Showing 12001 words to 15000 words out of 33002 words

Chapter 5 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

towell nan, ki dauki wanda kike so. Wannan kwandon ki zuba
kayan da kika cire kayan wanki ne a ciki”.
Rahane ta ce, “Ai ban zo da wasu kayan da zan canza ba in na ajiye wadannan”.
Ta ce, “Zan baki nawa in ji Daddy”. Ta juya ta fita tana cewa, “Ki yi wanka sosai”.

Rahane ta yi tsaye tana kallon katon ramin da aka cika da ruwa aka ce wai ta shiga ciki
tsulum! Ta yi wanka. To idan ta nutse fa?
Ta kai hannu a hankali tana shafa gefen kwamin, santsi kamar jikin tarwada. Ga shi fari kal!
Shi kansa ruwan kamshi yake. Ta fi minti ashirin ta shafa nan, ta kalli kanta a mudubi, ta kasa
ko da cire kayan jikinta. Ga bayan gida tana ji amma ba ta ga masai ba, sai fararen tangaraye a
rufe, da ta bude ruwa ne a kwance a cikinsu garai-garai, ta rasa inda za ta sa kanta, domin
bayan gidan ya matseta. Ta kuma rasa a inda za ta yi, sai ta goce da kuka.
Daga daki Abida da Jawahir suka jiyo ta, Abida ta kyalkyale da dariya ta ce, “Yanzu haka
faduwa ta yi cikin soka-way”.
Da sauri Jawahir ta iso bakin kofar tana buga mata tana cewa, “Lafiya?”
Ta ce, “Tutu nake ji”.
Ta ce, “Mene ne tutu?’

Ta ce, “Bayan gida”.
Ta murda kofar ta shiga gaba-gadi, nan ta tarar ko kayan jikinta ba ta tube ba balle ta yi
wankan, tana tsaye tana share ido. Tausayi ya kama Jawahir, ta bude masai ta zauna a kai.
Ta ce, “Haka za ki yi ki yi bayan gidan. Sai ki murda nan ruwa zai fito ya kora shi. Nan kuma
shima zama za ki yi ki danna nan zai yi miki tsarki. Ko ki fara gogewa da wannan (ta nuna mata
tissue). Sai ki sa sabulu ki wanke da kanki. Kin gane?”
Ta ce, “Eh”.
“To maza tube ki yi sai ki yi wankan. Ko in cuda miki baya?’
Ta ce, “A’a, zan iya kada ki fama ni. Amma ba zan iya shiga wannan koramar ba ki zuba min
a bokiti”.
Duk dauriyar Jawahir sai da ta ji dariya. Ta ce, “Ba korama ba ce, amma tunda baki so bari in
bude ruwan ya fita, sai ki kunna famfon ciki. Amma wannan famfon na zafi ne”.
Ta bude rariyar ruwan ya tafi. Ta kunna mata famfon ta dauko bokitin wanki ta cika mata
sannan ta fita.
Abida na durkushe bisa dan gadonta rike da ciki tana ta dariya, don duk tana jinsu. Jawahid
ta kai mata duka ta falla aguje ta yi falo tana bawa Mami labari.
Daga daki Daddy ya jiyota shima ya yi dariya, amma ya ciro wayar charger dinsa ya fito ya yi
kanta, ta yi tsalle ta boye a bayan Mami tana “Na tuba Daddy.......Daddy Allah ya huci
zuciyarka”.
Ya ce, “To kar in kara jin kina mata dariya in ta yi wani abun da baki sani ba, nuna mata za ku
yi a hankali ba ki dinga yi mata dariya kina ba da labari ba”.
Ta ce, “To Daddy”.
[12/24/2019, 17:56] Takori: Haka ta yi jika-jikanta a tsaye cikin kwamin da bokiti, ta daga kafa
za ta fito santsin kwamin ya kwasheta ya buga da kasa. Ta sake yunkurin fitowa ta sake shan
kasa. Rahane ta ce, “Wannan bala’i da me ya yi kama?” Ta koma ta cure jikinta a cikin kwamin
ta yi zamanta. Jawahir ta ji shiru wajen awanni biyu tana zaune gefen gadonta tana jiranta. Da ta tabbatar
ba za ta fito ba sai ta mike tana kwankwasa mata ban dakin.
Daga ciki Rahane ta ce,
“Ki zo ki fiddani na kasa fitowa”.
Jawahir ta murda kofar ta shiga ta kama hannayenta ta fito da ita, ta zari tawul ta daura mata
suka fito.
Jawahir da kanta take shafa mata vaseline a hankali kada ta fama ta. Ta ciro wasu Pakistan
ruwan kwaiduwar kwai cikin kayanta ta mika mata ta sa.
Sai ta ga Rahane ta kasa sakewa a cikinsu, domin dai a wurin Rahane dogon wando sutturar
maza ne.
Ta ce, “Don Allah ki bani zani na atampa wadannan santsi garesu”.
Jawahir ta yi dan jim, sai kuma ta bude wardrove ta dauko sabuwar danyar vlisco (Holland)
dinta ta bata, ta daura mata zanin, ita kuma ta sa rigar. Ta taimaka mata ta daura dan kwalin,
sai ta yi kyan gani.
Lokacin ne Mami da Dacta suka shigo. Dacta rike da gorar ruwan Myer da ledar magunguna
fara mai tambarin AKTH. Yana tafa hannu ya ce,
“Yar Dacta! Kin yi kyan gani kamar ba ke ba”.

