Showing 24001 words to 27000 words out of 33002 words

Chapter 9 - Rayuwar Raihana Part 1 chapter A Complete Hausa Novels.pdf

dauke ta tana goge mata jinin dake fita daga bakinta. Mami na ta
fada za su kashe mata ‘ya sai ka ce yau suka fara ganin Khalifan. Amma ko jin ta basu yi ba
balle su tsaya. Sai da suka dangane ga dan’uwansu suka rungume shi.

Khalipha na zaune ne a kan kujerar zaman mutum biyu, gwangwanin Maltina ne a hannunsa
yana sha, amma saboda rungumar bazata da kannen suka yi masa gwangwanin ya fadi ya
zube a cinyarsa.
Farin kaftan nashaddah (hilton) ne sol a jikinsa dinkin Mohammed, amma haka suka wanke
shi da Maltinar. Hakan bai sa ya yi fushi ba, surar Azizah ya yi daga hannun Rayhanah ya yi
sama da ita ya cilla ya cafe.
Ya ce, “I’m missing you.....”
Ya hadasu ita da su Abidar ya rungume gaba daya yana durkushe dai-dai tsahon su. Ba tare
da ya ankara da bakuwar fuskar dake gefe ba.
Ita Rahane daki ta wuce don ta ga hankalinsa na kan kannenshi ko ta gaishe shi ma ba jinta
zai yi ba, ta ce bari ta bari sai ya nutsu sai ta gaishe shin.
Khalipha bai samu kansa daga hayaniyar su Azizah ba sai da aka kira sallar magariba. Ya
mike dauke da Azizah ya kawota dakin Mami, lokacin ita Mamin tana shirin yin sallah ta wuce
asibiti, don yau ma aikin kwana za ta yi.
A gadonta ya dire Azizah ya ce, “Mami Dactan nan (Himu) ya bar miki mukullin daki ne?”
Ta ce, “Ka duba yana jikin kofar”.
Ya rungumeta ta baya ya daura kai bisa kafadunta ya ce, “You didn’t miss me Mami.....”
Ta ce, “Sai in yi ta rawa ina tsalle ka dawo sannan ka yarda na yi kewarka”. Dariya ya yi ya
juya ya fita.
Wanka ya yi, sannan ya daura alwala, ya zuba wata shadda kaftan ruwan kasa. Khalipha
Mansur baya sanya kananan kaya sam, sai shaddah, yadi ko jallabiyar Saudi ( in a gida ne). Shi
yasa Mami ke kiranshi (Dattijo) a yawancin lokuta.
Daga kallo na farko da ka yiwa Khalipha za ka gane mutum ne mai faram-faram da
haba-haba da jama’a (sociable) sabanin Ibrahim (anti-social in nature).
To haka a kamanni da sura, Khalipha Mami ne sak, fari sol da shi, ga tsayi ga zati. Kwayar
idanunshi ba baka ba ce (brown) ce mai sheki. Da ka ganshi ka ga Mami. Kamar ta yi kaki ta
tofar.
Khalipha na da kirkin da Ibrahim bai da shi, ko daga mu’amalar kauna bayyananniya dake
tsakaninsa da kannensa, wadda basa samu daga Himu ko kadan. Don haka suma basu dauke

