Showing 51001 words to 54000 words out of 79618 words

Chapter 18 - SEXXI'ES HOUSE COMPLETE BY MAMAN TEDDY.pdf

22 Nov 2025

1625

na Auren
Ƙanwar Jidderh Uwa Daya uba Ɗaya wato Aaliyah. Laha'ilah ha'illallah, ya tabbata....Cewan
Hajiya Rahina tana tafa Hannu kamin tace " Kai Wannan Yarinya kin zama mana ja'iba jaraba ,

da musiba....!
#Mmnteddy*Littafin na kudi ne Regular Group ₦300...Vip group ₦500... SPC ₦1000 via
6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number nawa
08081202932 idan VTU transfer ne sai a tura ta Wannan number 09061466409 #Mmn teddy*
35-36
#Mmnteddie's skin care#Gyara da kanki Uwar Gida...A yau zamu faɗi Hanyar Gyaran jiki guda
biyu...Ina masu fama da Kaushin ƙafa , Wasu na kira da Ƙaushin tafin ƙafa, kina so kiji shi
sumul to biyu Ni a wannan process ɗin ... Da yawa mata na amma Ni da Dutse ko Brush mai
ƙarfi Wurin cire Wannan kaushi ,wanda hakan tamkar ƙara lalata taffan Ƙafarki kike yi Bama
gyara ba , saboda Ƙaushin ƙaruwa zaiyi ya fi nada . To meye zakiyi Wurin fidda Wannan
Ƙaushin cikin sauƙi? Da fari ; Zaki samu Ayaba (Banana)� ki fidda cikin sai Kiyi amfani da
bayan wato ɓawon wurin goge ƙafarki dashi yayi consuming like 15mins sannan sai ki Wanke
Ƙafarki Ki jaraba na ƙwana uku kiga yanda ƙafarki zata yi #Mmnteddi'es skin care️ .

Kin zama mana jaraba ja'iba cikin Gida, Zuwan ki Rayuwar mu musiba ce. Dama tuni nasan
Bata bar yaran nan haka ba ,wa yakai Talaka mugun abu?....Muuumm .! Aydaaannnnn ya kira
sunan Momy Rahina cikin Ɗaga murya don lamarin nata ya fara ɓata masa Rai . Aaaman ne ya
amshe maganan nasa tare da cewa " Ni ne fa nace ina Son Jidderh ba Aaliyah ba.! Tun da Mun
koma ƴaƴan ku kuma kun zama iyayen. to a wannan karon maganan nan taka bazamu yarda
daa ita ba ,ko ke Momyn Aaman kin amince da wannan auren na Aaman? . Shiru Momyn
Aaman tayi tana nazari tabbas Tana Son farin cikin Ƴaron ta amma wannan abun da ya debo
tana ganin kaman babu zaman lafiya ,idan tayi duba ga Halin da Aaliyah a yanzu take ciki a
cikin gidan , to haka zai Auro yar mutane itama ayi mata ? Gaskiya bata tsammanin zata iya
jurar hakan ,don ita idon ta kar yake bata da kirki akan Ɗan nata guda ɗaya kamar Rai . Kinyi
shiru baki ce komai ba?. Cewan Momyn Hibba tana kumburin wuya sam sun manta da Wata
wai Hajiya Barmani zaune. Kamin Mahaifiyar Aaman tayi magana ne Muryar Hajiya Rahina ya
katse su a inda take cewa " Nifa wallahi da Ni ne Ammien Aydaan , ko Aydaan mene zaiyi ba
zan bari ya haɗa mun zuri'a da baragulbi ba ,sai ya cire duk wani ƙudurin sa akan Wannan
yarinyar ya watsar ya nemi ƴar Gata Ƴar Dangi ya Aura. Mom A'aman ne ta katse su da cewa "
Abun da kuke yi ya fara yawa Gaskiya , Wannan fa yarinyar Aaliyah ƴace ko nace duka mun
kusa jika da ita , Duka duka nawa ne shekarun ta ? Amma ku zauna kuyi ta zagin yarinya
ƙarama wanda sam bata da laifi ,laifin Aydaaannnnn zaku gani ,tunda inda bai mata dole ba
itama ba zata Aure sa ba . Wani irin kallo Hajiya Rahina tayi ma Momyn Aaman kamin tace "
Lallai baki san Waye mutum ba , musamman wannan yarinyar , Halin ta zai bar da ita gidan
nan. Ƙwaɗayin da iyayen ta suka bi suka Aura ta gidan nan to .....Haba Hajiya Rahina ,Is much ,
Wannan abun naki baiyi ba ,Ammmie tayi maganan ganin yanda Idanun Aaliyah ya gama
rinewa daga Farare tasss zuwa jah , Hawaye na wanke Kuncin ta . Duk kuma abun da Su Mom
Rahina keyi kan ta a ƙasa yake bata Ɗago ba. Ganin rikici na shirin ɓallewa ,a fili Momyn
Aaman ta nuna ba zata yi ma ɗan ta dole ba ,wannan ya ɓata Ran da Yawa iyayen Yaran. Don
sun bar Sun Daddy da Hjy Barmani hoto . Zagin Da Hajiya Rahina ke aika mawa iyayen Aaliyah
yasa Aaliyah cikin wani irin yanayi miƙewa jiri na ƙwasar ta ,da duhuwa ficewa tayi daga Falon
cikin Sauri ,wanda Ganin haka yasa Aydaaannnnn shima miƙewa yana barin Falon cikin
sassarfa tare da bin bayan matan nasa. Aaaman ne shima yabi bayan su ,wanda Ganin hakan

