Showing 48001 words to 51000 words out of 56966 words
Chapter 17 - WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf
da rayuwarki? Kin shirya zama mutuniyar kirki ko za ki ci gaba da yin
alakar kusanci da mazan da ba muharramanki ba?”
Ta yi saurin katse Momi da cewa,
“Na shirya zama ‘yar kirki Momi a gaba dayan sauran rayuwata......”
Momi ta ce,
“Aurenki da Mohammed ya riga ya lalace, sai dai dukkaninku ku yi hakuri da shi.
Maganar zuwa kotu domin karvar takarda a hannun Mohd. ma ba ta taso ba. Domin kanki za ki
tozarta. Za mu nemi sulhu da shi, jibin zan ganku tare. Amma ki yi dauriya, dole Isma’il ya ji
zancen nan, don shine waliyyinki.....”
Lailah ta zaro ido,
“Zai tsane ni Momi, zai yi Allah wadai dani Momi”.
Ta ce,
“Shirmen banza kenan, an ce da ke hannunka na rubewa ka yanke ka yar ne? Baki yi tunanin
hakan ba a lokacin da kike hutawar haram da kanin mijinki? Tashi ki bani wuri tun nima din ban
tsane ki ba”.
Mikewa ta yi tana goge hawayen idanunta. Ta shiga ‘toilet’ ta sakar ma kanta ‘shower’ ko ta ji
sanyi a zuciyarta.
****
[12/17/2019, 18:28] Takori: An zauna a falon marigayi mahaifin su Lailah a ranar (26) ga watan
Maris na shekarar 2000.
A gefen Mohammed Jama’are kanin shi ne Sa’eed Jama’are, wanda tun da ya shigo falon
kanshi ke sunkuye bai dago ba.
Sai Isma’il Yayan Lailah, kusa da shi Lailah ce cikin abayat da Momi a gefenta. Sai Hajiyar su
Mohammad a gefe wadda fuskarta babu alamun rahma, kada ma su ce sulhun a mayar da
Lailah gidan danta za’a yi, don a cewar ta Lailah karuwanci ta tafi Turai ba wani karatu ba.
To sai kuma kallo ya koma sama, a inda ta ji sulhun da Balarabiya Najla ta nema, wato a
warware auren Lailah da dan nata sakamakon kazantar da auren da suka yi da WASAN KANIN
MIJI.
Ta dube su tsaf, a ranta ta ce ‘yan kundun uba.
Sannan ta mike ta bugi kirjinta ta dubi Momi ta ce, “Ni Baida’u ban haifi dan iska ba, ‘ya’yan nan
biyu su Allah ya bani ban taba ji an ce an gansu suna aikata wani aiki na assha ba.
Balle Sa’idu ya nemi matar Yayansa da yake mutuntawa fiye da ni, yake kaunarta da zuciya
daya.
Ta je can ta nemi abokin shaidancin can a inda ta je karuwanci....Takarda kuwa ko baku ce ba
dama za a ba ta, don tuni na aurawa dana mace ‘yar usli wadda na san asalinta. Don haka.......”
“A’a, Hajiya ki yi hakuri ki zauna ayi maganar nan a tsanake..........” Sa’eed wanda ke sunkuye
da kai ya fadi cikin sanyin murya....
Ya kara da cewa,
“Don Allah Hajiya ki zauna....”
Ta koma ta zauna tana hararar sa..... Shi kuwa Mohammed jifanshi ya yi da wani kallo mai tarin
ma’anoni da dama.
Amma Sa’eed ya maida kanshi kasa, ba tare da ya sake hada ido da kowannen su ba ya ce.
“Hajiya da Yaya ku gafarce ni, tabbas abin da Lailah ta fada cewa mun aikata gaske ne. Mun
tava kusantar juna amma sau daya ne cikin ribatar shaidan.
Zancen haihuwa ne ban san da shi ba, don ina jin tun a ranar da al’amarin ya faru ta bar gidan,
nima ban kara ganinta ba ko ji daga gare ta ba sai yau.
Don haka Yaya ka yi hakuri, ka kuma yi min duk hukuncin da ka so.......kasancewa ta wanda ya
yi maka cin amanar da baka tava zato ba, na raba ka da abin da kake so, ba don ka daina son
shi ba.
