Showing 39001 words to 42000 words out of 43117 words

Chapter 14 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

cewa in ta takura din zai bi, tunda
ta lura da gaske bashi da lafiyar yin aure duk da ya musanta hakan ita yanzu ta yarda da hakan,
ta kuma barwa Allah ikonsa, tana addu’ar Allah ya bata ladan kyakkyawar niyyarta na dabbaqa
Sunnah a tsakanin Siddiqah da Prince, ya bata karfin zuciyar fuskantar iyayen Siddiqah ranar ta
mayar da ita su yarda da hujjarta na Prince baida lafiyar auratayya koda bai fadi ba.
Amma namijin duk da za’a baiwa lafiyayyar mace kamar Siddiqah a gaya masa matarsa ce ta
Sunnah ba tareda ya kashe ko kwabonsa ba, zuciyarsa ta kasa motsuwa to ba namiji bane mai
lafiyar mazantaka. Don in babu SO to akwai SHA’AWA a tareda kowanne Da namiji.
Ita bata kin Haseenah din da Taiwo take so dashi, kawai tsatsonta ne tace bata yarda ya
gauraya a cikin tsabtataccen jininta ba, ba kuma don komai ba sai don babu tabbacin halaccin
haihuwarta.
Amma tunda daga Taiwo har Kehinde su suna ganin abinda a wurinsu ita bata gani kalas!
Yaje ya auri Haseenan dama duk matan gidan marayun Ambursa masu wayewar kai da iya
rangwada in har yanada lafiya, don yanzu ita uwarsa ma tana tababa akan ingancin lafiyarsa.
Sai suyi mai fishshesu ta maida Siddiqah ga iyayenta ko ba takardar saki, don bazata iya
cewa ayi abinda Allah ya halatta amma baya so ba (saki). Dama Siddiqah din ba kwantai tayi ba
kuma ba wani girma tayi da iyayenta suka gaji dashi ba. Mutunci ne da sanin yakamata da
alkhairi yasa aka bashi ita. To amma ina mafita? Aisha zata dauwama ne da auren Kehinde da bashi da gurbin ajiyeta
cikin rayuwarsa ko lafiyar da zai iya ijjema bukatar aurenta. A rayuwarta kuma bata ko son jin
kalmar “saki” balle gittawarsa a aure, watakila ko don babu ita a kamus din gidan sarauta
gabadaya daga nasu gidan sarautar har na mijinta. Sai taji ta kasa ce da Kiki Aisha matar Uncle dinta ce, in tayi hakan tamkar ta cusa Aisha ne a
inda bata da kwarjini, tace da Kiki Aisha diyar kawarta ne kawai ta zo mata hutu daga Gombe.
Ai kuwa tashin farko Kiki ta makalewa Siddiqah tana rokon itama tayi mata lallen, Firdausi
tace “na kudi ne malama?” Kiki tace “Ke kudin kika biya Aunty Feedy? Imma na kudin ne kinsan
Uncle dina zai biya mun ayi mun” Ta fada cikin tsananin shagwaba irin tata, Aisha na dariyar
shagwabar Kiki katuwa da ita sai sokonci, tace. “Wasa Anti Feedy take miki kinji Kiki, zan miki lalle wanda yafi na Aunty kyau kin ji?” Kiki ta
hau murna tace “kuma zaki na koya min hausa?” (kasancewar maganar Kiki duk rabi yarbanci
ne sai kuma turanci da yafi yawa), Siddiqah ta ce “zan koya miki hausa har sai kin ce ta isheki”.
To dama a dakin Kikin Aisha Siddiqah take zaune, sai ga Kiki na shigo da jakunkunanta

