Showing 18001 words to 21000 words out of 33002 words

Chapter 7 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf


Komawa ya yi cikin kujera ya zauna, ita ma Mamin haka, dab da shi ta zauna.

“Idan ma’auratan suka samu kuskuren fahimtar juna, kowanne zai bi bayan bangarensa ne.
Sai ki ga su ma’auratan har sun manta sun shirya a tsakanin su amma abin zai yi ta zama a
zuciyar iyayen nasu, a dinga kallon juna da shi. Daga nan zumunci zai baci, kin ga garin hada
zumunci an lalata shi. Irin zumuncin da na taso na gani tsakanin Mai martaba Hakimi da Daddy ban taba ganin irin
sa ba. Bazan yardain zamo sanadin da zai yi tuntube ba ko kankani. Ina son yadda suka faro
shi suna yin sada gaskiya su cigaba da yin sa har karshen rayuwar sub a tareda mun samar da
tangarda a cikin sa ba. Idan na auri Nabila ko laifi tayi min bazan iya hukuntata ba, zan yi ta yi mata uzuri da Baba
Hakimi, haka shima ko wacce irin cuta zan yi mata bazai tada kai ba balle ya kalla, nikuma
yadda bana son a danne hakkina haka bana danne hakkin kowa. Don haka auren zumunta
baya cikin tsarina, don a ganina auren mugunta ne kawai.”. Murmushi ta yi ta ce, “Hujjarka is invalid. Kai dai kawai ka ce baka ra’ayin Nabila, don in kana
sonta har zuciyarka ba za ka tsaya yin la’akari da wadannan kananan abubuwan ba”.
Ya ce, “To Mami maganin kada a ji, kada a yi”.
Ya mike ya fice ta bishi da idanuwa. Sannan ita ma ta mike ta soma shirin tafiya ofis.

****
Kwanaki ke juyawa a hankali su koma satittika, satittika su bada watanni, watanni su bada
shekara. Kamar yadda rayuwa take a kullum kenan, komai ma juyawa yake. A haifa, a mutu, a
girma, a tsufa.
To hakan ce ta faru da Rayhanah, shekarun girma sun soma juyata daga kwaila zuwa
matashiyar budurwa. Mai dauke da wasu ilhamomi da dama.
A yau Rahane shekarunta goma sha hudu, sun kammala karamar sakandire a Darul-Arqam
suna jiran fitowar jarrabawarsu (placement) don wucewa babbar makaranta.
Shekaru biyu kenan da wucewar Ibrahim Jami’ar Chicagon Amurka, inda yake fafutukar
kwalin zama cikakken (nephrologist) likitan koda. Yayin da Khalipha tuni ya kammala bautar
kasa ya fara aiki da Ministry of External Affairs dake Abuja.
A yanzu idan kika ga Rayhanah zai yi wuya ki shaidata farat daya. Ta saje da ‘ya’yan Baba
Dacta, fari kawai suka fita, sai fatarta ta ba da wata irin kala ta wankan tarwada mai sheki,
jikinta ya fara cikowa ya nuna ilimi da hutu zallah.
Lokacin da jarabawarsu ta fito, kowacce makaranta daban ta ci. Amma Baba Dacta sai ya
tattarasu su duka ya kai su ULUL-ALBAAB (Science Secondary) dake Katsina. Azizah ce ta ci
gaba da Darul Arqam.
Har zuwa inda yau ke motsi, Abida bata daina cuzgunawa Rahane ba, musamman da aka
mai da su nesa da gida babu Baba Dacta balle Khalipha.
Jawahir kuwa dama ta riga ta rainata kamar ita ce babbar. Haka take fadawa ‘yan ajinsu da
‘yan hostel dinsu Rayha ‘yar matsiyata ce ta zo ta makale musu, Babanta na kauye ya asirce
babansu ya lika musu ita.
Sannan a gaban Raihan take fada, don ba tsoron Jawahir take ba. Uffan ko daga ido
Rayhanah ba ta yi balle ta yi magana. Son Abida take bilhaqqi, saboda darajar iyayenta da
Yaya Khalipha.
Khalipha wani irin mutum ne mai matukar tasiri da alheri cikin rayuwar Rayhanah, ko kadan

baya son ya ganta cikin rashin walwala. Duk da dai dama ba mai walwalwar ba ce. Abubuwa
iri-iri na gilmawa a zuciyar Khalipha a kan Rayhanah, yarinya ce da ta iya takun rayuwarta
matuka, ta kuma iya tafiyar da mutum da halinsa.

