Showing 51001 words to 54000 words out of 56966 words
Chapter 18 - WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf
kudi ko?”
Ya ce,
“Sosai kuwa Hajiya, don na yanke ma can gidana na Bauchi za ki koma, ni zan koma Old
G.R.A”.
Ta jinjina kai ta ce,
“To iyali fa?”
Ya yi dan duru-duru na rashin sanin abin cewa, don shi tun lokacinda A’isha ta sha mari bai kara
tuno ta ba ya ce,
“Tana can Bauchi, don kai tsaye nan na yiwo ban je gidan ba”.
Haushi ya kashe bakin Hajiya Baida’u, ta rasa me za ta ce masa. Ta girgiza kai ta ce.
“Na tabbata ba haka kwarorin nan suka barka ba. Yanzu abin da kake yi wa aurenka ka kyauta
kenan?
Baka ma san takamaiman inda matarka take ba. Ka kama ‘yar mutane kuma ‘yar uwarka da
duka kamar jaka aka aura maka?
Tun da ka yi mata dukan ka haure ka yi tafiyar ka ba tare da ka damu da halin da take ciki ba,
balle ka binciki lafiyarta, wai sunan tana matarka....”
Ya katse ta da cewa, “Ni fa Hajiya ban doke ta ba, marin ta kawai na yi da na ga za ta kawo min
rashin kunya, wato zuwa ta yi ta ce na dake ta kenan?”
Hajiya ta ce, “Ungo naka....”
Ta yi masa umbola. “Wato marin ma kawai ne. Ka fada da bakinka ka doketan kenan. To sam
ba zan lamunci wannan rashin hankalin ba, ka je can gidansu ka ba ta hakuri ka sa matarka a
gaba ku tafi, kada na kara ji ko da tsinke ka tsikare ta dashi balle mari. Idan ba haka ba wallahi
zan dauke ta, in ya so ka koma in da ba a san darajarka ba ka je can ku karata, ni kuma in fidda
hannuna a kanka”.
Ya sunkuyar da kai, “Duk me ya yi zafi Hajiya? Ki yi hakuri zan je in ga Baba Adamun, zan ba
shi hakuri amma don Allah ki sa min albarka!”.
Ya ba ta tausayi matuka, Allah ya ba ta ‘ya’ya masu gudun zuciyarta, su biyu kacal amma
kamar goma ta haifa. Zurfin ilimin zamaninsu bai sa sun kangare mata ba, komi ta ce ‘eh’ ne ko
da bai yi masu ba.
Sai dai har yau ba ta kara tada zancen Sa’eed da Lailah ba, ga dukkan alamu ba ta son zancen
kwata-kwata, duk da ta amincewa ranta gaskiya ne tun da har Sa’idun ya furta mata da bakinsa.
Ya dai nemi gafararta ya kuma ce ta taya shi neman gafarar Ubangiji. In Allah ya yarda wani
abu makamancin wannan ba zai kuma faruwa da shi ba, insha Allahu.
Ya sa aka fiddo jakunkunan da ya zo da su, sittiru ne dankare, ya ware na Sa’eed. Hajiya ta ji
dadi sosai.
Sannan ya ce, “Sauran a rabawa dangi”.
Ta ce, “To, matarka fa?”
Ya ware wasu ya ce, “A kai gidansu ita zai ba ta nata daban”. Bayan shi tun da ya tafi ma ko a
mafarkan shi ba ta zo ba. Tunanin shi na LAILAH ne, sai dai ya ce Allah ya yaye masa.
Duk kawaicin Baba Adamu yau ya fitittike ya gwada masa shi ma yana son ‘yarsa. Bayan dogon
kai ruwa rana da ban hakuri sannan da kafa sharudda sannan ya yarda ya kira A’ishan suka tafi,
wadda ita kam kamar a kan kaya ta yi watanni ukun nan cike da nadamar fitowar ta, domin ta
tabbatar kafin ta sake samun wannan daular da tsadadden miji irin nata a matsayi da ajin
rayuwarta, abu ne mai matukar wuya. Ko ko a ce ba zai yiwu ba. Allah ne ya kashe ya ba ta,
wautarta za ta kwace mata.
