Showing 30001 words to 33000 words out of 79618 words
Chapter 11 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf
dole zai fuskanta Wannan shi yasa a sati Uku Baya ya yanke mawa kansa Hukunci
akan komannsa . Momy Daddy Hajiya kuyi Hakuri da jin Abun da zai fito daga Cikin Baki na ,
Na riga na Auri Aaliyah , tun ranan dana hadu da iyayen ta ,na kuma san raunin ta ,sai naji duka
duniya bani da Wacce nake so sai ita ...Aure.!!! Falon duka ya amsa . Aydaaan buɗe idanun ka
ka faɗa mun Wannan Abun gaskiya ne ka Auri Aaliyah? . Ammiee da sai a yanzu ta yi magana
tana kallon Yaron nata ido cikin ido . Kuyi Hakuri Duka Daddy , Kuskure nayi shi ,amma SO ne
yasani .! Kun ra bani da Jidderh ,wanda a yanzu nake burin auren ta a na biyu , a kullum fata na
na kasance mijin mace Biyu , Aaliyah da Jidderh ,a yanzu ku karo mun na uku Sumayya ....kai
yi mana Shiru! Waye ya Amsan maka Auren? Eiyee? Daddy yayi maganan a zafafe yayin da
Hajiya Barmani tayi mutuwar zaune .
Kamin Aydaaan yayi magana ne Abban Ibadan ya karbe maganan da cewa " Nine na je na
amsan masa Auren Aydaaan.!
*#Mmn teddy**Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi ,
kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani
ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya
siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies
House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha
keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*
Yauwa Jama'a na ,ku ƙwantar da hankalin ku , inshallah ko bamu kammala littafin nan kamin
RAMADHAN ba , zamu cigaba da yin sa ina posting bayan An sha Ruwa , Don haka masu
cewa Mmn teddy ayi da yawa Ramadhan ya kusa ,mun san kamin ramadhan zakice kin gama
...a'a Indai bamu kammala ba Ni nayi maku Alƙawarin cigaba da posting har mu gama inshallah.
Jiya kuna ta jirar night update ban samu nayi ba ,ayi mun hakuri Don ALLAH .
17
Alh.Abubukar.! Kaine ka amshi Auren Aydaaannn ɗin ? A yaushe kenan? Kuma Auren shi da
Wacce Yarinyar? . Hajiya Rahina Tayi maganan cikin Jin Zafi , Don dama ita burin ta bai Wuce
ta ga Ranan da Ƴar nata Ɗaya Tilo zata Auri Aydaan ba , Don tafi burin ganin hakan fiye da ita
ƴar nata , A cewan ta Aydaaannn suruki ne Wanda zata nuna shi cikin bajinta ga Hajiyoyin
Ƙawayen ta . Mom Rahina macace Wanda take idon ta a bude a yage ,Wani Abun da take yi ko
ƴaƴan cikin ta basa yi , Don ce masu Sumayya take yi Ƴan Ƙauye , To Wannan Kaɗan ne daga
Rayuwar Hajiya Rahina , Wani zafi take ji akan maganan Abban Ibadan , zuciyar ta na tafasa
kaman ruwan Tafasa . Hajiya Barmani ce cike da Karaya don Alh Abubakar shine ɗan ta ƙarami
, don haka Sosai take Ɗaga masa ƙafa . Cikin Muryar su ta tsofaffi tace " Abubakar , Aure kaje
da kai akayi mawa Aydaan ? Kaima kaman ƙaramin Yaro.?
Daddy ne ya amshi maganan tare da cewa " A'a Ni ban yarda da Wannan maganan ta Alh
Abubakar ba , Har yaushe akayi haka ,duka duka yaushe ya dawo ƙasar ? . Shi dai Aydaan tun
da ya faɗa masu yana da mata bai kuma cewa komai ba sai kamewa yayi ,ya na koma masu
wannan mugun miskilin , duk maganan da suke yi bai ce uhm ba , Zuciyar sa babu Abun da
yake tunano masa sai Jidderh , yanzu ya zanyi da Ita?.
