Showing 45001 words to 48000 words out of 56966 words
Chapter 16 - WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf
sai kallon-kallo, the one that is always hunting his dream….
A hankali jama’ar dake katon falon suka shiga zamewa, ya zamo daga Lailah sai Mohammad
dinta, wadanda suka yi cirko-cirko suka ci gaba da kallon juna kamar yau suka fara ganin juna.
Tsohuwar soyayya ta motsawa Mohammed, ya mika hannu ya kamo hannun Lailah, sannu a
hankali ya hadata da jikinsa ya kankame ta ya rungume, a hankali ya kama sakin wata irin
sassanyar ajiyar zuciya.
Wasu irin dumammun hawaye suke kwaranyo daga idanuwan Lailah, hawayen da ita kanta ba
ta san ko na mene ne ba, na nadama ne? Na tunanin gurvataccen auren ta ne? Ko ko na
tunanin da wane harshe, da wace fuska za ta fuskanci Mohammed?
A hankali ta soma zamewa daga jikinsa, ta durkushe a kasa kan gwiwoyinta ta soma girzar
kuka mai cin rai.
Shi ma binta ya yi ya zauna dirshan a gabanta, ya ce,
“Lailah duk kukan nan na mene ne? Kin tafi a bisa na yi miki laifi, ko ko don ni ba na haihuwa?
Kin kuma yi tunanin dawowa wanda mun yi farin ciki da hakan.
Don haka ban ga me zai saki kuka ba, illa mu yi tunanin matsalolinmu da neman hanyar
warwaresu domin cimma rayuwa mai amfani.
Sai dai ban sani ba ko za ki iya ci gaba da zama dani duk da rashin haihuwata ko a’a?”
Ta yi saurin cira kai ta dube shi, cikin muryar kuka ta ce,
“Ban tava tunanin in guje ka ba wai don ba mu haihu ba, illa don hujjoji nan da na ambata maka
cikin wasikar da na bar maka.
Sannan ni din wata mai babban laifi ce a gare ka da Ubangijina. Sai dai nima ban san me ya kai
ni ga aikatawa ba. Amma ina da tabbacin cewa na yi tsarkakakken tuba wanda Allah (S.W.T) ya
yi alkawarin karvar sa, wato tuba da tabbacin ba za a sake komawa izuwa zunubin ba”.
A hankali ya ce,
“Laifin me kika yi min Lailah? Gaya min komin girmansa.......”
Ta mike daga jikinshi ta ba shi baya, ta isa ga taga tana kallon harabar gidansu inda ruwan
sama ke sauka a kan korran ciyayin da suka yi wa gidan kawanya.
Ta vata shiru na lokaci mai tsawo, tana hango girman laifinta, hoton ranar da ta kira “bakar rana”
na gilmawa a idanunta.
Hawayen idanunta na tsiyaya duk da ta amince da tubanta. Ganin ba ta da niyyar cewa komi,
ya kara taku ya isa bayanta, ya dora hannu a hankali bisa kafadunta.
Ta juyo suka yi ‘facing’ juna idanunta sharkaf da hawaye, kafin ta mika hannu ta share su,
sannan cikin karyayyar murya ta ce.
“Za ka iya yafe min idan na fada maka cewa har haihuwa na yi da Sa’eed?”
Idandunan shi ne suka yo waje tamkar an busa masu barkono, ya kasa furta komai, kai kamar
ma bai ji dai-dai ba.
Ta share ambaliyar hawayen da suka shimfido mata ta ce,
“Aure tsakanina da kai ya haramta Mohammed.... shaidan ya rinjaye mu mun aikata cin amana
a gare ka.
Ni kaina ban san ya aka yi ba, sai da mai afkuwa ta afku. Ina cikin kunyar ka, ina cikin kunyar
Mahaliccina………
Ka yi afuwa a gare ni Mohammed, ko na samu sassauci wurin Ubangijina.
Na tafi domin ina ganin zaman nawa ba shi da amfani, aurenmu ya riga ya gurvata, na yi asara
kuma na ci amanarka, duk da kai ma kana da naka kamashon.