Yaya daga ni har Lailah ta wani vangaran bamu da laifi, ko me muka yi kai ka bamu damar mu
yi shi.....”
Kafin ya karasa Mohammed ya kai masa wani wawan mari, ya bishi ya shake da kyar Isma’il ya
kwace shi. Ya galabaita yana haki abin tausayi.
Hajiya ta ce,
“Rufe min baki tun ban tsine maka ba, kai kuma Mamman rubuta takardar sakin ka basu idan ka
haifu cikin iyayenka......rubuta musu yanzun nan ka bani, ko in daga maka nono wallahi…….”.
Ya sunkuyar da kai hawaye fal idonsa. Isma’il ya bashi biro da takarda.
Yana rubutun hawaye na jika takardar, ya rubuta saki daya jallin-jal, ya mikawa Isma’il, ba tare
da ya damu ya goge hawayen da ke zuba tarara daga idanunshi ba.
Cikin macewar jiki Lailah ta daga ido ta dube shi, anyi sa’a a lokacin shi ma ya dago sashen da
take. Sai ta ji hawaye sun tsinke mata na tausayin Mohammed, tsohowar soyayyar dake
zuciyarta ta motsa. Da gudu ta bar falon ta yi cikin gidansu ta fada bisa gadon Momi tana kuka,
mai fita daga karkashin zuciya.
****
Kwata-kwata rayuwar Lailah ta sauya, domin duk inda macen da ta san ciwon kanta take,
wannan kalmar ta ‘saki’ ba karamin tashin hankali bane a gare ta, ko da auren kiyayya ne kuwa,
balle auren da aka gina a kan turbar so da kauna.
Gaba daya ta susuce ta fita hayyacinta, tsakaninta da mahaifiyarta sai gaisuwa, don tun ranar
da su Mohammad suka daga gida Najeriya ba ta kara ganin hakorin Momi Najla ba.
Ta ce sai ranar da ta ganta a dakin aure, sun daina jera kafada, sannan ita dai ba ta tava ZINA
a tsayin rayuwar ‘yammatancin ta ba, balle da auren ta.
Isma’il ko kallon ta ba ya yi balle ta ga hakoransa. Duniyar ta yi mata kunci ta buwaye ta. A
wajen kannenta su Najat kawai take jin sanyi, wadanda basa rabo da dakinta suna yi mata hira,
suna wasanninsu.
Aka kwashe sati biyu a haka, rama da zugewa da take yi suka addabi zuciyar Momi Najla.
Ta soma tunanin Allah ya sa ba kanjamau ta je ta debo a kanin mijin nata ba. Don haka yau da
safe Momi ta sanya ta a gaba suka nufi asibiti.
Laila na jin sanda Momi ke ce da likitan ta kawo ta a yi mata gwajin kanjamau ne. Sai hankalinta
ya kara tashi.
Ko numfashi da kyar ta shake shi. Wai me kowa ya dauke ta ne? Karuwa ko me?
(Kadan kenan daga irin bakin cikin da ‘ZINA’ ke haifarwa, domin ita ce karshen tozarci a
rayuwa, musamman ga diya mace).
Ba ta shaki numfashi sosai ba sai da result ya iske su cewa Lailah lafiyarta kalau.
Lailah ta kasa jure mu’amalar doya da manjan da Momi da Isma’il ke mata, don haka ta soma
tunanin kirkirarwa kanta abin da zai amfane ta.
Da farko ta soma neman aikin koyarwa a jami’ar da ta yi, ba ta sha wahalar samun aikin ba,
musamman saboda ingancin masters dinta na Ingila.
Ta shigo gida rike da tulin takardu a hannunta da gani a masifar gajiye take. Sanah da Najat
suka garzayo suka rungume ta.
Ta russuna dai-dai tsahonsu ta rungume su ta sumbace su daya bayan daya, ta tambaye su ina
Momi? Suka nuna mata dakinta.
