Showing 42001 words to 45000 words out of 56966 words

Chapter 15 - WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf

amma vatan dan mutum ba karamin tashin
hankali bane ga iyaye.
Ina mai shawartar ki da ki sassautawa zuciyarki, duk wani tsanani yana tare da sauki, kuma
babu wanda ba ya yi wa Ubangiji savo a bisa rashin sani ne ko akasi. Sai in ce ke kuma
wannan ita ce kaddarar ki”.
Hankalinta ya kwanta da nasihohinsa, amma a duk lokacin da ta yi tunanin wai dan kanin miji za
ta haifa, da aurenta, tana ji tana gani, zuciyarta kara dimaucewa take.
Ya ci gaba da tausarta da kalamai kala-kala, yana nuna mata wannan ba shi ne karshen
rayuwar ba. Ta ci gaba da istigfari ta fuskanci rayuwar dake gabanta.
[12/17/2019, 18:28] Takori: ****

Ya kwanta a hankali bisa madaidaicin gadonsa, ya rasa abin da ke damun sa. Wani al’amari ne
da bai tava faruwa da shi ba ke cin ransa.
Duk wani tunani nasa da ya mallaka ya dunkule ya warware a kan LAILAH. Bai tava tunanin
Lailan matar aure ba ce yake kauna, yana da burin ta zamo uwar ‘ya’yansa, ashe dukkanin su
basu da ‘yancin wannan al’amarin.

Ya yi parkin din motarshi kirar ‘Ferrari’ a kofar gida mai malalen siminti, irin gidajen nan na masu
kudin da can wani lokaci da ya shude cikin garin Jama’are.
Ya fito ya rufe kofar ya bude boot din motar ya yafito yaran da ke ta wasa a gida mai kallon su,
suka zo ya sanyasu suka kwashe kwandunan doya da dankali su kai cikin gidan.
Ya yi sallama a kofar dakin mahaifiyarsa, daga can ciki Hajiya Baida’u ta amsa tare da yi mishi
kallon kauna, kafin ta amsa sallamar shi. Ya zare takalman shi ya sanya kai cikin dakin.
Ya samu kujera mai fuskantar mahaifiyarsa ya zauna, kai da ganinsa da kuma irin zaman da ya
yi rigija…. ka ga wanda kwanciyar hankali ya yi wa karanci.
Ta tura mishi kwanon gurjiyar dake gabanta kamin ta mike ta je kitchen ta shiryo masa abinci
mai rai da motsi.
Sai da ya ci abincin ya sha ruwa kafin da ta yi masa wani irin kallo ta girgiza kai.
“Anya Mamman! Kana nemawa kanka sauki cikin tunanin yarinyar nan? Na rantse da Allah ba
ta sonka, da tana sonka da ba ta yi maka wannan abun da ta yi ba, data tabbatar zai daga
maka hankali, tunda tana sane ta yi tafiyarta ba shi ke nan ba?
Kiri-kiri ta nuna maka ta gaji da zama da kai ne don baka haihuwa, shi ya sa ta yi tafiyarta
amma ka bi ka kwazzabi kanka banza da wofi, sai ka ce dan kankanin yaro ne ya vata. Kana ta
asarar kudinka a cigiyar banza.
Tsiyar auren ‘kwara’ kenan, don ba za su zauna ba. To yaran yanzu ne idan kun so auren mace
kamar da ya so fitowa cikin mahaifiyarshi, ba za ku yi aure a gida ba inda a ka san mace, aka
san asalinta, a’ah, ku sai kyal-kyal banza”.

Maganar Hajiya ta shige shi ainun, da gaske Lailah ba ta sonsa! Ko ta so shi a baya, yanzu ta
daina!! Da tana sonsa da ba za ta tava gajiya da zama da shi ba, kowanne irin hali ne da shi
kuwa.
Balle kuma yana iya kokarin sa wajen fita hakkin ta. Da gaske ne Lailah gajiya ta yi da zama da
shi don rashin haihuwa shi ya sa tai tafiyar ta?
Zai so ya ganta a wannan lokacin, ko don ya yi mata wannan tambayar.
Hajiya ta gyara zamanta ta ce,
“Ban da abinku na ‘ya’yan zamani da ba a yi muku gwaninta, da sai in ce mai zai hana ka yi
auren ka ka huta?
Ga nan ‘yar kanin mahaifinka A’isha, ta gama karatun digirinta na farko a jami’ar Bayero, mai zai
hana ka tuntuve ta?”
Ya yi ajiyar zuciya abin tausayi, ya ce, “Hajiya duk yadda kika ce dai-dai ne”.
Ta ji dadi, ta shiga sanya mishi albarka.