jikake keeeyyy! Tana jansu a kasa cikin dakin cikin dokin zama tareda Aisha.
“Pretty, tare zamu dinga kwana har in koma gida, yaushe zaki koma Gombe zan biki in ga
gidanku?”
Aisha ta rasa me zata cewa kiki, ita kanta batasan sunan zamanta a gidan Engnr. Idris
Akanni ba, haka bata san matsayinta ba. Don haka a karshe sai tayi kundumbala kamar tasan
shirin da Nenne ke yi tace,
“Sai na gama WAEC zan koma gida”.
A daren Kiki bata bar Aisha tayi barci da wuri ba sabida hira, Nenne taji dadin irin reception
din da Aisha ta samu a gurin Kiki, ko dama bata jin ta, indai wajen son mutane ne da saukin kai
a gaskiya Kiki ba’ayi halin Anti Murja ba.
Ita daga nata sai nata, sai kuma wanda zuciyarta taga damar so, kamar Haseenah Ambursa
kenan da suka dade tare.
Kiki akwai surutu, sa'annan akwai kirki da manyance, sannan ga hannun kyauta. A take ta
hau daukan kayan kwalliyarta tsadaddu tana baiwa Aisha, don taga bata da kayan gyaran jiki,
wadanda ta sayo tun daga Santa Monica din Los Angeles. Ta kwana tana zuba mata labarin da
ya shafeta ko wakafi Kiki bata sakawa. “Ni dinnan da kike gani nice ‘yar gatan Hamma, I mean Hamma Prince na gidannan, ai kin
san shi ko?”
Murmushi Aisha tayi, tace “naga alama Kiki, ko daga wannan uwar sayayya da kika jido,
kamar zaki kwaso kasar da kika dawo bakidaya ai sai dan gatan”.
Kiki ta kyalkyale da dariya tace “ai Uncle dina bashi da wayau in dai a kaina ne, ya manta da
canjinsa a wurina basu kare ba, da nace zan yi shopping a “Santa Monica” sai kawai ya karo
min. Har sayayyar matar shi mai zuwa nan gaba a kudinsa nayi mishi ya dauka kudi nane, to
wa yake bani kudi in bashi ba? Mum (Taiwo) ba’a cin kudinta ko zaka yi yaya. Kinsan likitoci akwai rowa, Dad kuwa ina na
ganshi ma ko abu zai turo mana saidai ita ya tura mata yace ta saya mana.
Allah ya gani ina yiwa Uncle dina sha’awar kyakkyawar yarinya kamar ki. Inama zai yarda da
an yi ‘yar gida tunda Nenne tace Mamanki kawarta ce”.
Kiki ta dan yi shiru kafin cikin damuwa tace “to bazai yiwu ba, don naji ance aljana ta auri
Uncle dinane shiyasa yake gudun mata, ko zancen aure baya so ayi masa.
Yanzu gashi lamarinsa ya shafeni, Mum ta saka min takunkumin kin kula BoyFriend dina,
tace sai ranar da Uncle yayi aure don bazata yarda yayi jika bai yi aure ba.
Sabida Allah Aisha Uncle AK fa har furfura ya fara (clicking to 43 years), jiran gawon shanu
Mama take yi, da zai yi aure da tuni yayi, don ba irin matan da baya tare dasu a kasashen
ketare”.
Aisha taji ta kara tsorata da lamarin Prince Abdulrasheed, jin abinda Kiki ke cewa a kansa,
har a cikin idanunta da Kiki ta lura da taga tsagwaron tsoro tsantsa, wai har ya fara furfura, sai
ta tuno Ishaq din ta dan shekaru 28 National Youth Cervice Corp Member (dan hidimar kasa).
"Banza bata kai zomo kasuwa tabbas", inji hausawa, akwai dai abinda ya hana Hamman su
Firdausi yin aure ba haka kawai ba, har sai da aka zabo masa aka kuma yi masa bada saninsa
ba.
Komai kuma yazo ya kare a kanta, poor her! Saboda anga iyayenta masu karamin karfi ne
aka bata tsoho.

