Showing 54001 words to 56966 words out of 56966 words

Chapter 19 - WASAN KANIN MIJI BOOK COMPLETE BY TAKORI.pdf

ta gushewa. A haka yana ji yana gani ya baro Lailar
da a da mallakinsa ce.
Ba ta koma Saudiyya ba sai da Sujood ta fito daga ‘bed-rest’. Har da ita aka yi mata rakiya ta
tashi ranar Asabar.
Ta tarar da abokiyar zamanta a dakin (Dhuha) ta riga ta dawowa. Ta gyare masu dakin tsab.
Balarabiyar Afghanistan ce.
Suka ci gaba da karatu, wanda duk rabi bincike ne cikin manyan littattafai wato (research).

Tana tsaye gaban book-shelf na main library din Ummul-Kura, tana kokarin zaro wani littafi.
Dai-dai lokacin da agogon library din ya buga karfe goma sha daya na rana, ya yi dai-dai da
bugawar zuciyarta da faduwar gabanta. Dai-dai lokacin ta hango wani ‘giant’ yana tahowa cikin
fararen kaya, iska na kada shi, yana tafe yana waya, ba ta san lokacin da littafin ya suvuce, ya
fadi daga hannun ta ba.
Ba ta yi wani motsi ba har ya karaso . Ya russuna ya dauko mata littafin ya mika mata, sannan
ya kama hannunta suka fito daga library din. Ta zamo kamar mutum-mutumi, sai janta yake
tana binshi ba uhm-ba-umh-uhm.
A al’adarta tunda ta zo Ummul-Kurah, kullum sai ta kai ziyara shabbaki, kamar ya san hakan,
don kuwa da ya tare tasi shabbaki ya ce ya kai su.
Kasancewar masallacin maza daban da na mata, a nan harabar masallaci ya sata ta yi
addu’o’inta, shi ma ya yi. Suka fito ashe tuni ya yi masu ‘booking’ din mota wadda za ta kai su
har cikin Mecca.
A cikin mota Lailah ke bin shi da idanu, yadda ya damke hannunta kamar wata matarshi. Abbas
dinta.....abokin kan hanya!
Ya kara kyau na misali, ya kara murjewa. Ta yadda har ba ta gajiya da kallon kyakkyawar
fuskarsa.
Ta sunkuyar da kai cikin siririn sauti ta ce, “Amma ka san hannun nan da kake ta rikewa,
haramun ne ko?”
Ba ta kai ga rufe bakinta ba sai ya sa dukkan hannuwa ya rungume ta.

Lailah ta samu numfashinta yana sassarfa a cikin kirjin Abbas da kafadun shi. Ta yi ta kici-kicin
ta kwace amma ta kasa. Ta kuwa daga hannu ta kai mishi wani wawan mari ya goce, hucin
marin ya wuce ta gefen kunnuwansa. Ta fashe da kuka ta ce,
“Saboda na baka labarina shine ka dauke ni ‘yar iska ko?
To bari ka ji, ko na fi iblis iskanci ba zan yi a cikin garin da manzon mu ke kwance ba. Kai
malam tsaya da motar nan in sauka.....”

