiya ka ji?”
Ga mamakinsa sai ya ga ya yi masa alamar ya daga kai. Khalipha ya ce, “Zan je in yi wanka
in dawo Baba”.

Sai ya rike hannunsa da hannunsa mai lafiyar ya ki saki, yana ta kakarin magana. Da
Khalipha ya nutsu ya fahimci cewa yake “Ka zo da RAHANE”.
Ya ce, “To Baba Rayhanah za ta zo”.
Da yake Asabar ce duk suna gida, Khalipha ya dube su daya bayan daya, Jawahir ce kewa
Azizah kitso, Rahane na shafa mata lallen Rani a kan yatsunta. Abida dama ba ta dawo ba.
Basu ankara da shigowar shi ba saboda karar t.v don haka shima ya wuce dakinsa a hankali,
babu wacce ta ankara da shigowarsa.
Sai da ya yi wanka ya shirya ya fito dining nan suka san ma yana cikin gidan. Kowacce
gaishe shi take don tunda suka dan kara tasawa suka daina damukarsa sai dai gaisuwa ta
ladabi.
Ya dubi Rayhanah kadan ya ce, “Ki shirya asibiti zamu yanzu Rayhanah”.
A hankali ta juyo ta dube shi tana son ta tambaye shi waye ba lafiya? Amma ta kasa
sakamakon kwayar idanunshi dake sanya mata wani al’amari da ke taba zuciyarta da ilahirin
gangar jikinta.
Tsam ta mike ta dauko hijabi irin dogon nan mai hannuwa ta saka ba tare da ta tsaya ko duba
madubi ba, da takalmi flat. Ta bi bayan Yaya Khalipha wanda har ya tada mota.
Karo na farko a rayuwarta da ta shiga motar Khalipha. Wani ni’imtaccen sanyin A.C wanda ya
cakude da kamshin (car fresh) din citrus da turaren da Khalipha ya yi amfani Azzaro Chrome
(Legend) shi ya soma bakuntarta a sanda ta shiga gefen Khalipha ta zauna.
Ya dan juya kadan ya dube ta suka hada ido, inda ya gano alamomin tambaya fal cikin
idanunta amma ta kasa furtawa. Ya fi minti uku bai yi magana ba kuma bai ja motar ba.
Rahane ta gaza hakuri ta ce, “Don Allah Yaya Khalifa waye ba lafiya?”
Ya kunna motar a hankali ya fara yin reverse, sannan ya ce da ita, “Ki yi hakuri Rayhanah,
Baba Rashidu ne ba lafiya amma mun taho da shi nan asibiti har ya fara samun sauki”.
Kwalla fal idonta ta ce, “Tun yaushe ne?”
Khalipha ya ce, “Tun jiya, ai sammakon da muka yi ni da Daddy Takai muka tafi”.
Ta jinjina kai sai ga hawaye ya balle a ka kundukukinta. Ta yi saurin juyawa tana kallon titi
kada Yaya Khalipha ya gani.
Yana gaba tana binshi a baya har dakin aminity na male-ward din inda Malam Rashidu ke
kwance.
Da sauri Rahane ta karasa gaban Baban ta kama hannunsa, wannan lokacin kuka ne sosai
ya kwace mata da ta fahimci halin da Babanta ke ciki.
Khalipha (cikin bugun zuciya) da hawayen da Raiha ke fitarwa ya ce,
“To kuwa zan maida ke gida Rayha, ciwo ba mutuwa bane, ke da za ki ba shi karfin gwiwa da
kalamai masu dadi sai ki yi masa kuka?”
Ta soma share hawayen da gefen hijabinta. Dai-dai lokacin da Khalipha ya matso kusa da
Baban, don ganin kamar ya bude ido.
Ya ce, “Baba ga Rayhanah ta zo, Baba Allah ya baka lafiya”.
Sai ya mika mata hannunshi mai lafiyar ta kama, jikinta har rawa yake yi. Kamar wanda ya
warke a take ya bude ido garau yana kallon diyar tasa, tausayinta yake ji sosai, don ya san ba
ta da kowa a duniya da za ta bugi kirji ta ce nata ne sai shi sai Ubangijin da ya halicceta.
Yana ji a jikinsa wannan rashin lafiyar tasa ba ta tashi ba ce. Bayin Allah na gari (Saliheen)
Allah kan nuna musu karshen rayuwarsu. Duk da haka ya daure ya tattara kuzarin da Allah ya

ba shi a lokacin muryarshi da sanyi kwarai ya ce,

“Rahanen-Iya diyar Yalwati-na!!!”.

