Showing 21001 words to 24000 words out of 34489 words

Chapter 8 - AMINIYA KO KISHIYA COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN.doc

19 Nov 2025

125

kwasheta cikin dare tajishi a kusa da ita bata nuna alamun tajishi ba shima bayason yawan tambaya saboda haka ya hadiye kwadayinsa ya kyaleta tayi baccinta.


Wasa-wasa tafiya kullum qara miqawa takeyi kusan sati biyu kenan babu Amina a gdan hankali Fauzah ya tashi matuqa inda ta lura Dr ko a jikinsa tayi masa tambayar duniyar nan yace shi besan komai ba tun tana shareshi har ta fara nuna masa damuwarta da kanta ranar da taje awo ta biya gdansu Aminan dake Sheka bata sameta a gdan ba sai mahaifiyarta matuqa tayi mamakin yanda Maman ta karbeta saboda bata saba yimata hakan ba da qyar ta amsa gaisuwarta cikin sanyin jiki tace  mama Sister nazo nema na kira wayarta bata shiga 


Wani wulaqantaccen kallo tayi mata tace  Fauziyyah kenan sai yau kika tuna da Aminan uhm ai dama kinyi zamanki hankalinki ya kwanta kwarkwasa fidda me giji kinyi kutu-kutun munafurci kin rabata da mijinta to kuma yanzu me kike nema a wajenta rayuwarta ko me Jameel ne tabar miki tunda shidin kikeso saboda haka ina me baki shawara kiyi qaggawar fita daga rayuwar Amina kafin naci mutuncinki butulu kawai wadda batasan halacci ba 



Tunda Maman ta fara maganar hawaye ya wankewa Fauzah fuska tsananin tashin hankalinta yaqi boyuwa dafe kanta tayi tana karanta innanillahi wa innah ilaihirraji'un cikin rawar murya tace  mama karki zargeni wallahil azeem bansan komai ba akan tahowar sister gda kawai wayar gari nayi naga batanan mama niba butulu bace bazan taba saka alkhairi da sharri ba wlh mama bani bace banida hanu akan hakan ki taimakeni ki fadamin inda zan sameta inason ganinta mama pl....


Wasu tagwayen kyawawan maruka guda biyu taji a kuncinta wanda suka sanyata hadiye mgnr ta yayar Amina ce aunty Rabi tsaye a kanta ta nunata da yatsa tace  kutumar ubanki kikazo yi mana a gda shegiya kwarkwasa butulu maci amana ni dama na dade da sanin hakan zata faru Amina ce ta kasa ganewa yanzu ga irinta nan an shigo gdan ta an fito da ita ni dama na dade da sanin rariya zata zubar da ruwa tun muna sheda juna dake ki fice daga gdan nan kafin nayi miki sanadin wannan tsinannen cikin matsiyaciya sumumu kasau


Da kyar ta iya yunqurawa ta miqe jiri na dibanta ta kallesu tace  kuyi hqr nasani komai ya faru nice sanadi daban yarda na auri mijinta ba duk da hakan bata faru ba amma nayi muku alqawarin bazan zamo sanadin hawayen wadda ta sharemin nawa hawayen ba insha Allahu zanbar mata mijinta domin dama ba mijina ban....



Kukan da yaci qarfinta ne yasata saurin fita daga gdan motarta ta shiga taja ta fita daga unguwar cikin tashin hankali me gadi ne ya bude mata get ta shiga tayi parking tana shiga parlourn ta zube a kujera ta fashe da wani irin kuka ta qarfe shidda da rabi ya shigo gdan ya dade a kanta batasan ya shigo ba saida ya zauna a kusa da ita tukunna ta dago tanayi masa wani matsiyacin kallo hanu yakai zai tabata ta janye tare da zubewa a qasa tana kuka tace  ka cuceni Dr ka zalinceni ka batamin suna a idon mutane masu daraja a wajena nayi dana sanin auranka ina kanyi dama dalilin da yasa ka dage ka nace saida ka aureni kenan me nayi maka Jameel meyasa kakeson duniya ta nade ana zagina me na tsaneka Dr na tsani zama dakai Dr wlh nima saika sauwaqemin bazan zauna da butulu irinka ba kaico kaicon rayuwata da ka kasance miji a gareni ni dama nasan auranka bazai zamemin alkhairi ba Jameel.


