Showing 6001 words to 9000 words out of 34489 words

Chapter 3 - AMINIYA KO KISHIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.doc

19 Nov 2025

124

fadamin jiya ya hanani bacci qarfinta ta hade waje guda ta qwace tana haki juyawa tayi zata fita ya qara kamota wannan karon bata bari ya hada ta da qirjinsa ba qasa ta zame tayi zaman yan bori hanunta ta dora a kanta ta kwallah qara gabadaya hankalin mutanen dake cikin restaurant din ya dawo kansu.


Shima zama yayi ya tanqwashe qafafunsa tare da tallafe kansa da hannunsa daya dayan kuma yana cikin nata be damu da kallon da ake musu ba yace.


 Wallahil azeem Fauzah bazan bar gurinnan ba sai kin maimaita min abinda kika fadamin jiya da daddare. kin dauka nidin matsoraci ko kuma ragon namiji ne da wannan hargagin naki zai sa na janye qudiri na a kanki? Hmn Fauzah kenan bakisan waye Jameel ba to wlh inma kina tunanin hakan ki daina domin babu abinda zai hanani mallakarki Fauzah ban damu da ki soni ko ki qini ba inasonki kuma zan rayu dake a kowanne hali



Miqewa yayi ya gyara kwalar rigarsa yace  bismillah Fauzah yanzu aka fara wasan amma inason tabbatar miki bana loosing a rayuwata tun farko rabon Hairan da Affan shine ya hanani saninki sai bayan kin kasance matar abokina sannan kika bayyana gareni qaddarar data kashe Moha ba wata bace face qaddarar aurena dake Fauzah idan zan rabu da kowa zan rasa komai dana mallaka indai ina numfashi bazan fasa auranki ba, ki rubuta ki ajiye Jameel mijinki ne 



Juyawa yayi zai fita ta riqo hanunsa da sauri tana girgiza masa kai bude baki tayi tace  don Allah Dr kayi hqr wlh bana sonka bazan iya auranka ba Dr kar son zuciyarka yasa muyi abin kunya abinda duniya zata tsine mana wlh bazan iya aurenka ba ya zanyi da kunyar matarka ya zanyi da kunya Amina da wanne ido zan kalleta, pls na roqeka karka bari tasani Dr idan kai babu ruwa a idonka ni nawa akwai bazan iya wannan abin kunyar ba...... ta qarashe mgnr kukanta yana qara qarfi hanunsa ya dora a lips dinta yace.


 Ni ba abin kunya zanyi ba sunnah zan raya kece kika toshe tunaninki kika zubar da iliminki kike kallonsa a matsayin abin kunya yana kaiwa nan ya fice da sauri ya shiga morarsa ya bar mkrntar da gudun tsiya.



Zainab ce tazo ta dagata suka fita daga wajen idon kowa a kansu sosai tayi kuka me isarta kafin daga baya zainab din ta tambayeta alaqarta dashi, bata bata lkc ba wajan warware mata zare da abawa.



Shiru ce ta ratsa tsakaninsu kafin zainab din ta katse shirun da cewa  to Fauzah ke meyasa bazaki amince masa ba a kalaman Dr na fahimci batun yau ba yake sonki Fauzah nidai sai nake miki sha'awar auransa saboda ko ba komai zai riqe miki yayanki bazai wulaqanta kiba saboda yasan asalinki yasan abinda ya rabaki da mijink.... katse zainab din tayi da cewa  dakata zainab wannan shawarar taki bata da guri a zuciyata ki riqe kayarki banaso ni ba butulu bace kuma niba maci amana bace 



Hada takardunta tayi ta fice daga hall din tana fita ta samu dan sahu ya kawo wasu students ya dauketa suka fita tana zuwa ta zube a tsakar gdan ta rushe da kuka Ummah ce ta fito da sauri tana tambayarta menene


Zayyane mata komai tayi salati Ummah ta saki tace  yanzu yaronnan haka zaiyiwa mutane meyasa yakeson jawo mana tashin hankali muna zamanmu lfy? Yanzu nima fitarsa kenan daga nan yazo yana roqona akan nace miki ki amince nikuma nace masa aa bazaayi haka damu ba saboda tsabar shashanci harda hawayensa ni wlh har dariya ma ya bani"
Da Ummah ta rarrashe ta tayi shiru.


