Showing 24001 words to 27000 words out of 27762 words
Chapter 9 - Yar Tsakar Gida Complete Hausa Novels By Aysha Maman Teddy .pdf
,abun da kika gani bai hanaki barci ba ko.? Tsammm Tayi tana ƙasa basa amsa mintuna uku
yana expecting yaji wani Abu daga bakin ta but she make silent ,Amma sai tayi shiru ,hakan
yasa shi Fahimtar tana Miskilance...hummmm . Ya numfasa kana yace " Oya zaki iya fara Aikin
ki . Sum.sum tayi tana wuce shi tare da nufa inner Room ɗin shi . Ba laifi yau bai watsar da
komai kaman jiya ba . Nufan Bakin gadon sa tayi tana kokarin sauya Bedsheet din a zuciyar ta
tana cewa " Oh wai nan Asibiti ya dauka ko Gida.? Motsin shigowan sa yasa ta saurin juyowa ,
kallon kallo suke ma juna yana Sakin mata Wani Murmushin da ta kasa fahimtar menene
manufar sa na yin hakan . Tun karo ta yake yi yana takowa zuwa inda take . Nan take Amrah ta
rasa inda zata nufa ,wannan yasata nufar Hanyar Fita da gudu ,wanda tana isowa yayi caraf ya
riƙe ta . Mutsu² take yi tana kokarin kwace kan ta ,amma nan taga ikon Allah hannu daya yasa
yana kama hannayen ta duka biyun wanda motsi ta kasa . Sai fara masa kuka da tayi . Don
Allah,don Allah ka rabu Dani ....Ka rabu .....Wayyooo naaaa.....Maganan ta ne ya Datse ganin
yanda ya wurga ta saman Gadon sa yana haye mata tare da jan rigar aikin nata yana yagawa
ƙyaaaaaaaaaaaaaaa.............!
*Kuyi hakuri posting din yau ba yawa , muna biki ne sai mun hadu Posting din gobe wanda
kuma zai zama last Free page , daga shi ba zaku kara ganin pagen kyauta ba . Sai an biya kudi
nasa ka mutum a group .ga masu ɓukatar yin payment regular group ₦500 Vip group ₦1000
SPC ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan
number 08081202932*
*Aysha Mamanteddy*
[7/30, 2:19 PM] Matar Mijin Ta: *ƳAR TSAKAR GIDA*
*Romance love and Sympathetic Story*
*Story and Written by Aisha Mamanteddy*
_Page 10_
Last free page
Daga Wannan page Ɗin free page ya ƙare ga masu buƙatar cigaban wannan labarin regular
payment ₦500
Vip payment ₦1000
Special payment ₦1500 ,sai ki turo da kuɗin ki ta Wannan Account details 6037312299
mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932...idan Vtu
transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409 na gode ..! Don Allah daga Wannan
page duk inda kika ga page 11 zuwa sama to na sata ne ,kar ki karanta , ki biya kawai ki
karanta Littafin ki cikin aminci da salama na gode .
Sannan ina kira ga masu karanta mun littafai free don Allah ku dakata ,don sanin kan ku ne
littafaina na kuɗi ne ,masu sayar mun da littafai Wallahi ku rinƙa tuna gobe ba yau ba , Wannan
haƙƙi na ne ,ba Wani kuɗi ne mai yawa dasu ba kawai ki biya yafi Miki sauki kin san Wannan
saya kikayi a hannun marubuciyar ,idan kina buƙata ga number na contact me Ina da Enough
time inshallah da zaki samu ko mene kike buƙata . Masu karanta mun Littafai suna maida mun
shi izuwa Audio na faɗa bana buƙata please . Ga masu buƙatar karanta complete document
ɗina ga sunayen su a ƙasa Sannan kuma ga kuɗin ko wanne nan , so You chat me up
08081202932. Idan kudin ki zaki tura kai tsaye ga account number na 6037312299 mohammed
Aisha keystone bank don Allah mu kiyaye....!