Ita da Isma’il ta samu suna magana da kasafce-kasafcen tulin kudi a gabansu. Ko dai na
business dinsu ne ko na mene ne ba za ta ce ba. Domin Isma’il babban dan kasuwa ne. Ya kan
je Dubai da America kawo kaya kasar Egypt, sam-sam ya ki aikin gwamnati, duk da kwalayensa
na karatu masu inganci. Nan da nan dukkaninsu suka yi fuska suka daina zancen da suke, suka bi ta da kallo kamar sun
ga wata bakuwa.
A savule kuma kamar ta yi kuka ta zauna a gabansu, ta aje takardunta a gefe. Kadan ya rage ta
fashe da kuka.
Wai Momin ta da Isma’il ke nuna mata yau ita bare ce a cikinsu, don kurum ta yi kuskure a
rayuwarta?
Ta kai bayan hannunta tana share hawaye ta kasa cewa komai. Zuciyar UWA ta soma russuna,
amma Isma’il sai ya hau fada.
“Lafiya za ki zo ki sa mutane a gaba kina yi musu kuka kamar su suka saki kije ki zama ‘yar iska
ki ci amanar aure?”
Sai ta idasa rushewa da kukanta, ta ce,
“Na tuba Momi, na tuba na bi Allah na biku. Isma’il wane ne ba ya kuskure a rayuwarsa?
Idan kun juya min baya ina za ni? Idan kun watsar dani wane ne zai tallafe ni? Dan uwana ka yi
min aikin gafara kamar yadda nake nema a wurin wanda na yi wa laifin amma ba kai ba”.
Ya yi tsaki ya soma tattara kudin yana zubawa a jaka, ya ce da Momi
“Idan za su tafi kaiwa sai a gaya mani in raka su”.
Momi ta ce, “Babu laifi”. Ya sa kai ya yi ficewar sa.
Lailah wadda ke durkushe har zuwa lokacin a gabansu ba ta daina shesshekar kuka ba, kukan
da ya tava zuciyar Momin, ko ta ki Allah.
Ta mika hannu ta kama tattausan tafin hannunta ta ce,
“Ya isa.......ya isa”. Tana goge mata idanu da gefen abayarta.
Da kyar ta tsaida kukan ta jawo ‘file’ din dake gabanta ta ciro takardar daukar aikin ta mika
mata.
Momi ta sanya gilashinta tana dubawa, ta mika mata ta ce,
“Masha-Allah, yaushe za ki fara zuwa?”
Ta ce, “Sati mai zuwa”.
Ta ce, “Ga shi kuma za a yi auren Isma’il sati mai zuwan”.
Ta ce, “Wa zai aura?”
Ta ce, “Sujood”.
Sai Lailah ta vangale baki tana dariyar farin ciki.
Sujood diyar Yayar mominsu ce, tare suka taso da Lailan tun suna kanana. Ba za ta ce Sujood
kawarta ce ba, don ita ba ta kawance, to amma ‘yar uwarta ce da suka san juna suka fahimci
juna.
Sai da suka zo shiga jami’a ne suka rabu, inda Sujood ta tafi kasar ‘Syria’ ta yi karatu a kan
likitanci, Lailah kuma ta yi a nan Al-Azhar din Alkahirah.
Biki sosai suka yi irin na al’adarsu, Lailah na kan gaba a kan komi. Aka kawo Sujood nan gidan
su part din Isma’il, kasancewar gidansu katon gaske, mai sassa daban-daban.
Lailah ta shirya sassan sosai kai ka ce fadar wani gwamna ne kasancewar a al’adarsu miji shi
yake yin komai na kayan daki.
Musamman suka fita Oman don sayayyar kayan da za a zuba a gidan ita da Momi. Ganin irin
rawar jiki da wahalar da Lailah ta sha a shagalin auren sa ya sa ya soma sakar mata.
Amma ko an gode bai ce mata ba, duk da ya lura sayayyar da a kai ta zarta ta kudin da ya
bayar.
Ita kanta amarya Sujood ta lura da basar da Lailah da Isma’il ke yi a ‘yan kwanakin da ta yi a
gidan, amma ta ja bakinta ta yi shiru don ba ma’abociyar magana ba ce.
Bayan bikin ne Lailah ta mayar da hankali a kan aikinta. Wata rana idan ta fita tun takwas sai
shida na yamma.
