Showing 48001 words to 51000 words out of 79618 words

Chapter 17 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf

22 Nov 2025

1641

gogawa a saman laɓɓan ki , idan yayi kaman minti biyar sai ki goge da
Toilet paper ki shafa Vaseline dan kaɗan wannan yana taking more than 3days before ki fara
ganin change of reaction ,Amma Guarantee ne yana yi sosai ... inshallah zamu faɗo kaloli uku
na hanyar da laɓɓa zasuyi Pink gunun sha'awa , yanzu kuma mun fado na biyu . Pink lip yana
ƙara mawa mace ƙyau ainun Mmn teddi'es skincare taku ce️

Aydaaannnnn ne yayi Saurin yin gaba yana tare mata hanya tare da cewa " Wai kishi kikeyi ne?
. Kallon sa tayi tana cewa " Kishi? Kishin mene to? Na fiki ƙyau .! Wani dariya Aaliyah ta sa
masa ,duka don ta ɓata ransa ,amma kuma shi a nashi ɓangaren daɗin wannan Dariyar nata
yaji ko ba komai yasan yanzu ta huce daga Abun da yayi mata. Dariyar me kike yi haka? Ai ba
ƙarya na faɗa ba , idan kuma ƙarya ne to mu ɗau hoto yanzu don a tantance . Uhmmm to naji ,
Amma Malam likita kayi kuskure , ka manta shi ƙyaun Ɗa namiji ba mai ɗaurewa bane ba ,ta ƴa
macen nan dai shine yake mata da'iman don haka sai dai haƙuri . Kuma ma me zaka nuna mun
daƙwa-Daƙwan idanu wanda basa burgeni sam . Murmushi yayi mata don y lura ya tsakano ta
sosai . Okay Yanzu dai nafi ki ƙyau ko? . Ɗago idanun ta tayi tana sauke su cikin fushi akan
maganan nasa . Okay naji yanzu idan muka je Gida Su Hibba sai suyi mana Shari'a su faɗa
wayafi ƙyau tsakanin mu . Tsayawa tayi jikin ta nayin sanyi ƙalau a lokaci guda . Kasa masa
magana tayi kawai sai ta wuce shi tana ficewa daga Falon tare da nufar Farfajiyar gidan . A
bakin Moton sa ta tsaya , don ta lura ko ina a rufe yake . Ƙarikowa yayi fuskar sa Ɗauke da
Fara'a kamin ya kalle ta yana kashe mata ido ɗaya tare da cewa " Komai dai dai ?. Gyaɗa masa
kai tayi kurum Don duk ta ƙosa su tafi tabar wannan Gidan . Humm Muryar sa ta kuma ji yana
cewa " kin tabbata ?. Kasa masa magana tayi don taji ya fara isar ta ,wai dama yana magana
haka? Tambayar da take ta mawa zuciyar ta kenan ,kana takai hannu tana shirin muke murfin
Moton . Gani tayi tuni ya buɗe mata yana kallon ta ,ta shiga kana ya juya side din sa yana fara
yin ma Moton key tare da barin farfajiyar gidan .

A hankali yake Driving hankalin sa ƙwance ,idanun sa na akan Fuskar Aaliyah ,wanda sam bata
ta kansa duk ta kosa ta ganta a gidan Ammie don ta shaida mata halin da Ɗan ta ke ciki .
Kaman ance ta juyo taga yayi mata kurrr Lulun idanun sa na akan Fuskar ta . Saurin cewa tayi "
ka kalli Gaban ka fa Driving kake yi . Hummm . Sauke Numfashi yayi kamin ya juya yana kallon

saman titin hannun sa ɗaya ya sa yana kamo hannun ta tare da Haɗawa wuri ɗaya . Wanda jin
hakan yasa Aaliyah yi masa Wani irin kallo tana fuzgar hannun ta . Murmushi yayi kaman baiji
komai ba ,sai cewa yayi " Wannan fa iya hannun ki na riƙe , Kin manta yau da Safe Farjin ki na
taɓa ? Kin kuma manta jiya da dare Har nonon ki na taɓa babu abu ɗaya a jikin ki wanda hannu
na bai taɓa ba . Kallon sa Aaliyah tayi idanun ta na kaɗawa lokaci daya yana taruwa da ƙwallah
. Zaki bani hannun naki ne ko kuma yanzu na tsaya anan Gyefen hanya nayi Ko kaɗan ne
yanda nayi a daren jiya ?. A hankali ta miƙa masa hannun tana juyar da kan ta Gyefe tare da
kallon bakin hanya . Murmushi yayi yana kama hannun nata tare da cigaba da murza ƴan
yatsunta a hankali yana matsawa a haka ya cigaba da Driving ɗin nasa yana jin Wani irin sanyi
da sabon soyayyar Aaliyah na shigar sa .