Don haka tun a mota ta soma zuba masa hira, tun yana share ta har ya biye mata. Suna yi wa
Baba Adamu dariyar sharuddansa na duk ranar da ya kara dukan ta zagewa zai yi ya rama
mata, don bai fi shi karfi ba.
****
Tun zuwa Sujood, Lailah ta samu abokiyar debe kewa, duk sanda ba ta da darasi tana sassan
Sujood ko ita Sujood din na nasu vangaren. Ko su shiga gari idan Isma’il baya nan.
Cikin watanni biyar da suka biyo baya, account dinta ya yi nauyi, don ba ta tava komi cikin
albashinta, Isma’il ya dauki nauyin rayuwarsu gaba daya.
Kuma Egypt ba kamar London ba, ba ta biyan kudin haya, gida ne nasu na kashin kansu. Duk
da matsin tattalin arziki da kasar ke da shi wannan bai sa al’ummarta zama cikin talauci ba.
Egypt kasa ce mai dadin zama da albarkar abinci, da suttura da wadatar ilimi, da kwararrun
ma’aikata kiwon lafiya.
Kullum cikin kwanciyar hankali da wadata suke, ban da yanzu da suke fuskantar matsin
Amurka. Sai dai damuwar Lailah daya (ABBAS) ina za ta nemo shi?
KANO da girma, kai ita duk zamanta a Najeriya ma ba ta tava zuwa Kano ba, ba ta san ina take
ba.
Tana dai ji ana fada Kano-Kano a bakin Sa’eed da Mohammad, amma ba ta ma tava tambayar
su wani sharhi a kai ba. Ta kuma gwada nambobinshi na Britain an gaya mata ba a amfani dasu
sam.
“Watakila Allah ya rubuta iyaka haduwarmu kenan???”
Ta tambayi kanta cikin sanyin murya.
“Haduwar kan hanya ce ta zamo haduwar ZUCIYA…., aminci, kyautayi da abota ne suka hadu
suka yi gingimemen gini a ZUCIYA. Wanda hakan ya janyo ZUCIYAR take so, amma baki ya
gaza furtawa...... Saidai sau tari fuska kan gaza boye zahirin abin da ke ZUCIYA, domin
ZUCIYAR na ragaita....Sai dai kuma a rashin sani na ashe bani da ‘yancin wannan
al’amarin………
Ta tuno kalaman wasikarsa.
Idan ta yi wa wadannan kalaman fassara ta hankali....Abbas na son ta! Sai dai AUREN da ta ke
da shi ya zama shinge. Ta yi murmushi ita kadai, ta juya ta rungumi filo.
...... “Kana da ‘YANCIN Abbas, yanzu kana da ‘YANCIN, dukkanmu muna da ‘YANCIN. Allah ya
hada fuskokinmu cikin gaggawa”.
Idan ta ce tunanin Abbas da soyayyar shi da ta yi kane-kane a zuciyarta za ta dinga yi, lashakka
za ta samu matsala a kan aikinta.
Don haka take rufe ‘file’ din zuciyarta a duk lokacin da take tare da dalibanta, wadanda suke
kaunarta saboda karancin shekarunta da manyan kwalaye haka. Kuma a lokacin ne Jami’ar
Al-Azhar ta tura ta karo Karatu (in service) a Jami’ar Ummul-Kura da ke Madinah.
Duk yadda ta yi don ta cogewa hakan abin ya faskara, domin tsarinsu ke nan. Dole ka mallaki
kwalin PhD a matsayinka na ‘staff’. Wannan ne zai baka damar zama Dr. A ilimi. Sai dai aure da
iyali na sanyawa a barka a nan cikin Alkahira, wanda ba ta da ko daya.
Ta samu Momi da Isma’il take gaya musu batun tafiyarta Saudi-Arabia. Sujood sai ta hau kuka
ita ba ta yarda ba.
Isma’il na dariya ya ce,
“Haba Sujood sai ka ce wata karamar yarinya? Abin da za ta dinga zuwa ko mu muje?”
Budar bakin Sujood sai cewa ta yi, “Ni sai dai mu tafi tare”.
Lailah da Isma’il suka kwashe da dariya, Momi ba ta ce dasu komi ba.
Sai da Sujood da mijinta suka tashi Momi ta dubi Lailah sosai ta ce,
“Kina da yakinin cewa za ki iya rike kanki da mutuncinki tsayin wannan lokacin din?”