```Littafaina```
Ƴar Aiki na ₦200
Dijama yar Fulani ₦300
Walijaam ₦500
Siyasata ₦300
Ƙwarton manya ₦500
The virgin maid ₦500
Bafullatanan Ruga ₦300
Yar Waye ₦200
The Sexy Boss ₦500
Taɓarah ₦500
Zuma da Maɗaci ₦300
My Lady boss₦500
Ƙwaryar sama ₦300
Duniyar shahara X world ₦600
Fyaaɗe ₦1000
Gidan Ƙwarata ₦300
Gidan Zaurawa₦500
Yar maula ₦300
Idan kina buƙata ga kuɗin su nan sai ayi mun magana .
Tun da ya haye saman ta tayi laƙwaam motsi ta kasa yi sai nishi da take yi sama sama . Idanun
ta fal tsoro haka nan takasa Jajircewa wurin hana su zubo da Marayun Ƙwallah Wanda ta san a
yanzu bata da maceci sai ALLAH . Kallon Idanun Zaid Amrah keyi tana Hawaye tare da Girgiza
masa kai alamun yayi haƙuri ... Zuba mata tsayayyun idanun sa yayi na rashin tsoro ko ɗar
kusan mintuna biyu suna a haka , Gaba Ɗaya A iya Wannan lokacin Amrah ta gama jiƙewa da
Zufa da Hawaye. Haka ta kasa risinar da idanun ta daga kallon kyaƙyƙyawar fuskar Zaid . Gani
tayi ya sakin mata Murmushi yana ɗaga mata Gira tare da cewa " Meye Sunan ki.? . Lumshe
idanun ta tayi Wasu Hawayen na zubo mata sam ta kasa masa magana bare ta basa Amsan
tambayan sa a yanzu ita dai hanya ɗaya take nema Wato Hanyar Guduwa . Uhmmm Ya sauke
Wani irin gwauron Numfashi a zuciyar shi yana cewa" Ni yarinyar nan zata kawo ma miskilanci
? Duk miskilancin ki naga Nawaaf wato ƙanin sa . Juyawa yayi da kallon sa gyefe yana tunanin
mene zai mata ? , Mutsu² ta fara yi masa tana kokarin Ɗagowa daga dannan da yayi mata
,kawai sai dai taji hannun sa yana shigarwa tsakiyar Rigar ta da ya dirar ta tsakiya , braziyan ya
bayyana da duk Wani Albarkatun ta . Rintse ido tayi tana fashewa da kuka a hankali cike da
sarewa , cikin Sanyayyar Muryar ta Wanda duk yunwa ya cinye tace " Kayi Haƙuri Don Allah. Ji
yayi zuciyar sa na ingiza shi amma kuma sai ya janye Hannun sa daga Saman Breast din ta
yana cewa " Ya sunan ki ?. Motsa ƙaramin bakin ta Amrah tayi tana furta " Sunana Amrah ,ta
ƙare maganan tana ɗago da Lulun idanun ta tana kallon reaction din sa zai barta ne ya rabu da
ita ,tayi masa aiki ? , Ko kuwa still yana nan kan bakan sa ,yana so ya keta mata haddi?.
Ɗagota taga yayi yana mannata ta da ƙirjin shi tare da Rungume ta tsam , Amrah ina Son ki ...!
Saurin ware idanun ta Amrah tayi jin maganan nasa take tamkar saukar Aradu. Nan take
zuciyar ta tafara mata wasiwasi ,to me yake nufi.? Wata zuciyar ne ta bata Amsa da cewa " eh
yana son yayi lalata dake ne yaci Miki mutuncin ki . Ɗago ido tayi tana kallon sa yanda ya
kafeta da idanun sa yasa ta saurin gasgata zuciyar ta. Kuka ta fashe masa dashi tana cewa "
A'a wallahi , don Allah ka rabu Dani Wallahi Ni ba yar iska bace . Wayyo na shiga Uku Ni Amrah
zai rabani da mutunci na ...me nayi maka ? . Shiittt yayi maganan yana raba jikin sa daga nata
tare da miƙewa tsaye yana dafe kan saman Goshin sa . Ohhhh..... Ya furta yana juya mata
baya. Ganin haka yasa Amrah Saurin miƙewa tana janye jikin ta daga Gadon tana kokarin
Ficewa da gudu . A bakin ƙofan ne taja ta tsaya tana kallon rigar jikin ta yanda suka yi kokawa
ya kyeta mata tun daga Farkon shi har ƙasa. Hawayen idanun ta ne suka ci-gaba da Zubo
mata , Wanda Daga bayan ta ne taji Muryar sa yana cewa " Ki dawo ki zauna yanzu zan saka a
kawo Miki Wani kayan sai ki sauya Wannan . Juyowa Amrah tayi tana bin sa da kallo idanun ta
na Hawayen jin Haushin sa da tsoron sa .