A bangarensa kuwa tunda wannan abun ya faru ya shiga tashin hankali ya qauracewa zuwa gdansu saboda ya tanqwara zuciyarsa ya hqr ya qyaleta amma kullum abin kamar turi ko sau daya baitaba jin soyayyarta ta ragu a zuciyarsa ba saima qaruwa da take komai zai kaiwa yaran bata karba dawo da dan aiken takeyi dashi tun abin baya damunsa har ya fara damunsa takai ta kawo bacci ma yana neman qwauracewa idanunsa sosai Amina ta shiga damuwa da halin da mijin nata yake ciki tun tana daurewa har hqrnta ya gaza.


Yauma kamar kullum suna kwance ya zame jikinsa daga nata yaje yayi wanka ya mayar da kayansa ya zauna a gefen gadon zuciyarsa cinkushe da tunanin mafita cikin matsalarsa yanzu shikenan saboda hujjarsu mara tushe yana ji yana gani zai rasa burin rayuwarsa zai rasa farin cikinsa?


Wasu hawaye ne masu zafi da azaba suka shiga zubowa a idanunsa kuka sosai yakeyi har da shassheqa zuciyarsa nayi masa wani irin zafi da ciwo.


Tun tashinsa itama ta farka amma bata tashiba sai yanzu ta miqe cike da tsananin tsoro da mamakin dalilin kukan Mijin nata.


dafashi tayi tare da sakkowa daga gadon ta zauna a gabansa tana qare masa kalloh tace  Dr waye ya mutu kake irin wannan kukan haka?" Shiru yayi tare da dago idonsa ya sauke a kanta baisan lkcn da bakinsa ya fara furta.



 Inasonta ina qaunarta Wifey itace rayuwata ita nakeso wlh itace burina pls ki taimakeni na sameta ta qini saboda ke tace bazata aureni ba saboda ke wlh zan iya mutuwa idan ban sameta ba



Gabanta ne yayi muguwar faduwa zuciyarta tashiga tafarfasa hankalinta yayi qololuwar tashi.


 Inanillahi wa innah ilaihirraji'un tashiga karantowa da sauri ta ari nutsuwa ta sawa kanta muryarta na rawa tace  wacece wannan Dr wacece ita ka fadamin dan Allah wlh nayi maka alqawarin tayaka farautar abinda zuciyarka take so har kasamu cikar burinka cikin rawar murya yace  Fauzah ce Amina tun ranar dana fara ganinta a matsayin matar aminina Allah ya jarabceni da qaunarta har yau zuciyata bata huta ba ki taimakeni na sameta Amina 


Nan ya kwashe yanda sukayi tun daga farko har kawo yanzu ya fada mata duk da irin tashin hankalin da take ciki amma tayi iyakar qoqarinta wajan kwantar masa da hankali ranar tsakaninsu babu wanda ya rintsa kowa da abinda yake saqawa a ransa.


********************

Ita kuwa Fauzah hankalinta yadan kwanta kwanta kwana 2 sakamakon canza layukan wayarta da tayi tare da account din ta na WhatsApp saboda takurawar da Dr Jameel yakeyi mata.


Yau asabar kasancewar suna jarabawa sai 11:00am ta gama shirinta zata fita domin zuwa mkrnta har ta dauki Jakarta taji muryar Amina tana kwada sallama a tsakar gdan Ummah dake kitchen ita ta amsa mata suka gaisa sannan ta qarasa dakin a tsaye ta tarar da ita cikin faduwar gaba ta amsa sallamar tata tare da bata gefen katifar ta zauna murmushi tayi tace.