Ita dai murmushi ta yi, ta zame daga tsayuwa gaban Jawahir ta durkusa a gabansu. Da sauri
Mami ta dagota ta zaunar da ita a bakin gadon Jawahir tana cewa, “Ki daina yin wannan
durkuson mu mun yafe, ko da fatar baki ki gaishe mu kin ji?”
Ta sunkuyar da kai kawai. Mami ta karbi gorar ruwan a hannun Baba Dacta ta murda tana
juyewa a tambulan mai garai-garai, shi kuma yana ballo mata magungunan da ya kamata ta
sha a lokacin.
Daya bayan daya yake sa mata kwayar maganin a baki Mami na binsu da ruwa, aikinta kawai
hadiyewa..
Dai-dai lokacin da aka kira sallar magariba. A ka’idar gidan duka tare suke yin sallah in har
suna gida. Baba Dacta ne ke jan su.
To yau ma hakan, karo na farko da Rahane ta taba yin sallar jam’i a rayuwarta. Sai ta ga
banbance-banbance da yawa da irin sallah da alwalar da suke yi a kauye.
Ashe su kawai dungurawa suke yi su mike, babu irin wannan karatun sallar mai dadi da Baba
Dacta yake yi, basa bin ka’idoji da sharuddan da aka wajabta a kan sallar.
Sannan bayan an sallame isha’i, sai an dora da shafa’i da wutiri. Sannan ayi hadaka wajen
cin abinci a kan tebir. Wanda ba ta san wa ya dafa ya jera su a kan tebir din ba, ita dai kawai ta
gansu, ta san kuma ba Mami ta yi ba don suna tare da ita.
Daga nan kuma ta ga su Jawahir sun dauko wasu jakunkuna cike taf da litattafai har Aziza ta
dauko nata, suka zube gaban iyayensu.
Nan da nan suka canza harshe daga iyayen har ‘ya’yan suna ta koya musu ayyukan
makaranta. Jawahir ce ke tare da Daddy, ya yin da Abida da Aziza ke tare da Mami. Turanci
suke yi zallah ba irin wanda ake musu a TAKAI SPECIAL PRIMARY ba.
Sha’awa ta kama Rahane, sai ta ja gefe ta tattara hankalinta a kansu, jefi-jefi Baba Dacta kan
kalleta yana kuma sane da yadda ta kafa musu ido babu ko kiftawa.
Karfe tara saura minti biyar duk suka rufe litattafan suka maida su jakunkunansu, suka diba
suka yi dakinsu.
Shi kuma Baba Dacta ya mike cikin tuma-tuman kujerun falon irin leather seats din da ko
allura ba ta iya huda su, ya murdo labaran kasa na N.T.A yana sauraro.
Kalar kujerun Orange and Black. To haka tattausan kilishin da aka dora akan farin marbles
shima ruwan goro ne da ratsin baki, labulayen kuma light orange.
Mami daki ta nufa ta yi wanka ta fito cikin shiri, lab coat dinta fara kal da farin gilashi da hand
bag rike a hannayenta. Yau aikin kwana gareta a dakin yara na Isyaka Rabi’u (Paediatric-Unit).
Ta russuna ta sumbaci goshin Baba Dacta, ta shafa kan Aziza dake barci a kan cinyarsa, ta
dubi Rahane dake satar kallon su suna bata sha’awa ta ce, “Ni na tafi aiki Rayhana, dauki Aziza
kuje ku kwanta, da wuri ake barci saboda zuwa makaranta”.
Ta mike ta ce, “A dawo lafiya”. Ta dauki Aziza a cinyar Daddy ta yi dakin su Jawahir.
Likitocin biyu suka bita da kallo cike da tausayi. Mamin ta fita, Dacta ya ci gaba da sauraron
labaran tara cike da tunanin hanyoyin da zai bi ya inganta rayuwar Rayhana, wadda Allah ya
sanya mishi kaunarta kamar, koma fiye da yadda yake kaunar su Jawahir.
Tana shiga dakin karamin gado ta dora Aziza wanda ta fahimci shine nata. Abida da Jawahir
sunyi wanka sun wanke baki sun sauya kaya zuwa marasa nauyi wanda a ganinta kayan maza
ne (wando).
Abida ta balla mata harara ta ce, “Ga (diaper) nan ki sa mata”. (Tana nufin Azizah).

