Showing 30001 words to 33000 words out of 56966 words

Chapter 11 - WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf

mata?
“Sa’eed!” Ta fada cikin rishin kuka. “Sa’idu!” Ta sake maimaitawa cikin karkarwar murya. A yayin
da ta zauna a mazauninta na kujera mai lamba (22), hannun dama, na cikin jirgin (British
Airways). Kafin wasu irin dumammun hawaye su kara wanke kyakkyawar fuskarta.
Ba kuma tare da ta yi wani kokari na sharewa ko voyewa ba ta ce a fili…..
“Allah ya isa tsakanina da kai Sa’eedu….Allah Ya isa!!!”
Ta sake mai da kai cikin cinyoyinta ta ci gaba da kuka.
Da a ce cikin al’ummar mu ne Lailah ke yin wannan sambatun, la-shakka da an tsaya kallon
zararriya-mahaukaciya, amma ga wadanda ba halayyarmu daya ba, ko kallon ta ba su yi ba,
kowa ta kansa yake, kowa kansa ya sani.
Babu wanda ya kula ya damu da halin da take ciki sai mutum guda, musulmi Bahaushe dan
uwanta, wanda har zuwa lokacin ke bibiyarta da ido, da zuciya.
“…..Budurwa har budurwa…., kyakkyawa har kyakkyawa, mai kyau matuka. Amma Allah sarki!
Watakila tana da ‘Psychological Problem”.
Ya raya cikin wasikar jakinsa.

Hakika duk inda musulmi yake, zuciyarshi ta sha baban da ta arne ko ya ya ne. Allah ya halicci
dan musulmi da zumunci ga dan uwansa musulmi, ko da basu hada jini ba, wato ko da haduwar
kan hanya ce. Musamman a inda suke sune ‘minority group’ wato a inda suke da karanci. To
hakan ce ta faru da ABBAS. Ya kasa dauke hankalinshi daga Lailah, ya kasa daina jin son
taimaka mata. Ko ba da komai ba; da son gusar mata da wannan dimbin damuwar da take ciki
ko ya ya ne, koda da fatar baki ne. He want to turn this sadness to joy…., he want to make

these tears- murmushi.

Jingine yake tuntuni a hanyar da ta raba first class seats da kujerun baya yana kallon ta, amma
tsayuwar shi bai hana masu wucewa hanyar wucewa ba.
Ya duba lambar mazauninshi jikin tikitin hannun shi, ya mayar aljihun bayan wandonshi. Ya
karaso inda take fuska cike da fara’a ya sake yi mata sallama a karo na biyu.
Kanta na fuskantar taga ne, tana kallon taurarin dake makale a sararin samaniyar subhana,
ma’abota haske gami da hasken fitilun lantarki kala-kala da ya mamaye duhun daren, tana iya
hangen gine-ginen gidaje, motoci da ma’aikatan birnin tarayya miri-miri kamar abebaden wasan
yara, kamar a tafin hannunta. Juyowa kawai ta yi fuska babu annuri, ba tare da nuna ya fuskanci halin da take ciki ba ya ce.
“Hello lady, can I’ve my seat here?”
Tare da nuna mata tikitinsa mai nuna cewa shine ‘occupant’ na kujerar da ke manne da tata,
wato mamallakin kujera ta (23).
Hannu kawai tasa ta dauke jakarta da ta dora a ‘seat’ din ta ajeta kasan kafafunta. Ta mai da kai
inda take fuskanta tun farko, wato tagar jirgin, ba tare da ta ce da shi ci kanka ba......
“Taron tsinannu! Taron mugaye, taron mayaudara, macuta, maha’inta, ‘yan tofin Allah tsine! Duk
kune........ MAZA!!!”
Ta ce cikin zuciyarta. Tare da kai tausasan yatsunta ta yarfe wasu matsiyatan hawaye da suka
kara shimfido mata.
“Iko sai Mai-Duka!”
Shi ma ya fadi cikin-cikinsa.
“Watakila bayan ‘Psycho-disorder’ Mamanta ko Babanta sun rasu, a wannan hutun da taje na
‘summer’. Allah sarki! Gaskiya ba karamin rashi bane rasuwar iyaye. Karewa ma, it’s the
greatest loss of all losses! Shi zai gaya ma kowa ya ya rayuwar dan Adam take wakana babu
iyaye? Ya ya dan Adam yake ji idan bashi da wanda zai zo ya rava, ya saki jiki da zuciya ya
gaya mishi damuwar shi? Ya ya yake ji idan ba shi da mai daukar nauyin lalurorin rayuwarsa,
har ya samu ya mike ya gina kansa?
Sai dai kuma Allah ya kawo mu wani zamani da (dutyn) Uwa ko Uba kawai shine su kawo ka
duniyar, amma ko kai kadai za ka iya rayuwa, idan har ka san me rayuwar ke nufi, da inda ta sa
gaba.
Sai ka fuskance ta a yadda ta zo, ka manta da komi, ka kasance mai binsu da addu’a.