yasa Momyn Hibba cewa " Ahaf kun gani ko? Wannan mutane iyayen ta basu kawo ta gidan
nan ba sai da suka shirya ta tsaf suka malleke yaran nan . Dama ko zuwan ta aikatau gidan nan
da mission ne ,kuma sunyi archving . Momy Wannan Abun da kuke yi ba dai dai bane ba,
Mubarak yayi maganan yana kallon Momy cikin nuna rashin jin dadin sa . Aaliyah ta zama mu ,
haka mu ma mun zama ita...Saboda Aydaan ya riga ya Aure ta ,ta zama matar sa . Ba'a Saki
ne? Cewan Hajiya Rahina kamin ta cigaba da cewa " Naga ko yanzu ya sake ta ,zata tarkata
tabar mana cikin Estate , Ba saurin kare bin damo . Assshhaaaaa kayyyyaaaa , To tun da Ni
kun nuna ba a bakin komai nake a gare ku ba , daga yau ba zan ƙara Kirar ku da neman
shawara ba , Zan ringa magana da mazajen ku ,su sai su saka a hanya . Ku tashi ku fita duka
ku bani Wuri . Suka ji Muryar Hajiya Turai cikin fushi da Tsawa irin nata . Shiru Wurin yayi ,yayin
da t kara cewa su fice su bata Wuri . Hakuri Su Ammmie suka bata kamin kowa ya mike su
Summy suka fara ficewa cikin ƙunar rai da zuciya . Bin bayan Aaliyah da Aydaaannnnn yayi yafi
komai ɓata mata Rai . Juyawa su Ammmie zasu yi su fice ,nan Hajiya Barmani tace " Ki faɗa
mawa Aydaan ya ƙara riƙe masu yarinya da Amana ,idan ya zalunci yar nan to Allah zai saka
mata wannan shine .



