Showing 1 words to 3000 words out of 43117 words

Chapter 1 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

 ​
AISHA-SIDDIQAH




​​ 2






SUMAYYAH ABDULKADIR
takorikabara@gmail.com
babbangoro2015@yahoo.com

TUNASARWA/JAN HANKALI
Ba’a rubuta littafin AISHAH-SIDDIQAH don cin zarafin kowacce kabila ba, ko don nuna wata
kabila ta fi wata daraja a tsakanin kabilun Najeriya ba.
Kyakkyawar manufar dake kasan labarin itace dabbaqa kalmar WA-ZO-BIA da fadakarwa
cikin nishadi akan kabilancin da ake nunawa ita wannan kebantacciyar kabila dana dauka, da
kuma wanda suma suke nunawa ga kabilar hausawa.
Labarin AISHA-SIDDIQAH labari ne da aka gina shi kacokam akan manyan kabilun Najeriya
guda uku, don son samar da fahimtar juna da rage tasirin kabilancin da yayi katutu a zukatanmu
ga junanmu.
Asali mun san cewa Najeriya kasa ce bata kabila guda ba, bata yare ko harshe guda ba.
Bincike ya nuna kusan kabilu 371 da yarurruka sama da 500 suka hadu suka mallaketa,
wadanda suka fi yawa sune Hausa, sannan Yoruba, Igbo da kuma Fufulde.
In haka ne kenan babu wadda ya kamata ace tana faharin tafi wata, ko tata itace kan gaba ko
mafi daraja, in dai Allah daya muke bautawa sai mu rike ayar “Inna akramakum Indallahi
Atqaakum”.
Idan kuma ba addini daya ya hadamu ba, sai mu dauki ayar “Lakum Deenukum Wa liya
Deen” nan ma sai kaga an zauna lafiya da juna.
Fatan marubuciyar shine Hausawa mu daina kabilanci, in bazamu iya dainawa ba mu rage
shi, sauran kabilun suma su rage nasu kabilancin ga hausawa, ta hakane kadai za’a samu
hadin kai da fahimtar juna a tsakanin WA-ZO-BIA wadda zata iya zama jagora wajen cigaba da
haifar da auratayya da kyakkyawar mu’amala tsakanin kabilun musulmai a duk inda suke a
kasar nan. Don haka kada kayi tsalle ga tafiya karshen labarin ko ka dauki wani abu ya zama
cin zarafi ga yarenka ko kabilarka ba tareda ka ga karshen littafin ba. Taku har abada.
–Takori Sumayyah AbdulQadir.
SADAUKARWA
Aisha-Siddiqah ta sadaukar da labarinta ga daukacin mambobin whatsapp group na TAKORI’S

LOUNGE bakidayanku. Allah ya bar zumunci da kauna har ‘ya’ya da jikoki.
KIYAYEWA
Hakkin mallaka abin kiyayewa ne ga marubiciyar littafin, ban yarda a karanta shi a kowacce
kafa ta sadarwa ba tare da rubutaccen iznina ba. Yin hakan ya sabawa doka ta shari’ah kuma
abin tuhuma ne daga lauyana Barr. Sadiq Rufa’I Wali.
​ GODIYA DA JINJINA
Godiya da jinjina ga aminan kwarai wadanda suka taimaka matuka gaya wajen shawarwari,
tacewa da gyarawa Dr. Amina Jafaru Musa, Barr. Azima Musa Abdullahi, Aisha Muhammad,
Maryam Yusuf Abubakar, Haj. Zainab M. Ahmed da Bilkisu Askira.
​ In tsaya ina ce muku na gode kuma kunsan yayi kadan, saidai kawai in jinjina muku bisa
namijin kokarinku akan ingantuwar littafin AISHATU SIDDIQAH.

KAFIN MU FARA LITTAFI NA BIYU INA TALLATA MUKU AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME
AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.
-Takorinku