Abubuwa da yawa kan sa a so mutum, muhimmi shine halayensa ba kyan sura ba. Rahane
mai aji ce (classique). Duk da tushenta shine kauye. Ba kyakkyawa ba ce, sannan ba ta da wani
abu mai fizgar hankalin namiji banda halayenta. A fuska kam babu kyan, amma a halittar jiki sai
an tona cikin dubu kamin a samu goma irin Rayhanah. Ba ta damuwa da lallai cewa sai ta sanya hearing aid in ba lokacin daukar darasi ba. Sai ta yi
kwanciyarta shiru a kan gadonta, ta yi ta tunanin makomar rayuwarta.
Wato yanzu da Rahane ta kara shekaru, sai ta kara sanin ciwon kanta. Baba Dacta da Mami
ba jininta bane, ba ta da kowa da za ta bugi kirji ta ce nata ne banda Babanta. Wanda ke ta
fama da kansa a halin yanzu, yau ciwo gobe lafiya ba a san hakikanin abin da ke damunsa ba.
Ranar da Baba Dacta da iyalinsa suka gaji da rikonta, ina za ta je? Tsufa ya soma cimma
Malam Rashidu. A zahiri babbar matsalar ciwuwwukansa kenan, ta fahimci cewa ita din abin
tausayi ce. Karatun nan da Baba Dacta ya tsaya mata take yi shine kadai madogararta sai
Ubangijin Talikai. Duniya ba matabbata ba ce, haka komai na cikinta yana da lokaci. Ta fahimci akwai ranar da
dole za ta bar hannun Baba Dacta da Mami tunda ba su suka haife ta ba.
Ranar da hakan ta faru ina za ta? Takai?
Ai ko gida basu da shi a Takai. Babanta babu lafiya ga tsufa, ta kowanne bangare idan ta
duba sai ta ga kawai Allah ne gatanta sai yadda ya ga dama zai shirya mata rayuwa.
Wani tunani ne ya fado zuciyar Rayhanah farat daya, zuciyar ta ce AURE! Rayhanah ki yi
aure ki samu ki kafa naki iyalin ki yi tabbatacciyar rayuwar iyali. Ki haifi ‘ya’yan da za su rungumi
rayuwarki wata rana.
Amma abin tambayar a nan shine, wa za ta AURA? Wane ne zai iya aurenta da LALURAR
ta? Wane miji ne zai juri cewa sai matarshi ta saka inji kafin ta ji magana? Wane ne zai ba ta
kwarin gwiwa irin wadda Khalipha ke ba ta? Wane ne mai kirki irin Khalipha?
A cewar Abida ita MUNAFUKA ce, son Yaya Khalipha take yi, shi yasa ta damu da shi fiye da
kowa a gidan. Idan ita MUNAFUKA ce don tana son mai kyautata mata, ita kuma da take
tozartata a bayan idon Khaliphan yaya sunata? They are all the same kenan ko?
Kwata-kwata ma ita ba ta san wane irin so Abida ke nufi ba, don ta kan ce ya fi karfin ki.....ba
ajinki bane.....me zai ci dake? Ya yi kama da mai saran kofaton Doki ne? Da sauran maganganu
irin wadannan wanda inda sabo, to RAYHANA ta saba jin ire-irensu daga bakin Abida.
Abida ta fi Jawahir power, ta fita baki, ga tsiwa, ga rainin wayau. In ta raina mutum ya shiga
uku. ‘Abida Hukuma’. Sunanta kenan in ji Khalipa, domin duka baya karya mata zuciya sai dai
ma ya kara tunzurata ga abin da ake dukan nata a kansa. Ya kara kangarar da zuciyarta a
kansa.
****
Wani abu da ya kara ta da ma Abida hankali a kan Rayhanah shine, kokarin da ta zo ta fita
sakamakon wasa da tsokanar da ta sawa ranta.
Sunyi jarrabawar shiga aji biyar, Rayhanah ta kwace 3rd position na ajin wanda Abida ke kai

tun farkon shigarsu Ulul-Albaab, ita kuma ta kwaso na goma.
Sun zo gida hutu ranar Asabar, a yammacin ranar ne Khalipha ya iso, sanye yake da ‘yar ciki
da wando har da babbar riga na wata danyar shadda (sheraton) kalarta coffee wato ruwan
kasa. Ya dora hula damanga a kan goshinsa, daman dai Khalipha ba dai iya karya karin hula
ba, ita ma ruwan kasa ce. Takalmin fatar damisa ne a kafarshi budadde wanda kudinshi ya haura naira dubu ashirin,
Dattijon, daure yake da agogon polo na fata a damtsen hannunsa launin kayan jikinsa.
Shigarshi reception rataye da babbar rigarsa a kafudunshi da wata karamar bakar jaka mai
dauke da komatsansa masu muhimmanci. Da sassarfa ya soma taka steps don cimma falon sama, sai suka yi karo garam! Da goshinsu
shi da Rayhanah.
Goshin nasa ya kama ya ce, “Kai-kai-kai! Rayhanah goshi za ki fasa min in rasa matar aure?”
Ita ma ta kama nata goshin cikin irin muryar zolayar da ya yi mata maganar da ita ta ce,
“Kai Yaya Khalipha, kai ne fa ka kara mini”.
Ya bita da idanu luuuu! Wani chemistry ya yi aiki cikin ‘yan dakikai. Ba ta taba ganin irin
wannan kallon da Yaya Khalipha ke mata yanzu a idon kowa ba, ji ta yi ba za ta iya jurewa
kallon ba don haka ta yi saurin dauke idonta ta rabe ta gefensa za ta wuce, sai ji ta yi ya riko
hannunta ba tare da ya juyo ba. Mintuna uku suka dauka a hakan, ta yi saurin zame hannunta da sassarfa ta karasa sauka
daga matattakalar zuwa aiken da Mami ta yi mata wajen Mal. Dahiru maigadi.

