Showing 21001 words to 24000 words out of 33002 words

Chapter 8 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

ranar da ya rike mata hannu, ta kan samu kanta cikin
yawan tunaninsa da mafarkin sa cikin barci. Wani al’amari ne mai girma da zuciyarta ke fama
da shi a kansa da ita kanta ba za ta iya fassarawa ba. Abida tana Takai, Jawahir ce da Azizah a gidan, ita ma Mamin night duty za ta tafi. Don haka
a kintsenta ta shigo falon da lab-coat a hannu.
Ta ce, “Muje ka sauke ni ma gaisa a hanya”. Tare suka fita.
Rahane ba ta fito ba sai da ta bari suka fita ta lallaba ta koma dakinsu ta kudundune ta hau
barcin dole. Tana addu’a cikin ranta Allah yasa kada Yaya Khalipha ya neme ta.
Da ya dawo ba kowa a falon, Azizah ce ta fito daga dakinsu da gudu Jawahir ta biyo ta da
duka.
Ai tana ganin Khalipha ta yi tsalle ta dane shi, “Yaya Khalipha boye ni za ta duke ni”.
Ya kuwa boye tan, ya ce da Jawahir da ta karaso, “Kina tabata zan rama mata”.
Jawahir ta turo baki a shagwabe ta ce, “Don baka san me ta yi mini bane Yaya Khalipha, duk
ta cike min text books dina da zane-zanen ‘yan aljanu”. Abin ya bashi dariya.
Ya ce, “Wai haka Zizahna?”
Ta ce, “Yi hakuri Anti Jawahir ba zan kuma ba”.
Ya ce, “To kin ji ta baki hakuri, sai ki yi mata afuwa Allah yana son masu afuwa”.
Ta juya ta shige daki tana kumburi. Ya ce, “Zizah ina Rayha ne?”
Ta ce, “Tana wanka”.

“To maza je ki gano min ko ta fito ki ce ta zo ta karbi ‘She stillborn’ din da ta bani sautu tun
last month sai yau na samu”. Ta juya da gudu ta yi dakin.
Lokacin da ta fito wanka kayan sallarta da hijab dinta dogo har kasa ta sanya ta tada ikama,
don haka da Azizah ta ga tana sallah sai ta koma ta ce da shi tana sallah. Ta yi wucewarta
harkar gabanta.
[12/24/2019, 17:56] Takori: Haka Rahane ke ta hakuri da Abida, kullum da nau’in wulakancin
da za ta yi mata, amma ko cira kai ba ta yi balle ta dube ta,
A kwanaki talatin da suka biyo baya, Rahane ta ware sumul! Duk ciwukan jikinta sun kame
sai tabo. Ta yi haske, amma ba mai yawa ba.
Rahane ba kyakkyawa ba ce, amma halayenta masu kyau ne. Sai suka sayo mata kyan a
idaniyar jama’ar da ta samu kanta a cikinsu.
Mami ta sha gwada Rahane ta fannoni da dama amma ba ta sameta da wani hali mara kyau
ba.
Akwai sanda za ta kirga kudi ta aje a gefen gadonta ta kira Rahane ta ce ta dauko mata wani
abun, ta dawo ta kirga kudinta dai-dai take samun su. Anyi haka ba sau daya ba.
Kuma babban abin da ke burgeta da Rahanen shine, rashin son maganarta, da rashin son
hayaniya, wadatar zuci, sannan duk da kasancewarta bakauya, to ba ta fiye fiddo kauyancin ba.
Ga hidima da Azizah kamar kanwarta ta jini. Sun shaku sosai. An ce mai Da wawa...... to hakan
ce ta faru da Mamin. Ta kai ta kawo har barci Rahane da Aziza a gado daya suke yi. Abida ba ta fasa halinta ba,
sai dai in Daddy na gida ko Jawahir ta bude mata wuta. Uffan Rahane ba ta ce mata, ita har ta
saba ma da rashin mutuncin Abida.
Ina wuta Abida ta saka Rahane! Ranar da ta ganta shirye cikin uniform irin nasu direba zai
kai su makaranta.
Rahane aji hudu aka sanyata da aka yi mata gwaji, Abida da Jawahir na aji biyar. Dacta da
kansa ya kaita, ya yi mata komai na zama cikakkiyar dalibar DARUL-ARQAM, sai dai Allah ya
biya shi.
Sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba a zo ba. Rahane ta samu kanta a sabuwar
makarantar addinin Musulunci ta DARUL-ARQAM dake cikin tsohuwar Jami’ar Bayero.
Babu laifi tana fahimtar karatun, sai dai abin ya zo mata da tsauri kwarai, a hakan dai ake
kukkullawa don Malam Umar yana taimaka mata sosai, musamman da yake ya lura tana da
sha’awar karatun, fahimta ce sai a hankali, musamman idan aka yi la’akari da inda ta faro
karatun nata. A haka suka samu hutun karshen zango suka yi jarabawa. Kamar koyaushe ‘ya’yan Dacta
Takai sun dauko na dai-daya a ajujuwansu har Azizah, Rahane ce ta dauko na ashirin cikin su
arba’in.
Abida ta yi ta sheka mata dariya a mota. Sai dai kamar yadda ta zata Daddy zai yi fushi da
Rahane, ba ta ga hakan ba, yaba mata ya yi, ya kuma kara mata karfin gwiwa.
Sanda Malam Umar ma ya basu hutu Dacta ya shirya musu tafiya Takai don ziyarar dangi,
kuma Rayhanah ta ga mahaifinta za su yi kwana biyu, wato Asabar da Lahadi.
Ibraheem ke jan motar wanda ta ji kannen shi na kiran shi YA HIMU wato an yanke farkon
sunan an kira shi da karshe.
Rayhanah ta rasa irin kiyayyar da wanan dan tahaliki ke gwada mata. Bai taba yi mata