shi da wasa ba, suna bala’in kaunarsa.
Ya damu dasu suma sun damu da shi sosai ba kadan ba. Daga sanda ya zo gidan Mami da
Daddy sun huta da koyar da yara aikin makaranta. Ya hada digiri dinshi mai daraja ta daya daga
Jami’ar (BAZE) a kan hulda da kasashen ketare, sai jiran posting din Bautar Kasa.
Yadda kamanni da halayya suka sha ban-ban tsakanin Himu da Khalipha, haka dabi’u da
akidu. Khalipha dattijon ne da gaske, yaro mai halin manya. Don haka shi kansa Daddyn ma
sau tari kan kira shi da (Dattijo).
Bayan sallar isha’i duk suna bisa tebir kamar yadda yake a al’adarsu. Rahane ta fito jaye da
hannun Azizah, tana ta rigima duk hancinta ya toshe da mura. Rahane sai aikin share mata
hanci take da hawaye duka, da guntun tishu dake hannunta.
Ya dan juya ya dube su jin Mami na fadan a daina kunna A.C da daddare tunda ba lokacin
zafi ne ba. Ya dan kara juyowa sosai ya kalli yarinyar don a da ya yi zaton idonsa ne bai gani
sosai ba, ya dubi Mami ya ce, “Ina kika samo ‘ya?”
Ta ce, “Allah ne ya bani”.
Kamar zai yi magana sai kuma ya yi shiru ya ci gaba da cin abincinsa. Don ya ga bai kamata
ya ci gaba da yiwa Mamin tambayar a gaban yarinyar ba.
Rahane kujera ta hau kusa da Jawahir, don ko kadan ba ta zama daf da Abida, sakamakon
kisan mummuken da take mata, ‘yan yatsunta take murjewa da kafar kujerarta, ko ta faki idon
kowa ta takata da tsinin takalminta da take sawa musamman don muguntar. Iyakaci a ga tana
kuka in sun koma daki, tambayar duniyar nan Jawahir za ta yi amma sai ta ce babu komai Iya
take tunawa.
Sai dai kuma ta yiwa kanta maganin abun, ta daina yarda ta zauna kusa da ita. Wanda hakan
bai yiwa Abida dadi ba, don dai ita nan duniya babu wanda take jin haushi irin Rayhanah.
“Zauna mana Rayhanah”. In ji Mami.
Ta zauna sosai ta fara cin abincin da Mamin ta yi serving dinta. Sakwara ce da miyar
alayyahu da ganda da kifi, musamman don Khalipha Mamin ta yi girkin da kanta, don nan
duniya ba abincin da Khalipha ke so irin sakwara.
Sunanshi na ainihi sunan mahaifin su Mami ne da ya Musulunta wato (Abdallah). Dacta
Mansur da bai iya fadi a matsayin sunan na sirikin sa mai rasuwa shine yake cewa Khaliphan,
to sai kowa ya kama. Abdallah ta bace bat, sai Khalipha.
Da kyar Rahane ta iya cin abincin nan saboda kallon ta da Khalipha ke yi jefi-jefi. Ga kukan
Azizah ya dameta, jinsa take har cikin ranta. Ko kadan ba ta son kukan yarinyar.
Garin kallon nashi ne ya hango aid din dake makale bayan kunnenta. Ya zare gilashin shi a
hankali yana kara kalla ya ce, “Mami bakuwar taku ba ta ji ne?”
Ta bata fuska ta ce, “Wai kai Khalipha baka gani ka yi shiru ne sai ka ce dan jarida?”
Ya maida gilashin sa yace, “Sorry Mum, I’m curious in cases like these….!”.
Ta ce, “Iftila’i na rana daya, sun samu accident ne shine sanadi”. Yace “ta yaya accident zai
zamo cause to hearing impairment? Ku dai kara bincikawa, haka kawai ma ji kan dauke, mostly
as a result of typhoid fever ko meningitis, ko kuma hereditary factor (gado) na amosanin kunne
(otesclerosis)”. Mami tace “to Dr. Khalipha, babu daya kanwar biyu, professionals basu ga hakan ba har sai sun
gudanar da CT Scan and MRI Scan wanda abune dake neman naira miliyan biyu cash. Kuma
ba’ayin shi a Nigeria.

Mahaifinta kuma ya tabbatar lafiyar ta kalau ta baro gida kamin suyi hadarin kuma bata gada
daga ko’ina ba (uwa ko uba)”.
Ya mikawa Rahane hannu wadda ta sunkuyar da kai......
“Shake my hands, Rayha.....”
Murmushi ta yi amma bata bashi hannun ba.
Ya ce, “To shi kenan tunda bakya abotar dani”. Ya fada cikin launin shagwaba da langabar da
kai.
Ba ta san sanda ta yi dariya ba, fararen hakoranta yiri-yiri farare sol suka bayyana. Babba
dashi yana shagwaba a gaban mamarsa.
Ya ce, “Do not your problem slow down, you will achieve a lot in life!”
Ita bata ma ji mai ya ce ba saboda yadda harshensa ke harde da Turanci gangariya, sai
gwani a harshen ne kadai zai iya fahimtarsa.
Wannan ya samo asali ne da haihuwar Khalipha da Himu da Mami ta yi a Ireland (Dublin).
Inda Khalipha ya yi karatun shi har zuwa aji biyar na sakandire kamin su tattaro su dawo
Nigeria.
A haka aka kare cin abincin. Koyarwar Yaya Khalipha daban take, ko yaro shine jaki wajen
dakikanci dole ya gane koyarwar Yaya Khalipha.
Da ya zo kan littafin Rahane, ya gane Rahanen na da rauni a lissafi (Mathematics) don haka
ya tabbatar ta yi a gabansa dai-dai sannan ya kyaleta.
A daren ne Mami take ba shi labarin Rahane, ya saurara da nutsuwa. Yana tsaye jikin
balcony na dakinsu yana kokarin kunna Marlboro da lighter ya hango Abida ta fizge hearing aid
din Rayha ta yi cilli da shi tana cewa.
“Banza ‘yar kauye, wadda bata ji said a inji, ai sai ki ji mu gani”.
Da gudu Rahane ta bishi inda ta yar ta dauka, sai ta ga ya fashe. Abida ta gudu tana
kyalkyala mata dariya.
Durkushewa ta yi a nan tana kuka don ba ta san me za ta ce da Baba Dacta ba, domin ya yi
mata gargadi sosai a kan takula