Amrah Da gaske nake Ina Son ki , kuma nasan ke ba yar iska bace kanana ko? Yayi maganan
yana takowa zuwa inda take , kasa motsi tayi tana kallon sa . Amrah ina Son ki tun a ranan
farko da kika shigo Toilet kika ganni ciki , Yanda kika yi shi ya dauke mun hankali daga kallon ki
, shi kuma yasaka naji Soyayyar ki a zuciya ta . Ba kaman yanda kika gan mu a Wancen Ranan
za muyi Rayuwa dake ba , Aa mu namu rayuwar na Ma'aurata..., This is the first time Dana fara
mafarkin ganin nayi Aure har naji na shirya rabuwa da duk Wasu .....Wayyo kaina ..! Amrah tayi
maganan tana dafe kan ta da jiri ke diban ta ,gaba ɗaya ta gama galabaita a hannun sa ,
dannen ta da yayi ji tayi kaman an daura mata dutse don ko motsi ta kasa yi a wannan lokacin,a
yanzu kuma idanun ta basa ma gani da kyau saboda yunwan dake cin hanjin ta .
Saurin isowa kusa da ita yayi yana kama hannun ta tare da cewa " Amrah ....Yanda ya riƙo ta
ne yasa Amrah saurin yin baya tana daga Hannun ta tare da Wanke fuskar Doctor Zaid da Mari
tasssss. Cikin sanyin Murya ga duhu da bata iya ma ganin shi da kyau take faɗin " Doctor ka
rabu Dani , Ni ba yar iska Bace , ka rufa min Asiri,kar ku cuce Ni mutuwa zanyi a hannun Baaba
Zuwai zata kashe ni..........luuuuu tayi tana yin baya tare da kokarin zubewa anan . Saurin Kara
riƙota yayi a wannan karon da jikin sa ya hadata yana Rungume ta tare da Girgiza ta yana kiran
sunan ta Amrah...! Amrah...!! Zafin Jikin ta yasa shi saurin daukar ta cak kaman yar baby yana
nufar Gadon sa tare da Kwantar da ita cikin Sauri. Fuskar ta ya shafa yana jin yanayin zafin jikin
ta . A hankali ya furta " Tana da damuwa sannan kuma akwai yunwa a tare da ita ....!
12:01pm.
Nigeria Airport
Jirgin Su Nurain ne ya sauka , Wanda tun tsayuwar su yake jin Wani irin sanyi na Ratsa ko ina
na zuciyar sa . A hankali yake shaƙar iskar Ƙasar nasa Wanda ya barshi tsawon shekaru goma
sha bai dawo ba sai a yau. Lumshe sexxy eyes din sa yayi yana tunano da kyaƙyƙyawar fuskar
ta wanda har Abada ba zai taɓa mantawa da shi ba a rayuwar sa. Ɗan murmushi ya saki mai
nuni da jin dadin Dawowan sa . Fara sauka yayi daga Stairs din Jirgin data dauko su daga
America . Wani irin girma yayi da cikar kamala ,wanda idan ka ganshi sai ka kara kare masa
kallo zaka fahimci shine dai Wancen Nurain din ba wani ba . Yanda fatan jikin sa yake ko na
wata hadaddiyar macen Albarka luku² tamkar wanda bai taɓa fitowa rana ba . Idanun sa sanye
cikin baƙar space ( maganin ido) wanda ya kara daukar Hankalin ƴammatan wurin . Kowa da ya
gansa yasan Dawowan Nigerian yau ne . Sanye yake cikin shigar Track suit Mai haske kalon
Ruwan samaniya light blue . Yayin da ƙafarsa ke cin boot fari ...a hankali yake saukowa yayin
da Gaba ɗaya masu take masa baya (Securities) din sa suka rufa masa . A inda motocin su
suke ya tsaya yana kallon Daya daga ciki kamin yace ma drivern ya basa key din moton . Cike
da natsuwan nan nasa ga Dan Miskilanci da na gani a fuskar sa wanda a da baya ban san shi
dashi ba . Zaku iya tafiya ,zan taho daga baya . Ok sir . Suka yi maganan suna saurin Buɗe
masa moton ba tare da sun san inda zashi ba .
