Showing 27001 words to 30000 words out of 34489 words

Chapter 10 - AMINIYA KO KISHIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.doc

19 Nov 2025

132

rayuwa tare ki zo mu zauna tare kema Allah zai baki haihuwar nan ni nama bar miki wadannan din halak malak Amina wlh nafi buqatar ki fiye dasu wlh nabar miki su ni har Dr din bana buqata kizo kuci gaba da rayuwarku ga yaya nan kun samu dama nice bare a cikinku kuma zan fita daga cikinku Amina bana fatan zama sanadin hawayen ki pls ki yarda dani"....


_


Pls Share
and Vote





*UMMUH HAIRAN CE* ...
' [2/16, 09:09] Umm Hairan: https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*



* { _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




=?m? *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* =?m?




?#1? 8?




WRITTEN
AND
STORY



*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
? *FAUZAH*


*Wattpad* =?I?


*TRUE LIFE STORY*



*SHORT STORY*








Juyawa yayi zai fita yace  kiyi qoqarin komawa mkrnta cikin satinnan ranar da zaki koma ki kirani koda yake zan kawo miki motarki tunda ni ban isa ki kirani ki sanar dani kun koma skul ba Fauzah bazan takura miki ki dawo gdana ba amma kisani kina shiga haqqi na kuma kina cutar dani


Yana kaiwa nan yayi ficewarsa ta dade a tsaye sororo batare datasan dalilin tsayawar tata ba daqyar ta iya jan qafarta ta fita daga parlourn zuwa dakinta Ummah ta gani zaune tana feeding din Suheil guri ta samu ta zauna ta hada kai da gwuiwa zuciyarta nayi mata zafi Ummah ce ta kalleta tace  anya Fauzah bazakiyiwa kanki fada ba ki koma gdan mijinki yaronnan fah yayi kara kar haqqinsa ya tambayeki Fauzah kada kiyi amfani da son da Jameel yakeyi miki ki rinqa cutar dashi shi aure raine dashi idan Allah bai kashe shi ba babu wanda ya isa ya kasheshi 


Komawa tayi ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya ganin da Ummah tayi bazata magantu ba yasata miqewa ta fice daga dakin bayan ta kwantar da yaran, kwana biyu tsakani ta koma mkrnta kowa yayi mamakin ganinta da twins din saboda babu wanda yayi tunanin tayi aure sai Zainab da ta kira ta sanar da ita kawai yaran masha Allah kowa son daukansu yakeyi lecture ta fara daukan zafi Saheeb da yake rigimamme ya farayi mata kuka saboda haka baa tashi da ita ba tun daga ranar bata qara zuwa skull dasu ba.



Ranar wata asabar ta fita da wuri mkrnta qarfe biyu suka tashi sun fito ita da Zainab kasancewar batazo da mota ba suna takawa horn akayi musu ta baya kaucewa sukayi batare da daya cikinsu ta juya ba sake danna horn din akayi dole suka juya nandanan annurin fuskarta suka bace ganinsan da tayi Zainab ce ta tabota tace kije mijinki yazo daukanki fa Fauzah jikinta a salube ta nufi motar ya bude mata ta shiga yaja suka tafi daqyar ta gaisheshi shiru yayi mata batare daya amsa ba itama bata qara yimasa mgn ba tafiya sosai sukayi kanta yana qasa tana game da wayarta ji tayi an bude get da sauri ta dago daidai lkcn da yake bude mata murfin motar yace.


 Bismillah fito kallonsa tayi tace  ina zamu hade fuskarsa yayi yace  au kiyi hqr na manta fah ban sanar dake ba saidaki zanyi yanda yayi mgn a gadarance yasata shan jinin jikinta ta fito daga motar, kullewa yayi ya yayi gaba tabi bayansa bude qofar yayi ya shiga yace mata  bismillah shigo mana kike rakubewa gabanta na faduwa ta shiga parlourn mayar da qofar yayi ya rufe tare da danna mata key ya wata qofa ya bude ya shiga bin parlourn tayi da kalloh sosai ya hadu iyakar haduwa girmansa yafi komai burgeta bataji fitowarsa ba sai jinsa tayi a bayan ta ya rungumeta rintse idanunta tayi lkcn da yake yawo da hanunsa a jikinta rawa jikinta ya shigayi abinda yafi komai bashi mamaki kenan zagayowa yayi gabanta ya hade bakinsu guri guda har yanzu idanunta a rufe yake tana tsaye ya zare mata hijab din jikinta yana qoqarin dagota ta janye tayi baya tana girgiza masa kai murmushi yayi yace  meye hakan Fauzah karki yi qoqarin hanani haqqina wlh zan iya rasa rayuwata idan kikaqi biyamin buqatata a yau ina cikin matsala Fauzah komai zai iya faruwa dani... cafkota yayi yana qoqarin hadata da jikinsa kuka ta saki tace  karkayimin haka dan Allah wlh banaso Dr wlh banaso ka taimakeni.... hade ta yayi da jikinsa ya dagata cak ya nufi wani daki da ita ya kwantarta yana qoqarin rabata da ilahirin abinda yake jikinta turjewa takeyi tana tureshi tana kuka amma kamar baima sani ba ranar dai babu yanda Fauzah ta iya saida me afkuwa ta afku.


