Showing 15001 words to 18000 words out of 27762 words

Chapter 6 - Yar Tsakar Gida Complete Hausa Novels By Aysha Maman Teddy .pdf

" Eh mana Noory nayi maka
Alƙawari zanyi Karatu don na zama kaman kai . Murmushi Nurain yayi yana cewa " to mu fara
mu gani . Bude littafin yayi inda farkon page din ya fara da ALPHABET.nan take ya fara karanta
mata A_Z . Wanda sosai yayi mamakin fahimtar Yarinyar. Kamin Mama Nanny ta kawo masu
Abinci ta kusa iyawa ,wannan yasa koda Ta hada masu abincin tana gama ci ta Cigaba da
karatu don ita so take ta zama kaman Nooryn ta.

Wuraren Karfe 6:30pm . Ta kammala karatun ta tasss ta iya kuma tasan Alphabet a ido da kuma
kawo shi a haddace . Kallon ta yayi yana miƙa mata uniform din da Aka wanke aka goge ga
sabon jaka da Farin safa. Noory Wannan ai ba kayan makaranta na bane ko?. Murmushi yayi
yana kallon Mama Nanny itama dake Murmushin kamin Tace " Amrah sune , kullum idan kin
dawo ki rinƙa kawo mun ina wanke Miki kinji . Na gode mama . Amrah tayi maganan tana kallon
Nurain dake ta kallon ta . Gobe idan kika kawo mun Karatun duka akan ki to bayan sayen
gyada da sanyi har kyauta zan baki . Dariya tasa sosai tana cewa " Da gaske Noory ? , Gobe
zan kawo maka duka..........
**
To yau dai da Alama Wannan Yarinyar ta shirya miki Asara Zuwai . Har yanzu ana kiran Sallah
amma shiru kake ji . Jummai ce mai maganan tana yi tare da surfe Wake . Kai Wannan yarinya
anyi tsinanniya . Tirr duk inda aka ce maka shege yake to sai ya nuna halin sa, Bara ta dawo ta
same Ni.... Assalamu alaikum Muryar Amrah ya katse su cikin sanyin nan nata . Kasa magana
duka suka yi ,ganin ta da Sabon kaya a jikin ta , sai Farantin gyaɗan data dora wankakkun
uniform din ta akai . Ehhhhh...??? Larai ta furta tana kallon su Baba Zuwai . Ke gantali kika fara
ko kuwa mene ? Wane ne ya baki kaya har da chanja Miki . Mun shiga Uku mu , kin san fa
yanzu a lungu ake lalube yara a ƙwaƙule su tasss . Babban magana dama an haife ta akwararo
yanzu itama zata haifo mana dan kwararo .............!

```Tallah```
Assalamu alaikum jama'a yau gaku ga buxuwa empire

Dakinga wannan page din indai ke mace ce to wannan page din nakune mata iyayen gida

Mata kamar yanda kukasani nicedai *buxuwa empire* wanda nake kawo maku kalolin
mallaka,farin jini,kiranye dadai sauran su

Hajiyata mijinki duk dafa'insa kixo nan inshallah zamuyi maki maganin sa inshallah

Mace mai zama da miji mara kyauta mai mako kitaho inshallah magana ta kare

Kina zaune da saurayi ana mashi mgnr yaturo sai su gudu ki taho inshallah

Mace mai fama da matsalar jinnu matar aure ko budurwa

Budurwar da akalla zata kai shekaru 25 bata taɓa saurayi ba ta kitaho da izinin Allah

Budurwa mai samari amma da yazo ana murna zuwa daya bazai sake dawowa ba lamarin dai
Allah shi gyara

Masu bukatar kiranye ko farraku tana iya mun mgn ta wannan number kamar
haka:08139762831

Kiranyen miji
Aiki da tumfafiya
Aiki da idon dabba wato kamar bita zai zai
Aiki kan shanu a soke shi a bishiya

Aiki da sokakken dabba amma dabban da aka yanka sai a samu laya kamar guda 313 a xiba
shi a duk wata organ �� ta ciki da ta waje

Zamu saka wani a idonsa a ƙwaƙwalwa aciki sannan a saka a kogo Hajiya ta mijinki he is sorry
� Allah ina fadamaki ai baya da tacewa sai naki

Sannan ana mawa yammata irin shi amma na kiranye cikin kwanaki uku xaki gansa a kowani
hali aure kawai yake so

Bana tausayin namiji fa inkinsan kina tausayin mijinki kinfiso yarinka azabtar dake a maikuwan
yarinka maki kyauta soyayya dake da yara ki da yan uwanki ba

To inkinfiso komai ki zauna a baya to gaskiya kizauna bansan yanda zan maki ba domin nayi
ma mijinki mallaka ko saurayi ko yaƙi ko yaso sai yabiki yamaki abinda kk so kuma kk bukatar

Mallakar zuciya mai allurai a baima kare mai bukatar tabini pc

Mai bukatar mallakar ko kiranyen bakin Ruwa tabini pc inshallah mgn yakare

Nidai nafiso acemun Hajiya inason komai da min da mijina kamar kaza ......... Ya rinka mun
kaza kaza

Please ko kinbini pc kigayamun abunda kk so direct

Matan da kayan sallah wani baiwa shi ba
Sha'anin yan uwanki bai san wannan ba

Lamarin ki da wasu kananan hidimomin ki sodayawa baya biyamaki bukata

Kije wani gida kiga matan gidan nayin abunda baki isaba kice dame tafiki dashi ga abinda tafiki

dashi din .....