A ranar ya soma zuwa wajen A’ishar, doguwa, baka, mai kyakkyawar sura. Ya yaba da
hankalinta da nutsuwar ta, don haka ya sakarwa Hajiyar shi bakin aljihu ta soma shirye-shiryen

aure.
A karshen satin Sa’eed ya zo, nan ya tsinkayi labarin auren. Ya samu dan uwanshi a gidansa da
yammacin ranar asabar.
“Yanzu daga Jama’are nake, Hajiya ke gaya min wai ka amince ka auri A’isha”.
Ya ce, “Eh, haka ne, Lailah ta yaudare ni Sa’eed, ta yadda har ban san ba ta kauna ta ba sai
yanzu, da tana kauna ta da ba ta yi min abin da ta yi min din nan ba”.
Sa’eed ya ce,
“Ba yaudara ba ce Yaya! Idan ka dubi wasikarta da kyau, za ka fahimci halayyarka ne ba ta so.
Sai dai nima na yi mamakin dalilin da ya sa ta zavi tafiya, fiye da ta nemi saki”.
Ya ce,
“Koma dai mene ne ni aurena zan yi, tukuicin kaunata gareta kenan, to ta je, Allah ya ba ta
sa’a”.
Sa’eed ya ce,
“To idan kuma ta dawo fa?”
Ya ce,
“Bana jin Lailah za ta taba dawowa gare ni. Da za ta dawo, da zuwa wannan lokacin koma
mene ne in ta yi don ta hora ni ko don na gyara kuskuren da nake mata da tuni ta dawo”.
Sa’eed dai ya rasa abin cewa, can karkashin zuciyarsa kuwa nadama ce fal, don ya san shine
silar wannan al’amarin.
A wani bangaren tunanin ranar da Allah zai tona asirin cin amanar da ya yi wa dan uwansa mai
kaunarsa yake yi, don ya san ba shi da fuskar da zai dube shi daga ranar, ya kuma tabbata ko
ba dade ko ba jima wata rana Allah zai bayyana al’amarin.

****
Ya kwankwasa kofar ta taso a hankali ta bude, sanye da bakar jallabiya kirar Oman a jikinta.
Ya shigo rike da ledar magunguna a hannunshi na dama, ya yin da hagun ke rike da wata ledar
cike taf da ‘ya’yan inibi.
Suka yi ma juna murmushi a takaice, ya ja kujera ya zauna ita kuma ta koma bakin gadon tana
fuskantar sa.
Ya ciro magunguna a leda ya valla ya mika mata tare da dauko mata gorar ruwa mara sanyi a
firinjinta.
Ta amsa ta soma hadiya, ya ce,
“Lailah, yau dai ki daure ki shirya muje makaranta, don na ga jikin da sauki. An kafe maku
time-table din edam tun shekaranjiya”.
Hanadi, mutuniyar Somalia wadda dakinta ke kallon na Lailah ta yi masu sallama ta shigo, ta
samu gefen gadon da Lailah ke zaune ta zauna suka gaisa.
Ta ce,
“Kwana biyu bana ganin ki kin fito ko kin shiga kitchen, shine na ce bari in zo in ga ko lafiya?”
Tana maganar ne cikin harshen Turanci. Cikin jin dadin kulawar da ta nuna a gare ta ta ce.
“Wallahi kuwa, ina fama da zazzavi ne”.
Ta ce,
“Ayya! Ga shi nan duk ya ramar da ke, Allah ya kawo sauki”.
Su duka suka ce,