**
A hankali take Ware idanun ta Tana kallon Gyefen ta inda taga Wayoyin Zaid da laptop ɗin sa
amma baya wurin . Saurin kokarin tashi tayi dai dai tana jin Hannun Mom Cruzita na dakatar da
ita tare da cewa " Sannu da Jiki Amrah , Ai ban san baki da lafiya ba , Oga ya faɗa mun yanzu
bayan sun gama baki kula da sauran nurses . Kallon Mom Cruzita tayi tana son tambayar ta
mene yace mata? Sannan ciwon mene take yi kuma?. Wata Nurse ce dake Gyefe ta kalli
Amrah tana cewa " yanzu zamuje kiyi Brush idan kin fito ga Abinci nan da kayan motsa baki
Doctor ya aiko Miki dashi . Gyaɗa mata kai tayi a hankali tana Miƙewa don kayan karin ruwan a
gyede ta gansu da'alama har sun kare ne an cire su . Kamata Nurse din tayi tana nufa da ita
Toilet .
**
Ɓangaren Nurain Kuwa Bulayi yayi tayi amma ya kasa gane Hanyar ko ina , Wanda daga
karshe makarantar Jennylyna ya nufa inda suka yi . A dai dai bakin makarantar yayi parking
moton shi yana fitowa tare da kallon Gyefen Hanyar wanda ya Bisa babu iyaka . Kallon Wani
hanya yayi inda suke yin yanke shi da Amrah duk idan zasu koma gida , a hankali ya furta "
Kina Ina Amrah a yanzu.? Kin yi Aure ? ,Ko kin manta dani?. Rufe Murfin Moton yayi yana
tsallaka wa bakin Hanyar tare da bin layin nan da ya kasa mance dashi a memory din sa . Bin
hanyar yake yi wanda a yanzu yaga yayi faɗa , ga mutane sun yawaita a layin kaman a da
wurin ba kaman Daji yake ba . Lumshe idanun sa yayi yana tuno da rana na farko da suka fara
biyo layin , yana dauke da ita a keken sa . Realy Miss You Amrah ... Idanun sa ne suka hau
Rawa cikin sauri ya zare Bakar gilashin idanun sa ,. Wannan wurin mai tsiren da suke zama ya
gani ,ya koma wani babban Wurin sayar da nama ,an gyara Wurin har da yi masa Adon fitilu.
Saurin ƙarikawa yayi Wurin wanda a yanzu ma babu mai sayar da naman ,da'alama har yanzu
da yammaci suke fitowa . Rumfan ya shiga yana tsayawa yana kallon Gyefen sa tare da tuno
maganan Amrah da take kuka tana cewa " Shikenan Kaja mun na tsime , da kayana zan Kwana
Kuma Baba Zuwai zata bugeni...." . Ƙaran Kiran Wayar sa yasa shi daukar kiran a sanyaye
musamman Ganin kiran Mom Sa'adah ce . Nurain mene ya faru baka biyo Excouts din naka
ba.? . Cike da danne damuwar sa yace " Mom na tsaya dubawa ne ko zan gane gidan su
Amrah amma har yanzu Ban gane ba . Shiru Mommy tayi tana kallon Gyefen ta inda Dad da Su
Naana ke zaune . Kara danna wayar tayi a saman kunnen ta yanda ba zasu ji me yake fadi ba
tana kwantar da muryar ta cike da rarrashin da ta saba yi masa a kullum tace " Ka dawo Gida
yanzu kaji Nurain?. Ok mom . Murmushi tayi tana Datse kiran tare da kallon Su Naana tana
cewa" Yanzu zai Dawo. Cike da nuna farin ciki Nusaiba tace " Yauwa Mommy ina Cook dinnan
ta rannan ita ya kamata tayi ma my boo Duk abun da yake buƙata ,Cox ta iya komai gaskiya, ka
mata ma yayi ta zama masa personal maid din shi mai kula da shi da koman sa .