Tun da an tambayi Manzon Allah (S.A.W) cewa, “Kwana nawa ne mace mai aure za ta iya yi ba
tare da namiji ba?”
Ya ce, “Kwanaki arba’in”. To ni casa’in nake yi ban ganka ba.
Sai ya nuna shi yana da lokaci na, yana kula dani tamkar matarsa, yana kyautata min tare da
bin duk wata hanya don ya sama min farin ciki.
Sannan ka dauko baligi ka hada da matarka wacce ke cikin shekaru na kuruciya, alhalin kai din
baka nan. Ta ya ya varna ba za ta faru ba......?”
Tun da ta soma magana bai yi magana ba binta yake da ido, da zuciya. Jin al’amarin yake
kamar almara ko mafarki.
Idan ma Lailah ta kullawa dan uwanshi wannan sharrin ne don ta rabu da shi, wanda tuni ya
fahimci take-taken ta kenan, ko don ta hada shi da marayan dan uwansa da baya da ya shi a
duniya, to, ta yi karya, ta kuma yaudari kanta”.
Ta dai tafi ta yi gantalinta ta yi shegenta, ba zai tava yarda da wannan tozarci ga dan uwansa
ba.
Ya daga rinannun idanun shi da suka kada suka yi jawur suka kankance ya ce,
“LAILAH!”
Dagowa ta yi a hankali ta dube shi, har yanzu kuka take.
Ya ce,
“Mece ce hujjah? Ko shaidar da zan yarda da ke, wadda shari’a za ta yarda da shi ta
gurvata/haramta auren namu?”
A mamakance ta dube shi, wato duk irin bayanin da ta yi mishi bai yarda da ita ba. Ta ce, “Na
dubi Allah ne na fallasa maka sirrina da yake voye.
Wanda babu wanda ya sani daga ni sai dan uwanka, don in samu afuwa da yafiyar ka ko na
samu saukin hukuncin da Ubangiji zai yi min idan na ha’ince ka muka ci gaba da zaman
ZINA....”
Tare ta ya yi.......
“ZINA? Ai kin je kin yi abarki, wannan ke da Ubangijinki. Amma AURE NA yana nan ba abin da
ya same shi, ba kuma wanda ya isa ya sheganta min shi tun da ban gani ba.
Wace mace mai mutumci ce za ta tafi turai tsayin shekaru biyu ba tare da muharraminta ba, ta
ce wai wani wanda ke Najeriya ne uban shegen nata?
Kin ganni nan duk son da nake yi wa mace ba ta isa ta tozarta ‘yan uwana in kyale ta ba. Don
haka ki nemo uban shegen ki a inda kika baro shi, ba cikin zuri’ata ba”.
Lailah ta soma hasala, zuciya ta harzuko ta.
Ta ce,
“To me ya yi zafi Mohammed? Ka yar da kwallon mangwaro ka huta da kuda mana?”
Ya yi mata wani irin kallo wanda ta kasa fassarawa, domin kallo ne na kiyayya da rashin kauna,
wanda ba ta tava gani cikin kwayar idanunshi ba.
Ya yi wani irin miskilin murmushi ya ce.
“Ai hakan kike so. Na kuma ramfo ki yarinya. Sai ki sake dabara wadda kowa zai yarda dake ba
sai kin tozarta dan uwana ba. Don hakan ba karamar illa ba ce ga mutuncinki a idon duniya.
Aurenmu babu rabuwa.
Ba shege daya ba, ko dari ne zan karve su tunda ni musulunci ya baiwa. Don haka ki shirya
gobe mu wuce gida kawai cikin mutuncin ki.
Na yi alkawarin ba mai jin wannan katovarar taki daga bakina, sai idan ke kika sake furtawa.
Zan yi kokarin in gyara kuskurena kamar yadda kike so Lailah. Amma wannan magana, ki
barta.
Ki yi haka ki binne ta tunda baki da hujja ko shaida ko kotu ba za ta karve ta ba.......”
Ta katse shi,
“Allah shine shaida ta, kuma ba zan yi zama na zina ba. Da din ma soyayya ta rufe min ido
nake zaune da kai Mohd. Kana kwara ta, nake jure bakin cikinka har na kai kaina ga halaka.
