Showing 21001 words to 24000 words out of 27762 words
Chapter 8 - Yar Tsakar Gida Complete Hausa Novels By Aysha Maman Teddy .pdf
a haka ba . A Miskilance ya miƙe yana jan Rigar Wankan sa dake saƙale
yana gyarawa tare da zuro ƙafafun sa yana saka Toilet siliper ɗin sa . Ɗaga idanun sa yayi yana
kallon kansa a madubin Bathroom ɗin , fuskar Wannan yarinyar data shigo yanzu ya gani Wato
Amrah ,wannan yasa shi saurin juyawa Yana kallon Bayan sa ,amma sai yaga bata nan ,
murmushi yayi yana shafa Sajen fuskar sa tare da gyara rigar jikin sa ,inda faffaɗan ƙirjin sa ya
bayyana ,ga suma ya rufe luff....Huhhhh Ya furzar da iska yana ƙare ma kan sa kallo tare da
ɗan faɗawa tunanin Wannan yarinyar da ya fahimci babu shakka cleaner ce . Ni kuwa ƙare
masa kallo nayi kyaƙykyawa ne sosai kaman balarabe don idan a ƙasar can na gansa to babu
shakka zance masa Balarabe saboda kyau sa . Yana da yan matsakaitan Idanu amma a
ƙaƙƙafe suke dagani kasan babu kunya a cikin su . Dogo ne sosai tsayayyen ingarman Namiji
wato Sexy .
**
Mom Cruzita ne suka haɗu da Amrah Wacce take haki gaba ɗaya ta Fita a hayyacin ta . Wani
irin kallo Mom Cruzita tayi mata cike da Tsawa take fadin " Kin kammala Aikin naki ne?. Jikin
Amrah na rawa tayi saurin Girgiza mata kai Tare da cewa " Eh. Tana saurin wuce ta don
Hankalin ta ya tashi kai tsaye nufar ɓangaren su tayi tana ɗaukar Hijabin ta tare da ficewa daga
Asibitin ba tare da kowa ya sani ba .
Shiga Office din nasa tayi ,ganin komai ƙal yasa ta kokarin juyawa . Amma sai taji motsin sa
daga ciki wannan yasata dan dakatawa har ya fito yana gyara Necktie ɗin sa . Good morning
Sir . Tayi maganan tana dan risinawa . Morning mam Cruzita . Aammm Wannan yarinyar
ahmmm .... Dan kame² ya tsaya yi mata a Miskilance,wannan yasa Mom Cruzita saurin cewa '
Sir cleaner ce ,Fatan batayi maka Wani shirmen ba ,don akwai ta da shauni . No jeki kawai idan
ina bukata wani abu i Will let you know . Ohk Sir . Tayi maganan tana barin Office din .
Nufar Table din sa yayi yana ɗaukar Wayan sa tare da fara kiran numbern Aminin nasa dake
Abroad....
**
Bayan Fitan Amrah kai tsaye GRA ta nufa gida na biyu ta shiga inda zata roƙe su tana masu
Aikatau . Cikin ikon Allah Shamakin Hajiyar Gidan ta amince da ita ,ganin yanda taga Amrah
yasa ta yaba da natsuwar ta nan take ,kuma ta shaida mata Albashin ta a wata dubu goma .
Sosai Amrah tayi farin ciki da hakan ,don a washe gari suka ce ta fara zuwa aikin ta .