Tunda ta fara mgnr harta gama be tanka mata ba sai madai juyawa da yayi ya nufi dakinsa da sauri ta miqe ta riqo rigarsa ta baya ta tsuguna tace  kayiwa Allah ka sakeni wlh zaka cutar dani idan naci gaba da zama dakai Jameel zan iya kashe kaina idan kaqi saki na ka taimakeni Jameel ka taimakeni pls ka taimakeni 



Hanunsa yasa ya janye hanunta ya dagota yace  karki shigar da kanki cikin abinda babu ruwan ki my Angel karki jefa rayuwata da taki cikin damuwa kuma karki tsananta bincike a hurumin daba naki ba Amina matata ce kema matata ce inada ikon zartar da hukunci akan kowacce sannan inada ikon yin duk hukuncin da nake ganin zai zamemin mafita saboda haka nake umartarki daki janye hanunki akan duk abinda babu ruwanki, nasani Fauzah yau kinje Sheka gdansu Amina kin fita bada izini na ba kinje kin dagawa kanki hankali akan abinda bakida ikon yin komai akai bai dameni ba saboda ke kika kai kanki duk abinda kika jiyo ko suka miki amma inason kisani banason tambaya ki cire kanki daga cikin maganar nan Fauzah be careful 


Yana kaiwa nan ya shige dakinsa ya rufo qofar ita kuwa zamewa tayi a qasa ta saki wani marayen kuka gefe guda kuma mararta ta nayi mata wani irin ciwo.....




_

Pls Share
and Vote



*UMMUH HAIRAN CE* ...
' [2/16, 09:09] Umm Hairan: https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*



* { _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




=?m? *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* =?m?




?#1? 5?




WRITTEN
AND
STORY



*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
? *FAUZAH*


*Wattpad* =?I?


*TRUE LIFE STORY*



*SHORT STORY*




Kuka takeyi sosai kamar ranta zai fita sosai maganganun Dr Jameel suka qara daga mata hankali me yake nufi kenan me yakeson ya aikatawa rayuwarsu me yasa yakeson datse musu farin cikin da suka fara gina rayuwarsu akai?.


Tambayoyin da take ta yima kanta kenan wadanda batada amsarsu tafi awa daya a zaune a wajen kafin ta tashi cikin nauyin jiki ta shige dakinta tayi wanka sallaci magrub da insha tayi shafa'i da wuturi sannan ta canza kayanta zuwa gown red ta bacci ta daure kanta da band ta haye gadon tare dayin addu'o'in neman tsari sannan ta miqa hanu ta kashe glob din ta kunna deem taja blanket ta rufe jikinta badan tayi bacci ba saidon kawai jikinta yadan samu rest har yanzu maganganun su mama da aunty Rabi sun kasa gogewa a zuciyarta.



Tunanin ta ya tafi akan yanda zata bijirewa auran Dr Jameel badan komai ba saidon kasancewar ganin bata zama silar raba ma'auratan da suka gina soyayya akan gsky da amana ba dana sanin shigowa rayuwarsu takeyi sosai har gashi zuwan nata ya fara haifar musu da matsala.


Bataji shigowar sa dakin ba sai jinta da tayi cikin faffadan qirjinsa kukanta ne ya qara qarfi tanajin wani baqin ciki da nadama suna saukar mata jijjigata yakeyi yana bubbuga bayanta kamar wata qaramar yarinya janye jikinta tayi a hankali ta miqe ta koma saman resting chair din dake dakin ta kwanta kallonta takeyi yana mamakin halin ta tashi yayi yaje kusa da ita ya tsuguna tare da kamo hanunta yasa yatsanta a bakinsa yana wasa dashi.


A hankali ya shafo qirjinta yace  kiyi hqr ki tashi muje mu kwanta my Angel dare yayi fah janye hanunta tayi tace  dare fah kace Dr ashe kai kana ganin dare yayi kenan bayan zuciyarka bata aiyana maka abinda yake alkhairi gareka Jameel kana tunanin ni Fauzah zan sake hada shimfida dakai wlh aa Dr bazan sake hada shimfida dakaiba na tsani halinka Dr meyasa kakeson sakin damarka Dr me nayi maka zaka yankemin farin cikina...


Kafin ta rufe bakinta ya zura harshensa cikin natan kuka ta shiga yi tana tureshi miqewa yayi ya dagata ya dorata a gadon yaja blanket ya rufesu ya shiga jagwalgwalata tureshi takeyi tanayi masa magiya amma yaqi sauraronta saboda tagama bata masa rai.