Ba don Ubangijina ya yi gaggawar farkar dani ba, na san da har yanzu ina cikin halaka. Ka
tambayi duk malaman da ka sani.... babu aure tsakanina da kai, tunda na kwanta da shakikinka,
alhalin kana raye.
Mohammed na soka, na soka da zuciya daya, kuma har gobe ina sonka, ba zan iya komawa
aurenka ba muddin ina cikin hankalina.
Amma tun da ka ce sharri na yi wa Sa’eed, to muje a hakan, wata rana gaskiya za ta yi
halinta.....”
Da sauri ya katse ta,
“Ban sake ki ba Lailah.....ki kwana da sanin wannan. Ba kuma zan tava yin hakan ba, in dai
sunana “Mohammad!”.
Don haka na baki kwanaki uku ki yanke mai fissheki, za ki bini mu koma ne, koko zan ji
sammaci daga kotu........?”
Fuuu! Ya fita ya banko kofar har sai da Lailah ta razana, mamaki kam yau ta sha shi kamar ya
kashe ta, ta yadda mutum mai ilimi kamar Mohammed ya mai da kanshi katoton jahili cikin
addini, saboda soyayya da ta rufe mishi ido.
Ta dade tana sake-sake ita kadai, ko dai ita ma ta bar maganar ne kamar yadda ya ce a barta
ba tare da ta tozarta kanta ba?
Idan ta ce kotu za ta kai shi a kwatar mata sakin aure kanta za ta tozarta. Duniya ta ji abin da
WASA DA KANIN MIJI ya janyo mata.
Asirinta ya bankadu har Momi da sauran ‘yan uwanta su ji, ta kuma san har ‘ya’ya da jikoki ta
barma kanta abin gori.
Abu mafi a’ala dai shine a bar maganar, amma kuwa idan ta ci gaba da zaman auren da
Mohammed din da har gobe zuciya ba ta hutawa da kaunar sa, zaman ZINA, tana sane, wane
hukunci Allah zai yi mata?
Ta fashe da kuka sosai tana yi a hankali kada wani ya jiyo ta, kuka mai cin rai da soya zuciya.
Ta yi tunanin bari kawai ta je ta nemi shawarar Abbas a dakin baki, domin kuwa shi babba ne da
ya fi ta kaifin hankali da kaifin tunani.
Sannan shi ne mutum na farko da idan ta bi shawarar shi take ganin alfanunta. Bata nadama a
cikin duk shawarwarin da yake bata.
Ta fada toilet ta wanke fuskarta da sabulu, ta sauya abayar da ke jikinta ta murda kofar ta fito.
A babban falo su Momi ne da su Najat sun yi shimfidar leda suna cin abincin dare, sai lokacin
ne ma ta tuna rabon ta da abinci tun na daren shekaranjiya.
Amma wannan ba shine a gabanta ba, fita ta yi harabar gidan ta doshi dakin baki. Ta yi sallama
har sau hudu ba’ a amsa ba, sai ta murda kyauren ta shiga.
Babu Abbas babu ko jakar kayan shi. A kidime ta dawo falon tana tambayar Isma’il ina Abbas?
Hannu ya tura cikin aljihu ya fiddo ambulan fara tas ya mika mata. Ya kara da cewa.
“Ai tun zuwan Mohammed, da na gaya mishi shine mijinki ya tafi. Ya ce 4 o’clock flight zai bi
zuwa London.
Dama burinsa shine ya rako ki ya kawo ki gida, sauran bayanan za ki ji a cikin wasikar”.
Cikin sanyin jiki da kasala ta mika hannu ta karvi ambulan din.
Sanah ta cika plate da shawarmah ta mika mata, hannunta har rawa yake saboda yunwa. Ga
wata kewa da ta lulluve zuciyarta, irin wadda ta dade bata ji ba a rayuwarta, tun bayan rashin
mahaifinta.
Abbas wani mutum ne mai muhimmanci da kima a gare ta da ba za ta tava mantawa da shi ba.
Hanya ce ta hada su, amma tana jin shi da wani muhimmin matsayi a zuciyarta da ba za ta iya
tantance wanne irin, matsayi ne ba.