da shi, ita kuma ba za ta iya ce da shi ga laifin Abida ba.
Da hanzari ya ajiye abin da ke hannunsa ya fito zuwa harabar gidan, tsugunawa ya yi gaban
Rahane ya karba yana gyarawa. Ido ta dago ta dube shi sai ta hau share hawaye da hanzari,
don bata so ya ganta tana kukan ba. Da ya gyara sai ya mayar mata ya ce, “Tafi gida”.
Tun daga ranar Khalipha ya sa ido a kan mu’amalar Rayha da Abida, Jawahir da kuma
Azizah. Ya gane Abida bata son Rayhanah sam-sam, komi ta yi sai ta kushe ta gwale, ta
wulakantata. Ya ci gaba da bibiyarsu da hankali, nan ya gane kaunar da Jawahir ke wa Rahane,
suna son junansu sosai, da kaunar da Rahane kewa Azizah wadda ta sayo mata kauna a
zuciyar Mami.
Tara Abida yake yi, bai yi kuma niyyar sanarwa Daddy ba shi zai yi maganin abin. Yau suna
zaune shi da Malam Dahiru maigadinsu a kan benci suna hira, su kuma yaran suna can wajen
shukokin grass-carpet suna wasanninsu ya hango Abida ta janyo mesar da ake bai wa shukoki
ruwa ta saki ruwan a kan Rayhanah, tun daga kanta har kafafunta ta jikata sharkaf, amma ko
uffan yarinyar nan bata ce ba. Ta ja mesar ta gudu da ta hango Jawahir na tahowa.

Tun daga ranar ya lura Rayhanah ta daina shiga cikinsu. Ba ma ya ganinta kwata-kwata.
Daga baya ya lura kullum tana daki ne kwance a gadonta lullube da bargo. Sai ta ji Mami ko
Baba Dacta a falo sannan take fitowa, amma ko abinci in basa nan ba ta ci.
Ganin haka shi kuma duk sanda zai ci abinci sai ya tura Azizah ta kirata, ya cika mata filet ya
ce sai ta cinye a gabansa. Ya soma janta a jiki ta hanyar labarai da son jin damuwarta, da kuma
ba ta misalan rayuwa kala-kala a kan kaddarar da Ubangiji ya yi nufi ga bayinsa, sai su karbeta
su kasance masu godiya a gare shi, don in ya baka wannan, sai ya hana maka wancan, ya ga
cewa za ka gode masa ne ko za ka butulce a kan wannan jarrabawar kankanuwa da ya yi
maka?
Kwarai Rahane ke jin dadin hira da Yaya Khalipha, halinsa ba daya ne da na dan’uwansa ba,
komai nasu opposite. Ita Rahane yadda Yaya Khalipha ya damu da lalurarta ita ba ta damu
kanta haka ba. Ita fa ko babu injin nan za ta iya zamanta lafiya, tunda tana da lafiya falil-lahil
hamdu. Rannan da yamma kuma Jawahir tana falo, Abida ta ja Azizah daki ta cire mata pampers. Ta
yi kashi fal! Rahane na kwance a gadonta cikin bargo kanta ke ciwo sosai ga zazzabi-zazzabi
na neman kama ta. Ba ta son wannan na’ura mai mayar da daki kamar firinji. Duk da Mami ta
ce a daina kunnawa sai lokacin zafi su kam basa iyawa sai sun kunna in za su kwanta in ba
haka ba ba za su iya barci ba.
Abida ta kunso kashin pampers ta dawo dakin kamar abin arziki ta ce, “RAYHA!’
Ta dan janye bargon ta fiddo fuskarta idanunta duk sun kankance sunyi jawur alamun ciwon
kai mai zafi. Ba ta yi wata-wata ba ta kifa mata kashin a fuska.
Dai-dai lokacin da Jawahir ta shigo. Cikin karaji ta ce, “Abidaaaa!”
Wannan ya janyo hankalin Himu da Khalipha wadanda ke zaune a falo suka yo dakin aguje
saboda yadda ta yi maganar da karfi da kururuwa, tsammani suka yi Abidar mutuwa ta yi.
Ta ce, “Ku duba ku gani, kashin Azizah ta kifa mata a fuska”.
Ai kuwa Khalipa ya kama Abida da duka don dama bai iya fushi ba, kuma tarata yake yau ta
kai shi bango.
Shi kuwa Ibraheem juyawa ya yi ya fita ya ma bar gidan zuciyarsa na wani irin harbawa,
tsigar jikinsa na tashi, don baya son ya yi kowanne action a kan Rayhanah balle har ya fassara
reaction din sa a kanta.