Ta yi sukuti tana kallon ta don ba ta san wani diaper ba. Haushi ya kashe Abida, ta tashi da
kanta ta sa mata.
Rahane na tsaye saboda haushin da ta bata ba ta san sanda ta hankade ta ba, saura kadan
ta bugu da karfen gadon Azizah.
Jawahir ta ce, “Abida mene ne haka? Wannan ai rashin mutunci ne”. Ita ma ta danna mata
tata harar.
Ta fiddo ido ta ce, “Sai dai in a gadonki za ta kwanta wallahi ba dai nawa ba, ta yanka min jiki
da faso”.
Ta dau filo ta jefa a kan marbles ta ce, “Ki kwanta a nan, wa ya sani ma ko kwarkwata ce fal
kanta tunda ta zo ba ta bude shi ba.....”
Sauran maganar ta makale a makoshinta da ta daga ido ta yi ido hudu da Daddy a tsaye jikin
kofa yana kallonta kawai. Ta yi tsuru-tsuru ta yi shiru.
Ya dubi Rahane dake sunkuye da kai ya ce, “Rayhanah!”
Ta dago a hankali ta dube shi,
“Hau gadon Abida ki kwanta”.
Da kyar ta iya bude baki a hankali ta ce, “Baba Dacta ba zan iya kwana a kai ba fadowa zan
yi, nan din ya isa”.
Ya ce, “Hau ki kwanta na ce, ba za ki fado ba”.
Ba za ta iya yin jayayya da shi ba, sai ta hau gadon a hankali ta takure a karshensa, duk da
ba wani girma ne da shi ba, gadon silver ne karami.
Ya dubi Abida da matsanancin fushi ya ce, “Ke kuma dauki filonki ki kwanta a kasan ki ji in da
dadi.
Abida ki kiyaye ni, ki kiyayi taba min Rayhanah. Ban ce lallai sai kin so ta ba, don ba zamanki
take ba, kuma ba a kanki take zaune ba. Kin yi na biyu kada ki sake in ji na uku, karonmu dake
ba zai yi miki dadi ba”.
Ya ja lallausan bargonta ya rufawa Rayhanah. Ya juya ya fita bayan ya mika mata akwatin
hearing aid dinta yana gaya mata yadda za ta adana shi in za ta kwanta ko wanka ko alwala,
kada ruwa ya taba shi. Ya kuma nuna mata yadda za ta cire batir din da mayar da shi.
Jawahir ta kasa shiru ta ce, “Daddy wannan ai hearing aid ne, me take yi da shi?”
Ya dan dubeta ya ce, “Me masu amfani da shi ke yi da shi?”
Ta ce, “Karin karfin ji”.
Ya ce, “To ita ma Rayhanah haka”.
A takaice ya gaya mata hatsarin su Rayhanah, mutuwar kakarta, auren da Babanta zai mata
da yadda aka yi ya taho da ita.
Jawahir ba ta san lokacin da ta taso ta dawo gadon da Rayhanah ke zaune ba ta rike hannun
tad a babu ciwo tana share hawaye.
Ta ce, “Daddy ni zan dinga tayata kula da shi ma”.
Ya ce, “Allah ya kyautata miki kema Jawahir”.
Ta ce, “Zamu kwanta gado daya, ita Abida ta hau nata”.
Ya ce, “Wallahi yau a kan tayal za ta kwana, koma gadonki ki kwanta, ita ma gobe za a kawo
mata nata”.
Ta sauka ta koma. Ya kashe musu wuta ya fito ya jawo kofar yana gaya musu suyi addu’ar
kwanciya.

Washe gari Abida da ciwon baya ta tashi sakamakon kwanan dandaryar tayal, wannan ya
kara fushinta da shigowar Rayhanah cikin rayuwarsu, ta tsaneta, iya kiyayyar da ba za ta iya
fassarawa ba.
Tunda har a kanta ne yau Daddy ya yi mata haka. Daddyn da ko tsawa mai karfi baya yi
musu, sai dai ya yi musu nasiha.
A haka suka bi jam’in sallar asubahi tare da Daddyn tana ta kumburi, sannan suka soma
shirin wanka don tafiya makaranta.
Jawahir ce ta yiwa Azizah ta shiryata cikin kayan makarantarta na play group din
DARUL-ARQAM, direba ya kwashe su suka tafi, suka bar Rayhanah ita kadai a dakin ta takure
can gefe a kusurwar gado,.