Wani irin bugawa Ƙirjin Nusaiba yayi cikin sauri ta katse Nusaiba tana cewa " Aa duk Ma'aikatan
Gidan nan sai itane zuwan yanzu zata yi masa.? . Kamin Nusaiba tayi magana Mommy cike da
kashe zancen tace " Ai ita mai Girkin dare ne , ba anan take zama ba ,kullum zuwa take . To ai
Mom kudi ake biyan ta . Yanzu dole ta kasance 24hrs a cikin gidan nan . Idan ke kina buƙatan
ta to ai ba lallai Shi Nurain yana bukatar ta ba . Kin san baya ma Son takura shi , ko fa breakfast
baya yi a Dinning Falon sa ake kai masa .
Kallon Naana Nusaiba tayi tana cewa " To ai shiyasa nace Miki ta zama personal maid din sa ,
ta rinka masa aiki shi kadai . Amma kina ji bari ya dawo idan ya nuna yana bukatar ta zama
masa hakan ai kin san shi dai kaifi daya ne sai dai kiyi Haƙuri . Murmushi Mommy tayi tana dan
sa yar dariya kana tace ' Kudai ba'a iya maku . Mikewa Nusaiba tayi tana nufar ina Hadiza suke don ta sanar masu a kira Amrah don yau ita
zatayi entertaining din Nurain da yake dawowa .
**
Sosai Amrah taci Abincin wannan yasata jin karfi a jikin ta . Sai daga nan ne kuma ta fara
dawowa hayyacin ta , jikin ta take kallo Ganin an sauya mata kayan jikin ta zuwa Wata doguwar
riga bakar Abaya . A sanyaye ta kalli su Mom Cruzita da har a lokacin take kanta tana cewa "
Mom karfe nawa yanzu .? Mom Cruzita ce ta bata Amsa da " 2:30pm . Waro idanun ta tayi Waje
da sauri ta miƙe tana kokarin ficewa ne Zaid ya shigo . Kallon sa tayi tana dan yin ƙasa da
idanun ta a hankali ta furta " Na gode da kulawa da kayi dani . Murmushi taji yayi mai sauti kana
yace " Wannan ai dama wajibi na ne . Zan tafi ina zuwa gidan Wani Aiki yanzu lokaci ya ƙure na
gode . Kamin yayi mata magana tuni ta fice tana nufar Ɓangaren su ta dauki Hijab. Don tsoron
abin da zai kai ya kawo take ,kar a koreta a gidan Aikin nata .
**
Lekowa Nusaiba tayi a fusace take fadin Wai ina Yarinyar ne har yanzu bata zo ba.? Eh Hajiya
amma .... Assalamu alaikum . Ohh Gata nan ma . Mtswww Dan tsaki Nusaiba tayi kana tace "
Ke kin ɗauki Aikin ki kuwa da muhimmanci? . Kiyi maza yanzu ki haɗa ma Yaya na kunun Aya
irin wanda kikayi mana. Kece Zakiyi entertaining din sa . Wani irin danmmm Amrah taji Kirjin ta
ya yanke ya fadi , Tambayan kan ta take wani yayan nata ? Badai Nurain ba .? Ficewa
Nusaiba tayi yayin da Hadiza take fadin maza muje kitchen mu fara Aikin . Don kuwa ya dawo
kin san baya cin abinci a Dinning sai dai a falon sa . Mutum ne yanda naji labari Miskili baya
magana sai rashin mutunci