Aka ba da shelar a daura ‘belt’ jirgi zai nausa. Kowa ya daura ban da Lailah. Sarkin sa-idon
nata ya kuma cewa a ransa.
“To ko dai ba ta ji ne?
Amma kuwa a ganinsa da hakan bai sa ta kuka ba!.
Sai me don Allah ya rage ka ta wani fannin?
Ai dole ba zai hada maka komi 100% ba. Dole idan ya baka wannan ya hana maka wancan don
ya jarrabi imaninka ya ga cewa, za ka gode da ni’imomin da yai maka ne ko a’ah?
Za ka butulce ta hanyar kuntatawa kanka? Idan ka gode sai ya karo maka da wata falalar daban
ta inda baka zata ba.
Don haka a ganina in nine ke ‘yammata ba zan yi kuka ba. A hakan zan daddage in jure in

fuskanci rayuwa. In shiga al’amuran duniya a dama dani domin babu maraya sai raggo. In
kasance mai godewa Ubangijina (Yawaita Hamdala) wannan ba shine karshen rayuwar ba!!
Kuma babu cutar da Allah ya saukar ‘yammata ba tare da ya saukar da ita tare da maganinta
ba, sai tsufa, sai mutuwa.
Sai in ci gaba da neman waraka. Sai dai hakan ba yana nufin zan dakatar da al’amuran ci
gaban rayuwata bane, a’ah, ci gaba zan yi, har zuwa sanda (Arrahmanu) Sarkin Rahma ya ga
damar yaye mini. Idan kuma ya fi son ganina a hakan? Ow.k! All it takes….!!!”.
Shi kadai yake ta sake-sakensa, har da su watsa hannuwa gami da yarfar dasu tamkar wani
zautacce sabon kamu.
Haka ita ma ba ta fasa kukanta ba, ba ta kuma da alamun dainawa. Sassanyan sautin kukan na
kara ratsa kunnuwansa, tare da yamutsa tunaninsa a kanta. Yana kara raunana raunanniyar
zuciyarsa, musamman kasancewarsa mutum mai matukar rauni a kan tausayin MACE.
Zuciyarshi ta gama lugwigwita, domin tun da yake bai tava jin irin wannan kukan ba, mai girgiza
zuciya, mai ratsa kashi da vargo. Tsigar jikinshi ya soma tashi, bai san sanda ya rintse ido ba ya
ce.
“Na hadaki da Allah kanwata ki daina wannan kukan!”
Da sauri ta cira kai ta dube shi da jajayen idanunta da suka rine kamar gauta. Yana son yin
shisshigi a kan al’amarinta......
“Haka kuke da farko,… nuna tausayi da kulawa, har sai mace ta yi kuskuren fadawa a tarkon
ku, sai ku cuce ta ku raba ta da farin cikinta……”
“Kuka na dinga yinshi kenan…. har karshen rayuwata!”.
Magana take a zucci, ba ta san har ta suvuto ta fatar baki ta shiga kunnensa ba. Murmushi ya yi
kamar bai ji abin da ta ce din ba.
Ya ce, “ ki daura ‘belt’ din ki”. Ba musu ta jawo ta makala a kugunta. Don kada ya sake damun
ta da magana, ta sake mai da kanta cikin cinyoyinta.
Ya dauki ‘earpiece’ da aka ajiye a kowacce kujera ya manna ma kunnen shi, tare da murdo
rediyon BBC harshen Hausa yana sauraro. Sai dai a zahiri ya yi hakan ne domin kare
kunnuwansa da raunanniyar zuciyarshi daga sautin kukanta, mai lugwigwita zuciyarsa da
kassara gavvan jikinsa. He donno why her cry weakens him…..(bai san meyasa kukanta yake
raunana zuciyar shi ba). Mai raguwar zuciya ba zai iya daurewa ba sai ya tayata, and he don
want 2 be among….. !(baya so hakan ta faru dashi). Jirgi ya mike sosai bayan ya gama
ruguginsa mai gigitarwa, ya soma keta hazo ya naushi kasar Birtaniya.