Yana referring kowane motion dinsa a kanta da KARYA....... Bayan kuma sau tari tsoron kar
zuciyarsa ta ce ya yi KARYAR yake kidima shi ya yi mata KARYAR. Ya damu da RAYHANAH
fiye da kowa da komi a duniya, amma yana KARYATAWA da kalubalantar kansa a kullum. Wani
gini ne ke tsiro na TAUSAYI da ​KAUNA tun ranad da suka baro Takai. [12/24/2019, 17:56] Takori: Khalipha ya ci gaba da kallon labaran CNN da Mu’azzam Kanti ke
kwararowa (Alkawari Bayan Rai). Lokaci-lokaci ya kan duba agogon (RADO) baki dake daure a
hannunsa, sai kuma ya dan dubi kofar dakin nasu. Amma ko keyar Rayhana babu har karfe
goma. Tuni Azizah ta yi barci a dakin Mami. Yana jin sanda Jawahir ta yi musu light off (wato ta
kashe wutar dakin).
Sai ya mike a hankali jikinshi babu kwari ya nufi dakinsa ya sunce ya daura tawul ya sakarwa
kanshi shower, amma zuciyarshi ta ki yin sanyi. A azabce take matuka da zazzafar soyayya,
wadda shi kansa bai san ya zai yi ya amayar da ita ba ga kankanuwar yarinya kamar Raihanah

mai shekaru goma sha biyar wadda kuma ke matukar ganin girmansa.
Ya daura Pjs ya kwanta a sofa, ya janyo kwalin Marlboro ya soma tada karamin hadari da
hayakinta, duk don ya samu sassauci a zuciyarsa, ya danne wannan al’amari da ya kutso cikin
rayuwarsa ba da tsammaninsa ba, zuwa sanda Rahane za ta kara girma ta mallaki cikakken
hankali yadda za ta fahimci al’amarin, at least ko sakandire ne ta gama. Ya san Daddy ba zai
hana shi ba idan ya ce yana so. To balle kuma Mami da ta mai da Rayhan diyar cikinta.
Barci a wannan daren rabi-da-rabi Khalipha ya yi shi. Karshe shida dai-dai ya ji Daddy na
buga mishi kofa, abinda bai taba yi ba.
Idanunshi jajir kuma mitsi-mitsi cikin mugun barci mai dadi ya bude kofar. Kafin ya gaida
Daddyn ya ce, “In ce ko ka yi sallah Khalipha
Ya amsa “Eh, Daddy na yi”.
To ka canzo kayan jikinka mu tafi Takai”.
Tuni ya nemi barcin ya rasa, ya ce, “Lafiya Daddy?”
Ya ce, “Shiryo dai mu yi sauri kamin yaran nan su farka”.
Saboda zullumi Khalipha a bai-bai yasa rigarsa, ya suro hula da takalmi ya bi bayan Daddy.
Sai da suka hau titi dodar, sannan ne yake gaya mishi Hakimi ne ya kirashi a waya ya ce da
shi Malam Rashidu ya fadi a bayi (toilet) rabin jikinshi ya mutu (Pralysed) jiya da daddare.
Khalipha ya ce, “Subhanallah! To ai Daddy da mun taho da Rayha”.
Ya ce, “Zamu taho dashi asibiti ne ai, idan na ga yanayin jikin nasa. Ba zan so ta ganshi in a
bad condition ba, ka san damuwarta da mahaifinta”.
Khalipha dai shiru ya yi, amma kar ki so ki tona zuciyarshi da damuwa ta yiwa yawa. Har ya fi
Daddy damuwa. Har suka shigo garin Takai bai kara yin magana ba.
Da hantsi suka isa Takai. A kofar gidan Hakimi suka yi parking. A dakin Hajiya Karima suka
karya kumallo, kafin su shiga wajen da aka warewa Mal. Rashidu.
Yana kwance bai san wanda yake kanshi ba, har Baba Dacta ya gama dube-dube da
aune-aunenshi a kansa bai san ana yi ba. Bakinsa a karkace rabin fuskarshi ya mutu. Duk wani
taimakon gaggawa da ake yiwa masu lalurar Dr. Mansur ya ba shi, sannan ya gayawa Hakimi
za su tafi da shi asibiti, kwararru a fanninsa su duba shi. La’asar lis suna cikin asibitin koyarwa na Kano. A take aka ba shi gado a (aminity) aka soma
bincikarsa tare da gwaje-gwaje da dora shi a kan tretment din da ya dace da shi a
(physiothearapy department).
Sai magariba suka koma gida a gajiye likis. Suka yi sallah suka ci abinci suka samu nutsuwa.
Bayan sunyi sallar isha’i suka koma asibitin, zuwa lokacin ya bude idonsa amma baya magana,
sai dai duk abin da suke cewa yana jinsu. Yana ta motsi da bakin yana son gaya musu wani
abin amma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login