Ga dai mahaifiya ga ‘yan uwanta, ga kanne da yayye musamman Isma’il wanda a yanzu yake
matsayin tamkar mahaifi a gare su, amma jin ta take kamar ita kadai ta rage a duk fadin
duniyar.
Haka nan take caccakar abincin ba don dadi ko dadin rai ba, illa don ta faranta wa ‘yan uwanta
da mahaifiyarsu da suka zubo mata ido don ganin sauyawar da jiki da fuskarta suka yi da jin
cewa bakon ta ya tafi.
Ba ma kamar Isma’il dake kare mata kallo cikin nazari. Gaba daya ta susuce ta zama kamar
wata firgitacciya.
Tun dawowar ta ya fahimci da abin da ke damun ta, tana kokarin voyewa. Ganin cewa juriyarta
ta kare kada ta fashe da kuka a gaban su, sai ta aje cokalin a hankali ta mike ta yi dakinta.
Isma’il da Momi Najla suka bi ta da idanu masu cike da damuwa.
Ba ta bude wasikar Abbas ba sai da ta yi sallar isha’i, ta kara da shafa’i da wutri. Ta daga
hannuwanta sama tana hawaye tana rokon Allah ya yafe mata, ya kawo masalaha cikin
rikitacciyar rayuwarta.
Sannan ne ta bude wasikar Abbas, ga abin da ke rubuce:
LAILAH!
Haduwar kan hanya ce ta zamo haduwar zuciya...aminci, kyautayi da abota ne suka hadu suka
yi gingimemen gini a zuciya..., wanda hakan ya janyo zuciyar ta ke so, amma baki ya gaza
furtawa.....
Sai dai kuma sau tari fuska kan gaza boye zahirin abin da ke zuciya…… domin zuciyar na
ragaita, a rashin sani na ashe bani da ‘yancin wannan al’amarin....
Don haka na wuce London, a duk lokacin da kika tuna ni Lailah..... ki sanya ni cikin kyawawan
addu’o’inki. Ina yi miki fatan ALHERI.....
Ta dade tana maimaita wasikar Abbas, amma ta kasa fahimtar ta, ta karanta ya fi sau hamsin
amma ba ta fahimci sakon da yake son isarwa gare ta ba.
Wane al’amari ne ba shi da ‘yancinsa? Zuciyarta ta halarto mata da amsoshi da dama, ciki
kuwa har da mai cewa.
“BA SHI DA ‘YANCIN AURENKI TUNDA KE MATAR AURE CE......!”
Sai ta kwantar da kanta a kan dardumarta, tana hawaye. Abbas shine irin mijin da take so, take
fata, take kuma addu’a, Allah Ya bata, miji wanda ya san hakkokinta, ya ke wanzar da lokacin
shi da hidimomin rayuwar shi wajen kulawa da mace. Yake ririta ta tare da tattalin ta. Sai ta
samu kanta da kewar Abbas, kewa mai yawa kuwa. Yayin da daya vangaren na zuciyarta ya ki kewar Mohammed Jama’are, wanda ke son su koma
su yi zaman zina, da son ranta ko babu.
Ta alkawartawa ranta da dai ta komawa auran Mohammed, gara ta karasa rayuwarta babu
aure, don ba ta ga so da kauna da aminci a cikin shi ba.
A wani vangaren kuma idan ta ki Mohammed shi Abbas a ina za ta nemo shi? Ya ga mijinta ya
dawo ya yi tafiyarsa ba tare da ya yi mata sallama ba, balle su fuskanci juna su shawarta mafita
ga rayuwarsu.
Ina za ta nemo shi? Kano da girma, ina za ta nemo shi ba ta san komi a kan garin da yake ba
balle mazauninsa....
Ta kifa kanta cikin tafukanta ta soma kuka mai cin rai, kuka irin wanda ta dade ba ta yi a
rayuwarta ba. Kukan sabo, soyayya da kewa, soyayya mai laushi da taushi, da ba ta tava tsintar
kanta a ciki ba.
Daga karshe barci ya sace ta cike da mafarkai barkatai marasa kan gado, duk a kan
Mohammed da Abbas.