Kawai sai Lailah ta fashe da kuka. Ta rasa ranar da Momi da Isma’il za su daina yi mata kallon
wata mara imani.
Wane irin tuba suke so ta yi a kan kuskurenta wanda ba ta yi ba? Shekara guda har da doriyar
watanni sun kasa yi mata kyakkyawar shaida?
Momi ta saki baki tana kallon ikon Allah, ta ce,
“To mene ne abun kuka cikin maganata?”
Ta ce,
“Kun kasa yarda dani Momi. Da zinar halina ce da na yi ta inda babu mai ganin aibunta, kuma
da ban fada maku ba balle ku san na aikata.
Momi ki yarda dani, wallahi-wallahi ba zan kara ba, kuskure ne wanda ba wanda ya fi karfin
yinsa.
Ki yafe ni Momi, ki tayani rokon dan uwana ya yarda dani. Ku yi min kyakkyawan zato, kada na
mutu ba tare da shaidar arziki daga bakin ku ba....” Ta ci gaba da kuka.
Momi ta dube ta sosai ta ce,
“Kina tunanin da shari’ah ake bi a wannan zamanin da ba a jefe ki ba?”
Ta fiddo ido kwalala! “Momi duk da sahihancin tuba na da nadamata?”
Momi ta ce,
“Wannan ne dai ban sani ba, sai dai ki tambayi malamai. Lailah kin bani tsoro sosai, duk
tarbiyyar da na maki?”
Ta sa havar gyalenta tana share hawaye.
Hankalin Lailah ya kara tashi, ita ma ta kama kuka. Suna cikin kukan Sanah da Najat suka
shigo aguje suna kokawa a kan ‘yar tsana, dole suka share hawayen Lailah ta raba rigimar suka
fita.
Lailah ta dago jajayen idanunta ta ce, “Momi me zan yi ki yi farin ciki dani?”
Ta ce,
“Aure”.
Ta fyace hanci da ‘tissue’ ta ce,
“Insha Allahu Momi kamin in gama karatun nan na shekaru biyu zan kawo miki mijin aure na”.
Momi ta ce, “Da dai kin yi wa rayuwarki gata, amma ba wannan neman duniyar ba”.
Ranar litinin jirgin Egypt - Air ya sauke Lailah a birnin Jiddah, ta yi masauki a AL-JAMJOUM
zuwa washegari ta bi bus ta wuce cikin Makkah da niyar aikin Umarah.
Kwanan ta uku a Mecca cikin aikin Dawafi da neman gafarar Ubangiji a kan komai ma, tun safe
har dare ban da lalurar dan Adam ta ci da sha da shiga bayan gida ba abin da ke raba ta da
dakin Allah.
Daga nan ta wuce Madinah, ta kai ziyara shabbaki da duk inda ya kamata. Kwananta biyar ta
wuce Jami’ar Ummul-Kura.
Duk wasu cike-ciken takardu na ‘registration’ da ma an riga an gudanar da su ta computer, sai
dan abin da ba a rasa ba.
Ta zavi zama cikin ‘hostel’ din dalibai don ya fi mata kwanciyar hankali, ta soma karatunta cike
da himma da karfin zuciya.
Bayan tsayin watanni uku suna karatu suka samu hutun sallah break. Ta yi ‘booking’ jirgi sai
Egypt. Inda shigowarta harabar gidansu kenan ta soma cin karo da taron yara sa’o’in su Sanah
kowanne ya ci kwalliya kamar ranar ne sallah.
Sanah da Najat sun dora wuka kenan za su yanka ‘cake’ din ‘Birthday’ din su suka hango ta
tana ratso mutane. Suka yi wancakali da wukaken hannunsu suka sheka suka rungume ta.
“marhaba biki Ya Ablah” (Ablah suna ne da suke kiranta da shi sau tari, wanda ke nufin Yaya)”
Dole sai tare da ita aka yanka ‘cake’ din suka daddanna mata a baki aka yi tafi, sannan
kawayensu suka soma rero wakar ‘happy birthday’ cikin harshen Larabci, na cikar Sanah da
Najat shekaru goma-goma.
Don haka wunin ranar zungur hidimar da suka wuni yi kenan a gidan har magariba. Sujood na
asibiti an ba ta ‘bed-rest’ tana laulayin ciki mai wahalarwa.