Tun daga wannan ranar Rayhanah ta samu kanta da matsananciyar kunyar Khalipha, ba ta
kara bari ya ganta ba, in ta jiyo muryarsa a falo ba ta fita. Shi kuma dama tuni ya daina shiga
dakinsu, tunda suka dan tasa. Balle yanzu da suka zama ‘yammata ko yau aka yi musu aure
gobe za su haihu. Ya damu kwarai da ya ganta, don haka yake yawan zaman falon amma ko keyarta babu.
Mami da Dacta sun je wata seminar likitoci a kan cutar Shan Inna a kasar Algeria, daga ita sai
Abida ne a gidan, don Jawahir ma da Azizah suna Jos. Har ya kammala week end dinsa ya
koma Rayhanah na mishi boyo.
Khalipha Mansur, zaune a ofishinsa yana shigar da wasu sakonni cikin kwamfuta zuwa
Nigerian Embassy Accra (Ghana). A kan zuwan Ghanain President (Rawlings of Ghana),
wanda zai zo Nigeria cikin satin ya haura Philippines daga Nigeria suka samu matsalar visa za
su fito daga kasar Kenya. Haka nan ya ji aikin ya gundireshi. A dan tsukin nan tunda ya dawo daga gida, ya rasa gane
kansa, ya kasa gane me ke damunsa.
Gaba daya ya tattaro hankalinsa da tunaninsa wuri daya. Ya zubawa tafin hannunshi ido, a
hankali kuma ya kai shi hancinsa, still kamshin Escada Sentiment yana nan bai gushe ba,
domin ko da ya zo wanka bai yarda ya wanke hannun ba, kada ya daina kamshin turaren
RAYHANAH. Khalipha, duk da cewa yana kan gabar kuruciyarsa, kuma a kan matakin da babu macen da
ba za ta so shi ba. To fa ba kowacce mace yake kallo da kima ba har ya taba yiwa kansa
sha’awar aurenta, mata iri-iri kam ya yi mu’amala dasu tun zamanin yana karatu, anyi abokai

cikinsu an kuma yi ‘yammata, sai dai kuma babu wacce mu’amalarsu ta kai labari tsahon
shekara daya za ayi hannun riga, don shi bai yarda yana neman yarinya wani ma yana nemanta
ba, daga ranar da ya gane hakan duk son da yake mata ya barta kenan har abada.
Hibba kuwa da Hakimi ke son ya aura, har ta gaji da jiransa ta kama dahir, yanzu haka har an
sa mata rana. Saboda tamaula da hankalin da yake mata.
Da fari ya ce karatu, ta jira shi ya karasa, ya dawo ya ce Bautar Kasa. Nan ma ta jira shi. Sai
kuma ya dawo ya ce sai ya fara aiki, ta jira shi har ya samu. To fa kuma tunda ya fara aikinsa,
bai kara bi ta kanta ba, ita kuma ta ga ba rasa manema ta yi ba zai sa ta tsofe a gida alhalin
kuma ba shi da niyyar auren ta. Don haka ta yiwa kanta ludufi ta dauki na damo, ta bar Nabilah
da koshin wahala......
Yau shekara guda kenan da kammala karatunsu amma tana nan tana jiran Ya Himu, wanda
tunda ya cilla kafa a Chicago ba a kara jin duriyarshi ba, ko waya ba sosai yake yi da jama’a ba,
idan ya gaisa da Hakimi sai ya ce a gai da kowa.
Sannan ba shi da takamaimiyar lambar waya, wani zubin ma a bakin hanya zai tsaya ya sa
(credit card) dinsa a commercial ya kira wanda ya ga dama ya zare abinsa.
Kowa na kokari a kan Nabilah ta yi hakuri da Ibraheem amma sai tasa musu kuka. Hajiya
Karima kan ce, “Nabila ki yiwa kanki fada ki zabi daya cikin masu sonki ki aura tun tauraruwarki
ba ta dishe ba.
Kuruciyar ‘ya mace ta dan lokaci ce, shekarunki ashirin da bakwai ga kwalin digiri ga na
master, kina tunanin idan Ibrahim ya dawo yadda yake ji da kuruciyar nan zai aure ki? Wallahi
shi a lokacin ne zai fara samartakarsa, Juma’ar da za ta yi kyau tun daga Laraba ake gane ta”.
Nabila sai dai ta hura hanci ta zumburi baki, ko me za a ce in dai a kan Himu ne ta bayan
kunnenta yake wucewa.