A karshen sati ne kawai take zaman gidan, kuma zuwa lokacin Isma’il ya saki ranshi da ita. Ya
yarda ba wai sai mutum yana dan iska bane kawai yake yin iskanci ba, a’ah, dan kirki ma
kaddara da yanayin rayuwa kan kai shi da aikata laifi, ko ba da son ran shi ba.
Sai dai mu yi ta addu’a Allah ya sa mu fi karfin zuciyoyinmu. Ya raba mu da son zuciya, ya
nisanta mu da kaidin shaidan. Amin.
***
ko da jirgi ya sauke su Sa’eed da Hajiyarsa a garin Bauchi, basu kara ganin Mohd ba. Shi
Sa’eed ne ya yi masu shatar mota suka nufo Jama’are, don ya lura a yadda Yayan ke tunzure
da shi in aka ba shi wuka zai iya burma masa. Haka in yana da bindiga zai iya harbe shi har
lahira. Don haka salin-alin ya wuce Jama’are shi da Hajiya.
Mohd. yana kwance a sofa na falon gidan shi yana busa hayakin ‘Marlboro’, idanunshi a rufe.
Tiryan-tiryan yake tariyo rayuwarshi da Lailah, tun haduwarsu a babban filin jirgin saman Egypt,
sun rako mahaifinsu zai tashi zuwa Nijeriya.
Ya tuno gwagwarmayar da ya sha wajen neman auren ta, domin Hajiyarshi sam ta ki amincewa,
don a cewar ta ba ta son kwashe-kwashe da rore-rore.
Marigayi mahaifinshi shi ya tsaya mishi tsayin daka ya samu abin da ransa da zuciyarshi ke so.
Ya tuno irin soyayyar da suka gudanar a kwanakin amarcinsu. Wanda har gobe ba a samu
macen da yake so ya kuma ke kauna ya amincewa irin Lailah ba.
Ya kuma tuna cewa, tun daga wancan lokacin Lailah ba ta kara yin zaman farin ciki a gidansa
ba. Ta yi hakuri har ya kure ta domin ba shi da lokacin ta.
Idan har za a auna ne a mizani, to alhakin koma me Lailah da Sa’eed suka yi, to yana wuyansa.
Kuma nashi laifin zai rinjaya. Bai san yana son Lailah ba sai yau da ta kuvuce masa, zuciya ta
kuma tunkudo shi ta ce ya je ya dan huce a kan Sa’eed kawai ko ya rage asara.
Daga baya kuma ya ce,
“To don na daki Sa’eed me na yi? Yaro mai tsoron Allah da harshe daya, dukan da ba zai rage
komi daga suyar da zuciyarshi ke yi ba.
Ya tabbatar ya yi rashi tun da ya yi saken da ya rasa Lailah, mai kyautayi da hakuri da
tausasawa a gare shi.
Ko daya ba za a hada Lailah da Aisha ba. Ta fannin komai, shi dai kawai ya karvi aurenta ne
don ya faranta ran Hajiya.
Amma soyayyarta gaba daya in za a dora ta a sikeli ba ta wuce cikin cokali ba. Ai gaba da
gabanta... wai aljani ya taka wuta.
Me zai yi ya huce abin da Sa’eed ya yi masa? Babu, ya riga ya cuce shi. In ma kotu ya kai shi
karshe ma watakila shi zai je belinsa.
Idan ya doke shi bai huce ba, idan ya yi masa Allah Ya isa, idan alhaki ya lalata shi komai a
kansa zai kare.....
Bai ankara ba ya ji wata irin azaba a ‘yan yatsunsa, tuni tabar ta kare har ta soma cin yatsun
hannunsa.
Ya jefata ‘ash tray’ na silver dake gabansa ya bude idon shi sakamakon tsayuwar mutum da ya
ji a kanshi. A’isha ce.....
Ta ce,
“Majnoon na Lailah......!
Za ka iya tashi mu yi ‘break’ din ne ko Misra za ka koma a baka, tunda bikon bai yuwu ba?”
Ya valla mata harara ya ce,
“Idan komawar zan yi za ki iya hanawa ne?”
Ta kyave baki ta ce,
“A’a, ko bani da abin yi ba abin da zai kai ni inda ba’a so na.....”