Ba su samu kevewa da Momi ba sai lokacin barci. Suna hirarsu a hankali irin na da da mahaifi.
Lailah na ba ta labarin jami’ar Ummul-Kura da irin tsarinsu wanda ya bambanta da na Azhar.
Momi ta ce
“Af! Kinga kuwa na manta mutumin nan da ya rako ki Bahaushe ya zo bakya nan”.
Saura kadan Lailah ta fado daga gadonta, Momi ba ta yi aune ba sai ganinta ta yi durkushe a
gabanta, kirjinta kamar ya fashe saboda bugu.
Ta ce, “ABBAS?”
Momi ta ce, “Kwarai haka Isma’il ya gaya min sunansa”.
Ta ce, “Ya tafi?”
Momi ta ce, “Tun a ranar, domin daman a kan hanya yake zai wuce gida Najeriya daga London.
Ya ce ya zo ne ya gaishemu kawai, bai yi tunanin kun rabu da Mohd ba, ya dauka kina
Najeriya”.
Lailah dai gaba daya ta bushe a zaune ne don gigicewa, don ma tana kokarin saisaita kanta
kada Momi ta fahimci rikicewar ta.
To amma ai Momin ba karamar yarinya ba ce, ta fahimci akwai wani muhimmin al’amari
tsakanin Lailah da abokin tafiyarta, tun ranar da ta kasa cin abinci don an sanar da ita ya tafi, ba
tare da ya yi mata sallama ba.
Ta ce, “Hala saurayinki ne tun a Ingilar taku?”
Ta zaro ido kuru-kuru ta ce, “Wane irin saurayi Momi?”
Ta soma bai ma Momi labarin haduwarta da shi tun a filin jirgin saman Abuja ranar da za ta
tashi zuwa Birtaniya, da yadda ya taimaika mata da rayuwarsu a makaranta da gida.
Ta kara da cewa, “Ko da kuskure mutumin nan bai tava sauya kallon da yake min na kanwarshi
ba, ya taimake ni a kowanne fanni na rayuwata a can.
Ya kare min mutuncina domin da dama kallon mijina ake yi masa ko Yayana, don haka babu
wani mahaluki da ya tava dosa ta da zancen banza har na baro Ingila”.
Ta kare da cewa, “Momi shi ya yi min nasiha na dawo gida, shi ya hanani zub da ciki, Momi
Abbas yana da kirki sosai, kuma wallahi Momi shine irin mijin da nake mafarkin samu a
rayuwata”.
Momi ta yi murmushi ta ce, “Har kin sa ina son shi”.
Ta ce, “Kirkin shi ya wuce duk yadda kike zato Momi, ga tarin ilimi. Shi ma (Philosopher) ne, don
da ya kare karatu a take makarantar ta dauke shi cikin sababbin malaman ta”.
Ta ce, “Dan ina ne?”
Ta ce, “Kano-Nigeria”.
Ta ce, “Garin su mahaifin ku....”
Lailah ta ce, “Yauwa Momi, wai Babanmu ba shi da wasu ‘yan’uwa ne a can Najeriya?”
Ta ce, “Mahaifin ku maraya ne, amma akwai Baffanninsa guda biyu Kano a unguwar Kabara,
ban sani ba ko suna raye”.
Lailah ta ce, “Ya kamata mu neme su Momi, kinga dai yadda rashin dangin uba ya janyo min
gori da rashin kima a gun Hajiyar Mohammed”.
Ta ce, “Isma’il ya san inda suke, idan kun kara dawowa sai ku je, amma ni ba inda za ni”.
Lailah ta saki wannan hirar ta ce,
“Momi bai ce zai sake dawowa ba?”
“Wa kenan?”
Cike da jin nauyi ta ce,
“Abbas”.
Sai ta yi murmushi kawai ba ta ce mata komai ba.
Ko da Isma’il ya shigo daukar ma Sujood wasu kaya da za ta yi amfani dasu a asibiti bai ce da
ita komi ba game da zuwan Abbas.
Ta kasa daurewa ta ce, “Zan iya binka muje wajen Sujood?”
Ba tare da ya juyo ba ya ce, “Basu barin aje dubiya kar a damu mara lafiya”.