Ga mata masu bukatar kayan da'a available suke cikin price mai saukin gaske inshallah da
masu aiki aciki da marasa aiki
Duk wacce take buƙata tana iya mun mgn ta:08139762831
Muna godiya ga mata bakiɗaya masoya mu mun
gode

*NASRULLAH DATA SERVICES*

_Reach out all for all your cable subscriptions at very cool rate (Airtime data, Tv Subs, prepaid
bills)at comfort at your home_

*MTN*
500MB ₦150
1GB ₦300
2GB ₦600
3GB ₦900
5GB ₦1500
10GB ₦2500

*GLO*
200MB ₦100
500MB ₦150
1GB ₦300
2GB ₦600
3GB ₦900
5GB ₦1500
10GB ₦2500


*AIRTEL*
500MB ₦200
1GB ₦350
2GB ₦700
3GB ₦1050
5GB ₦1750
10GB ₦3500

*9MOBILE*
500MB ₦150
1GB ₦300
2GB ₦600

3GB ₦900
5GB ₦1500
10GB ₦2500

*VALIDITY 30 DAYS*


*PAYMENT DATAILS*

ISHAQ NASIR
0778991869 | 7055852908
ACCESS BANK OPAY

*YOUR SATISFACTION IS CONCERN*

Follow this link to view our item on WhatsApp:
https://wa.me/p/6501220559940694/2347055852908

*To kaman yanda na faɗa masu buƙatar na tallah ta masu hajar su a page ₦2000 ne idan kuma
a Status ne ₦1000 kacal sai Kuyi mun magana ta WhatsApp number na 08081202932*


Mamanteddy
[7/27, 1:36 PM] Matar Mijin Ta: *ƳAR TSAKAR GIDA*
*Romance love and Sympathetic Story*


*Story and Written by Aisha Mamanteddy*

_Page 0 7_

*Littafin Ƴar Tsakar gida na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 Special
payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan
number 08081202932... Idan VTU transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*

Kallon su Amrah keyi sam ta rasa fahimtar inda maganan su ya nufa , abun ka ga karamin yaro
Hausan har a lokacin koyan ta ake yi,wannan yasa ta kallon Baba Zuwai tana cewa " Wallahi
Baba.....yi mun shiru...!! Ta daka mata Wani irin gigitaccen Tsawa tana mai Cigaba da cewa "
Nawa Ɗaya shine ki bani Kuɗi na casss Don Ƙwandala ya ɓata sai na sauya Miki kamanni da
Duka a cikin gidan nan . Cikin Rawar Jiki Amrah ta miƙa ma Baba Zuwai kudin ,jikin ta ko ina
Rawa yake yi ,tsoron ta ɗaya kar yazo kudin bai kai ba . Muryar Baba Zuwai ne y katse ta tana
faɗin " Allah ya cece ki sun cika , wuce Ki Dauki bokiti ke debo ruwa ki zo ga kwanuka can ki
Wanke su . Tom Baaba . Amrah tace tana Saurin wucewa ɗakin Ikilima don anan yanzu Amrah

ke kwana ita Ɗaya ,don ikiliman bata nan . Duk da A wannan shekaran zata dawo Gida
Shikenan kuma an gama Sakandire . Aje uniform din nata tayi tana saurin fitowa tare da Ɗaukar
Bokiti da Wannan yammacin tana nufar makoton su inda suke da rijiya don ta debo Ruwan
wanke wanken . **
Akwana a tashi babu Wuya shakuwa da soyayya tamkar yaya da Kanwa ya shiga tsakanin
Nurain da Amrah ,wacce a yanzu take cikin zakukwuran yaran Ajin nasu . A farkon Term din tayi
na Goma wanda a jarabawa na gaba tazo na Uku . Sam a yanzu bata damuwa da Fitinan cikin
gidan su da tsangwaman da take sha , Don idan sun ɓata mata tana fitowa zata shige Gidan Su
Nurain , Anan zai Amsa kayan tallahn ta ya rabar suyi hira tayi barci idan ta huta sai suyi karatu
. Sosai kokarin Amrah ke basa mamaki don kullum a zuciyar sa cewa yake " An kashe product
anan , Don bata yi sa'an Iyaye ba ,duk da a yanzu ya san ita marainiya ce . Wannan yasa shi
sosai yake bata kulawa ,ya zama mata tamkar uwa uba bango majingina . A yanzu har yakai ya
kawo sunan ta a makarantar ƙanwar Nurain ,don da yawa wasu suna mata kallon ƙanwar sa ce
.