Muryar sa taji yana cewa " Darling love Meye halaƙarki da Jidderh?. Juyowa tayi tana jin
Haushin sa kamin tace " Yaya ta ce .! Maman mu ɗaya baba Ɗaya . Sakin hannun ta yayi cikin
sauri tare da dafe kan sa ji kake ƙuuuuuuuuu..... Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un, Aydaaannnnn
kashe mu zaka yi ne a ƙwalta. Saurin kallon hanya yayi kamin yace " I'm sorry dear . Bari yanzu
mun kusa ma .

***
Zaune Hauwa take a tsakar gida Gyefe Umma ke tanƙaɗar Garin tuwo , Ita kuma tana Ɗauraye
ƙwanonin gidan da tukwane . Gyarar Muryar Baba yasa Hauwa Saurin ɗagowa tana ƙasa da
kanta tare da cewa " Baba Barka da shigowa . Wani irin kallo ya watsa mata tare da juyawa
fuuuu yana nufar Ɗakin sa . Umma ne ta ɗan taɓa baki tare da Girgiza kai kurum tana kallon
Hauwa ,kamin tace " Hauwa cigaba da Aikin ki kinji . Ƙwallah Hauwa ta goge tana kallon Umma
tare da cewa ' Umma don Allah ki taimake Ni ,kije ki ba Baba haƙuri . Sakin baki Umma tayi
kamin tace "Haƙuri Hauwa? Haƙuri fa kika ce? To wai kece mai laifin? Miji yace bayayi to meye
laifin ki anan ?. Hawaye ne ya biyo Kuncin Hauwa , Umma don Allah kije don Allah Umma .
Hummm Numfasawa Umma tayi kamin tace " Okay Bari na shiga naji , amma Ni ban ga laifin ki
ba gaskiya haba .

**

Kallon Aaliyah yayi yana cewa " To muje daga ciki , ina zamu fara nufa ne? Part ɗin Ammie ko
na Hajiya ?. Kallon sa Aaliyah tayi cikin Sauri tace " A'a na Ammie za muje . Murmushi yayi
yana cewa "Okay . Ammie ce ke saukowa daga Up stairs din ta , don yanzu Daddy ke sanar
mata duka suna can part ɗin Hajiya Barmani . Kallon Aydaaannnnn da Aaliyah tayi wanda suke
shigowa . Cikin Sauri Aaliyah ta risina har ƙasa yanda suka saba yi masu tana cewa " Ammie
Barka da Safiya . Murmushi Ammie tayi tana takowa zuwa inda suke hannun ta tasa tana Ɗago
Aaliyah tare da cewa " Aaliyah sannu Har kun iso ? . Gyada Mata Kai Aaliyah tayi tana yin shiru
. Kin ci Abinci kuwa?. Eh Ammie . Amma Ammmie May be xata buƙaci Wani Abun ,tun da barci
ta tashi . Kallon sa Ammmie tayi tana ganin yanda yake rawar ƙafa kamin tace " Wai haka
Aaliyah?. A'a Ammmie na ƙoshi . Okay to yanzu ku muje part ɗin Hajiya Barmani . Okay mum
bari naje Wurin Aaman sai mu taho tare dashi yanzu . Aydaaannnnn yayi maganan yana kallon
Aaliyah tare da mata Murmushi ,saurin kauda kai tayi har ya fice sannan ta ɗago tana kallon

Ammmie . Ammmie ne ta kalli Aaliyah tare da cewa " Aaliyah babu wani matsala dai ko?. A
hankali Aaliyah tace " Wallh Ammmie Aƙwai ,amma ina Tsoro.! Subhanallah just feel free and
told me the Trued, I'm LYK your mother Okay? Ki faɗa mun gaskiya meke faruwa . Aaliyah ne
Hawayen da take dannewa suka fara zubo mata ...nan take taba Ammie Labarin Aydaan da
yanda yace mata yana da Ɗakin Dodon sa . Ai kamin ta ƙarike Ammmie ta hau Dariya har da
kyakyatawa . Okay Wato Aydaaannnnn tsorata mun ke zai dinga yi kenan ?.