“Ameen”.
Suka dan tava hira Abbas bai tofa musu ba, sannan ta tashi ta yi musu sallama ta fita.
Shi ma fita ya yi don ya ba ta dama ta shirya. Ta dauko farar suwaita ta sanya, ta kawo doguwar
‘coat’ har gwiwarta ta sanya tare da dogon wandon ‘cherokee jeans’, ta sanya socks na hannu
da na kafa da rufaffen bakin takalmi maras dunduniya.
Ta dauki katuwar jakarta mai dauke da littattafanta ta rataya, ta janyo kofar dakinta ta sa makulli
ta rufe.
Ta gangara kasa dakin Abbas, ta kwankwasa ya fito shi ma a shirye cikin DKNY, (trouser and
shirt), da bakar suwaita a kai. Ya yi matukar yin kyau, suka jera suka fita. Suka tsaya a ATM na
bankin ‘Lioyds’ ta dauki kudi suka karasa makaranta da kafafun su.
Da suka dawo suka tsaya a kantin ‘Morrisons’ dake nan cikin unguwar su (Acton) suka yi
‘shopping’ suka dawo gida.

Haka Lailah ta ci gaba da rainon cikinta da taimakon Abbas, tun tana damuwa da bakin ciki har
ta daina.
Yau da lafiya gobe babu, haka ta daure tana karatun ta. Sai da cikin ya shiga watanni biyar
sannan ta samu lafiya, kai in ka ganta a wannan lokacin ba za ka ce ciki gare ta ba, saboda
yanayin shigar ta na kaya masu kauri.
Allah sarki Abbas, tun daga wannan lokaci ya soma sayan kayan jarirai yana tarawa (unisex).
Lailah dai ba ta tava sayen komai ba, ita dai ta mika wuya ga duk yadda rayuwa ta zo mata, don
ba ta da tsimi ba ta da dabara.
Abbas ya samu aikin koyarwa (temporary) a wata makarantar sakandire (private), ya zamanto
Lailah ta daina tava ajiyarta ta banki, ya tsaya mata a kan komi, itada jaririnta dake ciki.
Katon na locozade, katon na fresh milk, cret din kwai, kwalin apple da kwalin inibi, duk haka
yake ajiye mata ba ta kuma isa ta yi godiya ba, yanzun nan zai hau fushi da ita.
Ya hanata yava ajiyarta ta banki sam, tana mamakin wannan al’amari, kulawar da yake nuna
mata da kwarin gwiwar da yake ba ta ya wanke duk wani bakin ciki da ke zuciyarta, sai fatan
Allah ya raba ta da cikin da ke jikinta lafiya.
Cikinta ya shiga watanni na tara, ranar wata alhamis sun dawo daga awo a NHS. Abbas ya
mika mata waya ya ce lallai ta kira Mominta su gaisa.
Atleast ko ba ta fadi mata inda take ba, ta sanar da ita tana nan lafiya don hankalinta ya kwanta.
Yana mai nuna mata mace mai haihuwa a kan gava take, baya fata, amma in ta mutu a ya yin
haihuwa me za ta ce da Ubangijinta a kan mahaifiyarta?
Jikinta ya yi matukar sanyi da nasihohin sa, jiki a sanyaye ta soma dialling number Momin,
wadanda suke kamar karatun sallah a cikin kanta.
Bugawa daya- biyu Momin ta dauka, ganin bakuwar lambar ta kasar Ingila. Lailah ta yi sallama
Momin ta amsa, sai dai ba ta gane mai maganar ba.
Lailah ta kai hannu ta share hawayen da suka zubo mata ta ce,
“Momi nice Lailah.....”
Momi ta ce,
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil! Lailah!! Ashe kina raye kika tafi da gangan kika barmu cikin
tashin hankali?”
Ta soma kuka. Ta ce,