Don haka da kyar ta samu ta yi sallar asuba a kurarren lokaci. Ta koma ta kwanta, ba ita ta tashi
ba sai karfe goma na safe da Momi ta kwankwasa mata kofa.
Ta yi mika ta yi salati sannan ta zo ta bude kofar.
Kallo daya Momi ta yi mata ta ga fuskarta a kumbure, idanunta sun yi luhu-luhu sun yi jawur. Ta
kama hannunta, har bakin gadonta sannan ta rungume ta. Ajiyar zuciya mai nauyi ta suvucewa
Lailah.
Hawayenta suka kwaranyo a bayan mahaifiyarta, ta yi kukan ta ma’ishi, Momi Najla ba ta
dakatar da ita ba.
Ta tabbatar akwai abin da ke damun diyarta wanda zurfin ciki irin nata ba zai bari ta bude baki
ta fada ba.
Ta kai hannu tana shafar bayanta tana lallashin ta. Ta ce.
“Idan baki gaya min abin da ke damun ki ba Lailah wa za ki gaya mawa? Ni mahaifiyarki ce, da
ta tsuguna ta haife ki, nice farko da ya kamata in san damuwar ki, in yi kokarin da zan iya in
warware miki ita.
Jiya na ga Mohammed ya fito cikin fushi, sannan tun da aka gaya miki tafiyar wanda kuka zo
tare kin kasa ko cin abinci. Kar dai ki ce dani aure kika yi a kan aure Lailah?”
Magana take cikin sanyi, da zuciya irin ta UWA, sannan ta kakkafe ta da idanu. Lailah na girgiza
kai tana cewa.
“Lala-lala Ummi......”
A hankali ta soma zayyana mata komai. Ta kare da cewa.
“Kwanaki uku kacal ya bani in bishi mu koma a bar maganar, ko in kai shi kotu in kwaci takardar
saki.
Duk yadda na so in nusar da shi rashin ingancin aurenmu ya ki sauraro na. Har yana zargina da
yiwa kaninshi sharri. Ummi ina cikin wani hali na kuncin zuciya da rashin yarda da kaina......
Me zan yi Ubangijina ya yafe mani ya kawo mani maslaha cikin rayuwa ta? WASAN KANIN MIJI
bai kare ni da komai ba sai jefa ni a halaka da wanzar dani cikin bakin ciki da nadama....”
Ta ci gaba da kuka a kan cinyoyin mahaifiyarta.
Momi ta rasa abin cewa, sai LA’ILAHA ILLALLAHU….. Allah ya kawo mu wani zamani
gurvatacce..... zina ta zama ba komai ba, daga wajen marasa auren da masu auren ma.
Ba ta tava jin irin wannan kwamacalar a cikin aure ba, sai dai al’amarin da ya riga ya faru ba
abin da za a iya yi a kai sai dai ayi kokarin gyarawa, don a guji gaba.
Ta dago fuskar Lailah daga cikin cinyoyinta ta ce.
“Kema kina da laifi Lailah, me ya sa a lokacin da ya bijiro miki da bukatarsa baki yi wani kokari
na kare kanki ba?
Me ya sa kika zavi yin nisa damu fiye da ki gaya mana a yiwa tufkar hanci? Ayi abin da ya dace
tun a lokacin?
Laifuffukan ki suna da yawa Lailah. Kin tafi zuwa wata duniya ba tare da yardar mijin da ke
auren ki ba, kin kulla alaka da wani da namiji da ba muharramin ki ba. Me zai hana soyayya ba
za ta gitta a tsakani ba? Da aurenki Lailah?”
Lailah dai ba baki sai kuka. Ta yarda ita ma da laifinta. Ta kama hannun Momin ta rike cikin
nata.
Cikin rishin kuka ta ce,
“Na yarda nima ina da laifi Momi.....sai dai na tuba, na dade ina tuba ga Ubangijina.....tuba irin
wanda Ubangiji ya yi alkawarin karbar sa.... wato tuban da aka tabbatar ba za a sake komawa
izuwa zunubin ba”.
Sai Momi ta rungume ta,
“To yanzu me kike so