A washe gari Asibitin Zaid ta fara zuwa ,inda Mom Cruzita tace taje Office din sa ta Yi
cleaning,amma sai ta nuna kaman bata Fahimce ta ba , wani Office din taje tayi ,tana gamawa
ta lafe ta buya tana ji ana neman ta amma ta gudu wani reception din na majinyata tana aikin a
can . Ƙarfe biyu tana fitowa ta nufi Gidan Data samu Aikin . Kai tsaye Falon Hajiya Sa'adah aka
nufa da ita . A ƙasa ta zauna kaman yanda taga shugaban nasu tayi . Ƙamshin turaren Hajiya
Sa'adah ne ya mamaye palourn wacce take saukowa daga Upstairs din tsakiyar falon . Fuskar
ta ɗauke da fara'a take kallon su , don ita Amrah bata Ɗago ta kalle ta ba . A'a Hadiza Wannan
itace Yarinyar.? Eh Hajiya itace . Jin haka yasa Amrah Ɗagowa tana kallon Hajiya Sa'adah dake
zama a daya daga cikin kosassun Kujerun palourn . Kasa motsa bakin ta tayi tana kafe Hajiya
Sa'adah da ido kyaƙyƙyawar Hausa Fulani ce ,baƙa mai kyau . Ƙwaƙwalwar Amrah ne ke juya
mata ina nasan Wannan fuskar . Ganin haka yasa Hajiya Sa'adah cike da fara'a cewa " ya
Sunan ki.? A hankali Amrah tace " Barka da Warhaka Hajiya . Yauwa ya sunan ki ne?. Sunana
Amrah . Kallon ta Hajiya Sa'adah tayi tana dan yin shiru kana daga bisani tace " Kin san dai
Aikin naki ko ? Zaki rinƙa yin Abincin Dare ko wani lokaci , sai dai ki tabbatar karfe 7:pm kin
tanadar mana dishes din mu a Dinning . Ok Inshallah Hajiya . Yauwa Hadiza kuje ki sanar mata
sauran Aikin ta ,sannan a fara bata Girkin a yau mu ji kalon nata dandanon . Ok inshallah Hajiya
. Hadiza tayi maganan tana kallon Amrah suna Miƙewa tare da nufa babban kitchen din gidan .
A zuciyar Amrah cewa take waye Alhajin gidan nan ne ? Kila soja ne , don taga Sojoji dake
yawo ko ina a gidan ,sune masu tsaron Gidan .
...7:00pm ...
Komai na Dinning ya kammala don a dai dai Wannan lokacin Kunun Aya take Aje masu a
Dinning ɗin don time table ake bi ,yau suna da jaloap Rice da farfesun Kaza sai kunun Aya da
Salad dasu waken Gwangani daga gyefe . Bin kujerun wurin tayi da kallo guda kusan takwas .
Amma Babu mutum ko ɗaya da ya fito . A hankali take jin motsin Isowa ana dan dariya cikin
Muryar ta tana furta " Ok dear miss youuuu uhmmm . Saurin juyawa Amrah tayi suna yin ido
Huɗu da fuskar da ta sani farin sani . Wato Naana . Sauke Wayar Naana tayi tana nuna Amrah
da Hannu tare da cewa " You....? Kece anann.? Kawai sai ta sheƙe da wani irin Dariya tana tafa
hannu tare da ƙarikowa gaban Amrah tana gyara Top din rigar ta ,don English wears ne a jikin
ta riga da Wando . Didn't I told you ? , Ban faɗa Miki ba Amrah ? Yau ina postion din Naki ,kar ki
manta a Class ni kika doke nazo na hudu kina yar talaka kika zo na Uku . Na faɗa Miki dama
Wata rana kece zaki mun shara da wanke² yo gashi,yanzu kece mai girka mana Abinci da
Sharan ma duk Abin da muka so shi Zakiyi mu biya ki yar talaka . Shiru Amrah tayi idanun ta na
kallon ƙasa .
Dafa ta Naana tayi tana cewa " Zan baki Albishir Uku zuwa Hudu wanda nasan zai shiga
Kwanyar ki da kyau tilent Class . Humm Numfasawa tayi kana tace " Na farko A yanzu ina da
takardan Digiri a hanyar nursing a yanzu ina basic nursing wato masters . Kefa? Hahaha nasan
Ina ko secondary ba'a gama ba . Na biyu kin san dai yanda mutanen Gidan suka tsani talaka
musamman Daddy baya son ido biyu da talaka. And na uku Humm kina da labarin Nurain ya
manta dake da Rayuwar ki ma, don kuwa tun da ya bar kasar nan shekara fiye da goma sha bai
dawo ,saboda ya manta dake da Rayuwar ki , Sannan na hudu nan da Watanni Biyu zan Zama
matar Nurain.....!