Muryar Abban Ibadan ne ya katse su yana cewa " Hajiya kuyi hakuri ,kar ku ga laifin Aydaan ,
Nine na yanke komai , kuma nima ba naje da zummar na yi hakan bane ,sai dai ALLAH ya
rubuta dama a uku ga Watanan Aydaan zai Auri Aaliyah . Nisawa Abba yayi tare da kallon
Daddy , Da kuma sauran yayyun nasa ,kamin ya cigaba da cewa " Aydaan shine Wanda yazo
Airport a ranan da na dawo daga China ya Ɗauke Ni muka dawo Gida . So nasan yanda yake ,
duk da shi ba mai yawan magana bane ba , amma a yanayin sa na fahimta aƙwai Abun dake
damunsa , Wannan yasa Ni Muna dawo Gida ,daga Ni Sai shi na tambaye sa meke damun sa?.
Bai ji nauyi ba ya fayyace mun Lamarin sa Akan Ƴar Aikin sa Wato Aaliyah , Ya ƙare maganan
hankalin sa a tashe don baya jin zaku amince da maganan auren ta , domun of course yasan
auren Gida za'a yi masu don ya faɗa mun , Ni ne na yanke Hukuncin zuwa Garin Yobe da ƙafa
na kuma ba tare da nayi shawara da Kowa ba . Bayan na isa Yobe , tabbas dangin Yarinyar
suna cikin talauci da zafin Rayuwa , mahaifin ta mai karamin karfi ne , Aydaan baya Wurin
lokacin da na yanke hukuncin daura masu Aure ,don neman Auren kawai naje muyi maganan
da Iyayen ta ,amma a yanayin condition din da na tadda su ,sai na yanke hukuncin a ɗaura
Auren nan take . Na kira Aydaaannn na kuma tambayar sa yana son Yarinyar ga Abun da na
yanke akan su .... Hajiya Tun da nake ban taɓa Ganin farin cikin Aydaaannn irin na Wannan
Rana ba ...Wannan yasa nan take aka tara mutane da Sauran dattijan unguwa aka kuma ba
Aydaaannn Auren Aaliyah nan take . Hummm Numfasawa Abba yayi tare da cigaba da cewa "
Hajiya Kar mu manta Halin da Aydaan ya shiga a sanadiyar So a Wancen Shakarun baya , Da
yaya muka samu kan sa? Idan Bamu haɗa da da Wacce yake So ,to wacece zata bashi kular
da ya dace?. Afuwan Bisa jin Wannan maganan tawa nasan na ɓata .... A'a Ya isa Abubakar ,
Babu komai shikenan ,zan rarrashi Sumayya tayi haƙuri su zauna su biyun ,tun da haka shima
Aydaaannn ɗin ya so.!
Hajiya Barmani tayi maganan tana Kallon Inda Sumayya take ,idanun ta na fidda Hawaye ,don
har ga Allah bata jin zata iya zaman kishi da wata akan Aydaaannn , Dole sai tasan yanda zata
yi don Taga ita kaɗai ta mallake shi . Miƙewa Summy tayi ba tare da tace mawa kowa komai ba
ta tsallaka tana ficewa daga Falon . Girgiza Kai Hajiya Barmani tayi tana cewa " Allah sarki ,kun
gani ko? Itama maganan bai mata dadi ba gaskiya , gayi nan kuka take yi , Aydaan zamuyi
magana dakai yanzu ku tashi kuje Allah yayi ma rayuwar ku albarka . Amin suka furta tare da
miƙewa suna barin Part ɗin Hajiya Barmani .
