Showing 9001 words to 12000 words out of 33002 words

Chapter 4 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

amma idan na yi mata aure hankalina zai fi kwanciya, kuma na riga na karbi
sadakinta.

Ado dai da kuka sa aka kama ku sako shi, don na riga na ci sadakinsa, tun kan a haifi
Rahane yake hidima dani, bani da abin da zan biya shi ban da in aura masa Rahane. Ku yi
hakuri don Allah, na riga na ba shi aure”.
Rahane ta fashe da kuka, “Baba Dacta ku ceceni bana son sa...wallahi bana son sa…!!!”.
Ta gurfana gaban Dr. Mansur tana rera kuka mai ban tausayi, ta buya a bayansa ta kankame
shi. “Baba Dacta kashe ni zai yi....kana gani fa ya yaga min riga a gaban Babana… amma shine
zai aura min shi?”
Ran Dacta Mansur ya yi mugun baci, lallai ya yarda komai akai da matsiyaci sai ya ci kara.
Wannan Mal. Rashidun a jahilan ma bai san a ajin da yake ba. Kai baka ce shi da bakinsa yake
fadar rashin arzikin da Ado ya yi masa ba, wai ya boye Rahane har ya yi attempting keta mata
mutunci a gabansa, wannan shine mijin da zai bawa aure. Ya ce, “Kai Malam! Ina jin dai ba lafiyarka kalau ba. Aure da wannan mutumin, mun hana, ya
lissafa duk abin da ya kashe maka a biya shi, bayan ya gama zaman gidan kaso na keta haddin
da yaso yi. Ba zan iya cin fuskarka ba albarkacin Rayhanah”.
Ya dau waya ya ce, “Ibraheemu jeka ofishin ‘yan sandan nan ka ce su zo min da wannan
mutumin da nasa aka kama yanzu-yanzun nan”.

I.M Takai tsaye ya yi rike da wayar hannunshi “What’s wrong with Daddy ne?” Ya dubi wayar
hannunshi sosai cike da takaici, sannan ya dubi Nabilah diyar Hakimi da suke tsaye tare, “Mts!
Daddy ya samu matsala Nabilah!”
Ta ce, “Matsalar me?”
Ya sake hura hanci ya ce, “Jirani ina zuwa”. Ya juya ya fita.
Cikin dan lokaci an kawo Ado fada. Malam Rashidu ya dube shi jikinsa yana ta rawa ya ce,
“Yauwa don Allah ku sa a sake shi”.
Haushi ya kama Hakimi ya ce, “Kai Malam ka nutsu ka san a inda kake bama son shirmen
banza”.
Malam Rashidu ya koma cikin nutsuwarsa. Dacta Mansur ya dubi Ado sosai ya ce, “Da gaske
kana son auren diyar Malam Rashidu?”
Ado wanda ya ci kaniyarsa sosai a hannun ‘yan sanda ya ce, “Eh”.
Dacta ya ce, “Shine kuma za ka yi mata fyade a gaban ubanta?”
Ya ce, “Ba nufina kenan ba”.
Dacta ya ce, “To meye nufin ka na tsaraita ta?”
Ya yi shiru. Dacta ya ci gaba da kallonsa a ransa yana mamakin Malam Rashidu, wai wannan
mutumin mai kama da ‘yan fashi zai aurawa innocent yarinya kamar Rayhanah.
Ya boye mamakinsa ya ce, “Sulhu nake nema da kai”.
Ado ya dago a fusace, sai kuma suka yi mishi kwarjini ya kasa cewa komai. Dacta ya ci gaba
da cewa, “Ka lissafa duk abin da ka kashewa Mal. Rashidu da ‘yarsa zan fanshe su ba ta isa
aure ba!”
Ado ya gallawa Mal. Rashidu harara wanda ya takure ya yi lakwam yana kallon Ado a
tsorace. Ado ya bude wawulon bakinsa ya ce cikin zafin rai, “Hakorana da aka zubar min fa?”
“Zamu makala maka na roba yanzu”.
Ya ce, “To a rabani da ‘yan sandan nan”.
Hakimi ya ce, “An raba ku”.

