Showing 6001 words to 9000 words out of 33002 words

Chapter 3 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

Mamaki ya kama su dukkansu, Doctor Mansur da kansa! Da sauri Nurse din ta karba tana
bata. Ya dan ja baya ya sarke hannun shi a kirjinsa bai kara kallon Ibrahim ba. Ya ci gaba da
feso musu lacca kamar Obama ya diro Nijeriya.

Kwana uku Dr. Mansur na kula da Rahane, ta ji sauki sosai amma ta ki magana. Don haka ya
soma tunanin akwai wani abu. “There must be something wrong beneath!” Ya fadawa su
Ibraheem.
Ya girgiza kai ya juya gare su, “Tana bukatar ganin likitan kunne da makogaro yayi examining
dinsu, wanda wannan ba shine darasin da muke a kanshi ba tukunna, muna neman lafiyar
gangar jikinta ne gaba daya”.
Cikin sati biyu Dr. Mansur ya ba da hankalin shi da kwarewar shi gaba daya a kan Rahane da
shi da Dr. Imam, kwararren likitan kunnen da ake ji da shi a AKTH. Duk wani taimako da ya
kamata ya bata sun bata, amma Rahane sai da aka dangana da hearing test wanda ya nuna ta
gamu da very unusual hearing issue, wanda ke bukatar ayi CT Scan da MRI Scan, dake
bukatar kudi na fitar hankali wanda zai nuna hakikanin menene matsalarta daga inner and outer
zones na kunne da kwakwalwarta, a dalilin rashin sanin daga inda ta bullo da kuma rashin sanin
kowa nata, suka samar da occasional hearing Aid gareta, sannan ta ji abin da suke cewa.
Amma idan aka cire bazata ji ba. Duka daga aljihun Dr. Mansur Takai, wanda Allah ya sakawa
kaunar Rahane da tausayin ta,
Yau Asabar ba shine on call ba, Dr. Hashim ne, amma sai da ya shigo asibitin musamman
don yaga jikin Rahane. ‘Yar shi karama AZiza na rike da hannun shi, caftan na shadda milk
colour ne a jikinshi da hular da ta dace dasu ba suit da lab-coat ba.
Rahane na hangoshi ta soma murmushi, shima murmushin yake mata. Ganin ta zauna ras
alamun lafiya na samuwa, ya ja kujerar dake gabanta ya zauna.
“Yar Doctor, lallai lafiya ta samu”.
A sanyaye ta ce, “Alhamdulillah!”
Lokaci na farko da ya ji furucin bakinta, tun ranar da su kai hatsarin.
Shima ya ce, “Alhamdulillah ‘yata ya ya sunanki?”
Ta ce, “Rahane”.
Ya bushe da dariya, “RAYHANAH kenan ko?’
“A’a, RAHANE!” Ta sake gyara masa.
“To na yarda Rayhanatu, ni ba zan iya fadar wancan din ba, saboda ba shi da ma’ana
kwata-kwata”.
Dr. Hashim na jinsu yana dariya yana auna patient din gadon kusa da ita. Lokaci guda

Rahane ta soma kuka. Duka likitocin suka tsaida dariyar suka yi kanta.
“Kuka Rayhanah? Daina kuka har gida zamu kai ki. Fatanmu shine Allah ya baki lafiya mu
tambayeki ke da waye kuka taho? Kuma ina ne garinku?”
“Ni da Iya ne, kuma ban ganta ba tun ranar”.
“Za ki iya gane ta cikin kowanne hali?”
Ta ce, “Eh”.
“Daga ina kuke?”
“Takai, zamu Tsangaya”.
“Takai? Ikon Allah”.
Ya yi dan shiru yana kallon ta. “Sunana Dr. Mansur Balarabe Takai....”
Ta dube shi da sauri. Ya gyada mata kai yana dariya. Dr. Hashim ya juyokadan ya ce, “Dr.
Takai, ashe ‘yar taka ‘yar garinku ce, dole a bata extra kulawa, kyakkyawa da ita, ina kamu
Doctor”.
Murmushi ya yi, ya ce da Nurse dake gefe a kawo Rahane ‘matuary”.
A kujerar daukar marassa lafiya nurses biyu suka turata zuwa mutuware.
Aka soma zarowa Rahane akwatunan gawarwaki abin babu kyawun gani. Rahane ba ta taba
ganin gawa ba sai yau a idanunta. Iyakacin firgita ta firgita, amma da aka zaro Iya Bilki, ba ta
san sanda ta fada kanta ta rungumeta ba. Kuka take na fitar hankali, domin Iya sumul take babu
ko kwarzane a jikinta. Idanunta ne kurum a rufe kamar mai barci, kamar ta ce “Iya”. Ta bude ido
ta amsa mata.
Da kyar Dr. Mansur ya janyeta, aka hada Iya cikin motar daukar gawarwaki na asibitin. Motar
Dr. Mansur na biye dauke da Rahane da I.M a gidan gaba, suka dauki hanyar Takai.