***
A farfajiyar Gidan ne Aaman ya kalli Aydan tare da cewa " Aydaan ka huta Zaka ji dadin
rayuwar ka ,Cox zaka Auri cikakkiyar mace , akasin mu da zamu Aura Ragowar mu . Kallon sa
Aydaan yayi duk da yana cikin wani irin yanayi marar Dadi , Amma sai yace masa " Kaman ya
kenan? Ai kai ne wanda kafara Kauda budurcin Hibba ,don haka don ka Aure ta ba laifi bane ai
. Girgiza Kai Aaman yayi tare da cewa " Bani bane , Cousin Mubarak ne , Kuma a yanzu wani
zafi nake ji tamkar na....shiru yayi da maganan idanun sa na kadawa yana yin Jah ,takaicin
duniya ya gama isar sa . Cak Aydaan ya tsaya yana jin maganan Aminin nasa har cikin Zuciyar
sa . Ganin yanda hankalin sa yake a tashe yasa Aydaaan riko Hannun Aaman yana cewa " taho
muje ka rani wani Wuri . Kallon sa Aaman yayi tare da cewa " Mu je to " . Moton sa ya shiga
tare da fara reverse yana ficewa daga Gidan. Ina zaka je da Wannan Ranan? . Garin su Kano.
Kano..! Aaman ya maimaita tare da kallon Aydaan ,me zaka yi acan?. Ba tare da Aydaaannnnn
ya kalle sa ba ya basa amsa da " Wurin Jidderh zani . Aydaaannnnn.! Aaaman ya kira sunan sa
tare da masa Alamun ya haƙura mana ,Amma kuma Aydaaan kallon sa baiyi ba ,don shi abun
da yasa ma ransa sai yayi yake Samun nutsuwa .
***
Kallon Su Ammiee Da su Abba Hajiya Barmani tayi kamin tace " To kune iyayen Wannan yaran
, ya kuke ganin Al'amuran zasu kaya? Yanzu waye Zai rarrasar mun Sumayya ?. Shiru Ammiee
tayi kamin tace " Hajiya Hakuri ya zama mata Dole , tun da babu yanda Zamuyi Aure ya riga
anyi , Yanzu Ni zan samu Sumayya mu rarrashe ta . Sauke Ajiyar zuciya Hajiya Barmani tayi
kamin tace " To ai yanzu dole ayi Ɗaya , Aydaaannnnn ya fara tarewa da Matar nasa da ya
Aura ,kamin tarewar sa da Sumayya , Wannan a ganina zai fi samun masa zaman lafiya ,akan
ace an kai masa matan duka rana Ɗaya . kallon ta Abba yayi tare da cewa Hajiya kaman ya
kenan? .
Ina nufin ko yau ko gobe ko jibi a tabbatar Wancen yarinyar ta tare a gidan Aydaan , Don nan
da Sati Guda za'a ɗaura Auren duka yaranan babu fashi ....*Don Allah don darajar Allah ki
taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki
biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi
ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki
iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC
₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number
08081202932 .*
18
Kallon Hajiya Barmani duka sukayi ,kowa na tsoron abin faɗi ciki har da Ammiee da ta tsaya
tana kallon Daddy ko zai ce Wani Abun ,amma kuma sai yayi shiru .... Ganin Hakan yasa
Ammiee sauke Muryar ta ƙasa tana cewa ' Hajiya Don Allah ayi hakuri ,A hada Tarewar Aaliyah
da Na Sumayya duka , Ai shi ba ƙaramin Yaro bane , shekara Talatin ai yayi hankali , Yasan
abun da ya dace , Idan muka yi duba Hajiya ga iyayen Aaliyah ba ƙarfi ne suke dashi ba ,
kamata yayi a sanar dasu iyayen ta....Ya isa Haka.! Hajiya Barmani tayi maganan tare da Ɗaga
mawa Ammiee Hannu . Ko su shirya ko basa shirya ba ,dama Wani Abin kirki zasu iya
taɓukawa ?. To bari kuji Ina Alh Abubakar?.