AISHA-INDO-SIDDIQAH 2
B
ada jimawa ba binciken Malam Yunus da Yayansa Malam Barau ya bayyanar musu da duk
abinda suke son sani game da ko waye Engnr. AbdulRasheed Idrees Akanni, ba kowa bane sai
Polo Legend “The Latest Yoruba Demon” (inji abokin aikin Malam Yunus, wani bayerabe mai
suna Abdulganiy musulmi da suke aiki tare a hukumar alhazai ta jihar Gombe wanda ya san
zuri’ar Sarki Akanni kakaf sani na sosai da sosai, farin sani, kasancewar mahaifiyarsa ‘yar Ilorin
ce kuma acan ya girma), mutuminnan ya gaya musu nasabar AbdulRasheed da iyayensa kaf
dinta, a karshe ya gaya musu Prince din babban jikan Sarki AbdulRasheed Abdullateef ne (Emir
of Ilorin) na yanzu, shine na fari cikin jikoki, sannan kuma jikan Sarkin Gombe ne na baya Sarki
Ahmadu Jalloh Umar.
Har ila yau, an tabbatar musu da cewa Prince din baida wani aibi takamaimi da za’a ce shi
ya hanashi aure akan lokaci, maiyuwuwa shahararsa a wasan Polo ce da arzikin da yake samu
a jikinta suka kwashe lokacin sa da sha’awarsa daga yin aure a sanda ya dace,Abdulganiy yace
don 'Polo Celebrities' na duniya irinsa aure akan lokaci na musu wahala matuka, musamman da
basa zama a wuri guda kullum a tafe suke, a takaice a bakin Abdulganiy suka ji kusan komai da
ya shafi Prince, suka ji cewa duka lokutan rayuwarsa na wasan tseren Doki ne a kasar Polo ta
Argentina, sannan ya kan fita tournaments a sauran kasashen da ake Polo a duniya.
“Babu wanda yasan hakikanin abinda ya hanashi yin aure har tsayin wannan lokacin da yake

cikin shekaru na 42”.
Amma koma meye, a cewar mutumin mai bada shaida bazai zama hujja na a hanashi aure
ba a wannan zamanin da masu auren wurin ma ba duka ne nagari ba, don iyayensa malamai
ne, mutanen kwarai, kuma sarakuna nagari.
Baban Aisha ya tsorata bayan jin wannan bayanin da kuma jin su waye Akanni’s, da
matsayin ita kanta Haj. Nenne Sappa a Gombe, don haka ya tuntubi iyayen Ishaq akaro na uku
kenan cewa Ishaq ya kawo sadaki ya aura masa Aisha a wuce wannan gabar don ya tsorata
sosai. Domin koda suka yi tsammanin Nenne Sappa a matar mai kudi kawai suka tsammaceta,
ba’a diyar sarkin Gombe, matar dan sarkin Ilorin, kuma uwar dan sarki mafi soyuwa a ran
Kakansa ba.
Ya tuna dadewar da Ishaq yayi tareda Aisha-Siddiqah, da karfin shakuwa da soyayyar dake
tsakaninsu tun farkon balagar kowannensu, don haka ya yankewa kansa cewa Ishaq shi yafi
kowa cancantar aurenta, yaro matashi kamarta, wanda zai rike masa ita da daraja da kima,
kada ya kaita inda bazata yi daraja ba, shi baya son auren hadin iyaye irin wannan, yafi yarda
da aure na na gani inaso daga namijin kansa ba daga iyayensa ko wani nasa ba.
Ishaq kadai zai iya baiwa Aisha hakalinsa ya kwanta, don shi ya san asalinta ya san halinta
ya san komai na iyayenta da ciwon asmarta mai dan tashi lokaci-lokaci.
Malam Yunus mutum ne marar kwadayin abin duniya kamar matarsa Zaynaba. Tabbas
duniya tayi musu wannan kyakkyawar shaidar akwai wadatar zuci. Shiyasa hankalinsu ya zo
daya suke zaune lafiya shekaru aru-aru ba mai jin kansu. Hankalinsa a kwance ya kira dan
uwansa Malam Barau ya gaya masa komai ya yanke, sai Barau yace su wuce gidan Malam
Hassan din kawai a yi komai yau a gama wato mahaifin Ishaq a yita ta kare su aurar da Aisha
su huta.
Shima Baba Barau ya dade da sanin duk duniya ba mai son Aisha irin Ishaq Hassan, yaron
ya jima yana hidimarta da dakon soyayyarta tun shigarta sakandire, ba wani mai mulki ko mai
kudi da zai rude su su yi wa Aisha auren cushe. Auren da bazata yi daraja ba ko a maidata
sadaka. Nan suka mike suka je har zauren gidan su Ishaq suka tadda mahaifinsa Malam Hassan
kuma makwabcinsu, suka share wuri suka zauna suka gaya masa duk abinda ake ciki, a karshe
Malam Yunus yace yana son aurar da Aisha a wannan gabar, yana tsoron al’amarinta, rana
daya ne ba’a zuwa a sameshi akan maganarta da manyan mutane, Aisha manema gareta bila
adadin ba tun yau ba, mafi yawansu kuma ‘ya’yan manya, sannan ‘ya’yan mutunci da iyayensu
ke takowa da kansu har gidansa nema musu aurenta, wadanda mutuncinsu yake sawa bazai
iya tula musu kasa a ido ba saidai yayi ta togaciya da Ishaq.
Yace yau gashi ‘ya’yan Sarakuna sun fara zuwa neman aurenta. Gaba kadan bai san su
waye kuma zasu zo neman auren Aishar da ya dade da ajiyewa Ishaq ba. Malam Yunus din
yace farin jininta yana bashi tsoro a shekarar nan data shiga ajin karshe na sakandire.
Budar bakin Malam Hassan kasancewarsa irin mutanen nan da basa tauna magana ko
kadan kuma basu da kawaici akan ‘ya’yansu musamman in suka lura yaran nama mace mugun
so, sai yace da Malam Yunus da dan uwansa Kawu Barau.
“ku gafarce ni Barau da Yunusa, domin dai ni na dade da yiwa Ishaq mata a cikin dangin
mahaifina dake kauyen Nafada, maganar gaskiya kawai kallonsu muke yi tuntuni (Aisha da
Ishaq din) nida mahaifiyarsa, shiyasa tun da farko da ka tuntubeni watannin baya kan batun