“Wallahi ba da son raina bane Momi”.
Ta ce,
“Koma me ke damun ki Lailah da har ya sa ki barinmu na dauka kafin kowa ya ji ni za ki fara
nema ki fada min damuwar ki, amma ba ki tsallake ni ki barni cikin tashin hankali ba.
Da auren ki Lailah…….. ki tsallake mijinki ki tafi wata uwa duniya, kin san hakkin aure kuwa?
Amma tun da hakan kika zavarwa kanki ai shi kenan”.
Ta kashe wayar ba tare da ta sake sauraron ta ba.
Hankalin Lailah duk inda yake to ya yi kololuwar tashi, ta tabbata Momi ta yi fushi da ita, fushi
kuwa mai tsanani tun da har ta ki sauraron ta.
Ta mika ma Abbas wayar tana kuka sosai. Ya barta ta yi abunta mai isarta, bai katse ta ba. A
karshe tashi ya yi ya bar mata dakin don ta ji dadin yin kukan sosai.
Ya kuma cire layin ya sanya wani don shi ma yana ganin ba yanzu ne ya dace lokacin da Lailah
za ta koma gida ba.

A can Alkahira Momi zugum ta yi cikin kwanciyar hankali, ko ba komi yanzu hankalinta ya dan
kwanta tun da ta tabbatar Lailanta na raye, kuma cikin koshin lafiya.
Tun da har ta fara tunanin neman ta wata rana za ta yi tunanin dawowa. Ko da Isma’il ya shigo
ta gaya mishi Lailan ta yo waya cewa ya yi ta ba shi lambar.
Ya gane lambar ta kasar Ingila ce, amma bai san wane yanki bane. Yayi-yayi ya kama layin ya
kasa dole ya hakura.
A ranar Lailah ba ta yi barci ba, tausayin Mominta ya hanata barci na abin kunyar da ta jawo
mata da kuma tunanin yadda za su karvi abinda za ta haifa.
Don ba za ta voye ba gaskiya za ta fadi duk ranar da Allah ya mai da ita gida, don ta san
aurenta vatacce ne a addini.
Ga rashin Babansu ga rashinta, ta san abun ya yi wa Momin yawa, musamman yadda take
sonta fiye da sauran ‘yan’uwanta, take kuma nunawa karara.
Suka smu hutun makaranta har na tsayin watanni uku. A irin wannan lokacin yawancin dalibai
kowa kasarsu yake tafiya.
Ban da Lailah da Abbas, a wannan lokacin cikin ya yi katoto ya kuma yi kasa sosai, don haka
suka sa rainon cikinsu a gaba, baya awa biyu cikakku bai san halin da take ciki ba.
Yana kuma yawan jaddada mata cewa duk wani motsi da ta ji ba dai-dai ba ta kira wayar shi. Ita
har tausayi yake ba ta, ba shi ya kar zomon ba amma ya dauki rataya ya dora a kafadunsa.
Ranar litinin da daddare misalin karfe goma sha biyu na dare. Lailah na barci ta tashi da wani
irin azababben ciwon baya, kafin ta ce meye wannan ta ji ta sharkaf cikin wani abu da ke bin
kafafunta.
Ta soma salati nan da nan ta yi kokarin daukar wayarta a kan ‘bed-side lamp’ ta yi dialling no
Abbas, ba wani vata lokaci ya ce
“ya ya ne? Haihuwar ta zo ne?
Ta ce, “I think so.....”
Ya kashe wayar ya jefar da bargon da yake ciki ya kira hospital van, cikin ‘yan mintuna ta iso da
nurses ya yi masu jagora suka fito da Laila sai NHS.
Kwana daya, biyu Laila na cikin matsananciyar nakuda amma ta kasa, in ka ga kai komon
Abbas a wannan lokacin sai ya baka tausayi.