Sai da ya kama hanya sosai ya zare ‘earpiece’ din tare da daukar karamin bargon ‘British-Air’
ya warware ya rufe jikinsa, daga kafadu zuwa cinyoyi saboda wani irin sanyi da ya soma keta
vargon jikinsa. Wanda inda sabo to sun saba.
To haka da yawan al’ummar jirgin suka yi, aka yi light-up wasu suka soma barci. Wannan ma
duka ban da Lailah.
Ya mika hannu aljihun bayan kujerar da ke gabansa ya dauki mujallar (TNT) ya soma buda
shafukanta, ba don komi ba sai don kawar da hankalinshi daga kan wadda ba ta damu da shi
ba, bare al’amarin sa.
Ba ta damu da kowa ba, ba ta san me yake yi ba. She’s undoubtedly suffering a zuci, ruhi, fuska
da gangar jiki, da al’amarin da duk tunanin mai tunani ba zai tava bashi ba.

A fuska she looks innocent…. A kwayar idanunta tsoro ne karara….. A shimfide kan fuskarta
nadama ce tsantsa….. A karance kan siraran levvanta istigfari ne. Zuba suke tarara daga cikin
idanunta, hawaye ne.
Baya iya banbance rubutun da hotonan da ke cikin mujallar, baya ganin komi a kansu face
kyakkyawar fuskar Lailah, tare da sauraron zazzakan sautin kukanta.
‘Yammatan jirgi zuka-zuka, farare kal cikin vingil-vingil din (minis) da rufaffen takalmi, bakaken
‘suit’ da shudin ‘tie’.
“Looking so cool...........”
Ya fada ta hanyar motsi da tausasan levvansa. Sai dai kuma duk gyaran ku da kwalliyar ku you
are not as good looking as she is, (baku kaita kyan gani ba) duk da ita ba ta yi kwalliyar ba.
Karewa ma hawaye ne sharkaf, jave-jave a idanunta. Haka ba ta nuna kowacce gava ta jikinta
ba, in ka dauke shatin fuskarta.
Sai dai kana iya hango kwantaccen gashi baki wuluk mai sheki da walkiya daga saman
goshinta, sakamakon mayafinta da ya dan zame baya cikin rashin saninta. Wanda ke nuni da
ba bafullatana ba ce.
Wannan kyan ya kere na fulfulde, kyau ne da launin mutane biyu ya haifar, wato baki da fari
(half - caste) da aka fi sani da ruwa biyu, daga uwa da uba.
‘Yammatan suka iso layin da suke tare da dan tebirin su mai tayoyi (troller) mai dauke da duk
wani nau’i na ababen jika makoshi, tun daga kan shayi, wine (giya), coffee, ruwa, jus da
kwalayen taba nau’i-nau’i.
Cike da ni’imtaccen murmushinsu suke tambayar Lailah da ke kife da kai abin da take so.
Ko kallon su ba ta yi ba. Dan sa-idon nata, tuni ya ari bakinta ya ci mata albasa, ya ce a bata
ruwa mai sanyi ta jika makoshinta.
Daya daga cikinsu ta ce,
“Hala amarya ce? Honey moon in the heart of England?”
Murmushi Abbas ya yi.
“Yap....... but we ‘ve a little misunderstanding (mun samu ‘yar kankanuwar rashin fahimta) shine
take fushi, irin na mata da miji, kin gane?”
Ta yi murmushi ita da abokin tafiyarta ta ce.
“Wannan ba wani abu bane, abu ne da ke faruwa a cikin SOYAYYAH. Idan babu irin wannan
babu ingantacciyar soyayyar a zuci. Cool down my friend……”.
Ta fadi tana mai dafa kafadun Lailah. Har da dan jijjigata.
Mamaki da haushi ne suka kashe mata baki ta kasa cewa uffan har suka wuce, bayan sun cika
mata dan kofin su da ruwan abarba mai sanyi.
“Kulawa ma yabawa ce”.
In ji Malam Bahaushe. Idan Abbas na tunanin irin shisshiginsa zai yi tasiri ya samu kulawar
Lailah, wadda ke kallon dukkan maza ‘naked’ (tsirara) babu sauran mutunci babu sauran
aminci da su a idanun ta ya yi kuskure. Har suka sauka a Heathrow ba irin shisshigin da bai
mata ba, amma uffan ba ta ce mishi ba. Hakanan bata kalleshi ba. Da yawan ma’aikatan jirgin sun yi zaton da gasken mata da miji ne duk da yadda fuskarta da
ma zuciyarta suke a jagule.
Don da za su fita jirgin ma’aikatan na ta yi musu fatan alkhairin ‘honey moon’ ne cikin kasar su
(kamar yadda ya ce) yana amsawa a dokance. Yana binta kamar jela, kamar wani ‘body guard’ ,