Saurin Ɗagowa Amrah tayi tana kallon Naana kamin a sanyaye tace " Ina Noory yake ?. Kaji
dabba ... Naana ta katse ta , ina zaki ga Nurain har yau bai dawo ba ,sai dai a satin nan zai
dawo amma yayi Miki nisa mutumin da securities din sa Sojoji ne ta ina zaki tunkare sa . To
yanzu dashi na gama waya , Sannan nan Gidan ba gidan kowa bane Fache Gidan iyayen
Nurain..... Hajiya Sa'adah itace Mommyn Nurain....ke Da'allah zo ki zuba mun abinci naci na
tashi...................
*This is just the beginning yanzu muka fara✍ free page yana dab da karewa maza ki
hanzarta Wajen mallakar taki Regular payment ₦500...Vip payment ₦1000... Special payment
₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number
08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki mun ta wannan number 09061466409*
```Tallah```
Assalamu alaikum mata yan uwana namaku kunyimun Allah ka bar zumunci ya shiryar mana da
zuri'a ameen
Dafari kuma san idan *buxuwa empire* da ta doso kunsan taimako ya kawo ta Allah ka
taimakamana ameen
Hmmm to mata nasan dacewa kuma kun sani duk wata mallakar da takai bakin mallaka ko
dadai tarihi baya canjawa kan cewa indai mijinki ya shiga list din aikin buxuwa empire topah
hajiya ya riga da ya gama mallakuwa sai kuma Allah he is sorry Allah ka mana jagora
ameen
Mallakar lilin kaza
Mallakar rushii
Mallakar gaban da namiji
Mallakar masai
Mallakar kwai
Mallakar ayoyi da sirri na surorin mahaliccin mu
Mallakar da muke samun hanta muja da sunansa danaki a dake da magungunan hadin mu
Farin jinin warwaro mai kaman kiranyen
Kiranyen toxali mai kamar bita zaizai
Kiranyen bakin Ruwa
Mallakar dauji,ko kiranyen saurayi ,ko macen da bata da cikakkun samari masu ajii to inkinga
kawarki dawannan to aikin cikin dajine masu yi dawanda nayomasu sunsan yanda yake yi
kamar yankan wuka topah hajiya bazama
Kitaho Gurin Hajiya *buxuwa empire* da tayi maku wannan kalolin aikin da zarar kinbini pc
please kifadi abun da kk so direct Saboda mutane sunyi mun yawa Allah
Matar da tashirya aure ko kinason amsar kudi wajensa ko kina buƙatar ayi masa farraku da
yammata ko wacce mace ,mallaka
Masu bukatar kayan da'a available suke cikin price mai saukin gaske masu aiki da marasa aiki
available zaku iya yin mana mgn ta wannan number kamar haka:08139762831
Muna godiya ga mata bakiɗaya masoya a ko ina mngd
[7/29, 2:12 PM] Matar Mijin Ta: *ƳAR TSAKAR GIDA*
*Romance love and Sympathetic Story*
*Story and Written by Aisha Mamanteddy*
_Page 0 9_
*Masu tambaya na complete na wannan littafin don Allah kuyi hakuri ku sani wannan littafin
sabo ne yanzu nake rubuta shi ba complete , yanzu nake rubuta labarin nawa . Sannan kuma
littafin na kuɗi ne a next page 10 Free page zai ƙare . Maza ki hanzarta don ki mallaki naki ki
kuma yi karatun ki cikin Aminci da Kwanciyar hankali* *Littafin Ƴar Tsakar gida na kuɗi ne Regular payment ₦500 Vip payment ₦1000 Special
payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan
number 08081202932... Idan VTU transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409*
Yanda Naana ta Daka ma Amrah Tsawa yasa ta a hankali takawa tana nufar inda take tsaye .
Zama a ɗaya daga Kujerun Dinning ɗin tayi tana daura kafa Ɗaya kan Ɗaya tana Girgizawa .