Ƙwantar da hankalin ki muje yanzu ,amma kawai yayi miki ne , yau dani za'a je gidan sai ya
nuna mun dakin . Kallon Ammmie Aaliyah tayi tare da cewa " Ammmie wai kina nufin karya
yake yi?. Eh mana Aaliyah rabu dashi dai kawai shakiyin Yaro ." Wallh Ammmie jiya ya mun
mugun ta haka yayi ta tsorata Ni . Allah Ko Aaliyah, ai bari yazo zai same ni. Miƙewa suka yi
daga Zaunen da suke tare da nufar part Dina Hajiya Barmani . Tun da suka shigo Falon Hajiya
Rahina ta shaƙa ganin Ammmie riƙe da Hannun Aaliyah . A hankali Aaliyah ta nemi Wuri tana
shirin zama can Gyefe ne , Hajiya Barmani tace " A'a Matso kusa jikalle ya zaki zauna can,
matso kusa ayi maganan dake ,don ya shafi Wannan taƙadirin mijin naki . Dariya Aaliyah tayi a
zuci kamin ta matsa a hankali kusa da Hajiya Barmani tana gaida ta ,kamin ta gaishe su duka ,
wasu sun amsa wasu sun yi mata banza . Tsawon lokaci babu wanda yace ƙala , har Aydaan
don tun shigowar su su tuni sun halar ta . Idanun sa gaba Ɗaya yana akan Aaliyah . Wanda tayi
shiru tana tunanin Abubuwa da asalin ta da talaucin iyayen ta . Bangare Guda kuma tsoro ne
yasa ta yin tsammm Duba ga yanda Ƴammatan ke wurga mata harara , su kam su Hajiya
Rahina abun nasu a ƙasa take .

Kallon Aaman Aydaaannnnn yayi yana amsan blank paper ɗin Hannun sa , biro ya amsa yana
budewa tare da zana mata emoji na smile � ƙamin ya kanannanɗa kamar jirgi irin yanda zaki
ga yara na yin jirgin takarda . Huuuu Aydaaannnnn ke nan aƙwai shi da ƙwaƙwalwa sosai . Idan
yana drwng ka rantse Architect ne . Ɗagawa yayi yana cilla mawa Aaliyah inda take sai a
Gaban Hajiya Barmani da ita Aaliyahn. Ɗagowa duka aka yi ana kallon sa ,wanda shi baya ta
kansu har a lokacin idanun sa na akan Aaliyah ne . Ɗaga mata gira yayi tare da mata Alaman ta
buɗe . Sauke idanun ta tayi ƙasa tana ɗaukar Takardar tare da Warwarewa . Emojin da ta gani
ne yasa sam bata san lokacin da ta saki Murmushin ba ,wanda har haƙoran ta na
bayyana�....!
#Mmnteddy*Littafin na kudi ne, Regular Group ₦300...Vip group ₦500... Special ₦1000 via
6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*

#Mmnteddie's skin care#Pink lip (3)
Hanya ta uku kuma na ƙarshe da zamu faɗa wanda yake saka pink lips . Zaki samu Lemun
tsami � lalli normal lalli namu ta gargajiya sai ki haɗa da sugar . Method ɗin kaman yanda
muka yi bayanin na baya haka zaki yi , ba'a so ya wuce 5mins ba tare da kin goge da tissue ba
,after All sai ki sa Vaseline a laɓɓan ki . Tried to do it in just 3 days you'll see Quickly reaction
Mmn Teddi'es skincare taku ce..
Sexxies House Book 3.
Page 33-34