Cikin Sauri Abban Ibadan yace ' Na'am Hajiya.! bana so da buƙatar ganin an kawo mana Komai
koda cokali ne na cikin Wannan Gidan ,kana Jina?. Kana Jina? . Saurin girgiza Kai yayi tare da
cewa ' Ina Jinki Hajiya , inshallah Ba za'a yi hakan ba ,Ni ai a matsayin mahaifin ta nake , Don
haka Ni na Ɗauki nauyin komai na Aaliyah tamkar Mahaifi gare ta ".
Taɓe Baki Hajiya Barmani tayi tare da cewa " Kaji dashi dama kaine ka kulla komai , ku tashi
kuje Allah ya kara maku arziki da Wadata . Amin suka furta ,jiki a sanyaye kowa ya bar Falon
Hajiya Barmani tare da nufar Part ɗin shi . Gaba Daya Hajiya Rahina ranta babu daɗi , jin zafi
take tare da ji kaman taje ta ƙarar da Dangin Aaliyah da ita da kowa nata ,sai taga Ƙarshen
Auren , Aydaan Mutuwa zaiyi idan bai Aure ta ba. A haka ta isa Bangaren ta ,Wanda da isan ta
kai tsaye Bedroom Ɗin Summy ta nufa .
Sautin kukan ta ne ke tashi a hankali , Yayin da ko ina na jikin ta Rawa yake Alamun Zazzaɓi
mai zafi ya kamata , Cikin Sauri Hajiya Rahina ta nufi Inda Sumayya ke ƙwance ta kululluɓe
gaba Ɗaya Jikin ta har zuwa kan ta . Summy ta.! Momy Rahina tayi maganan tana kai hannun
ta tare da Saurin yaye Blanket ɗin da Summy ta rufu dashi .
Ohhh Momy Sanyi nake ji , Momy ki rufe Ni." Summy ta ƙare maganan tana ƙanƙane Jikin ta ,
Hawaye na cigaba da fin Kuncin ta .!
*Kuyi hakuri guntun night update *
*#Mmn teddy*.!*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi ,
kema Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani
ba Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya
siyan Data na WhatsApp ,to kam tabbas zaki iya cire ₦300 dai ki saya littafin The Sexxies
House ƙaramin group kenan , Vip group₦500 SPC ₦1000 via 6037312299 Mohammed A'isha
keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 .*
19
Ɗaga Hannu Momy Rahina tayi tana shafa Gyefen Saman Goshin Sumayya ,kana tace " Sannu
bari yanzu na Kira Family Doctor Ya duba jikin naki da lafiyar ki duka?. Bana Buƙatar Family
Doctor Mom , Yau kema da bakin ki kince Family Doctor? Sanin kan ki ne tun ba yau ba ,bana
taba yarda Ko mun Rashin lafiya ,wani Doctor ya duba Ni ,in dai ba Aydaaannnnn ba. Summy
tayi maganan tana kallon Mahaifiyar nata tare da matso Hawaye , Kamin ta haɗiye Ɗaɗɗatan
Yawu tana cewa " Mom Yau A gaban kowa Aydaaannnnn yace baya Sona, Baya Son Aure na
baya bukata na ke nan yake nufi A rayuwar sa? Momy Ƴar Aikin sa yake So , Humm kuma yar
ba kowa ba . Mom bazan taba Warkewa ba daga ciwo nan sai dai na samu Sauki , Idan kin ga
Na Warke to Aydaaannnnn ya cire Soyayyar ko wacce mace ya aje a gyefe ya dauki nawa
Soyayyar da matuƙar muhimmanci.... Nisawa Momy Rahina tayi tare da cewa" Ya isa Sumayya
kiyi barci ,kamin Aydaaannnnn ya shigo , bana Son duk Wani abu da zai ɗaga miki Hankali ,
Amma Ni nayi miki Alƙawarin ganin Bayan Auren Aaliyah da Aydaan ke da ma ko wacce mace
da yake buri...ko da anyi Auren Aaliyah Wallh da makirci sai ta bar Gidan Aydaan .