Ya yi dariya sosai, sannan ya sake ta. Ya nuna mata agogon RADO dake daure cikin
kwantacciyar sumar hannun shi.
“Karfe sha daya na rana wanda ya yi dai-dai da karfe biyar na yamma agogon mu na gida
Najeriya.
Baffanninki Malam Ado da Malam Ilyasu da waliyyinki Isma’il suka damka mani igiyar rayuwarki,
suka shaida na zama mijinki har zuwa karshen numfashinmu”.
Sai jikinta ya yi sanyi, ta rasa abin cewa, kuka za ta yi ko dariya? Bakin ciki za ta yi ko ko farin
ciki? Bata sani ba.
Ya sake runtse hannunshi cikin nata sosai ya soma ba ta labarin yadda al’amarin ya faru. Ta
tabbatar karfe sha daya na rana ta ji faduwar gaba da bugawar zuciya, ashe igiyoyin Abbas ne
suka hau kanta.
Ya ce,
“Na je Egypt watanni biyu da suka wuce in gai da Momi da Isma’il. Yake gaya mani cewa kina
nan Madina. Na tambaye shi Umrah kika je? Ya ce, a’a, karo karatu ne, don aiki kike yi. Ya ce
kun rabu da mijinki tun wancan karon. Ban yi kauron baki ba ko A BARI YA HUCE.... na ce da
Isma’il ya yi mani alfarma, ya aura min ke. Ban san ya suka yi da Momi ba, ta ce, in ba ta lokaci za ta yi nazari tana so ta ji daga bakin ki.
Sanda na sake komawa ta ce ta gama nazarinta in turo wakilaina wajen Baffanin ki a Kano su
za su sake daura miki aure.
Don haka Isma’il ya taho Najeriya muka hadu, muka je Kabara aka daura auren, sadakinki yana
hannun Isma’il
Ba yadda bai yi dani ba in bari za ki zo karshen watannan ban saurare shi ba, dole ya bani
adireshin inda zan same ki wato jami’ar Ummul-Kura.
Ban sha wuya ba aka binciko min lambar dakin ki. Na tura a kira ki sai abokiyar zaman ki ta ce
kina nan. To kin ji.
Nima ba dan iska bane. Da kuma dan iskan ne da ba yau zan fara ba......” Ya karasa da dariyar
da ta cunkushe masa ciki.
Ita dai Lailah binshi take da ido, mamaki ya hanata magana. Hakika tana cikin mutane masu
sa’ar samun duk abin da suke so a rayuwa. Da da hali da itama ta rungume shi ta yi kukan
godiya ga Allah a kan kirjinsa.
Sai yamma lis suka shigo cikin Mecca, ko abinci basu nema ba sai da suka fara yin (Dawafi)
suka yi sallar magariba da isha da nafiloli. Sannan suka je wani ‘restaurant’ suka ci abinci, daga
nan suka taho Ka’aba suka ci gaba da gabatar da ibadodinsu.
Sai asuba suka koma masauki, wanka kawai suka yi ya shige ciki ya kwanta yana biyan bashin
barcin da bai samu ya yi ba saboda godiya ga Allah da ya mallaka mishi abin da yake so, bai
kuma tava tsammanin samu ba, ya samu a bayan fidda rai.
Ita dai Lailah ko gezau, tana zaune dungurgur a kan kujera tana kallon talabijin din da ke ta aiki
ita kadai ba ta san me suke yi ba.
Kamar ka ce kyat.....! Ta arta a na kare. Don ita kwata-kwata yanzu kowanne namiji ma tsoron
shi take ji balle ya kai hannu ya tava ta.
Bai tashi ba sai karfe goma na safe, shi ma din kiran Isma’il ne ya tashe shi, suna gaisawa ya
mikawa Laila.
Bayan sun gaisa yake mata bayanin da Abbas ya yi mata, ta ce a sanyaye,

“Toh!”
Momi na karva sai ta valle da kukan kaunar da take mata. Tana so ma ta yi mata godiya amma
ta kasa.
Momi ta ce,
“To kukan na mene ne?
Ke fa da bakin ki kika gaya mani kina son Abbas?”
Ta share hawaye tana murmushi ba ta ce komai ba. Ta ce, “A’a, in kin daina son nashi ne ki
gaya mani sai in ba shi hakuri ya karvi sadakin shi, tun da dama bai zo hannun ki ba.”
Ta yi saurin cewa, “A’a Momi”.
Ta yi dariya ta ce, “To shi kenan, a sha amarci lafiya, ki kula da shan ‘fresh milk’ da cin dabino
da shan zam-zam tare da inibi”.
Kunya ta kama ta, don ta san sune abubuwan da take ba ta sanda za ta yi auren fari.
Abbas ya fito daga shi sai ‘short – nicker’ kanshi da tawul yana goge ruwan cikin sumar kanshi.
Kallo daya ta yi mishi ba ta kara ba ta kara takurewa a cikin kujera. Ya juya mata baya yana
dariya ya zuba farar jallabiya mai santsi, ya fesa turaren shi (one-man-show), ya fesa turaren
baki (mouth fresh), sannan ya iso gare ta.
Ya zauna a gefenta yana so ya ja ta jikinshi amma ya lura da yadda ta ke a tsorace da shi. Sai
ya yi murmushi ya mike zuwa hammam (bayan gida) ya hada mata ruwan dumi cikin kwami, ya
ce ta yi wanka ta ji dadin jikinta su fita su nemi abin karyawa.
Ba don ta so ba ta mike ta shiga wankan, amma fa ta kukkulle kofar bandakin da (jam-lock)
sannan ta fara wankan, shi kuma ya sauka kasa ya samo musu abin karin kumallo.