Sai bayan laasar yayi wanka ya shirya tana kuka ta tashi tayi wanka mamaki sosai ya bata ganin ya bude wadroop ya fito mata da kayanta ya feshesu da turare da kansa ya dauka yaje zaisa mata taqi yarda murmushi yayi ya miqa mata taqi sawa ta mayar dana jikinta kiss dinta yayi ya kamota yace  muje na kaiki gda amma wlh bazan lamunci hanani haqqina ba Fauzah kawai kiyita boyemin abuna ya tsumu yana buqatar mahadi nifa zaman naki a gdanma banga amfaninsa ba amma bazan hanaki ba duk sanda kika gaji kya dawo ga gdanki nan yana jiranki


Juyawa tayi ta fice shima ya fito suka shiga motar yaja suka fita daga gdan saida ya biya yayi mata siyayya sannan ya kaita gdan bata tsayaba tayi shigewarta gdan ta fada katifarta ta fashe da kuka Dr Jameel ya cuceta a cewarta.


Yaran sunata wasansu a kekunan su da suke koyon zama bata ko kallesu ba taci gaba da kukanta shigowa yayi ya gaida Ummah kudi ya zara yabata masu yawa yace taci gaba da kula da kanta amma qememe taqi karba zube mata yayi ya tafiyarsa da yaransa basu dawo gdanba sai bayan insha kasancewar gdan Hajiyansa ya kaisu.


Tun daga wannan ranar bata sake yarda wani abu ya shiga tsakaninsu ba al-amura suka fara canzawa Fauzah zazzabi da tashin zuciya da amai ga wata dashewa da tayi daqyar take iya zuwa mkrnta Ummah ta lura da canjin da Fauzah ta samu batayi mata mgn ba wata biyar yaran suna rarrafensu ko ina lamarin ya fara bawa Dr tsoro musamman yanzu da Fauzah ta rasa lfy kullum tana kwance kamar ruwa.


Yau a gdan ya wuni saboda rashin lfyr da takeyi hankalinsa ya tashi sosai ba arziqi ta shirya suka tafi asibiti suna zuwa yasa mata ruwa gwaje-gwaje yayi mata ciki wata biyu farin ciki gurin Dr baa cewa komai sai dare sosai suka bar asibitin mamakin fara'arsa tayau takeyi saida suka kusa gda sannan ya katse shirun da cewa  kinga ikon Allah ko my Angel yabani yaya biyu lkc daya wata uku tsakani yakuma bamu wani banda Allah waye ya isa yayi maka wannan dunqulalliyar kyautar lkc daya ni dama nasan soyayyar da nakeyi miki bazata tashi a banza ba


Tunda ya fara mgnr ta zuba masa ido cikin alamun rikicewa da tashin hankali tace  nashiga uku Dr ciki fa kace ya akayi na samu ciki Dr wanne irin ciki yaushe ma na haihu da har zanyi wani cikin? yanda take mgnr ne ya bashi mamaki ajiyar numfashi yayi yace  ikon Allah kenan Fauzah Allah ne yakeson nuna miki ikonsa shiyasa kika samu ciki Fauzah ina alfahari da cikin nan na jikinki kuma ina alfahari da kasancewar zuri'a ta ta tsatsonki inason cikin nan Fauzah


Harara ta zabga masa tace  ina wlh bazai yuwuba Dr ban shirya sake zama dakai ba balle haihuwa wadancan ma tsautsayi ne da qaddara yasa na haifesu amma bana buqatar wannan cikin ba kuma na sonsa saboda haka kasan yanda zakayi dashi


Yanayin parking ta balle murfin motar ta fice binta yayi da kallo yana mamakin irin qiyayyar da Fauzah takeyi masa da har take iqirarin batason hada zuri'a dashi, cikin muguwar mutuwar jiki ya fito daga motar ya nufin cikin gdan Ummah ya tarar a tsakar gda tararsa tayi tace  meyake faruwa Jameel naga Fauzah ta shigo cikin tashin hankali na tambayeta taqi mgn shafa kansa yayi yace  am Ummah ba wani abu bane kawai dan ance tanada ciki shine take kukannan jinjina kai Ummah tayi abin yafi qarfinta saboda haka ta ja jikinta ta koma dakinta lallai ta yarda yayan zamani sai abarsu basusan kunya ba ita dama tasan komai zai iya faruwa.