Sai yanzu ne kewar Iya Bilki ta dawo mata sabuwa, ta shiga kuka a hankali amma mara amo,
domin ta toshe bakinta da dan kwalin kanta.
Karfe takwas da rabi dai-dai na safe motar Mami ta shigo farfajiyar gidan, I.M ke tukin, shima
a asibiti ya kwana.
Jefi-jefi suna hirarrakin da suka shafe su shi da mahaifiyarsa, ya yi parking din motar a
muhallinta yana cewa,
“Nifa gaskiya Mami zaman yarinyar nan da Daddy ya kwaso bai min ba, kuma ba matsayin
‘yar aiki ba, duk taimakon da ya kamata ya bata na likita da patient dinsa ai ya ba ta, hatta
hearing aid din fa shi ya saya da kudi ba kadan ba.
To na mene ne kuma na tahowa da ita? Shi bai san yanzu zamani ya canza ba (sunan litafin
Takori mai zuwa) Kowa ta kansa yake, ka jawo mutum inuwa shi kuma da ya ji sanyinta ya
turaka rana”.
Mami ta ce, “To ni dai babu ruwana mun riga mun rufe wannan babin da shi. Da ai na kowa
ne HIMU (sunan da take kiranshi kenan wato Ibrahimu)”.
Ya kyabe baki bai sake cewa komai ba, ya dauko jakar Mami da lab-coat da sauran
takardunta suka shige ta kofar kicin.
Firji ta fara budewa ta dauko robar ruwan FARO mai rangwamen sanyi ta sha tambulan biyu.
Al’adarta kenan a kullum da safe kafin ta sanya komi a cikinta yana da fa’ida sosai, ga lafiyar
jiki da ta zuciya.
Ibrahim dakinsu ya wuce don ya yi wanka, jinsa yake kamar a kwatami saboda rashin
wankan. Mutum ne mai masifaffar tsaftar gaske, sannan mai baudadden hali.
Abin nufi, da wuya ka gane inda Ibrahim Mansur Takai ya sa gaba, ba za ka iya gane farat
daya yana da kirki ko ba shi da shi ba, mahaifinsa kadai ya san kansa, shi kuma kadai ya iya
tafiyar da shi da baudadden halin nasa.
Ibrahim na da kyau, wanda kallo daya za ka yi mishi ka ga hakan. Wankan tarwada, mai tsayi
da rashin kauri. Yana da siririn saje a gefen fuskarsa mai laushi da sheki, da ka ganshi ka ga
Mansur Takai, ta karan hancin, da manyan idanunsu.
Sannan mai tattsauran ra’ayin akidun Malam Nasara. Sai dai kuma mutum ne mai riko da
sallah, tabon sujjadar dake tsakiyar goshinsa kadai ya isa shaidar hakan.
Ba za ka iya dorar da wani abu a kan halayyar shi ta zahiri da badani ba, wannan sai
mahaifinsa, duk yadda kuke da shi kuwa.
Nutsuwa irin ta Ibrahim daban take, za ka iya ganin hakan a kan ko me yake yi, kamar cin

abinci, sallah, tafiya da duk wani motsi da zai yi ko a karatun likitancinsa.
Dacta Mansur na son Ibrahim son da baya yiwa Yayansa Khalipha, saboda komi nashi
Ibraheem ya dauko. Magana in ba mai muhimmanci ba ce Ibrahim baya yinta, ko hira ake cikin
abokan karatu Ibrahim baya tofa nashi in ba mai ma’ana ba.

Kasancewa ranar Lahadi ce, Dacta bai zuwa office don haka basu fito ba shi da Mami sai
karfe goma na safe, cikin sassaukar shiga ta zaman gida. Mami doguwar riga ce kirar Kuwait
ruwan toka a jikinta, ta kame jelunan kitsonta da ribom. Shi kuma Dacta shirt ce mara nauyi fara
da shudin jeans a jikinsa. Ibrahim suka tarar bisa tebir yana kalaci, shima ya yi wanka ya yi fes da shi cikin Hilfiger
Jeans ruwan bula, gashin kansa da ya yiwa saisaye yana kwance bakikkirin da shi sai sheki
yake. Ga turaren shi mai sanyin kamshi na tashi a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login