Sai ta yi murmushi idonta fal da hawaye. Ya ci gaba da cewa,
“Idan Allah yasa na tashi abin da zan fara yi miki Rahane shine AURE. Bana son in kwanta
dama ban ganki a dakin mijinki ba.
Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafina, wato Likita
Mansur. Na yarda shi mai kaunarki ne saboda Allah ba don wani bayyananne ko boyayyen dalili
ba.
Don haka Rahane na horeki da yi masa biyayya kwatankwacin yadda kike mini. In ya saki ki
yi, in ya hanaki ki hanu. Rayuwar dan Adam Rahane gajeriya ce, don da ta shigo saba’in shi
kenan ta kare komin jin dadi kuwa, kada ki shagala da dadin duniya ki manta da Allah.
Duk rintsi ki yarda cewa mutum bai isa ya tsarawa kansa rayuwa yadda yake so ba sai yadda
Ubangijinsa ya ga dama. Rahane ban bar miki gadon komai ba sai na tarbiyyar da na yi miki,
wadda na tabbata za ta yi miki jagora har karshen rayuwarki.
Kada dadin duniya yasa ki shagala ki manta ko ke wace ce; talaka, diyar talaka, jikar
talakawa. Talakawan ma na kauye. Don haka ki taimaki talaka a duk inda kika samu dama
kema Allah zai taimaka miki kamar yadda likita Mansur ya taimakeki.
Ki zabi miji dai-dai ke, abin da nake nufi a nan shine, ki auri talaka dan’uwanki wanda zai
daraja ki ya mutunta tushenki, in har zai ci dake ya shayar, ya tufatar, kada ki kai kanki inda
Allah bai kai ki ba.........”
Kuka take sosai tare da katse shi da cewa, “Baba don Allah ka daina wadannan
maganganun, masu kamadawasiyya, ni ba wani aure yanzu a gabana neman ilimi zan yi, shine
sutturar mara galihu. Kuma Baba ni wa zai min auren idan babu kai? Baba me yasa kake yanke
kauna da rayuwa a dalilin zafin ciwo? Ya Allah kada ka nuna min wannan ranar, wato ranar da
zan wayi gari babu kai.....”
Ta ci gaba da wani irin kuka, ta kifa kanta jikin karfen gadon da Baban ke kwance.
Rahane dai ba ta sani ba, ba ta san abin da Khalipha ya ankara da shi ba. Ji ta yi an dafa
kafadarta da wasu yatsu masu bala’in taushi. Ba sai ta juyo ba ta san Khalipha ne tunda su uku
ne kawai a cikin dakin, ba ta kuma ji wani ya murda kofa ya shigo ba.
Ta dago a hankali ta dubi Khalipha idanunta kamar an gumbuda musu barkono. Shima
nashin sun canja launi, ya kasa jarumtakar da zai rarrasheta bai san lokacin da hannayenshi
suka yi motsi ba suka sarrafa kansu suka kai ga rungume Raihanah.
Sannan ya rufewa Malam Rashidu ido, ya ja zanin gado ya rufe shi har kansa. Dai-dai lokacin
da Mami da Baba Dacta da wasu daga cikin Phyisothearapists na ward din suka shigo.
Idanun Mami a kan Khalipha dake rungume kam-kam da Rayhanah, ya kasa sakinta don kar
ta fahimci abinda ya faru, ya rasa inda zai sa kansa, rikon da yayi mata mai karfi ne don kar ta
juya, gaban Mami ya yi wani irin mugun faduwa ta tsaya turus! A bakin kofa.
Da gudu su Baba Dacta suka karasa suka bude rufar da Khalipha ya yi masa, gaba daya
suka ce, “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”.
Baba Dacta ya juya yana share idonsa da hankici. Da karfin gaske Rayhanah ta zame daga
jikin Khalipha ta juyo da gudu ga Babanta, ta bude rufar ta ga abin da kowa ya gani.

Dora haannu ta yi a kan kirjinsa wai ta ji bugun zuciyarsa, ba ta san alamun mutuwa ba,
amma ta tabbatar Babanta ya mutu. Tunda ga shi ta ji ba ya numfashi. Zuciyar shi bata bugawa
ko alama.
Bayan wannan ba ta kara sanin me ke faruwa a duniyar ba, bayan gilmawar wasu taurari a
idanunta. Da gudu Khalipha ya yi kanta shi da Baba Dacta, suka hanata kaiwa kasa, yayin da
su Mami ke rufe Mal. Rashidun, likitocinsa na ta rubuce-rubuce cikin file din sa.