Shiga yayi ya zauna kusa da ita ya dagota yace  kiyi hqr Fauzah nifa bansan laifin da nayi miki ba amma dan Allah kiyi hqr ki yarda mu koma gdanmu mu raini yaranmu cikin aminci pls  Dr meyasa zakayimin haka dama kasan ciki zakayimin ranar meyasa kasan kanason haihuwa ka kasa yima matarka cikin ta haifa maka saini Dr banaso wlh ban shirya haihuwa ba yanzu ka taimakeni ka zubarmin da cikin nan


Da sauri ya rufe mata baki yace  wlh bazan iya zubar da cikin nan ba Fauzah shekarata nawa ina neman haihuwa Allah bai bani ba sai yanzu ina bazai yuwu ba ki nemi ko menene a gurina amma banda wannan miqewa yayi ya fice daga dakin Suheil da Saheeb ya dauka ya sakasu a mota ya nufi gdan Hajiyan sa tayi farin cikin ganin jikokin nata wasa ta shiga yi musu sunata babbaka dariya dagowa tayi zatayi masa mgn ga mamakin ta taga ya hadakai da qwuiwa tasan damuwarsa bazata shige ta iyalinsa ba maida hankalinsa tayi wajensa tace.


 Jamaluddeen meye yake damunka ne? dagowa yayi fuskarsa da hawaye ya matso gabanta ya kamo hanunta yace  hajiya ki taimakeni kije ki dawo min da Fauzah Hajiya ina buqatarta hqr na ya qare don Allah karta zubar min da cikina wlh inason cikina dubanshi tayi tace  me kakeso kacemin Jameel ciki ne da Fauzah yanzun ma?


Kada kai yayi yace  hakane Hajiya cikine da ita yanzu daga asibiti muke amma tace saita zubar dashi Hajiya Fauzah bata Sona bansan meyasa ba ki taimakeni Hajiya pls... ajiyar zuciya tayi tace  to Jameel ya kakeso nayi dakai nace ka dawo da matarka kaqi kuma nasan matsalar ka kenan kada kai yayi yace  nifa kubar wannan zancan Hajiya kawai dai Fauzah nake buqata yanzu karta salwantar min da cikina ganin da gaske ya rikice mata yasata amsa masa da  to naji tashi kaje anjima zanje nayi mgn da ita dole badan yaso ba ya miqe ya fice yabar mata yaran.



_

Pls Share





*UMMUH HAIRAN CE* ...
' [2/16, 09:09] Umm Hairan: https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*



* { _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




=?m? *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* =?m?




?#1? 9?




WRITTEN
AND
STORY



*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
? *FAUZAH*


*Wattpad* =?I?


*TRUE LIFE STORY*



*SHORT STORY*




Tunda ya fita ya barta take aikin kukan daqyar ta miqe tayi sallah tana hawaye take kaiwa Allah kukanta Ummah ce ta shigo tace  idan kin idar kinada baqi a parlour kuma babanki ma yananan yanason ganin ki


Miqewa tayi ta nufi parlourn jiki a salube gabanta ne ya fadi ganin Hajiya zaune da aunty Ummah yayar Dr binta sukayi da kallo ko tambaya babu daka ganta kaga me qaramin ciki qarasawa tayi ta zauna a dan kunyace ta gaidasu amsawa sukayi sunayi mata sannu da jiki aunty Ummah ce ta katse shirun da cewa  Fauzah mijinki ne ya tasomu yace muzo mu baki hqr ki koma ki raini cikinki a gdanki cikin kulawar mamallakinsa...


Baba ne ya shigo yace  ummah daina bata hqr wlh koda ace baku zoba yau nayi niyyar mayar da Fauzahtuljannah gdanta saboda shine rufin asirinta da yayanta saboda haka ki tashi maza ki shirya kibi surukarki kuka tasaki tace  don Allah Baba karkayimin haka kayi hqr wlh banason sake zama da Dr Jameel ka barni na rayu anan tare daku yafi min kwanciyar hankali...