Ɗaukar Plate Amrah tayi tana kokarin buɗe Rice bowl din ne taji Muryar Naana tana cewa "
Kama ta yayi kome zaki yi ki tambaye Ni bakiyi gaban kan ki ba ,ko kin manta matsayin ki ne
na tuna Miki.? Ɗan kallon ta Amrah tayi kana ta motsa laɓɓan ta a sanyaye tace " Kiyi Haƙuri,
mene kike buƙata a farko .... Ohh My daughter Ina Nusaiba take.? Muryar Daddy ya katse ta
Wato Alh Mubashshar . Juyawa Naana tayi tana murmushi kana tace " Daddy...ganin Momy a
gyefen shi ashe tare suka ƙariko yasa ta cewa " Daddy , Mommy yanzu zata Sauko .
Ja ma Daddy kujera Amrah tayi cikin sauri yana zama yayin da Mommy ta zauna a Gyefen shi .
Ga sabuwar mai aiki fatan zakuji daɗin Abincin ta . Hummmm To Mommy bari mu dai muci muji.
Barkan ku da dare . Amrah tayi maganan jiki ba kwari , murmushi Mommy tayi tana cewa "
Thank you my dear , Zaki iya tafiya Bara Ni nayi ....No mommy ita fa mai aiki ce just allow her to
Do her Work ,wannan Aikin ta ne fa . Cewan Naana tana bin Amrah da Wani irin kallo na Wutan
Ƙiyayya . Amma naga tayi kokari ai duka wannan ita tayi shi , at least she need to be rest . Ba
Aikin ta bane ? , ki barta tayi Aikin ta , ai shi iyayen ta suka turo ta tayi , to Meye ma Abin
tausaya ma Talaka ? , Mutanen da zaka yi masu Rana suyi maka Dare . Bana son ƙara jin haka
daga Bakin ki . Muryar Daddy ya katse su , wanda daga ji kasan mutum ne kosassan tsohon
dan boko , wanda basu dauki talaka da Wani ƙima ko daraja ba . Hasali duk idan suka ga
Talaka to ƙiyayyar su a kan su baya ɓoyuwa .
Shiru Mom tayi tana jin ba dadi sam , A hankali Amrah ta fara Aikin ta tana aje masu Abin da
suke buƙata wanda tana haka Nusaiba ta ƙariko inda suke . Mamaki ne ya kama Amrah Ganin
yarinyar bata da banbanci da Yaran Turawa wanda basu san darajar kan su da jikin su ba .
Ashe Naana shigar mutunci ne a jikin ta , ita kuwa Nusaiba irin Ƙaramin Matsatsen Wandon nan
ne a jikin ta iya cinya . (Bom short) . Sai normal rigar ta iya Qugu . Kunnen ta maƙale cikin Head
phone , hannun ta dauke da Wayar ta kirar Iphone 14. Jan Kujerun tayi tana zama yayin da
Amrah ta ke Tambayar ta Abun da take buƙata ,a maimakon ta bata Amsa sai A wulaƙance ta
daga mata hannu tana dakatar da ita . Humm Sauke Numfashi tayi a hankali tana ja baya tare
da yatsawa tana mai jiran Umarnin su . Kunun Ayan Naana ta fara zubawa a Glass cup tana
kaiwa bakin ta Muryar Nusaiba ya katse ta tana cewa " Daddy Ya Nurain Nan da Kwana Biyu
zai dawo . Saurin Ɗagowa Amrah tayi tana kallon Nusaiba ,yayin da bakin ciki ya tokare Zuciyar
Naana . A fusace su dai kawai sun ga ta sheƙa ma Amrah Ragowar Kunun tana Fadin banza
dabba ,wannan Wani irin Abu kika yi ma mutane ba Daɗi ba daɗaɗawa ?. Wani irin Ajiyar zuciya
Amrah taja mai ƙarfi da sanyin Kunun har bargon ta . Nan take idanun ta suka fara Fidda
Hawayen, jikin ta ko ina Rawa yake yi karrrr³ . Uhmmm Uhummm . Nusaiba tayi maganan tana
dan kallon Inda Amrah ke tsaye tare da bin ta da kallon sama da ƙasa kana tace " Mom wannan
yarinyar yaushe ta fara Aiki .? Tun da ba ta iya abincin ba ta koma bangaren masu shara da
goge² mana it's Will be simple . Juyawa Hajiya Sa'adah tayi tana kallon inda Amrah ke tsaye
gaba Ɗaya Naana ta gama tsuma mata jiki . Amrah zaki iya tafiya Gida yanzu sai gobe ko.? .