Jiki a sanyaye Ammmie tace " To Hajiya Ayi haƙuri don Allah . Itako Momyn Aaman juyawa tayi
tana ficewa daga Falon a zuciyar ta faɗi take naga Ɗan iskan da zaiyi mawa yaro na dole , Ai a
hakan Auren nan da zaiyi na haɗi an cutar dashi ,Baga maganan so ba , a'a shi kan shi yasa
Watsatstsiya zai Aura . Cikin da jin zafi ta nufi part Ɗin ta .
Ɓangaren Aaliyah kuwa tana ficewa daga Falon kan ta tsaye farfajiyar gidan ta nufa tare da
nufar Gate masu Gadi suna buɗe mata ta fice daga Gidan . Wayar nan naga Nokia ɗin ta ,ta
fiddo tana fara kirar numbern Hajiya Munaya. Ringing biyu taji bata ɗaaga ba wannan yasa ta
saurin fara barin layin tare da nufar mai adaidaita. Tana shigewa adaidaita Aydaan na fitowa .
Ganin sa da tayi a can bayan ta yasa ta ce mawa mai adaidaita yi sauri ka ƙara Gudu . Kamin
Aydaaannnnn yazo tuni sun bar layin . Tsayawa yayi yana Kirar sunan ta amma ina Bama ya iya
hangen su . Ji yayi an dafa shi tare da sauke ajiyar zuciya . A hankali Aydaaannnnn ya juyo
yana kallon Aaman dake tsaye a bayan sa . Aaman Ni zaka cuta? Ni zaka yaudara?. Ina
Aaliyah take? Ina ta nufa yanzu ?. Banza Aydaan yayi masa kamin a zafafe yace " Matar ka ko
matata? Ka bani Amsan tambaya ta malam.! Shiru Aaman yayi kana yace " Kayi haƙuri
Aydaaannnnn , Har Abada babu Aure tsakanin Kai da Jidderh Indai Aaliyah na raye kuma kuna
tare da ita . Tausayin nan nata da kake ji shine ya kamani a lokacin da ka faɗa mun cewan
Aaliyah da Jidderh yan uwa ne . Sannan kuma kar ka manta Jidderh soyayyar ta yasamu gurbi
ne daga yarintar ka ,a lokacin baka san So ba kawai kana faɗan ta ne....a yanzu ne
Aydaaannnnn kasan SO domin dai dai da Minti guda ba zaka taba iyaye a rayuwar ka hankali
kwance ba tare da kaga Aaliyah ba ko kaji Muryar ta ,wannan shine Son Gaskiya . Bari na faɗa
maka wani Abu da baka taba Sani ba , Shine kana Mugun masifar Ƙaunar Aaliyah soyayyar ta
wannan a jinin ka yake .

Numfasawa Aydaaannnnn yayi kamin yaji Muryar Aaman Na cewa " Yanzu a tunanin ka ina ne

Aaliyah ta nufa? . Kai tsaye Aydaaannnnn ya furta " Gidan Munaya . Okay Bari na fito da Moton
ka muje can ,daga can sai ku wuce gida kawai . Juyawa Aaman yayi ba tare da ya jira cewan
Aydaaannnnn ba wanda ya tsaya yana faɗawa duniyar tunani ,idan suka matsa mun zan bar
Aaliyah dani kaina ƙasar nan sai kowa yayi shi kaɗai .
**

Tun da Aaliyah ta shiga Falon Munaya ta kasa ɗaga koda ɗan yatsar ta saboda tashin hankali
da kuma ɓacin rai . Tsayawa tayi a tsakiyar Falon hawaye na cigaba da bin Kuncin ta . A hankali
ta fara jin fitowar Munaya cikin wannan takon nata mai dauke hankalin maza da mata baki daya
. Wani irin crazy dress up tayi , rigar mai kama jiki kuma roba ,duk ƙiban ta Wando ta saka ta
ɗame cikin English wear tana saka ƙatuwar Ɓakar gilashi wanda ya mamaye rabin fuskar ta .
Kan nan nata yasha fixing na attachment...Saurin sauke gilashin idanun ta tayi kamin tace "
Aaliyah kece yau?. Me ya kawo ki gidana? Mayaudariya azzalumai muguwa ,Ni kika ha'inta ,
bakiyi mun aiki na ba , kika sa nayi gidan yarin na tsawon ƙwana ki , Aydaaannnnn ya sa aka
tura Ni nan . Bayan fitowa na wai labarin Auren ku nake ji , Anya ke mutum ce Aaliyah? Butulu
ce ke ,mai manta alƙawari .


Kallon Munaya Aaliyah tayi kamin taja magina tana sa hannun ta tare da goge Hawayen Fuskar
ta . Hajiya Munaya.! Aaliyah ta kira sunan ta cikin wani irin murya kamin ta kalle ta tun daga
Sama har ƙasa . Bakya ne ya kamata kimun wannan munanan maganganun naki ba , a'a nice
Wacce ya kamata na faɗa miki su . Tsakani na dake ALLAH ya isa ba zan yafe miki ba ,kin
haɗani da musifa...tun da na fara miki Aiki hankali na yaƙi Ƙwanciya har iyau . Aaliyah ni kaka
zaga? . Na zageki Munaya Kiyi mun duk Abin da zakiyi . Kuma Wallh ba zan bar gidan ba sai
munje wurin Aydaan kin faɗa masa cewa ' ke ce kika sani komai bani nasa kaina ba ,don ban
taɓa sanin sa a rayuwa ba sai a sanadiyar ki ...... Aaliyah Aydaaannnnn ya san komai ki ƙwantar
da Hankalin ki . Suka ji Muryar Aaaman dake shigowa , Aydaaannnnn na biyo bayan sa . Wani
irin kallo Aaliyah tayi masu duka kamin tace " To saura ya bani takardan saki na ,ya Auri
Munaya itace ta shirya komai ,ita zai dauki fansa da mataki akan ta ba Ni ba .