magana ba, haka bai taba daga ido ya kalle ta ba. Duk da ta lura rashin son magana halinsa ne,
amma ai yana amsa gaisuwar kannensa.
Wani lokacin har yana daukar Azizah su fita harabar gidan, amma ita bai daga ido ya kalle ta.
Duk da dai bai fiya zaman gidan ba yana hattama karatunsa,.
A cikin motar ana ta hira, Rayhanah da Ibraheem ne kadai basa magana.
Daddy ya ce a ransa, “Duk halinsu daya!”.
Ana sallar Azahar suka shiga Takai, kai tsaye gidan Hakimi suka zarce. Uwargidan Hakimi
Haj. Karima mace ce mai kirkin gaske, kuma ita ce uwar dakin Dr. Asma’u. Tana da yara tara
duk mata, duk ta aurar dasu sai autar ta Nabilah wadda ke masifar son Ibraheem, duk sanda
suka zo Takai ita ce ke kula da al’amarinsa. Sai dai shi din har yanzu babu wanda ya san inda ya sa gaba a kanta, tunda har yana kula
ta, suna shiri sosai. In sun je gidansu can Kano ko su sun zo Takai, kuma suna waya sau-tari,
duk da shi ba kowanne lokaci yake harkar wayar nan mara kan-gado ba, a kwana ana yinta, a
wuni ana yinta, babu sallah babu salati, babu amfanawa kai komai, amma ko salatin Annabi ba
kowannenmu ke yi kullum ba ko da cikin carbi ne.
Amma waya ita ce rayuwar al’umma a yanzu. Idan ya kashe waya sai week end yake bude
ta, week end din ma idan baya komai, kowa dake tare da shi ya san hakan.
Sai Hajiya Indo, ita ce uwar ‘yan mazan gidan, mai bi mata Sadiya, ta rasu wajen haihuwa,
sai ta dauki ‘yar ta rike, tunda dama ita duk ‘ya’yanta maza ne sunanta Hibba, sa’ar Nabila ce,
ita kuma ita ce ake wa Khalipha kamu, da ita da Nabilan duk suna karatu a Canadian Univeristy
of Dubai, yanzu ma sun zo hutu ne. Sai amaryar Hakimi da ya aura bayan mutuwar Sadiya Inna
Luba, tana da yara biyar maza da mata.
Hajiya Karima ta dubi Rahane dake zaune gefen Mami ita da Azizah, da yake su Jawahir duk
sun fice cikin sa’anninsu.
Ta ce, “Ina kika samo ‘ya mai nutsuwa haka? Ko mai rainon Azizah ce?”
Ta ce, “A’a, ‘yar amana ce Dacta ya bani”.
Hajiya Karima ta sake juyawa tana kallon Rahane ta ce, “To ko ita ce na ji Nabilah na labarin
Dacta ya tafi da ita daga nan Takai? Babanta kuma na nan tare damu?”
Ta ce, “Ita ce”. Tana lallatsa wayarta.
Hajiya Karima ta ce, “Allah sarki! Ai kuwa na ji Mai Martaba yana yabon Babanta, ya ce
dattijon kwarai ne yana kula da Barga yadda ya kamata. Dawakansa sun kara lafiya da girma,
sannan kullum fes suke, wajensu fes kuma ba ya karbar ko taro in ba ihsanin kansa ya yi masa
ba”. (Not interested ga hirar) Dacta ta ce, “Allah sarki, ita ma Rayhanah ba ruwanta”.
Wata baiwar Haj. Karima ta shigo, ta umarceta da ta raka Rahane wajen mahaifinta. Ta kama
hannunta suka fita. Azizah ta like mata sai ta bita.
Mami ta ce, “Dauke ta ku je”. Ta kuwa sungumi Azizah a bayanta suka tafi.
Mahaifinta ta fara yin tozali da shi durkushe gaban wani kosasshen doki yana rage masa
kofato. A gefe Ibrahim ne ke shafa gashin wata godiya sabuwar haihuwa. Ga yadda ya mai da
hankalinsa a kan dawakan za ka fahimci yana son su.
Da gudu ta karasa ta zube gaban Babanta tana dariya. Ibraheem ya kallo su ta gefen ido, sai
suka ba shi tausayi, su wadannan wato basu da kowa sai junansu, amma wai shine yake jin
haushi don mahaifinsa ya taimake su.