Ado ya ce, “Naira dubu dari biyar zaku bani, kuma su tashi su bar min gidana”.
Hakimi ya yi murmushi, ya jawo wata bakar akwati ya bude, ya dauko daurin kudi ‘yan
dubu-dunu dauri biyar ya zube su a gaban Ado.
“Gasu, gidanka kuwa ko komawa ba zasu yi ba. Duk tarkacen dake ciki ma sun bar maka.
‘Yan zaman makokin ma in kaso ka koresu ka koresu su zo nan su yi”.
Ado ya gigice don dai kawai ya shaci kudin ne da gayya bai taba zaton ba za suyi musu ba.
Ya kwashi kudi ya nade cikin rigarsa ya mike zai fita, cike da tsoron kada su kwace kafin ya
kai kofa. Dariya ta kama Dacta Mansur ya ce, “Hakoran fa Ado?’
Ya ce, “Barsu kawai, zan je kudu a sa min”.
Gaba daya suka sa dariya har Mal. Rashidu dake takure a gefe sai da ya murmusa.
Karshen diramar Ado da Rahane kenan. Tunda ya hada kudin nan ya gudu ya bar Takai, ya
bar ‘ya’yansa da matarsa ba a kara jin duriyarsa ba. Aka bawa Mal. Rashidu muhalli a cikin
gidajen bayin Hakimi, washegari ya fara aikinsa na kula da Dawakin Hakimi.
Dr. Mansur da dansa I.M suka taho Kano da Rahane, bayan ta yi sallama da babanta.


RAHANE A GIDAN DR. MANSOOR
Gidan Dr. Mansur Balarabe Takai babban gida ne mai tsarin gaske a unguwar Lamido
Crescent, wanda ke rufe cikin bakin girgijejen get. Asalinsa Turawa ne suka zauna cikinsa
shekaru masu yawa da suka gabata lokacin mulkin soja sanda suka bude kamfanin PZ da za su
koma kasarsu suka sayarwa gwamnati. Lokacin da Dr. Mansur ya yi kwamishinan lafiya a Kano, lokacin Gwamna Kabiru Gaya,
gwamnati ta bashi gidan ya zauna, da tenure din su ya kare ya yi kokarin da ya sayi gidan da
taimakon mahaifinshi mai girma Hakimin Takai na III (Balarabe Sardauna).
Haka ya ci gaba da sabunta gidan, yadda zai yi dai-dai da zamanin da ake ciki har kawo yau.
Gidan farin fenti ne da shi, kana shigowa cikin get din gidan mikakkiyar kwalta ce wadda zata
sadaka da rumfar adana motoci a kalla biyar, ba tare da kowacce ta gogi ‘yar’uwarta ba.
Idan ka yo gaba kadan grass carpet ne wanda zai kai ka bakin kofar reception din gidan. A
cikin reception din matattakalar bene take wadda za ta sadaka da falon sama da yake kunshe
da dakunan barcin jama’ar gidan.
Dakunan barci hudu ne a cikin falon, daya na Dr. Mansoor, daya na Mami, daya na I.M da
Yayansa Khalipha, wanda a halin yanzu yake karatu a jami’ar BAZE dake Abuja, yana karantar
hulda da kasashen ketare wato (International Relation). Daya dakin na Abida da Jawahir ne, sai
autar su Azizah. Abida shekarunta takwas, Jawahid goma, Mami ta dade bayan haihuwar Abida kafin ta haifi
Aziza wadda ke da shekaru uku a halin yanzu.
Saboda tsantsenin tarbiyya irin na Dr. Mansur bai warewa I.M da Khalipha daki a wajen
gidansa ba, duk da girmansu tare yake dasu yana ganin kowanne motsinsu. Idan abokai ne ga
reception nan bai yarda ko baskwata su zauna ba, masu aikace-aikacen gidan ne a baskwatan.

Motar Dr. Mansur ta sako kai farfajiyar gidansa. Ibraheem ne ke tukin. Dacta na gaban motar
rike da jaridar This Day da ya saya a go slow din roundabout na kofar Nassarawa. Rahane na
baya a makure jikin kofar motar kamar ka ce kyat! Ta bude murfin motar ta arta a na kare.

Abida da Jawahid ne zaune a rumfar adana motoci tare da malamin Islamiyyarsu dake zuwa
duk Alhamis da Juma’a yana koya musu karatun Alkur’ani da Hadisi, tajweed da Tawheeed, ga
bakin allo (black board) an kafa musu cikin rumfar adana motocin. Ta bala’in raina malamin, don
Abida ‘yar rainin wayau ce, sabanin Jawahir da ko magana ba sosai take yinta ba. Jin shigowar motar Daddy Abida ta nutsu daga mintsinin Jawahir da take yi, shi kansa Malam
Umar ya lura Abida ta shiga taitayinta, don haka ya juyo don ganin abin da ya nutsar da ita.
Daddy ne da Ibraheem ke fitowa daga mota, tare da wata dukun-dukun din yarinya baka
wuluk! Kanta a daure cikin wani bakin tsumma da wani sidadden silifa a kafarta, ko’ina a jikinta
ciwo ne, wani da plasta wani plastar ta daye.
Abida ta soma zungurin Jawahir don ita ma ta juya ta ga abin da ta gani, amma Jawahir ta yi
banza da ita ta ki juyawa ta ba da hankalinta sosai ga Malam Umar.
Malam din ya aje Alkur’anin dake hannunsa ya isa ga Daddy ya tsugunna yana gaisuwa.
Daddy ya amsa ta hanyar bashi hannu sukayi musabiha. Tuni Ibraheem ya shige gida. Daddy
ya kama hannun Rahane suka doshi reception.
Rahane dai taku take a tsorace, don ita tunda Allah ya halicce ta bata taba ganin waje irin
wannan ba, kamar Aljanna da ake kwatantawa.