Aydaan mijin mace Ɗaya ne Wato Ke .! Bayan Sumayya shida mace sai kallo . Wani irin Sanyi
Summy taji Dadi na mamaye Zuciyar ta . Momy kin tabbata?. Gyaɗa Mata Kai tayi tare da sakin
Murmushi tana Cewa " Inshallah Sumayya,zaki gani .
**
Yobe
Yammacin wannan Rana Aaliyah ce zaune tana aikin yankar kuɓewa , Inna Turai ne ta iso
gaban ta tare da cewa " Aaliyah aje yankar nan ki taho Malam na Son magana damu shi da
baban ki Salihu. Haka kurum taji ƙirjin ta ya buga ,gaban ta na yanke wa tare da Faɗi , Inna
lafiya dai ko? . Aaliyah bana ce ba , Tun da nidai muje muuji Kirar . Amsan kubewan Inna tayi
tare da aje shi a kitchen tana yin gaba Aaliyah na bin ta a baya suka isa Ɗakin Abba . Bakin Su
dauke Da Sallama suka shiga dai dai Baba Salihu da Abba na amsa nawa Inna Turai da
Aaliyah . Tsugunawa Aaliyah tayi har ƙasa tana gaishe da Baba Salihu kamin ta koma ta nade
Gyefe tana jirar jin musababbin kiran nata .
Aamm'amm Baba Salihu yayi gyarar murya tare da kallon su su duka yana fara faɗa masu
dalilin Kirar nasu . Da farko Inna Turai ,Kiyi haƙuri ,kece Uwa ga Aaliyah ,amma munyi Abin da
Bamj nemi shawarar ki ba a matsayin ki na Uwa gareta . Itama kuma Aaliyah Batasan da
Wannan Abu ba . Abun ya kuke ne shi yasa har muka ga ya zama wajibi a yau a yanzu mu
sanar maku ,don ku fara shirye-shirye .
Kallon sa Inna Turai tayi cikin Rashin fahimta tace " Babu komai Malam Salihu me ya faru fadi
muna jinka.!
Humm a gaskiya Mun bada Auren Aaliyah ga Aydaan Moddibo tsawon sati Uku kenan da
Faruwar komai . Wani irin tsoro ne da Firgicin ya dirar ma Aaliyah ,wanda ya sata Ɗagowa da
Sauri tana ware idanun ta akan na Baba Salihu... Inna Turai kuwa Cikin ɗaga murya tace " Ban
gane ba , Me kuka nufi? . Abba ne ya amshi zancen tare da yi masu bayanin yanda auren nata
ya kasance , tare da kara basu haƙuri ,daga karshe ne yake sanar masu da cewa " Jibi Dangin
Aydaan suka shaida zasu taho a tafi da Amarya .
Malam Wannan wani irin Aure ne? Shin neman kai muke da Aaliyah? Haba Wannan anya
.....Haba Turai haba da hankalin ki? Cewan Baba Salihu kamin ya cigaba da cewa " Addu'a ya
kamata kiyi Allah ya albarkaci Auren ,ba Wai ki na rinka Wannan zancen ba . Aaliyah ne da tuni
idanun ta suka tsinke da Hawaye , Shi kenan Na Auri Ƙwarto marar imani , Na ƙare rayuwata a
gidan Harijai ,gidan Ƙwarata.....!
Naji kuna ta maganan ba tayi morning update ba ,to a gaskiya ban dade da dawowa school ba
gashi muna shirye-shiryen fara yi ma yara Exam , wannan yasa kuka ji Ni shiru , ga kuma Ɗan
aikace² na Gida , Amma kuyi hakuri da Wannan Zuwa anjima zamuyi mai tsawo sosai .
#Mmn teddy*Don Allah don darajar Allah ki taimake Ni kar ki fitar mun da Wannan littafi , kema
Don Allah kar ki karanta mun Indai baki biyani Haƙƙi na ba , Idan kin karanta baki biyani ba
Wallahi keda Allah , Don banga Tsadar shi ba da Zaki kasa cire kuɗi ki saya ,Indai kina iya siyan