Ya manta cewa duk wanda ya taimaki dan’uwansa Musulmi shima Allah zai taimake shi, shi
yasa mahaifinsa kullum cikin nasara yake, saboda taimakon da yake yiwa al’umma. Balle
maraya da Allah da kansa ya ce a taimake su.
Yana kallon su kowannesu bakin shi ya ki rufo. Ta ce, “Baba kai ne ka yi kyau haka?” Shima
ya ce, “Rahane ke ce?” Sai suka sa dariya.
Ta ce, “Allah Baba in a hanya na ganka ba zan ganeka ba”.
Ya ce, “Ni din kuma fa? Kin canza gaba daya Rahane”.
“Sai mu gode Allah Baba, suma mu gode musu. Mu ci gaba da zama dasu cikin amana, Allah
ya ji kan Iya”.
Sai tasa habar zaninta ta share idonta. Shima kokarin mai da kwallar idanunsa yake, ya ce,
“Amin ya Allah, Rahane ki yafe ni a kan tirsasawar da na yi kan cewa sai kin auri Ado shine silar
da Iya ta rasa ranta don ta tserar dake daga wulakantacciyar rayuwa. Wallahi nima kaina a
lokacin ban san dalilin da yasa nake tsoron Ado ba, sai yanzu na gane ba haka ya barni ba, to
Allah ya fishi”.
Ta ce, “Kada ka ce kai ne silar rasuwar Iya Baba lokacinta ne ya yi, ko tana dakinta ajalinta
ya zo, dole za ta tafi. Baba Dacta ya ce duk sanda muka tuna ta addu’a za mu yi mata, suratul
Mulk, Yasin da Ikhlas, shine soyayya ta gaskiya da zamu yi mata”.
Ya ce, “Ikon Allah, Rahane har ilimi kin kara da hankali”.
Ta ce, “Ai Baba makaranta muke zuwa safe da yamma, da dare ma su Baba Dacta na koya
mana”.
Ya ce, “Alherin Allah ya tabbata a garesu”.
Himu ya bar wurin don basu ganshi ba, kuma baya so su ganshin. A soro na biyu suka ci
karo da Nabila ta hado abincinsa cikin kwandon kayan abinci.
Ta ce, “Ya Himu ina ka shiga ne? Ga shi ina ta kiranka ya ki shiga”.
A takaice ya ce, “Ina barga”.
Suka juya cikin gidan tare.
Yana zaune ya mike dogayen kafafunsa a kan tattausan kilishin (sitting room) din da suke
zaune, Nabila na faman zuba mishi jellop din cous-cous wadda ta ji kayan lambu, a gefe cikin
dan tangaran farfesun hanta ne, ta diba a cokali ta kai bakinsa.
Ya yi murmushi ya karbi cokalin daga hannunta yana ci suna ‘yar hira. Sai dai duk rabi
Nabilan ce ke yin hirar tana ba shi labarin rayuwar makarantarsu.
Sama-sama yake sauraronta, He is curious about something different (wani abu daban yake
son sani) kan Rayhanah da Babanta.
Kadan ya ci ya cika ruwa a tambulan ya sha. Ya mike yana laluben mukullansa a aljihunsa ya
ce,
“Am coming Nabeelah (ina zuwa)”.

Ibraheem Mansur, (HEEMU ko I.M) kamar yadda kannensa da abokansa ke kiransa. Bai da
shiga sharo ba shanu balle abin da bai shafe shi ba.
Amma a yau, haka nan ya samu kansa da son sanin asali da tushen su Rayhanah, da
rayuwarsu ta baya. Abinki da karamin gari, kowa ya san kowa.
Don haka bai sha wuyar samun tarihin su Rayhanah ba. An gaya mishi uwarta ta rasu tun
lokacin haihuwarta, kakarta da suka yi hatsari tare ita ta raine ta.