ko ko mai take mata baya, da kula da al’amarinta.
Duk wannan na faruwa ne cikin Air-port din ‘Heathrow’ cikin dakikan da basu fice mintuna talatin
ba.
Da suka zo kanta wato wajen tuhumar ingancin visa na karshe ga wadanda ba ‘yan kasa ba,
wanda daga shi sai shigewa cikin garin London. Ya fahimci Lailah ba ta tava shigowa Ingila ba,
domin daga ganinta ta fara tsorata daga tsabar binciken da ake yi mata, har ta zamo perpleded
(rudaddiya).Ya ce sai ta tsallake wannan ‘inter-view’ din tukun shine na karshe. Tare da gaya
mata cewa ta kula sosai wajen basu amsoshin tambayoyin duk da suka yi mata, ban da dadi
ban da ragi, domin hakan na iya janyowa a hanata shiga.
Hankalin Lailah ya kai kololuwar tashi, idan da abin da yake na karshe da ba ta son ji a wannan
lokacin, to komawa gida Najeriya ne. A dai wannan lokacin da ba ta san matsayin rayuwarta ba.
Ta zo ne domin yin karatun da za ta yi wa kanta hukuncin da addini ya tanadar a kanta.
To amma why a Britain?
[12/17/2019, 17:50] Takori: Idan ilimin addinin musulunci ne ai yana kasar musulunci. Wannan
kuma yana daga cikin dalilanta na son vatar da hankalin kowa nata daga tunanin inda take. Ta
san nan ne kadai waje na karshe da iyayenta da shi kansa ba za su tava tunanin za ta zo ba,
tunda ba ta tava zuwa ba. Kuma bata da kowa. Sai dalilinta na biyu shine, tana da masaniyar cewa babu kasar turan da ke zaune da al’ummar
musulmi lafiya irin Ingila. Kasa ce da ta bai wa kowa dake cikinta ‘yancin yin addininsa da
walwalarsa, ba tsana ba tsangwama, idan har ka bi ka’idojin da ta shimfida maka. Wannan
shine babban dalilin ta na zavar kasar Ingila a matsayin mafaka ga ruvavviyar rayuwarta.
Lailah ce tsaye can gefe a kanta tare da (UK Boarder Agency) masu binciken ingancin bisarta
na karshe kamin su barta ta wuce. Tana amsa tambayoyi na karshe. A nutse take tsaf, cikin
kamalarta da voye vacin ranta, tana mai amsa dukkan tambayoyin da a kai mata daki-daki da
tsaftataccen turanci mara amo. Sun gamsu, sun yarda da zamanta cikin kasarsu baya nufin
ha’inci ko vad-da-kama, ko kuma ci - da - gumin - wani. Saima su da za su kara bunkasa tattalin
arzikinsu daga asusunta wanda ke cike taf da (sterling pounds).
To nan suka fi kauri, don haka suka daga mata kafa ta wuce. Ta fesar da ajiyar zuciya mai
nauyi, domin ta riga ta tsorata da tambayoyin ka-ka uwar ki ta haife ki da suke antayo mata.
Ta yi tunanin idan aka ce ta koma gida a yanzu ina za ta dosa? Ba ta fata, sai ta yi wa kanta
ilimin da zai tallafi gurvatacciyar rayuwarta.
Already shi har ya dau jakarshi. Ta dan yi mintuna kamin tata ta iso ta dauka. Suka jero gwanin
ban sha’awa kamar mata da mijin gaske zuwa bakin titi.
Hadaddun Jeep-Jeep ‘yan gujif-gujif amma wai tadi ne (drop), su Laila ta fara yin tozali dasu a
jere raras suna tsimayen mai hawa.
In kin san wani abu wai shi dacewa, wato (matching) na karshe, to Lailah da abokin tafiyarta ne,
wanda har zuwa wannan lokacin ba ta yi mishi wani kyakkyawan kallo ba balle ta tantance
kamanninsa.
Shi kuma haka nan ya bi ya nace ya manne kamar wani tsohon maye yana bibiyarta kamar
bindi. Ba tare da damuwa da halin ko in kulan da take nuna masa ba.
Ya lura ba ta cikin cikakkiyar nutsuwa, haka nan ba ta san ko ‘ina ba. Sai dai kuma ba ta da
duhun kai, don ba ta tambayi kowa ba. Ta san iliminta zai mata jagora a ko’ina.