Rahane na baya ta kankame jikinta tana kuka mai cin rai, sai dai daga Doctor har dansa
Ibraheem babu mai jin ta sakamakon kira’ar Ahmad Sulaiman da Dr. Mansur ya saki a motar
har suka isa garin Takai.
Rahane ke nuna musu hanya da aka shigo Takai har kofar gidansu. Tana hango Akori-Kurar
Ado a kofar gidansu gabanta ya yi mugun faduwa. Hakan bai hanata fitowa daga motar ba a
lokacin da Ibraheem ya bude mata, yana ta zabga mata harara kamar ya hankadata.
“Shiga ki karawo shi Rayhanah”. In ji Baba Dacta (kamar yadda take kiranshi)
Da addu’a tasa kai cikin gidansu. Ta yi sallama ba a amsa ba. Sai kawai tasa kai. Caraf! Ado
ya cafke ta ya danneta a dakin Iya, nan ta ga babanta a makure a gefe daga shi sai gejeran
wando, ko’ina a jikinsa shatin bulala ne, jini ya bisu ya kwanta.
Ado ya ce, “Munafiki! To gata ta dawo da kafafunta, auren ma na fasa a gabanka zan yi
kaca-kaca da mutuncin ta in fanshe wahalata ta shekara da shekaru”.
Bai yi la’akari da halin ciwuwwukan da ke jikinta ba ya hadata da bango ya keta rigar jikinta
tun daga sama har kasa.......!

Ihun da Rahane ta zabga ya amsa kuwwa har sauran gidajen da ke makwabtaka dasu suka
jiyo. Dr. Mansur na waya, dansa Ibraheem ya yi saurin dagowa ya ce,
“Daddy.....yarinyar nan ihu fa take yi”.
Da sauri Dr. Mansur ya juyo, shima kunnuwansa suka jiyo masa kururuwar da Rahane ke
zabgawa. Shi da Ibraheem suka runtuma cikin gidan ba tare da sunyi wata maganar ba.

A lokacin Ado ya kaita kasa, dan kamfai ne kawai a jikinta. Ga Malam Rashidu a gefe
dunkule wuri daya yana ta kwararar da hawaye sai tsima yakeyi ko uffan bai ce ba.
Ibraheem ya danko kwalar rigarshi ya finciko shi ya hada shi da bango, ya dunkule hannu ya
sauke a bakin Ado, sai ga hakora biyar sun zubo, jini ya biyo bayansu. Ya tankada shi tsakar
gidan da doguwar kafarsa.
A lokacin jama’a makota har sun cika gidan, shi kuma Daddy waya ya yiwa ‘yan sanda nan
da nan sai gasu a (shiga-ba-biya) suka danna Ado a ciki, jama’a na ta sallallami ganin Malam
Rashidu daga shi sai gajeran wando gaba daya ya fita hayyacinsa ya zama dan tsurut. Jikinsa
ba masaka tsinke da tambarin bulala. Rahane na gefe ta kankame jikinta tana ta kuka.
I.M Takai, ya ciro suit din dake jikinsa ya rufa mata, don ta kare tsaraicinta.
Nan Malam Rashidu ya matsa gaban Rahane ya saka kuka. Cewa yake

“Ina Iya Rahane?”

Jama’a makota suka soma cece-kuce kan cewa yau sati biyu kenan basu sa Malam Rashidu
da Rahane a idanunsu ba, sun dauka ma barin garin suka yi ba tare da sun yiwa kowa sallama
ba.
Dr. Mansur ya ciro malun-malun din da yake snaye da ita ya sanyawa Malam Rashidu. A nan
ya soma gaya musu yau sati uku kenan Ado ya kulle shi yana azabtar da shi a kan sai ya fada
masa inda ya kai Rahane don kar ya bashi aurenta. Bayan shima bai san inda suka tafi ba ita
da Iya. Kowa ya ce, “Ado zai aikata fin haka. Allah ya saka masa”.
Dr. Mansur ya ce, “Sunyi hatsari ne ita kadai ta sha aka kaita asibitin su, Allah ya yiwa Iya
rasuwa tare suke da gawarta”.
Malam Rashidu ya rikice da kuka shi yana yi Rahane na yi. Jama’a na ambaton “Innalillahi
wa’inna ilaihir raji’un! Allah ya ji kan Iya Bilki, Allah ya yi mata rahama”.
Kan ka ce meye wannan jama’ar Takai ma’abota kara da hadin kai sun cika kofar gidan. Tare
da Dr. Mansur da I.M aka sallaci Iya Bilki, aka dauketa zuwa gidanta na gaskiya. Dacta da I.M
suka wuce gidan Hakimin Takai.