Ji kake fauu! Ya wanke mata fuska da yatsunshi biyar...har sai da ta ga wuta da taurari. Ta
kama kuncinta duka biyu ta sunkuya tana neman kwayar idanunta da ta neme su ta rasa na
wucin gadi.
Da kyar ta ce, “Ni ka mara daga magana Mohd.?”
Ya yi tsaki ya yi ball da ‘center – table’ din gabansa na gilashi tsantsa, a take ya ragargaje. Ya
yi sama fuuu! Kamar zai bi ta kanta, ta yi kwafa ta mike ta ce.
“Wallahi ka mari auren ka”.
Ta yi dakinta tana kuka tana hada kaya. Azahar a Jama’are ta yi mata, ba ta nufi gidan Hajiya
ba don ba sulhu take nema ba, gidan iyayenta ta nufa.
Kwananta biyu Hajiya ba ta san ta zo ba, sai mahaifinta ne Malam Adamu ya zo yake gayawa
Hajiyar yadda aka yi.
Hajiya ta girgiza kai ta ba shi hakuri, ta ce, “Za ta dau mataki ita ma zata yarda da komai amma
banda duka. Amma ya yi hakuri ya turo mata A’ishar ta zauna a wurin ta kafin ta kira shi”.
Malam Adamu ya gyara zama ya ce, “Hajiya idan Muhammadu baya son auren nan ina ganin
gara a raba shi cikin mutunci ba tare da zumunci ya lalace ba.
Don ta fadi abubuwa da yawa, wadanda abin dubawa ne a cikin aure. Ta ce sai ta yi watanni
uku ba ta ganshi ba, kuma bai neme ta a waya ba.
Sannan in zai tafi ba ta isa ya yi mata sallama ba, sai dai ta ga kudi a kan tebur, haka in zai
dawo. Allah ya ga zuciyata ba don kudi na wanke A’isha na ba wa Mohammadu ba, sai zumunci
da mutuncin da ke tsakani”.
Hajiya kamar ta yi kuka, ta ce,
“Don Allah ya ba ta lokaci ta kira shi, in Allah Ya yarda za ta tsawatar”.
Kwana uku kenan Hajiya na buga layinshi ana gaya mata a rufe yake. A lokacin ma shi yana
‘Bangkok’. Daga can ya wuce ‘Austria’ yana yi wa jirgin Virgin Atlantic lodi.
Sai da ya kwashe watanni uku cur sannan ya yo Bauchi. Bayan motarshi fal da tsarabar Hajiya
da Sa’eed din da ba shi da yadda zai yi da shi.
Hajiya na sallar walha ya daga asabarin dakinta kasancewar ana zabga sanyi, kamshin
turarensa kawai da ta shaka ta san cewa shine.
Ya yi sallama ya shigo ya kwanta cikin kujera yana waya. Ba ta bi ta kansa ba sai da ta gama
sallolinta da laziminta, sannan ta aje mayafi gefe ta juyo ta dube shi kawai ba ta ce da shi komai
ba, don bakin cikin da yake shaka mata Allah ya yi yawa da shi.
Sai shine ya rufe wayar ya sauko kasa yana murmushi ya ce,
“Barkanku da safiya Hajiya, na same ku lafiya?’
Da da ne sanda yake yaro idan ya ba ta haushi irin haka carbinta za ta jawo ta tsutstsula masa,
to yau ma tunanin da ta yi kenan.
Sai dai kuma da ta dubi girmansa da haibarsa hadi da kwarjinin da Allah yai masa, sai ta rasa ta
ina za ta tsula mai carbin ya ji zafin shi a jikin shi?
Ko’ina guraye ne murdaddu na ingarman namiji, mai cikar halitta, ma’abocin haiba da kamala.
Sai birkitaccen hali da babu macen da za ta jure shi.
Dole ta aje carbinta a gefe ta dube shi cikin ido ta ce.
“Barka kadai”.
Ko a kwalar rigarsa, don shi ya manta ma da wata A’isha, ya soma ba ta labarin irin
tafiye-tafiyen da ya yi a wannan tafiyar.
Ta gaji da soki-burutsun da yake mata ta ce,
“Duk na ji, ka samo