Ta karanta adireshin makarantar da ta zo, (20 Creffield, Earling, London), ta maida takardun
inda ta dauko su a jakarta, ta nufi daya daga cikin tasin.
Tun kan ta karasa wani dan motsattsen Bature ya iso gare ta ya amshi jakarta yana kokarin
sanyawa a boot.
Hannuwanshi biyu ya sanya ya ciro jakar daga boot din tasin, ya ja Baturen gefe yana
murmushi ya ce da shi cikin harshensa.
“Kyale ta fushi take, ka san amare abu kadan sai su hau, su yi fam!”
Baturen ya kyalkyale da dariya ya ce, “To ai kai ma abokina amare lallava su akeyi”.
Ya ce, “Ina lallava ta tana kara hawa sai ka ce alkubus, ka gane rigima ce da Madam, ta fi son
mu sauka a DUNDEE ni kuma na fi son London. Shin akwai inda ya kai London dadin ‘honey
moon’ ne a Birtaniya?”
Da sauri Baturen ya girgiza kai ya ce, “A’ah, garin sarauniya ai babu kamar shi a duk fadin
Ingila”.
Ya juyo ga Lailah yana murmushi wadda tuni ta yi mutuwar tsaye.
“To kin ji sai ki daina fushi, ki daura aniyar zaman London da kin ki da kin so. Ina da ‘oyster’
(katin hawa jirgin kasa) har biyu, zan baki guda. Gara mu bi ‘train’ yafi saukin kudi.Wuce muje
Ma sis..........”
Wannan karon da Hausa yake magana don kada mai tasi ya fahimce shi. Ya zaro fam ishirin
cikin wallet dinshi ya mika ma mai tasi, amma ya ki amsa, su kai sallama ya yi gaba.
Ba ta da zavi ban da ta bi shi, domin da jakarta da nashi ya hada ya wuce.
Ba ta tava ganin mutum mai shisshigi irin wannan ba. Haka ba ta tava ganin mutum mara
zuciya irin shi ba.
“Uffan ban ce maka ba, kallo wannan baka ishe ni ba. Amma ‘still’ baka fasa naci ba”.
Ta furta cikin takaici, tare da jan wani matsiyacin tsaki, “Tsuuut!”
Ya ji sautin tsakinta, amma bai san ko me ya sata yin tsakin ba. Ya murmusa har cikin ransa ya
ce.
“haka nake kiyi hakuri dani, naci akan abinda na kwallafawa rai, nake kuma son sani. Wanda
akafi sani da ‘curiosity’. Am curious about you! Yanzu meke damunki? Yunwa ko gajiya?
Kada ki damu, I’ll cook deliciously for you........ (zan miki girki mai dadi, ni gwani ne wajen girki,
lokacinda matata ke raye).

A mamakance Lailah ta cira kai ta dube shi, wannan karon cikin ido. Ta tsorata, ta mamakantu,
haka ta firgita da abin da ta gani cikin kwayar idanunsa (Mohammed sak!).
Amma hakan bai kada ta ba kamar zallar kyau da haiba irin na wannan mai naci. Duk da cewa
baki ne amma bakin shi mai kyau ne. Ta ko’ina ba ta inda Ubangiji ya rage sa.
Ba ta san yaushe murmushi ya suvuto daga bakinta ba. Karo na farko da ya ji sautin muryarta
ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login