Keee waya ce ki taho Gidan nan ? Da izinin Wa kika zo gidan nan? . Aydaaannnnn yayi mata
maganan cikin arrogant voice Din shi babu alamun wasa . Wani irin kallo ta masa cike da
mmkin halin sa kamin Aaliyah tace " kai kuma a wane? Ai yanzu bakin alkalami ya riga da ya
bushe , a yau yanzu sai ka sake Ni... Babu rabuwa a tsakanin mu sai dai mutuwa.! wani irin
waro ido Aaliyah tayi idanun ta na cigaba da Ambaliyar hawaye. Wallh baka isa ba ,sai ka rabu
dani a yau ... Ta ƙare maganan tana fashewa da Kuka . Wani irin sheƙeƙen kallo yayi mata
kamin ya tako zuwa inda take . Hannun ta ya kama yana cewa " Oya mu tafi kar kuma na ƙara
Ganin ki a cikin gidan nan. Janye jikin ta tayi da hannun ta kamin tace" Me ka ɗauke ne
Aydaaannnnn ,kalli yanda kake mun kaman yar cikin ka ? Babu inda zan tafi .........!
#Mmnteddy
#Rmdnkareem*Littafin na kudi ne Regular Group ₦300...Vip group ₦500... SPC ₦1000 via

6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number nawa
08081202932 idan VTU transfer ne sai a tura ta Wannan number 09061466409 #Mmn teddy*
38-39
#Mmnteddy
Da fari bani ce Wannan masoyiyar taka ba da kake nema , Adda Hauwa ta saka Ni a masifa ,ta
fahimci komai amma ta tirsasani Auren ka , na biyu Bani ce na shirya zaluntar ka ba , Ɗaurani
Akayi kuma ka sani ,ƙarshe ma ga wacce ta sani , to meye yayi Saura ? Kawai Ka ɗauki mataki
akan ta mana ,sai kace akai na ne zaka Ɗauki Fansa? To a yau sai ka sake Ni ka Auri Wanda
.....Kamin ta rufe baki ne taji tasssssss Ya ɗauke fuskar ta da Wani irin Mari ,wanda sai da taga
Tartatsin Wuta . Baya tayi taga -taga zata faɗi ya finzota da hannu ɗaya ta Faɗo Jikin shi. Jah
baya Munaya tayi cikin tsoro tana nufar can Ƙusurwa tana manne kan ta kaman bango Ya tsage
ta shige Ganin Aydaan take tamkar Damisa ko Zaki . A zuciyar Munaya cewa take " Tabbas
Wannan Yarinyar bata san Waye Aydaaannnnn ba . Ba kuma tasan Irin fusataccen Zuciyar sa
ba . Tabbas don So yana Son Aaaliyah da badon hakan ba ,wannan Maganan ma ba zai bari ta
tsaya ta rinƙa faɗa masa ba . Aaaman ne ya matso cikin Sauri yana ƙoƙarin takowa zuwa inda
Aydaaannnnn ke Riƙe da Aaliyah sai ihu take tana Kirar Sunan Abba amma kuma bashi yasa
zuciyar shi yin salama ba . Wani irin kallo ya Watsa masa Aaman tare da ɗaga masa Hannu
yana dakatar dashi , Juyawa yayi da Fuskar sa yana kallon na Aaliyah dai dai lokacin A'aman
na cewa " A'a Aydaaannnnn Kar kayi mata Wani Abu , Cikin Salo da dubara zaka saye zuciyar
ta har ka samu gurbi a ciki ba ta wannan hanyar da ka ɗauka ba . Plsssss Aydaaannnnn Ka
saurare Ni .