****
Kwanansu uku suna Umrah, amma ya kasa gane kan hutsuwar amaryar tashi. Ba ta umh ba ta
umh-umh, duk ta takura kanta. Maganar duniyar nan idan zai yi sai dai ta bishi da ‘eh’ ko ‘a’ah’.
Har yana mamaki kamar ba Lailan shi ba.
Ya kuma soma tunanin ko dai ba ta son auren ne. Ta hana mashi amarcin har zuwa ranar da za
su rabu, dama shi a kan hanya yake zai wuce London.
A daren ranar dai ya rantse yau sai ya gane abin da Lailah take nufi da shi, ba ta son shi ne ko
iya shege ne? Ita ba yarinya ba balle a yi mata uzrin kuruciya.
Tana zaune cikin kujerar falon hotel din da suka sauka, hannunta remote ne tana canza channel
ya kwankwasa kofar.
Ta tashi ta bude idanunshi cikin nata aka jefe shi da wani miskilin murmushi. Turata cikin dakin
ya yi da kafadunshi ya aje ledojin dake hannun shi. Sannan ya juya ya karvo na hannun yaron
hotel din da ke waje ya aje gefe ya rufe kofar.
Ba ta yi aune ba sai ji ta yi ya sunkuce ta ya yi sama da ita. Bai dire ta ko’ina ba sai cikin
kwamin wanka, duk da kayan da ke jikinta.
Ta ce, “Haba Abbas, ya za ka jikani? Yanzu na yi wanka fa”.
Bai saurare ta ba ya saukaka kayan jikinta ya manne bakinta da nashi da wasu irin matsiyatan
‘kisses’ da ba ta tava sanin akwai irinsu a duniyarta ba.
Ya saki ‘shower’ a kansu, cikin wani sabon al’amari da Lailah ba ta tava tsintar kanta a
kwatankwacin sa ba.
Ashe dai wannan ita ce soyayyar, na baya duk shirme ne? Wane Sa’idu wane Yayansa!?

Wadanan MANYAN MAZA ke magana…., wadanda basa furta SO ko I luv u a fatar baki, sai dai
ZUCIYA da GANGAR jikinsu ya nuna.
Fatan alkhairi gare ku ABBAS DA LAILAH! -Takori

Washegari ta kama Lahadi, Abbas kam yau sallar asuba a gida aka yi ta, Lailah ta samu kanta
da kasa hada ido da angon nata. Shi kuma hakan bai hana shi gudanar da amarcin shi ba,
soyayya ruwan zuma gangariya ake gunadarwa cikin kwanaki biyun da suka biyo baya.
Ya kasa amincewa wai ya tafi ya bar Lailah, har na tsayin watanni uku. Ga ayyuka ya bari masu
dimbin yawa. Ita kanta Lailar ta baro nata ayyukan a makaranta don haka ta karfafe shi da su
daure su tafi, lokaci kankani ya rage mata ta kammala gaba daya sai su tsara mai yiwuwa.
Sai da ya kaita har Madinah tamkar ba za su rabu ba, hakan dai aka daddaure aka ciccije aka
rabun da alkawarirrika masu yawa da ma’ana.
Ya biyo Ajrah (tasi) ya dawo Jiddah, karfe goma na daren ranar ya bi British-Air zuwa London.