Ihun Ɗaliban ne yasa Nurain Wanda a yanzu suke SS 3 kuma yana da muƙamin Headboy
saurin juyowa shi da duka abokanan nasa suna kallon inda Yaran primary din suke a layi .
Sunan Amrah ne ashe da aka kira a matsayin wacce tazo na uku yasa Ɗaliban ihu suna kiran
sunan ta Da Fine Girl fine girl don sunan da suke kiran ta dashi kenan . Tsayawa yayi yana
murmushin nan nasa yana gani Amrah ta fita cike da karsashi da gwarin Gwiwa ta ta amsa
Kyautar nata tana juyawa tare da kallon Ɗaliban tana mai ɗaga masu cike da fara'a . Juyawa
Nurain yayi yana kallon Abokanan nasa suna barin Wurin don ita Amrah bata Gansu ba ma . A
cikin Ajin su babu wacce Amrah ke shan Wuyan ta irin Naana bata da kirki ,kullum aikin ta
kenan bin ajijuwan tana cewa " Ai Amrah yar talakawa ce har tallah take yi , basu hada komai
da Nurain ba . Duk tana faɗin Wannan maganan ne saboda Tasan Familyn Nurain . Don da
mahaifiyar ta da Momyn Nurain ƙawaye ne sosai . Don a bakin Naana Mommyn Nurain ta fara
jin sunan Amrah da Halakar su da Nurain . Kallon Marian tayi tana dalla mata harara tare da
kallon Amrah wacce ta dawo inda suke tsaye . Bakin ciki ya ishi Nana do mun kuwa ita ce ke
daukar positon din da A yau Amrah ta dauka , ita kuma tayi baya don na Huɗu tazo . Humm
Wacce kike ne ? Amrah Ko? , Kar ki manta Wacece ke , Haka zalika kullum talaka a kasan mai
Arziki yake , Ki daina farin ciki don a yau kin zo na Uku a gobe ina nufin a kwana a tashi Ni zan
zama ta gaba dake , sannan ke matsayin ki ba zai wuce mai mun shara da goge goge ba .
Mtswwwww...! Saurin buɗe baki Marian tayi zata yi mata magana sai Amrah ta riƙe ta tana
Girgiza mata kai Alamun ta rabu da Naana don ita bata son tashin hankali gaba Ɗayan ta
,sannan kuma sam bata ji zafin maganan Nana ba ,don dama tasan Naana ba tsaran ta bane .
Duk Hutu suna Abroad kin ga ba zata hada kan ta da ita ba . Idanun ta sun ciko da ƙwallah
sosai Amma sai ta maidasu tana lallashin Zuciyar ta daba kan ta Haƙuri .
**
A hankali take kutsa kan ta Izuwa Falon Gidan ,cike da Sanɗa wai a dole tana so tayi surprising
din sa . Yanda taji Muryar nasa ne yasa ta saurin ƙarikawa inda yake , Sakin Takardar da
kyautan nata tayi a ƙasa Ganin Hawaye na bin Kuncin Nurain , Jarumin Namiji wanda ko karaya
bata taɓa Gani a idanun sa ba ,amma a yau taga Hawaye . Cikin nuna damuwa ya furta "
Please Mommy ki bari na kammala SS 3 ɗin After all sai na dawo America, idan na tafi Wane

zai kula da Amrah.? . Wacece Amrah ? , Muryar Daddyn shi ya katse shi cikin zafi ,wanda
da'alama mutum ne mai zafi , gobe zan sa a zo dauke ka , jirgin 11am zaku biyo zuwa America.
Tare aka haife ku da ita yarinyar ne ? , Ƙanwar Nusaiba tana SO ta ganka duk ta damu , yau ne
fa karin Shekarun haihuwar ka ,amma baka sai dai muyi ta kallon hoton ka . Shiru Nurain yayi a
zuciye cike da sangarci irin na yaran Hutu ya Datse kiran yana cilli da Wayar can Gyefe . Kallon
sa Amrah tayi a hankali ta kira sunan sa da " Nurain ...! Ɗago da sexy eyes din sa yayi yana
kallon ta kamin yace " Na'am Amrah . Meke faruwa ? Tafiya zaka yi ? Zaka koma America ne
inda Mommy da Nusaiba suke kaima?. Duka a lokaci daya take jero masa tambayoyin nata .