Murmushin da ta yi masa ne yasa Su Hibba Sakin baki zuciyar su na masu baƙi ,tare da jin
zafin Aaliyah a zuƙatan su . Ɗago da idanun ta tayi daga kallon takardar tana kallon inda
Aydaaannnnn yake wanda duk Wani motsin ta akan idanun sa . Har kuma A Wannan lokacin
fuskar ta Ɗauke yake da wannan Sanyayyar Murmushin wanda yaƙara mata ƙyau sosai .
Murmushin nan nashi ya sakar mata Wanda har Hushiryar sa na sama tana bayyana . Ɗan
tsamm taji don a jikin ta taji Idanun mutanen Wurin na akan su Wannan yasa ta saurin Sunkuyar
da kan ta ƙasa tana haɗe takardan Wuri Guda. Sanyi taji yana ratsa zuciyar ta ,wanda ta rasa
Gane na menene? Me kuma ya haddasa mata jin Wannan sabon Annashuwan? . Hajiya
Barmani ne ce ta katse Aydaaannnnn da yake shirin yi ma Aaliyah magana kamin tace" To
marar kunya , takardan meye Wannan? Har a gaban Iyayen naka ma ,shakiyi Allah ya shirya ku
duka . Shiru Aydaaannnnn yayi yana yin ma Hajiya kaka baya da niyyar Tankata . Aaman ne ya
amshi Hajiya Barmani da cewa " Hummm Hajiya saƙon soyayya ne a ciki fa, ko na karanta miki
ne?. Jin wannan maganan tasa yaba iyayen dariya sosai ,wanda cikin sauri Hajiya Barmani
tace " A'a a'a Wannan ai sai ku ƴan zamani ,bana Son ji. Murmushi Momyn Mubarak tayi kamin
tace " To ai kene Hajiya irin Wannan abun ma ba'a magana tun da yaran nan Ba kunyar mu
suke ji ba . A'a Momy mu mun isaaaa? Cewan Lukman yana dariya. Su Daddy dai kame suke
babu wasa ,don sun lura duk Wani Rashin kirkinn da yaran suke dama iyayen nasu mata ne
suka saka su a hanya. A yanzu kuma sun taru ne har iyayen mata ba zasu ƙyale ba ,kowa sai
sun faɗa mashi laifin sa...Wurin ne ya fara zama wurin hira , Don samarin gidan su Aaman an
saki jiki da gyara zama tamkar ba Faɗa aka zo ayi masu. Muryar Hajiya ne ya katse su tana
cewa " Shifa Aydaan har yanzu bata kan mu yake ba ,kallon sa kaf yana akan Aaliyah ne ku
duba kuga...!


Dariya Mubarak yasa yana cewa ' To Hajiya ai ku kuka kira su da sanyin Safiya ,da Ni
ne....Dakai ne mene? Ammmie tayi maganan babu wasa . Tsit suka yi don sosai suke shakkar
Ammmie . Hummm shakiyan yara . Hajiya ya kamata ayi abun da ya tara mu duka .

Wannan haka yake Tabbas. Hajiya Barmani tayi maganan tana kallon duka ƴaƴan da jikokin ta
da kuma surukan ta. Yanzu Ni bana kira ɗaya daga cikin ku bane don naji bakin Wani cikin
magana ta , Bana bukatar jin Maganan kowa . Shiru duka aka yi ana jirar jin mai zai fito daga
Bakin Hajiya Barmani . Da farko Komai ya faru sai dai muce Innalillahi wai'inna ilaihir raji'un
shine kaɗai kalmar da zan iya fara ambata a yanzu . Naji duk Abun da ya faru tsakanin ku duka
, iyayen ku mata sun faɗa mun , kuma Wallahi ban zata ba , tarbiyyar da muka baku Bai maku
Rana ba ,tun da har kuka iya aikata Saɓon Allah . Kun bani Kunya ,kun bani Kunya ƙwarai .
Gani suka yi Hajiya Barmani tasa Habar Zanin ta tana share ƙwallah ,wanda cikin Sauri su
Ammmie da Abban Ibadan Daddy suka fara bata Haƙuri tare da rarrashin ta . Ɓangaren Su
Aaman Aydaaannnnn da sauran samarin daɗi suka ji a tunanin su Za'a ce an fasa Wannan
Haɗin Auren nasu. Muryar Hajiya Barmani suka ji tana cigaba da cewa " Don haka har yanzu
Auren ku yana nan a yanda muka tsara ,sauran duk wani Abu ya rage naku . Mudai Aure babu
fashi . Kune zaku iya rufa ma kan ku asiri ,wani Bare ba zai taɓa yi maku ba . Sai dai idan cikin
ku da mai ra'ayin Ƙara Aure ai wannan bamu isa mu hana ku ba . Don haka ina Sauraren ku
duka . Shiru Hajiya Barmani tayi tare da Sauraren jin mai zai fito daga Bakin Su Mubarak.