Dr. Mansur dan asalin garin Takai ne. Da shi da Mai-Martaba Hakimin Takai cikinsu daya, sai
dai shi Mansur dan boko ne na a buga a jarida, kwata-kwata baya sha’awar sarautar tasu, ko
zaman garin su sai dai ya zo da ziyara, yana Kano tare da iyalinsa. Shekararsu goma a kasar
Ireland suna karatu shi da mahaifiyar su Ibraheem (Asma’u) wadda ‘ya’yanta suke kira (Mami). Mami ‘yar asalin garin Jos ce, (arnan Jos), a da, bata da addini, sunanta (Anita Shiyana). Sun
hadu da Dr, Mansur a jami’ar TRINITY dake (Dublin). A hannun Mansur ta karbi musulunci ta
kuma rike shi da kyau, ya sanya mata sunan mahaifiyarsa (Asma’u) wadda ta dade da rasuwa,
don haka shima Mamin yake ce mata. Mami cikakkiyar likitar yara ce (paediatrician) da ta san aikinta. Duka yaransu biyar, kowane
da rata sosai tsakaninsa da wanda yake bi a haihuwa.
Rayuwar Mami zallanta na (Irish) wato na mutanen Ireland ne, ga masifar son ‘ya’ya. Ba ta
son kowa ya rabe su, daga ita sai ‘ya’yanta sai mijinta. Sabanin mijin, Dr. Mansur mutum mai

kara da kawaici, ga faram-faram da mai da kowa nasa, ga son zumunci da muhimmanta shi. Ga
son mutane da saukin kai,

Tunda ya shigo gidan Hakimi tunanin Rahane da Babanta yake, da yanayin ban tausayin da
ya baro su a ciki. Suna hira da dan’uwansa Hakimi Abdullahi Takai, amma ya lura sam hankalin
dan’uwan nasa baya tare da shi.
Ya yi gyaran murya “Wani abu ya faru ne Mansur?’
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce, “Wani abin tausayi nake tunani, Allah ya ja da ran Hakimi”.
Ya warware masa komai. Shi Hakimi bai san su ba. Ya ce, “Yanzu da kasa kanka cikin dogon
tunani irin haka me kake ganin za ka iya yi a kansu? Talakawa fa na da yawa a kasar nan, ba
su kenan ba, kuma ba za su kare ba”.
Dr. Mansur ya girgiza kai ya ce, “Allah shi ya hada jinina da wannan yarinya, zan tafi dasu
Kano. Shi ya yi min aikin gadi, ita kuma yarinyar zan hadata da su Abida in dau nauyin iliminta,
don da ganinta ba haka Allah ya yi nufin barinta ba!”.
Hakimi ya girgiza kai, jin yadda yake maganar (with confidence) kuma tun daga karkashin
zuciyarsa “Ka tafi da yarinyar kawai, ka bar min uban a nan za sa a kula da shi. Daman kuma
sarkin Dawaki ya rasu, ina neman nitsattsen mutum wanda zai jure hidimar Dawakai na babu
lalaci har na baza cikiya a cikin gari. To ka san halin talakawan namu basu yarda su rabemu saboda gudun wulakanci, na shaidi
jama’ar Takai a nan”.
Dr. Takai ya ce, “Hakan ya yi, na ji dadi sosai Yaya. Bari in tura Ibrahimu ya zo dasu”.
Ya dauko waya ya kira I.M ya ce, “Daddy ina barga tare da Dawakan Mai Martaba”.
Ya ce, “Daure ka zo maza, ko da yake ba sai ka dawo ba, ka je ka zo min da yarinyar nan da
mahaifinta yanzu. Ina tare da Hakimi”.
Ya rausayar da kai ya ce, “Daddy why me (me yasa sai ni)?”
Doctor ya ce, “To wa ya san gidan idan ba kai ba?’
Yana daga cikin mota yana kallon yadda jama’a ‘yan zaman makokin Iya suka cika harabar
gidan, yana daga cikin motar bai fito ba yana ta shan kamshi da jan numfashi.
Can kuma ya yafito wani saurayi ya ce don Allah ya daure ya zo masa da Malam Rashidu da
‘yarsa, ya sanar dasu wadanda suka kawo yarinyarshi daga Kano ne suka aiko shi ya tafi dasu
inda suke (gidan Hakimi).
Mutumin ya juya ya doshi gidan. Shi kuma I.M ya ci gaba da zama cikin motar yana kallon
rusasshiyar kofar gidan. Cikin ranshi yana kissima abubuwa daban-daban, ko neman me kuma
Daddy yake wa muten nan bayan taimakon da suka yi musu, me kuma zai yi musu oho!
Bai gama tunaninsa ba ya hango Malam Rashidu tafe yana rike da hannun Rahane wadda
duk aka kwailewa ciwonta dake cikin bandeji jini sai zuba yake.
Ji ya yi tsigar jikinshi ya tashi, don bai son ganin fitar jini daga jikin dan Adam ko kadan. Tun
kan su karaso ya tada motar, ya mika hannu ya bude musu kujerar baya suka shiga ya ja motar
suka tafi ko uffan bai ce musu ba.
Tsakanin gidan Malam Rashidu da gidan Hakimin Takai akwai tazara sosai, Malam Rashidu
bai taba zuwa gidan Hakimi ba sai yau.
Tun daga soron farko ya tube takalmansa ya rungume, ita kuwa Rahane a hannu ta rike
abinta, tsaf take cikin nutsuwarta. Ibraheem bai tsaya dasu a ko’ina ba sai a falon da Doctor