Iyakar wuya ya bata saboda baitaba yi mata mugun ci irin na yau ba kuka takeyi masa tanayi masa magiya miqewa yayi ya shiga wanka ya fito ya zauna kusa da ita ya yaye mata bargon yace  idan har zakici gaba da yimin mgnr nan nikuma zanci gaba da hukuntaki ta haka da hakan har ki gane abinda nake nufi Fauzah ina qara yi miki tuni da ki cire kanki daga wannan mgnr babu ruwan ki a ciki wlh zan iyayin komai akan kare qimata da mutunci na kuma Amina da kike cewa na zalince ta ai babu zalinci tsakaninmu ita ta zaunar dani tace nayi mata alfarma nace tame ce tace ita so take kawai na saketa nayi iyakar qoqarina na ganin hakan bai faru ba qarshe takani qara wajan iyayena Alh da kansa ya kirani yace yanason ganina ina zuwa suke sanar dani karo na uku kenan matata tana zuwa tana roqonsu susa na saketa suna bata hqr amma wannan karon tace in har basusani na saketa ba to zata kaini court inyaso sai alqali ya raba aurenmu.


To akan mene zaisa na bari har takaimu da zuwa kotu Fauzah meyasa ba zanyi mata abinda takeso ba wlh ban taba nadama ba ba kuma zanyi ba akan na saki Amina saboda ita ta buqaci hakan duk da yanda zuciyata take karkatar dani a bangare daya amma ina qoqarin kwatanta adalci Fauzah banida burin cutar da daya cikinku



Yunqurawa tayi ta tashi zaune tana kuka me cin rai tana girgiza kanta rarrashinta yakeyi sosai amma taqi yin shiru ganin da gaske bazatayi shirun ba yasa shi miqewa ya zura rigarsa juyawa yayi zai juya ya fita daga dakin tayi saurin riqoshi tsayawa yayi tare da zama yana dubanta yace  ya kikeso nayi miki Fauzah nayi miki bayani na baki hqr kinqi ganewa Fauzah badan raina yanaso na saki Amina ba saidon ina ganin hakan shine zai zame mana maslaha saboda ita ta nema ki fahimceni my Angel pls



Kanta ta dora a qirjinsa ta bude baki a hankali tace  na fahimceka Dr amma dan Allah Nima kayimin kamar yanda kayi mata ka sawwaqemin auranka saboda nasan nice sanadin hakan Dr saboda ni Amina ta yanke shawarar rabuwa dakai saboda nine wlh daban shigo cikin rayuwarku ba da hakan bata faruba ka taimaka ka sakeni Dr bazan iya zama dakai a halin baka tare da Amina ba....



Rufe mata baki yayi da hanunsa yace  karki dorawa kanki damuwa akan abinda bazan taba sakacin aikatawa ba Fauzah dake da yayanki ku amanata ne bazan taba iya banzatar da rayuwarku ba sannan har idan kika bari shaidan yayi tasirin raba tsakaninmu akai matsala saboda mun riga mun hadu haduwar da babu rabuwa Fauzah itan da kikaga ta aikata hakan saboda tasan bata da kaico ne bata da waiwaye tunda ba haihuwa mukayi ba kefa zaki iya matsawa mu rabu ayau gobe ki haihu kinga ai anyi baayi ba kuma inasonki Fauzah son da bantaba yiwa wata mace irin sa ba bantaba ayyanawa a raina zan iya rayuwa babu ke ba Fauzah ki bani dama na nuna miki kulawa da gata da irin soyayyar da nakeyi miki keda yayanmu...



Katseshi tayi da cewa  aa bazan iyaba Dr me kakeson na zama wato kanaso na zama butulu ko me saka khairi da sharri kanason na zama kwarkwasa fidda me giji kanason na mutu duniya tana tsinemin wlh aa Dr dolene nima ka sakeni Dr ka sakeni nace banason ka ni bazan zauna dakaiba meye amfanin zama dakai din da zanyi wlh garamin rayuwata ni kadai akan rayuwa dakai


Bazai iya jure kalaman nata ba saboda haka ya miqe ya fice daga dakin ya rufeta daqyar ta iya miqewa tayo wanka tare da alwala tayi nafilfili sannan ta zauna taci gaba da lazumi da neman mafita a wajen ubangiji.