Cikin Sauri Amrah ta juya tana barin Wurin yayin da Daddy ya mike yana kallon Naana yana
cewa " Idan basa buƙatar Girkin ta Acan masu wata mana .? Ok . Mom tace tana kallon yaran
mata su biyu . Barin Dinning room area din yayi yana nufar Under ground inda Apartment din
shi yake . A hankali Nusaiba ta fara zuba kunun Ayan tana sha , wanda kurba daya ta ɗago
tana kallon Naana cike da mamaki tace " Naana Wai Meye kike ce ba daɗi ? ,Ohh Mom Sha kiji
mommy dadin gaske wallahi ,ban taba shan Wannan abu mai dadin wannan ba . Kallon Ta
Hajiya Sa'adah tayi kana ta kalli Nusaiba wacce take cin Abinci tana yamutsi sam bata tanka
Nusaiba .
Gaskiya Naana ina tunanin may be daga bakin ki ne , amma Wannan ai daɗin shi yayi yawa .
Tsakanin Mom da Naana babu wanda ya tanka Nusaiba wacce ta janyo jug din gaban ta tana
sha hankalin ta kwance.
**
Mom Cruzita ne ta kalli Amrah cike da masifa take cewa " Duk ranan da kika kara missing wani
Aikin ki , to abu biyu ne zai hada Ni dake , ko na Kore ki ,ko na baki Half Salary a watan . Na
lura dake kwana biyu kin maida mutane kaman dodon Ni . To kin san Aikin ki ba sai na tuna Miki
ba Gaskiya, Ni kawai Abun da yasa kika ga ina tura ki cleaning saboda yanda mutane ke son ki
a lokaci guda zan ji suna firar ki wannan shiyasa . A yanzu a aikin ki na ƙara Miki duk safe kina
rinƙa zuwa Office din Doctor Zaid kina masa Aikin sa . Yanzu Rana tayi kalli Lokaci Amrah ?
Sha daya na rana sai yanzu nayi ido dake ? , Na tura masa Su Hajara yace yafi yabawa da
Aikin ki , ko mun rana idan kinzo kije kiyi masa . Don haka kiyi sauri ki tafi yanzu ,idan kuma kin
gama kizo ina son ganin ki . Cike da Sassanyar Muryar ta tace " Tom Mam Cruzita amma don
Allah Kiyi Haƙuri...A'a No next time bani Zaki yi ma laifi ba , Oga ne ,don kin ji dai Cleaning din
ki yake so ba na kowa , so You have to maintain . Ok mah... Amrah tayi maganan cikin sauri
tana juyawa tare da nufar benen da matakalan shi kadai ya isa ya sarar da mai tafiya akai .
Wannan yasa Wasu suke bin lifta don Asibiti ne yanda kasan a Turai haka yake . Amma su
cleaners dole su bi matakala ko mun tsayin shi .
A bakin Office din ta tsaya tana kai hannun ta tare da murɗa Handle Door ɗin . Muryar sa taji
yana fadin " You no what ? Na haɗu Wata fine girl, which really love her ba wasa ...shigowan
Amrah yasa Zaid Aje wayan sa a Gyefe yana kallon ta , sam ta kasa hada ido dashi don kallon
Wani irin Ƙwarto take masa . Haka shima ya gagara dauke idanun sa daga Kallon ta . Excuse
me Sir. Tayi maganan tana dan Ɗagowa tare da kallon sa . Hummmm Wani irin gwauron
Numfashi ya sauke kamin ya miƙe daga Zaunen da yake yana kallon ta tare da cewa" me yasa
jiya bakiyi taking Excuse kaman haka ba? Kika faɗo mun Privacy ? , Fatan dai kin iya barci