aurar da Aisha nayi shiru ban baka cikakkiyar amsa ba.
Amma zuwa yanzu ba zan boye maka ba Ishaq ya jima da samun mata daidai da
ra’ayinmu”.
A karshe yace “bazai aura ma Ishaq (mai ciwon numfashi) ba, kamar aka ce mata sun kare a
duniya, don Asthma ana gado, kuma (allergy) ne a cewarsa. Yace kuma shi za’ayiwa barazana
da sarakuna da masu kudi don a takura shi tashi tsaye yin aure bai shirya ba dansa ma bai
shirya ba sabida ka gaji da sayen inhaler da maganin Asma da yawon kwanciya a asibiti? Yace to ba sarakuna ba Barau da Yunusa, ko dan shugaban kasar Najeriya ne yazo neman
aurenta na lamunce ka aurawa diyarka damuwarku ce.
Ishaq yanzu yake kokarin hada hidimar kasa, baida halin aure a yanzu. Shiyasa na nema
masa yarinya ‘yar shekara goma sha daya wadda zata yi daidai da zabinsa da namu”.
Wannan magana ta fusata Malam Yunus da dan uwansa Kawu Barau, ta kuma bakanta ma
Barau rai ba kadan ba, kasancewarsa mai saurin fushi da yawan harzukar zuciya a kusa, sukayi
shiru shi da kaninsa Yunusa zaune akan tabarma a zaurensu Aisha. Barau tun fil azal mutum
ne mai saurin daukar zafi akan ‘ya’yansu, sabida ko a cikin ‘ya’ya takwas maza da mata da shi
yake dasu a gidansa manya da yara, tofa yana ji da Aisha-Siddiqa a cikin yaransa,
kasancewarta daya tilo da Allah ya barwa dan uwansa, kuma duk rashin kwaramniyarta da
kazarniyarta irin na sauran ‘yammata yana son dabi’unta.
Bayan sun baro soron Malam Hassan Kawu Barau ya samu wuri ya zauna a zauren gidan su
Aisha, ya dubi dan uwan nasa Yunusa da idonsa ya kada, yace “bayerabe ne kace dan ita
Hajiyar Lagos din ko me? Kuma ya jima bai yi auren fari ba? Sannan ba’a kasar nan yake
rayuwa ba gabadaya kuma dan wasan Polo ne shiyasa kake tababar bashi auren Indo ko?” Malam Yunusa ya gyada kai. Sai Kawu Barau yayi kuta yace. “To gara shi sau dubu akan
zuri’ar wannan marar karar makwabcin naka daka kwallafawa rai, da bai san mutunci da kara
ba, kamar ba bafullatanin mutum ba, na bi kabilanci da gudu na kamo shi na kawo cikin
zuri’ata”. Nan take Kawu Barau ya shiga cikin gidan ya gayawa Haj. Zainab ta gayawa kawarta Haj.
Sappa take ko Safiya? Duk sanda suka shirya su turo an basu auren “Aishatu-Siddiqah Yunus”.
Kawu Barau yace cikin bacin rai, “ba Bayerabe ba ko dan sarkin Nufawa da Agalawa ne Dan
nata, a gaya musu ya bashi Aisha. Tunda har uwarsa da kanta tazo ta durkusa a gabanka har
da hawayenta tana rokon a basu auren Aisha sabida kauna, cikin darajawa da mutumtawa irin
haka ba tareda la’akari da matsayinmu ba, alhalin ita ta san da Asmar Aisha, don haka shi ya
basu Aisha-Siddiqah ko dan nata yayi saba’in a duniya ba arba’in da ‘yan kai ba, koda kansa
fari fat ne yana dogara sanda don tsufa an bashi, in yaso Aisha ta yi zaman zuba ruwa a buta
da kai masa ruwan wanka bayan gida, wato (tayi zaman kula da tsufansa ba zaman soyayyar
miji da mata ba)”.
**** **** ****