Koda gari ya waye kwanciyar ta tayi a dakin bata fita parlour ba kasancewar asabar ce sai 11:00pm ta fito a parlour ta tarar dashi yana aikin danna laptop dinsa dagowa yayi ya zuba mata idanunsa da sauri ta shige shi ta nufi kitchen murmushi yayi tare da miqewa ya bi bayanta bata ankara ba saijin hanunsa tayi a qasan mararta yana shafa cikinta daure fuska tayi qasa da kanta tace  ina kwana juyota yayi yana qoqarin dago da fuskarta yace  nima nemansa nake in kin ganshi daqyar ya dago kanta ya zuba idonsa cikin nata yace  me kikejin tsorone da kike guduna yau nine fah gwarzonki mijinki Jameel Fauzah dan Allah ki saki jikinki dani kinji?


Kawar da kanta tayi tare da janye hanunsa daga jikinta ta nufi inda ta dora ruwan zafin ta dauka ta juye a flask sannan ta dora Irish dinta kusan tare suke aikin yanata janta da hira amma taqi kulashi haka suka gama aikin sukayi break fast a daddafe ta miqe ta koma bedroom dinta ta kwanta bacci ne ya fara daukarta cikin baccin taji mararta ta daure tayi saurin miqewa tare da ambaton sunan Allah kamar wasa ciwon ta yake qara qarfi da qyar ta sauko daga gadon ta nufi toilet saboda fitsarin da takeji tana tsugunawa jini ya balle mata qara ta qwallah wadda ta jawo hankalinsa ya shigo dakin da sauri ganin bata dakin yasa shi qarasawa toilet din ya tarar da ita cikin jini hankalinsa yayi qololuwar tashi ya fita da sauri ya gyara parking ya dauketa ya sata a mota yaja a guje suka fita daga gdan kai tsaye asibitinsa ya nufa da ita kiran wayar Ferciwally yayi ya fada masa yanayin parking nurse's din suka fito da keken tura marasa lfy suka turata zuwa ciki.


Saida sukayi mata duk abinda ya dace kafin sukai ga yimata aikin Allah cikin ikonsa ya kawo mata haihuwarta yaranta biyu maza saboda farin ciki Dr Jameel kamar yayi hauka hana kowa taba masa yaya yayi shi da kansa ya ya yankensu cibiya ya gogesu sannan ya fito dasu daya a hanunsa daya a hanun Ferciwally suka shiga dakin hutun Hajiyansa ce ta tare shi tare da karbar yaran a hanunsu gdy sosai tayiwa Allah daya azurta autanta da yayan biyu masu kama dashi bayan tsayin shekaru yana nema bai samuba.


Zama yayi kusa da ita kamo hanunta yana murzawa farin cikin Dr Jameel yakasa boyuwa duk wanda yake wajen yasan yana cikin farin ciki sabanin Fauzah da bazaka iya gane yanayin da take ciki ba kiran sunanta yayi a hankali amsawa tayi batare data dagoba daidai kunnanta yace  kinyi farin cikin samun qaruwar nan kuwa Fauzah?" Girgiza kanta tayi alamar  aa


Sakin hanunta yayi jikinsa a sanyaye ya miqe ya fita daga dakin shigowar su Ummah ne yasata dago kanta da tunda ta sunkuyar dashi hawaye takeyi.





pls Share
and Vote




*UMMUH HAIRAN CE* ...
'[2/16, 09:08] Umm Hairan: https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R*



* { _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }




=?m? *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* =?m?




?#1? 7?




WRITTEN
AND
STORY



*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
? *FAUZAH*


*Wattpad* =?I?


*TRUE LIFE STORY*



*SHORT STORY*







Ganin da gaske Fauzah na neman karya mata gwuiwa yasata miqewa ta fice daga dakin tana kiranta amma bata saurareta ba komawa tayi ta kwanta eyes dinta naci gaba da zubar da tears.

Wannan kenan a bangaran Dr Jameel kuwa sosai zaman yan marina sukeyi da Fauzah saboda tunda ta haihu tabar gdansa tsayin wata guda kenan bata daga wayarsa takai ta kawo ma ko gdan yaje domin ganin yayansa bata ko kallon inda yake balle yasa ran zamata saurareshi, hakan da takeyi ba qaramin ciwon rai yakesa masa ba amma bashi da yanda zaiyi da ita zuciyarsa babu dadi sosai abin har yana neman shafar aikin sa da lfyrsa Suhail da Saheeb kawai yake kallo yanzu yaji dadi duk ya rame ya zama kalar tausayi Dr Jameel dan gayu amma gaba daya ya zama sususu wannan lamari sosai ya damu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login