“Mami! Mami!!”
Daddy ke kira a falon sama.
Ta fito daga laundary inda take shanyar kayan Azizah data wanke cikin injin wanki, sanye
take da riga da siket na wani bakin material mai yarfin light green flowers, gashin kanta kame da
hair-bound, shima light green ya sauko har kafadunta. Duk wani likita kirki ne da shi, to haka Dr.
Asma’u Takai, musamman kasancewarta likitar yara. Amma a yau kam ga dukkan alamu za suyi fada da Dactan nata, don kirkin nata bai kai nan
ba.
Za ka rantse ba ta haifi Da kamar I.M ba, balle kuma Yayansa Khalipha. Ta fi kama da
matashiya ‘yar shekaru talatin ba talatin da tara ba.
Ta fito falon tana fadin “Dacta na!” Shima ya ce, “Mamina!!”.
Ya juya ga Rahane, “Rayhanah matsa ki gai da Mamanku”.
Sai a lokacin ta kai idonta ga Rahanen da ta zube a gabanta tana fadin “Barka da yamma
Hajiya”. A firgice ta juya ga Ibraheem, sannan Daddyn ta kasa tambayar komai.
Dariya ce ta kama Ibraheem ganin idanun Mami sunyi mitsi-mitsi, ya lallaba ya shige dakinsa
kada dariyar da yake yi ta fito.
Daddy ya yi murmushi ya isa ga Rahane yasa hannu ya cira ta daga zubewar da ta yi kamar
bawa a gaban Ubangijinsa. Ya zaunar da ita a kujera yana ce da Mami
“Karin ‘ya na kawo miki, sauran bayani sai anjima, yanzu ba ta abinci da ruwa tukunna mun
sha tafiya”.
Ta dan saki fuska ta koma kicin ta zubo abinci a plate da robar ruwan Eva mai sanyi da
lemun La-casera ta kawo mata kan tebir. Amma da ta kira yarinyar ta ce ta zauna a kujera ta ci,
sai ta ga ta sauke plate din kan marbles ta bararraje abinta tana ci kamar Allah ya aikota
saboda yunwa. Ta bi bayan mijinta cike da mamaki. Ta same shi yana cire safar kafarshi a gefen gado, ta
zauna a kasan kafafun nashi ta karbe shi. Sai da ya yi wanka ya kwanta yana hutawa, Mami ta

matsa jikinsa tana cewa,
“Ina ka samo yarinya bakauya haka?”
Ya ce, “Garinmu Takai”. Ta ce, “Yar waye?”
Ya ce, “Yar AMANA!”