 Sister kamar bakiyi farin cikin zuwana ba ko? ajiyar numfashi tayi tace  habadai sister sai kace wadda kikayimin wani abu wlh nayi farin cikin zuwanki kawai dai kin sameni ina shirin tafiya makaranta ne shiyasa


Qara fadada fara'arta tayi tace  okay nayi tunanin laifi nayi shiyasa nazo baki hqr naga kusan wata guda baki kai mana ziyara ba Dr har ya gaji da tambayata ya hqr gashi wayoyinki duka baa samunki ko meyasa? tunda ta ambaci Dr din taga ta daure fuska amma sai tayi kamar bata ganiba tace layuka na canza ne shiyasa


 Any why ko madai menene inason kibani aron kunnuwanki Fauzah ki saurareni don Allah wata alfarma nazo nema wajenki karkice min aa Fauzah ki taimakeni ki yarda da abinda zan fada miki pls


Dagowa tayi cikin sanyi jiki tace  ina sauraronki sister insha Allahu bazan baki kunya ba" kallonta Amina tayi idonta cikin nata tace  are you sure Fauzah ? kada kanta tayi tare da cewa  yeah



Riqo hannuwanta tayi tace  Fauzah Dr aure yakesonyi kuma ba kowa yakeso ba ke yakeso don Allah ki taimaka ki amince mishi....


Fisge hanunta tayi da sauri ta miqe tana ja da baya hawaye ne suka shiga zarya a idanunta, itama miqewa tayi nata idanun na zubar da hawaye tace.


 karkice min aa Fauzah Dr bashida wata tawaya da zatasa ki qi shi nasan be wucce kice ni ba ni kuma na amince miki Fauzah na yarje miki kizo mu zauna qarqashin inuwa daya kizo mu zauna qarqashi Dr Jameel Fauzah



Fita tayi daga dakin da gudu itama ta bita dakin Ummah ta shiga itama Aminan ta shiga ummah ce ta miqe daga saman kujerar da take zaune tace  meye hakan Ku kuma lafiyarku kuwa? Fauzah ce tace.


 Ummah zargina takeyi akan mijinta wlh koma me ya fada miki Amina qarya yake bazanci amanarki ba Amina ni ba butulu bace bazan taba soyayya da mijinki ba pls ki yards dani sister" kukanta ne ya tsananta ta shiga girgiza mata kai tace


 Wlh bantaba zarginki ba Fauzah nasan komai Dr ya fadamin duk yanda kukayi Fauzah rayuwar Dr da tawa tana cikin garari indai kika qi aminta dashi ke yakeso Fauzah kece farin cikinsa ya rantse min idan ya rasaki zai iya rasa rayuwarsa ya fadamim zai iya hqr da komai indai zai sameki pls Fauzah ki yarda ki auri mijina mu rayu tare ....




Pls share




*UMMUH HAIRAN* *CE* ...
' [2/16, 09:07] Umm Hairan: https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*



* { _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




=?m? *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* =?m?




?#8?




WRITTEN
AND
STORY



*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
? *FAUZAH*



*TRUE LIFE STORY*



*SHORT STORY*




Mikewa tayi tana murmushi ta shige dakin da aka bata a matsayin masaukinta wanka tayi sannan ta gabatar da sallar isha da shafa'i da wuturi ta kwanta tare da bude data ta fara chart da qawayenta sai goma sannan ta kwanta.


Rayuwa mai dadi takeyi a Adamawa bata da damuwar komai sai ta yaranta data barosu a Kano saboda mkrnta amma suna ranta kuma kullum sai sunyi waya da Ummah da Baba Amina ma sunyi waya da ita sau biyu shidinma Aminan ce ta kirata saboda ita yanzu dukkansu haushinsu takeji.



Yauma kamar kullum suna parlour ita da aunty Rafi'ah suna hira Baffah Mukhtar ne ya shigo fuskarsa dauke da fara'ah Aunty Rafi'ah ya kira suka shiga daki itama mikewa tayi ta shiqe nata dakin agogo ta duba 4:37pm, guda taji aunty Rafi'ah ta saki a parlour gabanta ne yayi wata muguwar faduwa daidai lkcn da ta turo dakin ta shigo.