Khalipha ya yi baya da lallausar kujerarsa, ya bi jikinta ya kwanta ya lumshe ido. Abubuwa da
yawa ke sawa ya so mace, amma ba kyan fuska da kyale-kyale ba, dukiya ko zuzzurfan ilimi.
Yana son mace wadda ta san kanta (mai tsare gida da rashin kula maza). Kuma yana son ta
kasance mai aji ba kyakkyawar da kowanne karabiti zai biyota a dalleliyar mota ya ce yana
sonta ba.
Yana son mace mai kunya, wadda ba ta iya hada ido da namiji in ba dole ba. Mai karancin
magana, ba wadda za ta zauna cikin mutane ta yi ta zuba kamar ‘ya’yan kanya ba.
Baya son mai alfahari da son nuna iyawa, baya son mai gwalli da kwarkwasa, baya son
wadda za ta cika fuska da jan baki, eye shadow da su maskara da hoda. Baya son wadda za ta
rambada ‘yan kunnaye da sarkoki bula-bula (Barima da hudar hanci sun isa). Baya son mai
hasken kanti, sai baka mai gogaggiyar fata tunda shi fari ne sol, wadda ba mai ne ya gogeta ba,
irin yanayin da take ciki ne.
To amma ya hanga ya duba cikin mata bila adadin bai ga mai wadannan extraordinary
characteristics din ba sai RAYHANAH, bai taba jin yana so ya yi aure ba sai yau. Ba kuma da
kowa ba da ita kadai Rayhanan Baba Dacta. Hannunta kawai ya kama (by mistake) a ranar ya
tuna cewa ashe shima NAMIJI ne mai bukatar mahadin rayuwa. Lokaci daya kuma lalurar Rayhah ta fado mishi a rai LOVE HAS NO BARRIER ( soyayya
bata da shinge). Hasali ma Ji ya yi lalurar tace tun farko ta dasa tausayin ta a zuciyarsa, wanda
yayi ta rikida har yau daya bayyana ainahin kalarsa; daga tausayi zuwa kauna.

Lalurar ce kuma har ila yau, da tsantsar hakurin ta akanta da komai ma na rayuwa ta sa ya
kara sonta da tausaya mata. Ya ji wani bangare na zuciyarsa na gaya masa kai kadai ne za ka
aure ta ba tareda lalurar tat a dame ka ba, ka zauna da ita cikin kowanne hali. Tana da lafiya ko
bata da lafiya. Ka tallafi maraicinta, ka tallafi kanka ta hanyar samarwa zuciya abin da take so, in addition ka
samawa ‘ya’yanka uwa ta gari, ka kuma mallaki ragamar rayuwarta da ita kanta Rayhanah.
Ya lumshe ido a hankali ya koma ya jingina da kujera.

****

Duk yadda ya so ya je gida a satin hakan bai samu ba, sai da ya gyara matsalar visar
Rawlings daga Nigeria zuwa Philippines. Kawai so yake ya yi tozali da Rayha.
Duka kannenshi akwai hotonsu cikin wayarsa, Raihahn ce kawai babu. Ya dokantu, ya jigatu
a tsayin satin gaba daya da son ganin Rayhanah.
Ranar Juma’a da daddare Mami na zaune gaban madubinta tana shafa bayan ta fito wanka.
A gefen ta Rayhanah ce take jera kayan Mamin da aka kawo daga wanki a sif din Mamin.
Doguwar riga ce ruwan bula a jikinta da farin Hijab mai santsi iya kafadunta, sallamar
Khalipha a falo suka ji yana fadin “Mami na!”
Ta ce, “Ina zuwa”.
Ta karasa shafar ta sanya kaya tana ce da Rayhanah “Dan hayaniyar nan ya iso yau
kunnuwanmu ba hutu”.
Ai da jin haka Rayhanah ta lallaba ta shige bayin Mamin ta rufe kanta ta yi zamanta a kan
kwamin wanka tana kokarin daidaita numfashinta.
Khalipha ya zame mata dodo, ita kanta ba ta san dalili ba, zuciyarta na jigatuwa a duk lokacin
da ta tuna shi. Wannan ya fara ne tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login