A kwanaki biyun nan kaf ba abin da ya sanya a cikinsa sai ruwa, kamar shine mai nakudar.
A karshe aka sanya mata ruwan nakuda har leda biyar amma duk a banza. Don haka suka
nemi shi mijinta (kamar yadda suke tsammani) da ya saka hannu ayi mata CS don ceton ta da
yaron gaba daya.
Ba tare da wani tunani ba Abbas ya rattaba hannu, nan da nan likitoci suka fara aikin ceton rai.
Ya samu ‘waiter chair’ ya zauna yana yi wa Lailah addu’ar fatan alheri.
Awanni biyu cur aka dauka ana aikin kamin wata nurse ta fito daga dakin da aka shigar da
Lailah.
Da sassarfar shi ya mike ya cimmata. Ta dube shi cikin tausayi ta ce,
“Am sorry, yaron bai zo da rai ba. Ya dade da mutuwa a cikinta”.
Ya yi ajiyar zuciya mai karfi ya ce, “Lailan fa?”
Ta ce,
“Komi lafiya tare da ita”.
Ba ta rufe bakinta ba aka turo Lailan a kan gadon marassa lafiya zuwa dakin kwana.
Ya ja kujera dai-dai kan Lailah ya zauna, ba a jima ba ta bude ido sannu a hankali tana kallon
shi.
Ya dora sassanyan hannunsa a goshinta, abinda bai tava yi ba, yanzun ma bai san yayi ba,
rudewa ce. Ya ce,
“Are you alright Lailah?”
Ta girgiza mishi kai. Sannan ne ya samu nutsuwar zuciyarsa.

Kwanansu uku, wajen da aka yi wa Lailah ‘operation’ har ya fara kamewa, aka sallame su a
rana ta hudu. Bayan asibitin ta hadata da nurse da za ta dinga zuwa gida tana taimaka mata
har kwana goma sha hudu.
A kwanakin nan duka ba ta bar tsiyayar da hawaye ba, na asarar jaririnta. Hakannan Allah Ya
dauki kaunar yaron Ya sanya mata. To haka shi ma Abbas da ya dauki rai ya dora a kan abin da
Lailah za ta haifa. Ya gama yin duk shirye-shiryen tarvarsa.
Da ta murmure ta koma makaranta, kowa da suka sani tsammani yake ita da Abbas mata da
miji ne, daga su sai Allah suka sani.
Jegon Lailah a kasar England, ya zamo wani abin tarihi a rayuwarta da ba za ta manta ba. Haka
babynta da ya koma ga Mahaliccinsa har abada ba za ta daina tunaninsa ba.
Abbas ya ce, “Yana da kyau ta fara istigfari tun daga yanzu, domin yana ganin lokaci ya karato
da ya kamata ta soma shirin komawa gida, tunda karatun ya zo karshe.
Ba tare da musu ba ta bi shawarar Abbas, sai dai har yau ba ta san da fuskar da za ta dubi
Mohammed ba.

****

Watanni uku bayan nan suka karvi kwalin masters din su, shi kuma Abbas saura shekara daya
ya karvi na PhD. Jikin Lailah a sanyaye suka soma shirye-shiryen tahowa Egypt.

A ranar wata litinin Momi ba ta zata ba ba ta tsammana ba, kararrawar kofar shigowa ta kada,
mai sanar da su cewa akwai bakon d ake son a bude masa kofa.

Budewar nan da za ta yi suka yi arba da diyarta Lailah. Lailah ta rungume mahaifiyarta tana
kuka mai tsanani.
Sanah da Najat, suka taso cikin al’ajabi suka rungume ‘yar uwarsu. Tare suka rankaya falon
cikin yi ma Allah godiya maras iyaka.
Sai da murnar ganin Lailah ta lafa, take sanar dasu tana da bako, don haka Momin ta ba wa
Najat makullin sashen baki ta ce ta bude ma bakon Lailah. Akai masa ruwa da abinci.
Momi ta fiddo waya ta kira Isma’il daga wajen aiki ta ce ya zo yanzu-yanzu ya ga abin mamaki,
addu’arsu ta kwana da kwanaki farat daya yau Allah Ya karva.
Isma’il ya iso gidansu a sukwane, amma maimakon ya yi murna si ya rufe ido ya soma balbale
Lailah da fada, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba a kan tashin hankalin da ta jefa su a
ciki har tsayin shekaru biyu cur.
In ban da sharar hawaye ba abin da Lailah da Mominta ke yi. Daga baya shi ma sai ya rungume
‘yar uwarshi ya fashe da kuka.
Suka yi kukan su mai isar su, kamin da Isma’il ya fiddo waya ya kira Mohammed, wanda
already ya yi aure.
Hakan bai hana shi tsallake aiyukan gabansa ba ya yi landing a Egypt. Suka tsaya cirko-cirko
shi da Lailah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login