Bayanta Amina ce zuba masu ido tayi cike da mamaki aunty ce ta nunawa Amina gurin zama ta zauna itama zama tayi tana kallon Aminan, kawar da shirun Amina tayi tace  wannan kalloh haka Fauzah kamar na canza miki 


Ajiyar zuciya tayi tace  mamaki ne yake neman sheqeni Amina ya akayi kika zaqulo gdannan? murmushi tayi tace  ba wannan zaki tambayeni ba tambaya ta zakiyi meye yake tafe dani yanzu tunda kin baro Kano saboda mun dameki mun hanaki zaman Kano to kiyi hqr yanzu mun biyoki ne domin mu daukeki mu tafi dake


Dubanta tayi tace ku tafi dani kuma ke da wa zaku tafi dani? kafin amina takai ga bata amsa aunty ta shigo tace  Fauzah kizo inji baffanki yana parlourn sa  miqewa tayi gabanta na ci gaba da faduwa ta zari hijjab dinta ta saka ta fita.


Shiga tayi bakinta dauke da sallama idonta cikin nasa yana zabga mata wani qawatacce murmushi saurin dauke kanta tayi tare da zama nesa dashi kadan ta sunkuyar da kanta tace  Baffah gani aunty tace kanason ganina"

Gyaran murya yayi yace  fauzah bakiga baqonki bane? sake qasa tayi da kanta tace  naganshi ina yini a nutse ya amsa mata tare da tambayarta lfyrta, a gajarce ta bashi amsa shiru ta dan ratsa kafin baffah ya kawar da shirun da cewa  alhamdulillahi Fauziyya ga Dr Jameel yazo tafiya dake wanda yake a matsayin mijinki a yanzu saboda Allah cikin ikonsa sati guda daya gabata aka daura aurenki dashi bisa sahalewar mahaifinki....


Zabura tayi ta miqe jikinta na wata irin rawa mgn take sonyi amma takasa saboda tsabar dukan da zancen na Baffah Mukhtar yayi mata jin yanda bakinta ya harde yasata saurin zubewa a qasa ta dora hanunta a kanta ta saki kuka me sauti wanda ya janyo hankalin Amina da aunty Rafi'ah suka nufo dakin da sauri.


Tarar da ita sukayi ta hada kai da gwiwa jikinta yana wani irin tsima da gudu aunty ta qaraso ta riqo ta tureta tayi tace  ki qyaleni aunty qyaleni na mutu aunty na shiga uku meyasa rayuwata banida sa'a meyasa komai yake zuwa min a baibai meyasa Baba zaiyimin haka meyasa zai auraddani ga Jameel na shiga ukuna mutuwata kizo Allah dama kasheni kayi da ganin wannan baqar ranar ni Fauzah na auri mijin aminiyata Innanillahi wa innah ilaihirraji'un..... ta qarashe mgnr muryarta na shaking.


Dagota taji anyi idonta a rufe ta fada jikinsa tunaninta Aunty ce tana cewa aunty don Allah kice ya sakeni bana sonsa wlh bana qaunar zama dashi pls aunty ki taimakeni a sanyaye ya bude bakinsa daidai kunnenta yace  kiyi hqr Fauzah naso qyaleki ki samu abinda ranki yakeso amma zuciyata taqi bani damar hakan inasonki Fauzah bazan fasa fada miki ba kuma inason yaranmu su samu tarbiyya nagartacciya daidai da wadda Moha zai basu idan da yana raye Fauzah banason yarannan suyi kukan maraici don Allah kiyi hqr kibani dama muyi rayuwar da zamuyi alfahari da junanmu Fauzah ki tausaya min bani na jarabci kaina da qaunarki ba Allah ne ya jarabceni saboda yafi kowa sanin abinda ya boye tsakaninmu... 


Tureshi tayi da qarfi ta kalleshi kamar zatayi magana kawai kuma sai ta fasa saboda tana ganin duk abinda zata fada masa ma kamar bekai wanda ya dace ta fadiba juyawa tayi zata fita yayi saurin riqo hanunta kasancewar duka sun fita yace  kiyi saurin shiryawa yau nakeson mu juya



Yanda yayi mgnr babu alamun wasa a fuskarsa amma hakan besa taji ko gezau ba ta fusge hanunta ta juya ta fice.