Tana canza kaya a dakin su Dhuha ta yi sallama ta shigo, kallon mamaki ta yi mata tare da
tsoro, ta ce cikin harshen Larabci.
“Ke kuwa ina kika shiga Lailah har tsayin kwana biyar? Yanzu haka daga kai ‘report’ din vatanki
nake ga ‘security’ din makaranta. Hankalina ya tashi sosai”.
Lailah ta yi dariya ta ce, “Kai Dhuha? Ana yankan kai ne a Saudi-Arabia?”
Ta ce, “Ina na sani, tun da na ga wani ya zo neman ki kuma tun daga ranar ne ban kara ganin ki
ba, ba dole in yi zaton ya sace ki ba?”
Lailah ta kara yin dariya ta ce, “Sai ki koma ki gaya musu gani na dawo”. Ta juya tana cewa,
“Yanzu kuwa”.
Lailah ta kwanta a gadonta ta lumshe lumsassun idanunta tana tariyo rayuwarta filla-filla tun
daga kuruciya har girma.
Ta tuno Mohammed da rayuwar ta dashi, ta tuno Sa’idu. Sai ta samu kanta da yi musu addu’a.
Ta kuma gode Allah da ya musanya mata da miji na gari dai-dai yadda take buri a rayuwarta ta
duniya.

****
Bayan shudewar watanni uku suka samu hutu ta koma gida Egypt, ta tarar da haihuwar Sujood,
ta haifi kyakkyawar yarinya mai kama da Momi Najla. Wannan ne ya sa take yanayi da ita
Lailan, don duk cikinsu ta fi su kama da Momi. Duk yadda ta so ayi shagalin suna da ita hakan
ya faskara, sakamakon rashin isasshiyar lafiya, komai ta ci sai ya dawo ba ta ko son ganin
abinci ko kamshin sa.
Daga rowan lipton din ‘Tetley Tea’ sai gugguru, su kadai ne in ta ci ko ta sha ba ta amansu. A
matsayin Sujood na cikakkiyar likita, a take ta gane abin da ke damun Antin tata, ciki ne na
watanni biyu ko Momi ba ta gane ba.
Sujood ta rubuta magungunan da za su taimaka mata aman ya tsaya ta ba wa Isma’il ya siyo
mata ba tare da ya san na wace ce a cikin su ba, tun da ba ranar ta fara aiken shi siyan magani
ba.
Baby ta ci sunan Momi wato NAJLA, suke kiran ta Nawal. Sujood ta dage da kula da Lailah don
duk hidimar Nawal Momi da su Najat ke yi, tsakanin ta da ita sai shan nono wanda sai ta wuni

ba ta sha ba, saboda Momi tana ba ta madara.
Suna wajen motsa jiki Sujood ta dakata ta dubi Lailah ta ce,
“Antinmu ni fa kallon mai ciki nake miki, ki daina edcercise dinnan”.
Lailah ta jinjina kai ta ce,
“Nima na dade da zargin kaina, don watanni uku kenan rabona da al’adata.....”
Hawaye suka zubo mata na tunawa cewa; wannan dan HALAAL ne a jikinta, wanda kowa zai
karva.
***
A yammacin ranar Abbas ya iso. Washegari suka wuce London. Ga mamakin Lailah Abbas ya
tashi daga gidan hayarsu, gida guda Muslim College ta ba shi a cikin gidajen malamai. Aka
koma rainon ciki, tattali da kulawa wurin Abbas wane na baya, wanda ake da shamaki a cikinsa.
Watan ta guda ta koma Ummul-Kura. Ta karasa rubutunta na (project) ta mika, ta amshi kwalin
Dr. of Philosophy (PhD). Suka tattara suka koma Ingila.
Haka rayuwarsu ke garawa cikin nasara da ci gaba kala-kala. A NHS Lailah ta haifi ‘bouncing
baby’ dinta mai kama da ubansa har duhun kalar.
Abbas ya ba shi sunan Isma’il, a cewar shi shine ya shige masa gaba ya ba shi Lailah a lokacin
da ya riga ya fidda rai.

ABBAS da LAILAH, sun zamo manyan-manyan malaman Falsafa a kasar England, a babbar
Jami’ar Musulunci (Muslim College) da ke birnin London.
Akai-akai kuma suna zuwa gida Najeriya gai da Baffaninsu, da yi musu hidima iyakar karfin
aljihunsu. Balle Egypt kuma da ba sa yin watanni uku kwarara ba su zo ba.