Ta ce cikin fargaba, “Ashe Abbas ya zo?”
Ya juyo yana kallon ta, shi kansa ya rasa dalilinsa na tsanarta, ya ce, “Eh, wani abune?”
Ta hadiye kukan da ya taho mata ta juya da gudu ta yi gidansu ba tare da ta ce da shi komi ba.
Ta kwanta rub da ciki a kan gado, tana kuka mara sauti, wanda ta toshe shi da bakin mayafin
abayarta kada Momi ta jiyo sautin kukanta.
Ba ta ji murda kofa da rufe ta ba sai zaman mutum a gefen ta. Kamshin turaren shi a gefenta ya
sanya ta dagowa da sauri, Isma’il ne.
Ya mika mata hankicif dinshi ya ce, “Share hawayen”. Cikin sassanyan Larabci.
Ta karva ta share amma ba ta dube shi ba. Ya yi shiru sannan ya ce, “Ki gafarce ni, haka nan na
samu kaina da daina ganin farin ki. Domin........”
Ta kai hannunta ta toshe masa baki don ba ta son jin abin da zai fada, zancen nan ne dai da ba
ta so a kara tuna mata.
Ya sauke hannunta daga bakinshi ya ce, “To ki yi hakuri”.
Ta ce, “Na yi”.
“Abbas ya zo baki nan, ya yi mamaki kwarai jin cewa all these while kina gida. Amma baki
neme shi ba, na gaya mishi ko waya baki rikewa. To amma zai dawo”.
Ba ta so ya ga ta fiya ci-da-zuci. Da ta tambaye shi yaushe zai dawo din?
Ya mike ya fita yana cewa, “Sujood ta damu tana so ta ganki. So ki daure ki yi ko sati ne ta
dawo ta ganki”.
Ta ce, “Allah sarki Sujood, Allah ya raba su lafiya”.
Ya amsa
“Ameen”.
Washegari ta tashi da nishadi, don haka ta je aka yi mata kunshi da gyaran gashi, akaifa da
wankin kafa. Ta wuce makaranta ta dawo.
Bakuwar mota ta gani a harabar gidansu, ta karasa ciki da sassarfa bayan ta rufe motar ta.
Mohammed ta fara yin tozali da shi, sannan Sa’eed da wasu kyawawan mata guda biyu da fara
da baka.
Tana tafe cikin falon har hardewa take yi, ya yin da Isma’il ke ta wadata ‘dining’ da abinci da
abin sha shi da Amatullahi mai aikin su.
Momi na gefe ita da A’isha suna ta hira, Momi na ta zuba shakakkiyar Hausarta kamar jakar
Kano.
Kallo daya Lailah ta yi wa Sa’eedu ta ga yadda ya rame ya lalace kamar ba shi ba, ta dauke kai
kamar ba ta ganshi ba.
Za ta wuce ciki Momi ta riko hannunta ta ce,
“Baki ga bakin naki bane?”
Dole ta zauna gefen Momin tana kallon su kawai da idanu. Sa’eed na kuka bayan shigar su
A’isha sassan baki, yake rokonta ta yafe masa, ta yafewa Mohd.
Don a dalilinta yanzu Mohd ya aje aiki, ya ce, tunda aikin ne ya raba shi da ita, yake kuma
barazanar raba shi da duk matar da ya aura to ya barshi, zai gwada wata sana’ar.
Kuma anyi masa aiki, yanzu haka A’isha na da ciki wata biyar. Wannan kuma Zanira matarshi
ce, ita ma ‘yar uwarsu ce. Shi kuma ba shi da lafiya suga ta kama shi sosai.
Shi yana kuka Lailah na yi. A da kam ta yi alkawarin ba za ta tava yafewa Sa’eed ba har
karewar numfashinta, amma a yau ta tuna wani karin magana da Hausawa ke cewa.
“....... Idan vera da sata.....to daddawa ma da wari”.
Sai ta ce, “Allah ya yafe mana bakidaya”.
Ta zage sosai ta karvi su A’isha, karva ta karshen mutuntawa. Shi dai Mohd sai ido yake binta
da shi ganin yadda ta kara komawa yarinya danya sharaf ba ‘yar shekaru talatin ba.
Soyayya gaskiya ce, kuma har abada ba