Baffah ne a men parlour ya kirata tsayawa tayi batare da ta juyaba yace  Mahaifinki yace ki shirya kibi mijinki ku tafi saboda abinda ya kawoshi kenan bata ce masa qala ba ta shige dakin ta fada saman katifar ta fashe da kuka me ciwo da taba zuciya tambayar kanta takeyi  dama ashe magungunan da aunty take bata saboda wannan mugun auren ne dama ashe tasan komai ta boye mata ashe tana sane da cewa an qullah aurenta da Dr amma ta kasa fada mata dama ashe wannan dalilin ne yasa taketa hada magungunan gyara dana gyaran jiki take titsiyeta tace sai tasha ko taci ko kuma ta takura mata sai an gyarata dama dalilin da yasa kullum sai ta sata ta shiga wani mgn data kasa gane na meyene kenan amma idan ta tambayeta sai tace maganin sanyin mata ne???


Kukanta ya qara qarfi a fili ta furta  meyasa banida hankali meyasa banida wayo meyasa bana ganewa??? aunty kin yaudareni wlh da nasan saboda wannan banzan baqin maci amanar mutumin kike bani wadannan magungunan da bazan taba shaba....


Bugun qofar da akeyi da qarfi ya sata saurin miqewa aunty ce ta shigo ta shiga hada mata kayanta tare da ce mata  yace kiyi ki fito yamma tana qarayi ko kallonta batayi ba harta gama hada kayan ta fita, bata jima da fita ba wayarta ta shiga ringing jikinta yana rawa muryarta na sharking ta daga tayi sallama cikin kuka.


Tausayi tabawa mahaifinnata amma sai ya dake yace  kiyi hqr Fauzahtuljannah ki tashi maza ki biyo mijinki wlh banyi miki haka don ina qinki ba nayine saboda naga shine Mijin da yafi dacewa dake nasan yata me biyayya ce wa umarni na saboda haka kiyi hqr ki tashi ki biyo mijinki hakan shine zai tabbatar min da har yanzu kinanan a yanda nasanki kinji


Bude baki tayi cikin dashewar murya tace  amma bab..... saurin katseta yayi da cewa  karki cemin komai Fauzah ki nemi albarkar abin wlh inaji a jikina zakiji dadin auran Jamilu zakiyi alfahari da ssmunsa a matsayin miji kiyi hqr kiyi abinda na fada miki Allah yayi muku albarka qit ya kashe wayarsa ya barta da kwararar hawaye ta zafin zuciya.



Saida Amina ta shigo tace mata  kefa muke jira Fauzah munason isa masaukinmu kafin dare yayi aunty ce ta fito daga toilet tace  kije kiyi wanka ga ruwa can na hada miki


Jiki a mace ta miqe ta shiga toilet din ruwan maganin da taketa dafa mata ne tsayin wata guda tana shiga cikinsa na yau har yafi na kullum kauri qin shiga tayi ta zubar dashi ta hada ruwa tayi wanka batayi wata kwalliya ba ta zura doguwar rigarta tasaka mayafinta ta zauna,


Sosai aunty tayi mata nasiha akan tayima mijinta biyayya haka shima Baffah Mukhtar jinsu kawai takeyi amma bata shigarta tayi qudurin gurza masa rashin mutuncin da dakansa zaice ya gaji da ita ya sawwaqe mata.


Haka suka fita har lkcn bata daina hawayeba saida suka fita ta fahimci ashema basu kadai bane harda direbansa.


Shida driver suna gaba ita da Amina suna baya tunda suka taho babu wanda yayima wani mgn ita kanta yana cikin cinyarta tana aikin kukanta sukuma sunata saqar zuci,


Wani katafaren Hotel dake bakin hanya suka shiga a cikin motar suka barta suka fita domin yin abinda ya dace lkcn an idar da sallar isha suna shiga Amina ta dubeshi tace am bakaji ba Dr  tsayawa yayi ya kalleta, rausayar da kanta tayi tace idan ka tashi ka biya kudin daki uku ni daya Sule driver daya kaida sister daya murmushi yayi yana yaba sadaukarwa irin ta Aminan.

Haka yaje ya biya kamar yanda tace ya dawo suka tasota lkcn har ta fara bacci suka shiga, tana shiga ta shiga daki tayi sallah ta haye gadon taja bleaker ta rufe jikinta baccinta ya fara nisa sosai ta ji ana tashinta miqewa tayi a firgice ganinsa tayi tsaye a kanta daga shi sai boxer da singlet baqaqe.



Janye jikinta tayi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login