Cike da son kawar da damuwan sa ya kalle ta yana kafe ta da idanu,kawai sai taga ya zaro
mata idanun sa yana tsora ta ,saurin bata tayi ,nan take ya hau yin mata Dariya yana faɗin "
Matsoraciya . Taho muje kasa palour . Bin bayan sa tayi tana faɗin " Nurry ka daina tsorata Ni
da yawa haka .

Me hoto ta gani a tsakiyar falon , yayin da Nurain ta kalle ta yana cewa " Amrah today I'm + 1 .
Wow Happy birthday Nurry . Murmushi yayi yana rike hannun ta tare da furta " Thank you
Amrah . Cake din da Mama Nanny ta kawo masu ne Amrah ta kallah kamin ta tsinkayi Muryar
sa yana cewa " Mama Shigo Mai Photograph yana jira a dauke mu duka . Rungume Nurain
Amrah tayi a tare suka dau hoton wanda yawan su yafi talatin fiye da Ashirin suna tare daga ita
sai shi suka yi shi . A wannan rana sun wuni cikin nishaɗi har wuraren yammaci . A farfajiyar
Gidan ne ta kalli Nurain tana cewa " Nurry ina keken ka yake.? Juyawa Nurain yayi yana kallon
Can Gyefen Garden kamin yace muje can ki gani . Kai tsaye suka nufa Garden din Nurain na
fiddo da keken sa Taho ki hau . Yayi maganan yana kallon Amrah don yasan Abun da take so
kenan . Kallon sa Amrah ta tana masa dariya tare da cewa " yeeee tana saurin hayewa ta
gaban shi yana fara juyi da ita a keken suna kaiwa da komowa a tare . Su kan su basu san
mintunan da suka ɗiba a hakan Amrah ..... Taji Muryar sa ya kira sunan ta. Ɗaga idanun ta Tayi
tana kallon sa fuskar ta cikin matsanancin fara'a ,Kiyi Haƙuri kinji..." Uhmm mene kayi mun
Noory.? Murmushi taga yayi mata yana Girgiza kan sa tare da cewa " ba komai . Kallon sa Tayi
tana jin akwai wani Abu kamin tayi masa magana Muryar Mama Nanny ya katse su tana faɗin "
Dare fa ya fara yi , Amrah ta tafi Gida haka . Sauka Amrah tayi daga keken tana kallon Sa tare
da daga masa hannu tana faɗin " Sai da safe. Ba zan jira ka ba gobe makaranta xan tafi ,idan
ina jiran ka Zango daya ke wuce ku kullum . Idan kazo school ma haɗu . Juyawa tayi da gudu
tana barin Wurin . A hankali Nurain ke sauke Numfashi don ji yake tamkar zuciyar sa zata
tarwatse. Idanun sa na fidda Hawaye masu zafi da raɗaɗi .

Kama hannun sa Mama Nanny tayi tana nufar palour dashi . Nurain kayi hakuri Kabi maganan
iyayen ka , ko mun daɗewa wata rana zaku hadu da Amrah . Tafiya ba mutuwa bace ba . Mama
yanzu ba yanda za'a yi Amrah tabi Ni mu tafi America,ko na roƙi Baba Adamu ?. Cikin Sauri
Mama Nanny tace " A'a Ba zai yiwu ba ,ko itama Amrah ba zata bika ba . Rintse idanun sa yayi
yana cewa " ki haɗa mun kayan da zan tafi dasu . Gyada masa kai Mama tayi kurum tana gani
ya wuce ciki ,a zuciyar ta hamdala take yi daya amince da tafiyar nasa do mun kuwa
bakaramun fada ta sha ba a gurin mahaifin sa , a cewan sa tayaya ta bari har Wata mu'amala ta
shiga tsakanin sa da yar talaka...?
**

Zama yayi a kasan tiles din yana bin gift din Amrah da sakamakon jarabawar nata da kallo . A
hankali ya kankafe yana yo kasa dasu tare don yaba Mama ta sanya masa a jakar tafiyan sa .

Safiyar Alhamis .
Zaune Amrah take a cikin Ajin suna fira da ƙawayen ta . Kaman Ance ta juya idanun ta ya
sauka akan Naana dake mata wani irin Dariya . Humm sauke Numfashi tayi a hankali tana
Cigaba da Rubutun ta a haka har aka Tashi break . Marian ina zuwa ko zaki rakani Secondary
Section . Hahaha....Uban me zakiyi a secondary section din.? Muryar Naana ya katse ta ,
takowa tayi gaban Amrah tana faɗin " Nasan Wurin Nurain Zaki je ? Shin baki da labarin Nurain
ya koma America da zama. ? Kirjin Amrah ne ya buga daaam . Ai ba zaki ƙara ganin Nurain

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login