Kai malam don Allah kayi mana shiru kana ji da kunnen ka wannan yarinyar zata na rinƙa faɗa
mun Abubuwa son ranta , Just because I love her? Wannan daman kaɗai ta samu take shirin
maida Ni yaron ta ?Hannun sa yasa yana ɗago fuskar ta yana kallon idanun ta da suke fidda
Ƙwallah masu raɗaɗi " Aaliyah kar Kiyi tunanin barazanar ki ,ko nuna tsana a kaina zai sa na
sauya Ra'ayi a kan ki ,No.! Ba zan taɓa daina Son ki ba saboda son ki ba a fatar baki na take
ba , daga Zuciya ne , haka yake pumping tare da gauraya da gaba Ɗaya ilahirin jinin jiki na .
Tabbas Maganan Ammmie gaskiya ne ,a baya nayi soyayya a makance ne , a kuma yanzu da
duka biyun nake , zanyi komai ma wanda yayi yunƙurin raba Ni dake ,koda ke kan ki ne.! Ina
Son ki a yau ,gobe kullum kuma a koda yaushe har izuwa numfashi na na ƙarshe . Wuce mu
tafi....! Ya ƙare Maganan yana fuzgar hannun ta . Tsorata Tayi sosai da yanayin sa , Dama ta
dade tana tunanin Lafiyar ƙwaƙwalwar mutanen Gidan Moddibo's Family , Musamman yanda
take ganin Suna lalata da junan su . A yau ne a kuma maganganun Aydaaannnnn ta tabbatar
mawa da kanta Cewan Yaran gidan basa da cikakken Ƙwaƙwalwa . Me kake nufi da ko Nine ba
zaka bari ba Indai na yi yunƙurin raba mu? To duka-duka yaushe ka Sanni ma? Ka cika mun
hannu na , ba zan tafi ba ,ba zan bika ba.... Aaliyah ki bishi Aydaaannnnn yana cikin Wani irin
yanayi wanda zai iya aikata komai . Aaaman yayi Maganan yana kallon Aaaliyah . Tsayawa
Aaliyah tayi a tsorace tana kallon Aaman tana ji tana Gani ya fice da ita yana saka ta a mota ko
tsayawa bi takan A'aman baiyi ba ya Jah Moton yana ficewa daga Gidan cikin Wani irin
mahaukacin gudu .

**

Ɓangaren Dangin Aaliyah kuwa an samu gutsiri tsoma a cewan su ,tun da suke basu taɓa
Ganin Aure irin na Aaliyah ba , Dangin Ango mutane ƙalilan ga cin mutunci , sam suka ce babu
Wanda zai zauna dasu sai Amarya . Hasali ma babu Wanda yakai Amarya ɗakin ta a matsayin
su na dangin Amarya . Duk dai Ƙananun Maganan da Dangin Aaliyah keyi Inna Turai ta toshe
kunnen ta , a zuciyar ta ita dai babu Abun da take yi sai fatan Allah ya basu zaman lafiya . Duk
da itama hankalin ta ya tashi Ganin su Hajiya Rahina da Momyn Hibba . Gafara Dai ,sannun ku
sannun ku.". Juyowa Inna Turai tayi cike da mamakin Ganin Hajiya mai riga wanda take Yaya a
gurin Abba ,Indai iya masifa ne ita kankat ne ,tsoran ta kowa keji . Cikin Rawar murya Inna Turai
tace " Hajiya Barka da Hantsi ?. Barkan mu dai Turai ,ashe kuma haka Abun ya kasance? Kun
ɗauki Marainniyar Yarinya kun ba ahalin da bamu san nagartarsu ba ?. Duka me yasa haka?
Eiyee ko don Saboda Mahaifiyar wannan Yarinya bata a raye ne akayi mata haka?. Shiru Inna
Turai tayi tabbas maganganun Hajiya mai Riga ya dafata sosai , A yanzu tana ganin Aaliyah
babu bambanci da itace wacce ta haife ta . Kuma wannan Abu tabbas in ba don ta ga Yaro na
Son Aaliyahn ba itama ba zata bari hakan ya faru ba . Muryar Hajiya Mai Riga taji a sama tana
cewa " Ko da yake bake ya kamata nayi magana dake ba , Shi Uban yarinyar da suka amshi
Auren ya kamata na samu . Juyawa Hajiya Mai Riga tayi fakan fakan da silifa ɗin ta tana gyara
mayafi ta fice daga Gidan . Kasa sukuni Inna Turai tayi wannan yasa ta aje Shinkafar da take
tsinta tana ba Sha'awanatu tare da cewa " Sha'awanatu ku cigaba da tsintar Ni Bara naje na
Dawo . Yaya Turai Don Allah kar Wannan magann ta ɗaga miki Hankali. ko kaɗan Sha'awanatu
babu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login