Doka mata tsawa Baba yayi yace  ashe baki da hankali Fauzah bansani ba yanzu yazakiyi da rabonnan dake jikinki yazakiyi da rabon da bakisan adadinsa ba tsakaninku dashi ina zakikai zunubi da haqqin mijinki dake kanki kike danne masa Jameel yayi qoqari kuma yayi kara saboda haka wlh bazaki mayar dani qaramin mutum a gurinsa ba naji komai kuma nasan komai nasan tujarar da kikayi masa saboda ance kinada ciki to wlh kinji na rantse ki kiyayi fushina Fauzah ki miqe kibi iyayen mijinki iyakar abinda zan fada miki kenan idan kuma kinason nunamin kinyi karatun boko ban isa dake ba to bismillah 


Tashi tayi ta fita daga dakin ta fada dakinta ta fara hana kayanta cikin kuka Dr Jameel shine musabbabin kowacce matsala tata shine silar komai na damuwarta meyasa qaddararta ta hadata dashi?


Tambayar da taketa yiwa kanta kenan Ummah ce ta shigo dakin ta tayata hada kayan tana tausayawa yar tata halin da take ciki na damuwa tasan babban tashin hankalinta shine zamowarta dalilin mutuwar auren aminiyarta kishiyarta Amina ita dama tun farko bataso auranba to amma yazatayi da wannan rabo me gaggawa.


Saida suka gama hada kayan tsaf sannan yar uwarta Amina ta shigo gdan zaunar da ita Ummah tayi tayi mata nasihohi sosai tare da misalai akan rayuwar aure dagowa tayi tace  yanzu Ummah shikenan nazama sanadin rabuwar Dr Jameel da Amina Ummah ta yaya zan daina jin haushin kaina da Dr har na yarda muyi rayuwa dashi kamar kowanne ma'aurata Ummah wlh banason rayuwa dashi kwata-kwata saboda shi cikine me manta kyautar jiya kuma butul...." toshe mata baki tayi tace  duk naji Fauzah amma ya zakiyi mijinki ne uban yayanki saboda haka ke hqr ya kama tunda kece uwar yayansa balle ma ke da Allah ya taimakeki yana sonki Fauzah ki kwantar da hankalinki ki zauna da mijinki da zuciya daya ki daina azabtar dashi akan kinga yana sonki haka tacigaba dayi mata nasiha har lkc yaja ganin dare ya farayi yasa ta tursasata tashi ta canza kayanta suka tafi har lkcn kuka takeyi.


Aunty Ummah ke jan motar sai aunty Hadiza a kusa da ita baya kuma ita da Hajiya ne sai Suheil da Saheeb a hanun Hajiyan tanata yi musu wasa suna zuwa me gadi ya bude musu suka shiga bata manta gdanba shine gdan da ya kawota yayi mata cikin dake jikinta yanzu.



Saida suka gyara mata ko ina duk da dama komai a gyare yake kasancewar Dr akwai tsafta sannan sukayi mata sallama suna shirin tafiya ya shigo fuskarsa dauke da fara'ar da take nuna farin cikin sa yace  ah ya naga har kun miqe Hajiya badai tafiya zakuyi ba? aunty Ummah ce ta cafe da cewa  to me zamu zauna muyi maka kuma tunda mun dawo maka da matarka da yayanka ai mun gama aikinmu sai mu kauce muma shafa sumarsa yayi yace  shikenan na gode sai nashigo saida ya rakasu suka shiga mota shikuma ya dauki aunty Hadiza ya kaita da tarin abin arziqinsa sannan ya juyo gdan zuciyarsa cike da matsanancin farin ciki Fauzan sa ta dawo gareshi saida ya biya yayo musu take away sannan ya nufi gdan lkcn qarfe tara saura na dare, Baba mairo tazo tana dakin daya ware mata a qasa shigowa yayi tare da sallama babu kowa a parlour sai baba mairon ita da twins din gaisawa sukayi ya haye saman a dakinta ya sameta ta fito daga wanka daure da towel iyakar cinyarta ta baza gashinta tana busar dashi da handdryer

Wani qamshi ya shaqa mai rikita qwalwa nandanan yaji wani abu na yawo a cikin jininsa zagayawa yayi ta bayanta ya ajiye kayan dake hanunsa ya rungumota ta baya yana sauke wasu tagwayen ajiyar zuciya wasu hawaye ne suka zubo masa ya dora kansa a kafadarta yace  inasonki da yawa Fauzah babu abinda zakiyimin naji haushinki don Allah ki tausayamin kija ragamar rayuwata a hankali karki watsar dani karki wofintar dani Fauzah kece rayuwata kece farin cikina wlh Fauzah tunda kika barni ban qara farin ciki ba sai yau don Allah Fauzah ki yafemin laifin da nayi miki hukuncin ki yayi tsauri a gareni pls



Tunda ya fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login