R
anar da Nenne Sappa ta koma Lagos tareda Aisha ta sauka a gidanta a Banana Island da
tsakiyar marece, Aisha rike da ‘Handbag’ din Nenne tun daga Gombe ta riko mata, duk da bata
son tafiyar kuma hakan ya kasa boyuwa a fuskarta duk yadda Nenne ta dinga kokarin daukar
hakalinta da hira cikin fulatanci don dai ta saki jiki da ita, amma har suka sauka a Lagos

kalaman Aisha a matsayin amsa basu fi biyar ga Nenne ba, haushin ta rabo ta da Ummanta ya
ki barin ranta, tana dai kula ma Nenne da jakar hannunta da kan wayoyinta uku bata bari ta yi
dakonsu ba, yadda take Ummanta in zasu unguwa ko ta rakata asibiti, suna isa gida ko hutawa
Nenne bata yi ba ta kama hannun Siddiqa zuwa cikin gidan, babu kowa zaune a babban falon
kasa sai talbijin dake ta aiki ita kadai cikin tashar kasar Yemen, barorin gidan dake giftawa kowa
naaikinsa sunata russunawa sunama Nenne barka da sauka, tun daga fitowarsu a mota
(Venza) da direba ya dauko su daga filin jirgin Murtala Mohammed har shigarsu ainahin kwaryar
cikin gidan Engnr. Idris Akanni Aisha taga ma’aikata sun kawo gaisuwa sun kai su biyar, kai
tsaye Nenne ta wuce rike da hannun Aisha-Siddiqah har dakin “Princesses” yadda take kiran
(Firdausi da Fatima).
Princess Fatima na kishingide a gado rike da wayar ta tana Magana da fiancé dinta
Abdulganiyu Dasuki, yayinda Firdausi ke stretching gashin kanta da na’urar tazar gashi Nenne
ta tayi sallama a kansu, Siddiqah na biye bayanta, Fatima ta kashe wayarta da sauri cikin
murnar dawowar Nenne lafiya, Firdausi ta dago kai da murmushi suna amsa sallamar
mahaifiyarsu da murna fal a fuskokinsu kafin su kula ba ita kadai bace, wata siririyar
kyakkyawar yarinya mai ruwan ‘yan Gombe biye a bayanta, Nenne tace “shiga daga ciki ki huta
kinji ko Siddiqah, Fatima a hada mata ruwan wanka, diyata ce na taho da ita daga gida
(Gombe), ku kula min da ita da kyau, kamar yadda kuke kula da Ruqayyat (tana nufin Kiki),
kafin a gyara dakin da zata sauka, zan shiga inga Dade, ina fitowa zuwa anjima”.
Princess Firdausi da Princess Fatima suka dubi juna fuskar kowacce fal curiousity, sun sha
mamakin inda Nenne ta samo ‘yar kyakkyawar bafullatanar yarinya haka. Kodayake tace daga
gida Gombe take. Saidai basu santa cikin dangin Nenne ba kaf. Bata sauraresu ba da tarin
tambayoyin data gani fal fuskokinsu ta wuce turakar mijin ta tana gaya musu cikin harhen
yarbanci “su tabbatar Aisha-Siddiqah (feel at home) wato su tabbata ta saki jikinta dasu.
Baba na faman aikin nasa na karatun jarida wanda ya zame masa lazim kullum tun bayan
ritayarsa, Nenne ta zauna a kusa da shi cikin gajiyar tafiya bayan ya amsa sallamar ta ya kum a
ajiye jaridarsa a gefe. Kallo daya Baba Engnr. Idris Akanni ya yi mata ya ga farin cikin da bai
taba hangowa cikin idanunta ba. Tun kafin yaci abincin data shigo masa da shi ko suyi doguwar gaisuwa yadda suke yi idan
dayansu yayi tafiya Nenne ta kasa jinkirta abinda ke bakinta. Ta gayawa Baba, ta samowa
AbdulRasheed aure a Gombe.
Engnr. Idris Akanni ya dago manyan idanunsa daga kan jaridar dake hannunsa yana duban
matarsa Hajiya Sappa a hankali cikin nutsuwa, wato yana mata irin kallon nan na kodai tayi
gamo ne? prince din zata ganowa mace? Shi baida idon gano matar data dace dashi a shekaru
irin nasa sai an gano masa? Shi Engnr. Idris Akanni Waziri of Ilorin ya riga ya sakawa ransa
Prince baida ra’ayin aure ne kawai shiyasa baya shiga sha’anin maganar auren da kowa ke yi a
kansa kamar shikadai suka haifa, afterall sunada ‘ya’ya masu yawa a family dinsu da suka tara
musu jikoki fal, maiyasa kowa zai damu kansa da Abdulrasheed shikadai? a rayuwar Idris
Akanni shi bature ne baya shiga rayuwar kowa hatta ‘ya’yansa ya basu dama suyi abinda suka
tsarawa kansu da wuya kaga ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login