Ya tashi daga kishingidar da ya yi ya kama hannayenta masu taushi ya ce, “Mami batun yau
ba ni da ke muke da bambancin ra’ayi a kan al’amura da dama, amma kowa ya kasa rinjayar
dan’uwanshi ya bi nashi ra’ayin.
Amma a yau ina neman alfarma Mami, wadda na san mai girma ce a gare ki, ita ce ki rike
min Rayhanah kwatankwacin rikon da kike yiwa ‘ya’yan da kika haifa.
Ko da komai bai zamo hundred parcently equal ba, ki kwatanta kara da karamci. Rayhanah
da ubanta ba shegiya ba ce. Sai dai marainiya ce ba ta da uwa, ta rasu tun lokacin haihuwarta.
Ta girma a hannun kakarta, ita ma yanzu babu.
Na tserar da ita ne daga kaskantacciyar rayuwa da ubanta ke so ta yi, wato early and
abusing marriage, sakamakon wasu extraordinary characteristics dana gani a tare da ita.
Ban taba haduwa da pateint din da ya shiga raina irin ta ba. Sannan ta gamu da ‘lalura’
wadda dole a tausaya mata, a bata kwarin gwiwar da zata fuskanci rayuwa a, duk yadda ta zo
mata.
Ta samu hearing impairment wanda bazamu ce a sakamakon hadarin da suka yi bane, har
yanzu source din, bai bayyana garemu ba, har sai anyi CT Scan and MRI Scan, wadanda bamu
da injinan yin su anan Nigeria, in kin lura akwai hearing-aid a kunnenta. Mami ban taba neman
alfarma kin kasa yi min ba, a yau wadda nake nema ma ba za ta gagareki ba, tunda kin saba
haihuwa kin san ciwon DA. Yadda naki yake a ranki haka na kowa yake a zuciyar nashi iyayen.
Ki yi min alfarma cikin dimbin alfarmominki gareni, ki rike min RAYHANAH da zuciya daya, ni
kuma duk abin da kike so zan miki Mami. Wallahi-wallahi ko da bani da shi zan nemo. Kawai ina
so Rayhanah ta yi rayuwa mai kyau kamar ‘ya’yanki. Ta yi ilimi, ba tare da nakasunta ya
nakasta rayuwarta ba. Zan samu Mami?” Ta sauke idonta a hankali kan mijin nata, ta rasa shi wane irin mutum ne, mai maida
damuwar wani tasa. Ba ta da muguwar zuciya ko kankani, sai dai ba ta son kowa ya rabi
rayuwarta da mijinta da ‘ya’yanta.
Ba ma wannan ne abin tsoron ba, za ta hada ‘ya’yanta ne da yarinyar da ko asalinta ba ta
sani ba? Kai rigimar Daddy da yawa take.
Ta ce, “Daddy zan yi maka alfarmar da kake so, amma a bisa sharadi biyu”.
Kallonta ya yi, kallon ke nake sauraro. Ta ce, “Ka yi min alkawarin WATARANA ba zaka ce za
ka hada aure tsakanin ‘ya’yana da wannan yarinyar ba. Sharadi na biyu shine, zan raba musu
daki da su Abida, don hankalina ba zai kwanta ba idan tana tare dasu”.
Dariya ta bai wa Daddy sosai. Ya ce, “Mamee!”
Ta ce, “Dacta naa!!”
“ki kwantar da hankalinki da Rayhanah, ba zan kawo abin da zai cuci su Abida ba. Am their
Dad, remember? Baki fini son su ba!!!.
Maganar aure da ‘ya’yanki kuwa kisa ranki a inuwa sassanya, Allah zai baiwa Rayhanah miji
na ban mamaki wanda zai kaunaceta domin Allah ya rungumeta da lalurar ta, ba ‘ya’yanki ba,
masu hali da akida irin taki, ‘ya’yanki ba sune kadai MAZA a duniya ba! MAZA ma tukunna, baki

gansu ba Mami.
In kin so ki aura musu ‘ya’yan Queen Elizabeth, karshenta dai kenan ko? Ki rubuta ki ajiye,
babu aure tsakanin ‘ya’yanki da Rayhanah! Tunda ita baki dauketa cikakkiyar mutum ba”.
“Ba haka nake nufi ba Dacta na?”
“To ya ya ne?”
“(A bit.......depressed). Ta ce, “Ni dai in hakan za a yi bani da matsala da yarinyar”.
Dacta ya ce, “Mami, hoo!”

Rahane tuni barci ya kwasheta a kan marbles din dining, inda ta ci abinci. A haka su Abida
suka shigo suka sameta, Abida, Jawahir da Azizah suka sunkuya suna kallonta.
Abida ta leka tafin kafarta ta ga faso da kaushi! Ta ce, “Ehoo! Yau faso zai yaga bedsheet din
Jawahid, don kuwa ba dai gadona ba”.
Aziza kuwa dukanta take tana cewa, “Tashi-tashi, cinnaka zai cijeki, ki hau gado”.
Jawahir kuwa hannunta ta kama tana cewa, “Tashi muje daki za ki dauki sanyi a nan”.
Ta bude idonta a hankali tana kallon su. Ba ta taba ganin kyawawan mutane irin wadannan
yaran ba.
Dacta ne da Mami suka fito tare jin hayaniyarsu, suka gansu zagaye da ita kamar sun ga
wata sabuwar halitta. Mami ta ce, “Mene ne haka? Ku kaita daki mana ta yi wanka sai ta
kwanta ta yi barcin”.
Abida ta ce, “Ar! Mami kafarta faso! She is smelling bad!! Da soson wa za ta yi wanka?”
Dacta ya dunkule hannu ya danna mata, “Da na Uwaki. Ja’ira mara hankali”.
Ya matsa gabansu ya ce, “Kamata Jawahir kuje daki ki taimaka mata ta yi wanka, kin gani ba
ta da lafiya”.
Jawahir ta bi umarnin mahaifinta. Suka shiga daki da Rahane. Ta cika mata ruwan dumi a
kwami, ta zuba dettol, ta bare sabon sabulun zest da sabon soso ta bata.
Ta ce, “Ki yi wankan sosai kin ji, amma ki yi a hankali kada ki fama ciwukan ki”.
Ta nuna mata hanger, “Ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login