Mansoor da Hakimi suke zaune.
A nan ya tube nashi takalman suka shiga. Idon Dacta Mansoor a kan kunnen Rahane, bai ga
hearing-aid din da suka makala mata ba. Ya juya ga Malam Rashidu ya ce, “Ina abin da ke
makale a kunnen Rayhanatu?’
Malam Rashidu wanda ke ta kwasar gaisuwa gurin Hakimi ya juyo ga Dacta Mansoor ya ce,
“Eye? Na’am?”
Dacta Mansoor ya ce, “Akwai karamar na’ura makale a kunnenta sanda muka zo, ina take?”
[12/24/2019, 17:56] Takori: Malam Rashidu bai wani fahimce shi ba sakamakon wani suna da
ya ji ya ambata wai Rayhanah, sai ya dauka ba da shi yake ba.
Haushi ya bala’in kama Doctor Mansur ganin Malam Rashidu ya saki baki yana kallonshi
kawai bai ba shi amsar tambayar shi ba. Shi dai Mal. Rashidu tun dazun yake ta yiwa Rahane
magana bai ji ta ba shi amsa ko daya ba, sai ya dauka duk cikin halin rasuwar Iya ne. Bai kawo
wani abu daban ba. I.M ya dubi mahaifinshi ya ce, “Ina ganin sanda mutumin banzan can ya cafketa hearing-aid
din ya fadi”.
Dacta Mansur ya ce, “Maza ku koma ku dubo”.
Malam Rashidu ya ce, “Ranka ya dade me zan dubo?”
Ya dubi Ibraheem ya ce, “Ka tashi ka je ku dubo na ce”.
Ibraheem ya cika fam, kiris yake jira ya fashe. Ya mike suka fito falon shi da Mal. Rashidu
kamar ya shake shi don takaici. Shi bai ga dalilin da zai sa Daddy ya daura masa al’amarin
talakawan nan ba, babu dangin iya babu na baba.
A guje ya fizgi motar suka koma gidan Malam Rashidu, dakin Iya inda akai gumurzun
Rahane da Ado suka yi ta dubawa har Allah ya bawa Mal. Rashidu sa’ar ganin dan injin a
bayan randar Iya.
“Wannan ne?” Ya tambayi I.M. Karba kawai ya yi ya fice bai ce da shi ko uffan ba, ya yi gaba
ya bishi a baya. Suka koma gidan Hakimi.
Dacta Mansur ya karba ya bude ya canza batir wanda dama yana cikin aljihunsa ya matsa ya
makalwa Rahane ‘yar na’urar a bayan kunnenta.
Ya ce, “RAYHANAH!” ta dago ido a hankali ta ce, “Na’am Baba Dacta”.
“Za ki bini gidana in sanyaki cikin ‘ya’yana ko za ki zauna da Babanki a nan gidan Hakimi?
Daga yau Babanki ya dawo nan za a ba shi aikin yi da kyakkyawan muhalli”.
Ta juya ta dubi Babanta wanda ya zaro ido yana kallon su. Dacta Mansur ya dube shi ya ce,
“Ka amince in rike Rayhanah har illa masha-Allahu a Kano?” Ya girgiza kai ya ce,
“Aure zan yi mata!”.

Gaba dayansu suka dube shi sosai har Rahanen. I.M ya mike ya fice a ranshi yana yiwa
Babanshi Allah ya kara. Haka kawai don bala’i da kwashe-kwashe zai kwaso musu wasu shirgin
kauye babu gaira babu dalili. Ai gara da uban nata ya gwale shi, ya yi tafiyarsa cikin gida.
Hakimi ya karbi Dacta Mansur wanda ya yi mutuwar zaune ya ce, “Yar wannan yarinyar za ka
yiwa auren? Wa za ka aura mata? Wa ya ce yana sonta?”
Mal. Rashidu ya ce, “Ku yi hakuri don Allah, na gode da taimakon ku garemu ba wai ban
gode ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login