Har makarantar su Rahane ya je ya binciko takardunta. Malamansu sun shaideta wajen
kokari da son karatu. Sai ya ji hankalinsa ya kwanta da rayuwarta tare dasu.
Sai dai ko a fuska bai nunawa Baba Dacta komi ba. Malam Rashidu ya samu kyakkyawar
shaida daga bakin makwabtansa. Amma a da sam hankalinsa bai kwanta da zaman yarinyar
tare dasu ba, saboda halin rayuwa da butulci irin na dan Adam.
Sai kuma yake tambayar kansa, shin me yasa ya damu kansa kan yarinyar? Damuwa irin
wadda bai taba yi a kan kowa ba??? Ya tattara zancen ya watsar ya shiga sabgoginsa.

Da yammacin ranar yana barga tare da kaninsa Sha’aban dan Hakimi, kowannensu
ingarman doki ya zaba Sarkin Dawaki ya aza musu sirdi suka dane suka nufi ‘yar shakatawa
bayan gari.
Suna tafe hira suke yi kan sabbin gine-ginen zamani da Hakimi ke yi a cikin garin da ginin
gidan saukar baki mai dauke da bukkokin zamani, inda Turawa ke sauka idan sun kawo ziyara.
Haka nan Hakimi na sauke bakin alfarma idan sun zo.
Ibraheem ya yi sha’awar wadannan gine-ginen sosai. Yake ce da Sha’aban duk lokacin da ya
tashi ginin gida zai sanya ‘Hut’ wato bukka ta gargajiya mai suffar zamani.
Sanda suka dawo magariba ta gabato, suka sauka daga dawakan suka soma alwala a
famfon wajen. Kamar an ce da Ibrahim ‘juya’, ya hango Rahane na yankewa Babanta akaifa da
nail cut. Sai dai bai jin me suke cewa a tsakaninsu.
To haka washe gari da misalin karfe goma na safe ya shigo bargar domin an kawo sababbin
(Polo Horses) daga Ireland duka na Baba Dacta ne, yake ba da hayarsu ga masu sana’ar
tseren Dawaki ake masa kiwon su anan bargar hakimi. Sun bambanta sosai da sauran
dawakan ko daga koshinsu da shekin da suke yi da kuzari. Ya dan juya ido sai ya hango Rahane da jibgin kayan wankin Babanta da ta tattaro tana ta
dirzarsu kamar Allah ya aikota. Shi kuma Baban yana gefe yana yiwa dawakin askin jelarsu da
katon almakashi. Yana cewa,
“Wato Rahane ba kya jin magana ko? Na ce ki bar wankin nan ya fi karfinki in na gama zan yi
abina”.
Ta ce, “Albarka nake nema Baba, ka barni in samu, in ban yi maka ba wa zan yiwa? Idan
mun tafi ban san yaushe zamu kara dawowa ba”.

Ibraheem ya jinjina kai suka kara ba shi tausayi.
Washegari suka yi sallama da kowa za su tafi, Rahane har kuka ta yi saboda ba ta son barin
Babanta. Amma ba ta bari Baba Dacta ya gani ba, sauri ta yi ta dauke hawayen da yatsunta.
Da gudu ta koma ta sake rungume Babanta, sannan ta shiga mota tana share hawaye da
sauri.
Har Ibraheem ya kunna mota ya hango Mal. Rashidu tafe da sassarfarsa rike da katuwar
leda, don haka ya dakata.
Baba Dacta ya sauke gilashi sai ya mika masa, “Yalo ne da kashu (cashew) babu yawa a
yiwa yara tsaraba”.
Hannu biyu Baba Dacta yasa ya karba, ya ce, “Yara sun gode Baban Rayhanah. Allah ya
kara nisan kwana”.
Ya sanya hannu cikin aljihu ya zaro naira dari biyu ya mikawa Aziza, “Ungo yarinya ka sha

ruwa a hanya kin ji?”
Mami ce ta karba fuskarta fal fara’a ta ce, “Aziza ta gode Baba”.
Ya daga musu hannu suka ja motar suka tafi. Abida ta juyar da kai gefen taga tana tsaki mara
sauti. Kamar ta rufe Mamin da duka da ta karba.
Su kuwa iyayen sun ji dadi har ransu. ALHERI komi kankantarsa dadi gare shi, amma ga
wanda ya san mutuncin dan Adam.
Kafin la’asar sun iso Kano. A harabar gidan bakuwar mota ce kankanuwa mai santsi (one
door, Camero) fake a harabar adana motoci.
Ai kuwa daga Jawahir, Abida har Azizah fita suka yi a guje har Azizah na faduwa, ta kuwa
fashe da kuka, don har bakinta ya fashe.
Da sauri Rahane ta fito ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login