****
A gidan Hakimi aka yi jana’izar Mal. Rashidu. Ya kuwa samu jama’a na ban mamaki, kwana
uku ana karbar gaisuwa, har zuwa lokacin Rahane na gadon asibiti jininta ya hau sosai, ta ki ci
ta ki sha, sai ruwa ake ta kara mata leda-leda.
Ba kuka take yi ba, don ta nemi hawayen a idanunta ta rasa. Kwance kawai take ba ta umh
ba ta uhm-uhm sai kallon gilmawar mutane da shige da ficen likitoci.
Wato shi kansa kukan (wuri shi ka samu), wani tashin hankalin ya fi karfin ka yi masa kuka.
Kuka rahama ne a lokacin da zuciya ke ciwo, ciwo irin wanda babu irinsa a rayuwa. Rahane
ta kasa kuka sai addu’a take cikin zuciyarta ita ma Allah ya dau ranta ta bi iyayenta da Iya ta
huta.
Yanzu kam ta tabbata ta zama marainiyar gaba da baya. Da dai-dai da dai-dai Allah ya yi
ikonsa a kan wadanda ya bata su zame mata garkuwa a rayuwa, kuma bango abin jingina.
Shi kenan kuma ita yanzu ba ta da kowa! Idan Baba Dacta da iyalinshi suka gaji da rikonta
ina za ta je?
...........“Sai dai kuma da na yi wani tunani sai na ga cewa kina da Uba makwafi na, wato
Likita Mansur.....”
Ta tuno kalaman Mal. Rashidu masu kama da wasiyya. Ashe hirar karshe ce Baba, kaicona
da na katseka!!!
A wannan lokacin ne ta samu hawaye suka zubo, ba tare da ta san suna kwarara ba sai ta ji
an sa tissue ana share mata.
Ta juyo kadan sai ta ga Jawahir, ita ma kukan take tayata. Ta ce, “Rayha ki yi hakuri, Baba
kwananshi ne ya kare, kin sani ko muma zamu iya mutuwa a kowanne lokaci. Addu’a za ki yi
mishi. Rayuwa yanzu kika fara ta Rayhanah, ko ba iyaye za ka rayu idan haka Allah ya tsara
maka. Belle ke kin rayu da Baba, ya yi miki tarbiyya, ya baki ilimi dai-dai karfinsa. Sannan bai barki a
hannun da za ki wulakanta ba.
Rayha ki daure ki tashi mu ci gaba da fafutukar rayuwa, darussa za su wuce ki, alhalin Allah
bai nufa rayuwarki ta zo karshe ba.
Ina miki ta’aziyyah Raihanah, Allah ya ji kan Baba, ya ji kansa ya yi masa rahama, yasa
Aljannah ce makomarsa, ya sanya mana dangana”.

Kwanaki bakwai da suka biyo baya, aka yi sadakar bakwan Mal. Rashidu. A cikin wadannan
kwanakin, kwana biyu kacal ta yi a gida, ragowar a gadon asibiti.
Tuni Khalipha ya koma bakin aikinshi cike da alhinin RAYUWAR RAYHANAH!. Ga nakasa ga
hawan jini, sannan ga maraiaci na uwa da uba da rashin dangi. Tausayi ba zai barshi ya ci gaba
da ganin Rayha cikin wannan halin ba.