MURFI
A'study’ ya same ta tana shirya litattafanta cikin kabinet, a gefe Isma’il ne (Sayyid) da Khalisa
(Sayyidah) tare da autarsu Najwa suna wasansu cikin na’urar koyon karatu mai Alifun-Ba’aun.
Ya yin da babban yaya wato Sayyid ke gefe yana ta rubuce-rubucen sa, dukkansu basu ankara
da shigowar Daddyn ba, kasancewar kowannen su ya mai da kai ga abin da yake yi ko sallamar
shi basu ji ba.
Ya karasa ga Momin ta bayanta ya rungume ta, kamshin turaren shi kawai ta shaka ta lumshe
idonta tana murmushi.
Ya dora habarshi a kafadunta ya ce, “Momy fatawah nake nema”.
Ta ce, “A kan me Daddy?”
Ya ce, “A kan karin aure?”
Ta zumvura baki ta zame shi daga kafadunta ta ci gaba da shirya littattafanta tana cewa,
“Bani da sani a kan wannan sam!”.
Ya juyo ta ya ga yadda ta yi kicin-kicin da fuska sai ta ba shi dariya, ya ce, “At thirty five Momi
kin girma fa, ki barni in dauki sweet sidteen, ta zo daga Muzambikue yin Diploma, shine nake
neman fatawa a kai.
Shin wanda Allah ya yi wa baiwa da mace mai ilimi, kyautatawa, biyayya, tausayi da jin kai ga
mijinta, tare da kular masa da tarbiyyar ‘ya’yansa da gamsuwar sa a shimfidar su, ta tsare masa
mutunci da dukiya idan baya nan, ta zamo mai himma da kokari ga son faranta masa rai, ta
cancanci ayi mata kishiya?”

Abin ma ita sai ya ba ta dariya, ba ta san sanda ta ce,
“Idan mijin butulallen Allah ne, ba sai ya yi mata ba?”
Ya jinjina cikin dariya ya ce,
“Kada fa ki manta, Ubangiji (S.W.T) cewa ya yi, “Ku auri abin da ya yi muku dadi daga
daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hur-hudu.....”
Ta zame cikin sanyin murya ta ce,
“Don Allah Abbas ka auri goma-goma.....” Sai hawaye suka zubo.
Ya kai hannu ya shafo hawayen yana murmushi ya ce,
“Ni din me Lailah? Da za ki zub da hawaye a dalilina? Idan kin ga na hada rayuwa da wata, to
sai a Aljannah, idan Allah ya yi min kyautar Hurul-eeni, sai in hada da ke ta zama
kwarkwara........wannan alkawari ne Lailah. You are more than enough to me......and I’m only
yours!” Ya kara rungume ta. Ta yi murmushi wanda ya fito tun daga karkashin zuciyarta, kaunar mijinta ta kara kwanciya
cikin ranta kamar ta hadiye shi don so da kauna. Sai itama ta rungumeshi sosai. Sannan ta yi
mishi nuni da Sayyid wanda ya aje rubutunshi ya zubo musu ido.
Ya sake ta ya koma gabansa ya zauna, ya kama hannun shi kafin ya yi magana yaron ya riga
shi.
“Me ta yi maka ka sa ta kuka?”
Suka kyalkyale da dariya shi da Lailah. Ya dora hannun daman shi a kan yaron ya ce.
“Ban yi mata komai ba, tsokanarta na yi na ce zan kawo muku Aunty, shine take kuka”.
Ya ce,
“To Daddy ai mu muna son Auntyn”.
Ya ce,
“Ban isa ba Sayyid in yi abin da Momi ba ta so, ko ina so kuwa, balle ma wasa nake. Ba na son
kowa sai Momi.....ni mijin ta-ce ne, ku kawai nake so..... I luv you all......” Ya hada su ya
rungume gaba daya.


MASHA ALLAH LAKUWWATA ILLAH BILLAH!

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login