Mubarak ne ya fara magana kaman haka ' Hajiya Ni bana da Ra'ayin ƙara Auren ,zan zauna da
Ummi . Mashaallh Alhmdlh . Lukman kai fa? Nima haka Hajiya . Mashaallh shine kalmar da ta
furta kamin su kalli Aydaaannnnn , Nuni yayi masu da Aaliyah wanda tun da aka fara maganan
kan ta na kasa . Girgiza Kai Ammmie tayi tana mmkin rashin kunyar Aydaaannnnn baya jin
kunyar ya nuna soyayyar sa a gaban kowa . Hajiya Barmani ce tace " Masha'allah . Aaman ai
kai ma nasan kai ma hakan ne ko? .


Kallon Hajiya Barmani Aaman yayi kamin yace " A'a Hajiya Nima ina da Wacce nake so ,sai a
haɗa Auren a rana ɗaya. Saurin kallon sa duka sukayi , Hibba kuwa idanun ta ciko da ƙwallah ,
shikenan na shiga Uku na . shima Ƙwaxin Aaman Auren budurwa zai yi irin na Ƙwazin Aydaan .
Muryar Ammmie ne ya katse su tana cewa " Muna sauraren ka ,a ina yarinyar take ? Yar waye
ita? . Hummm Numfasawa yayi kamin yace " Jidderh.! Wani irin shiru Wurin yayi kamin Mom ɗin
shi tace " Aaman ban gane ba ,wata Jidderhn??.


Kallon Aaman Aydaaannnnn yayi cikin rashin fahimta tare da kullewar Kai yace " Wata Jidderh
kake magana ? Jidderh ta?. . Eh Ita Aydaaannnnn. Miƙewa Aydaaannnnn yayi a zafafe kamin
yace " Ban gane ba . Aaliyah ce itama ta Ɗago idanun ta cikin tashin hankali da tsantsan
mamaki tana kallon Aaman wanda idanun sa da fuskar sa ke nuni da gasgata tsantsan
Gaskiyar Abun da ya furta . Kunsan bahaushe na cewa " Labarin zuciya A tambayi fuska .
A'aman da Gaske kake yi ,wannan guzumar bazawarar zaka Aura ? Yar Talaka ? Summy tayi
maganan cike da jin bakin ciki da Ɓacin rai ,ji take kaman tayi ta sharara mawa Aamaan Mari .
Bazawara?? Ammien Hibba tace tana dafe kirji kamin tayi duba ga Sauran iyayen nasu da
kowa na wurin . Kai Gaskiya Hajiya Barmani ya kara duba Wata ,Tayaya Zan hada Hibba na
kishi da Bazawara? Wanda sun san komai ciki da Waje ,na dauki jaririyar ƴata na hadata kishi
da Bazawara? Wanda ta cinye zuciyar Aydaaannnnn tun yana yaro na fahimta wacece Wannan
yarinyar, Makira sheɗaniya. Mom...! aydaaannnnn ya kira Sunan momyn Hibba yana dakatar da
ita . Ba gaskiya bane ba? Ai Gaskiya ne ,har yanzu soyayyar ta shi ke tasiri a zuciyar ka... Don
haka Aydaaannnnn kai ke Son Jidderh ka Aure ta in yaso ka haɗa Uku ai Dama an halarta
hakan a musulunci,sunna ce .


Juyawa Aydaaannnnn yayi yana kallon Aaman kamin yace " Aaman Why? Me yasa ? Me yasa
zaka mun haka?. Saboda na kwantar maka da hankali ,da kuma kullum tunanin ta da kake yi
akan Wani hannu zata faɗa ,shin zata samu kulawa ko a'a? Wannan yasa Ni yanke hukuncin
nan . To Ai Duk kular da zaka bata Bai kai yaƙwantacin Shi Aydaaannnnn din ba...don haka
shine ya kamata ya Aure ta . Momyn Hibba tayi maganan a zafafe. Aaman ne kan sa tsaye
yace " Mom Babu Aure a yanzu tsakanin Aydaaannnnn da Jidderh , Saboda Aydaan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login