Ta rame kwarai, ita dama shiru-shiru jiki ba jiki ba, yanzu abin ya koma daga eh, sai a’a. Sai
da Baba Dacta yasa aka soma rubuce mata Alkur’ani tana sha tsayin sati biyu.
Hatta Abida ta rage rashin mutuncin ta don ganin Rayhan, a yanzu kam wani dan Adam bai
da abin da zai bata mata rai da shi, ko yankata za ta yi ba za ta daga ido ta kalleta ba balle ta
san tana yi. Tunda ta jure rabuwa da Iya da Baba, to mene ne ma ba za ta iya jure shi a
rayuwar duniya ba? Duniya ta fita a kanta sai fatan cikawa da imani. Sati biyu bayan nan suka koma makaranta suka soma shirin zana jarrabawar shiga aji shida.
Rahane kam ba fus, sakamako bai yi kyau ba. Sun ba ta maimaicin shekara guda (repeating),
yayin da su Abida suka shige aji shida suka barta a aji biyar.
Amma maimakon Baba Dacta ya yi fada kamar yadda suka zata, sai ya ce “Rayhanatu a
hakan ma kin yi kokari, Allah ya yi miki mai kyau a duniya, mai kyau a lahira a dalilin juriyar ki
kan kaddarorin ki da kyawawan halayenki”.
Sati biyu Khalipha bai zo gida ba, ba don komi ba sai don baya son abin da ke zuciyarshi a
kan Rayhanah ya fito sarari. Ya zo wani limit da ba zai iya boye soyayyarta ba zuciyar ba za ta
iya basarwa ba.
In kuma har ya yi kokari ya boye din, to za ka iya karantar hakan cikin kwayar idanunsa cewa
yana so.........kuma yana tausayin Rayhanah.
Haka nan ya samu kansa da wani sabon tunani, wato ya kai Rahane waje, masu jajayen
kunnuwa su duba lalurarta. Babu cutar da ba ta da magani. Likitocinmu ba finsu kwarewa aka yi
ba, kayan aiki ne bamu dasu kamar sauran kasashen da suka ci gaba.
Daga fara aikin shi zuwa yanzu yasan yanada account mai nauyi don bashi da
almubazzaranci kuma babu nauyin kowa a kansa. In ma ya kakare ya tabbata Baba Dacta zai
agaza masa in ya gaya masa kudurin sa.
To amma Rayhah ta balaga, shekarunta goma sha shida ya za ayi Baba Dacta ya yarda su
tafi wata uwa duniya tare? Duk da neman magani ne?
Wata zuciyar ta ce, “To ka fito fili mana ka sanar da Daddy kana sonta ya aura maka ka tallafi
rayuwarta da taka? In ta zama matarka shikenan babu sauran shinge. To amma anya ba ta yi
kankanta ba? Ya tabbata ko Daddy giyar wake ya sha ba zai aurar da Rayha a wadannan
kananun shekarun ba. Don haka furtawar ma bata da amfani. Da ya kwashi wata daya bai zo gida ba, kewarshi ta damu al’ummar gidan, kada Azizh ta ji
labari. Duk sanda Mami ta kira wayarshi sai ta jita a kashe, haka in ta yi amfani da social
network baya responding.
Zuciyar UWA! Ba irin tunanin da ba ta yi ba. A yau dai ta kasa daurewa ta samu Daddy da
zancen.
Ya ce, “Lafiya ita ke buya Asma’u, amma ba rashinta ba”.
Duk da haka ta kasa sukuni, a ranar Alhamis Daddy ya daga kasar Ireland domin halartar
taron “Old Students Alumni of Trinity University”. Kwananshi daya da tafiya ta dauki hanyar
Abuja ita kadai a motarta, tana tafe tana zancen zuci.

Khalipha na kwance cikin leather seat din falonsa bakake, a gabansa ash-tray ne na silver
wanda ke cike taf da guntattakin Marlboro, a wannan lokacin ma abin da yake ta yi kenan, wato
gajimare da hayaki.
Ya yi baki ya bar kasumba ta cika masa fuska, wannan kwantaccen gashin nasa duk ya

kanannade saboda rashin gyara. Falon kaca-kaca ga kuma kura da kayan wuta suka yi, don ya
hana yaronsa Jibril shigo masa daki balle ya gyara masa sai idan shi ya kira shi a waya ya sayo
masa abinci.
Kararrawar shigowa falon ta yi kara, ta yi ta sake yi yana kwance bai motsa ba. A zatonsa
Jibril ne alhalin ya san ya hana shi zuwa inda yake in ba shi ya kira shi ba. Farar singilet ce a
jikinshi da dogon bakin wandon DKNY.
A fusace ya mike ya bude don ya yi masa marin da uwarsa bata taba yi masa ba. Amma sai
ya yi tozali da tashi uwar wacce ko cikin mafarkinsa bai zaci ganinta a nan ba.
Kallon shi kawai Mami ke yi, bayan mintuna uku ta bi gefenshi ta shige falon ba tare da ya
bata damar hakan ba.
Sai ta fara kiran ‘Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un....... smoking ABDALLAH???”
Sai ta zube cikin kujera ta saka mishi kuka.
Jikinsa ya yi bala’in yin sanyi, ya zube a gabanta ya kwantar da kai a cinyoyinta cikin
matsanancin tashin hankali; mahaifiyarsa na zub da hawaye a dalilinsa.
Ta kara dago ido ta dube shi, “Ashe addicted ka zama? Shi yasa baka nemanmu? Abdallah
tun yaushe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login