Can anjima kuma Kiki ta saki zancen Prince ta koma bata labarin footballer dinta, apple of
her eyes; TosinAbdulNasir.
Labarin soyayyar Kiki da dan ball gwanin burgewa da ban kaye, domin soyayya ce suke yi
mai tsafta ba tareda suna ganin juna ba sai a hoto da vedio call da Imo. Har lokacin sau daya
Tosin ya ganta, itama sau daya ta ganshi a LA (Los Angeles). Kiki ko shafa labari shuni ce ita
sai haka wurin bada labari. Ga saurin sabo. Koda yake zamu iya kiran al’amarinta da Aisha da
haduwar jini na farat daya.
Haka itama Siddiqah Kiki ta shiga ranta from day 1 ta ji ta kamar kanwarta ciki daya. Don Kiki
irin yarannan ne frank da basu da munafurci ko nunkufurci. In tana son mutum kawai tana fara
son shi ne daga sanda ta fara ganinsa ba tareda wani dalili ba. Kiki is innocent, kwatakwata
bata dauko tsauraran halayen yarbawa na Aunty Murja ba. Washegari Kiki har makaranta ta raka Aisha suka dawo tare da Seun, tace “Aisha kiyi karatu
da kyau kinji, ki fito da 9 credits, in kika yi wannan kokarin, ni kuma zan sa Uncle dina ya kai ki
makarantarmu kiyi irin course dina.
Yayi sponsoring karatun ‘ya’yan marayu ma balle ke diyar kawar Nenne? Uncle AK is a
philanthropher. Yana daukar nauyin karatun marayu da yawa a wurare da dama a ciki da wajen
kasar nan. Kinsan hatta Ex-dinshi Haseenah Mum ta taba bani labarin cewa a irin yawon shi na
a gidan marayu ya daukota”. Aisha dai haka take ta biyewa surutun Kiki, da murmushi da gyada kai, ba don duka take
ganewa ba. In fact, tana yi tana hadawa da yarbanci ko turanci. Daga jiya zuwa yau Kiki ta
ambaci Uncle dinta yakai sau malala gashin tunkiya. Wannan kadai ya nuna (how close) karfin
kusancin da take dashi da Hamma din. Wani mutum da tun bayan komawarshi, ko na minti
daya Aishah, bata taba zama ta ware muhimmin lokaci ta zauna tayi tunaninshi ba.
Da shi da wanzuwarshi da rashin wanzuwarshi cikin rayuwarta duka sammakal. Karshen
yankan kauna an gama mata itakam tunda an rabota da mai sonta da ya san darajar soyayyarta
(Ishaq Nafada).
Amma tasa a ranta komai ma zai zo ya wuce ne kamar ba’ayi ba cikin hukuncin Ubangiji, don
bata ga ta ina rayuwarta data Prince ta zo daya ba. Iyayenta zasu hakura su maidata ga Ishaq
komai daren dadewa, ranar da suka gaji da jiran gawon shanun basarake Hamman da baya da
tabbas. Ta jinjinawa (down to earthiness) din Nenne (halin tawali’un Nenne) da har tayi tunanin
mace kamarta marar zurfin ilmi, mara nasabar sarauta, marar ajin rayuwa irin nasu zata iya
zama mata ga Hammansu Fatima.
Ya Allah kanwarsa Fatima da ‘yar uwarsa Taiwo ma ya aka cika dasu wajen kasaita balle
kuma shi kansa? Ita sau dubu gara mata Ishaq da yake bahaushe/bafillace ba dan kowa ba
akan Bayeraben Prince din. Darajar idon Nenne kadai ya hanata cewa don Allah in ya tafi kada
ya kara dawowa. Tafi jin dadin rayuwa cikinsu da ya bar gidan. Don a dan zuwan Prince gidan hatta numfashi
wuyar shaqa ya koma yi mata. Kwarjininsa ya bi ya cika kowanne sako na gidan Engnr. Idris
Akanni.
Dade kadai ne ya san cewa Siddiqah murna take da komawar Prince, don yafi kowa lura da
reactions dinsu ita da shi, don lokacin Nenne bata gama samun kanta ba, so bata ta tasu ta
lafiyarta take, amma shi yana hankalce da motsin kowannensu, shi kansa Prince ya takaitawa
kansa magana cikin ‘yan uwansa a wannan zuwan da yayi ba kamar yadda ya saba ba.

Daga irin kalaman bakin Nenne na yanzu Dade ya fahimci ta fidda rai akan al’amarin, wato ta
fidda ranta akan auren Prince da Aisha. Jira take, Allah-Allah take Siddiqah ta gama WAEC ta
maidata Gombe, akalla zata cigaba da rayuwa da mahaifiyarta a gefenta. Ita kuma ta fita zargin
kanta na cewa bata kyautawa Siddiqah ba. Don haka Dade ya fara nasa shirin shima don ruguza na Nenne. A wurinsa Aisha tazo cikin
ahalinsa kenan. Aure tsakaninta da Abdulrasheed anyi kenan, ko yace yanzu aka fara daga nan
har gaban abada, bazai yi saken da Siddiqah zata bar Abdulrasheed ba no matter ho worst
things are becoming. Hasalima bada sanin ita Nenne ba shi da mahaifinsa maimartaba sarki sun riga sun yi
shawara, ji da Emir yayi Abdulrasheed yazo har ya tafi bai nuna bukatar daukar Siddiqah ba
yace lallai jikan nasa sai an fito masa ta bayan gida, Emir ya gayawa dansa Engnr. Idris yadda
za’ayi da Prince, yace in ma aljanar ce tare dashi da macen aure ta shiga gidansa alkadarinta
ya gama karyewa, wato sunada yadda zasuyi maganinta cikin sauki.
Don haka yasa Dade ya fara shirin abinda ya dace akan Prince da Siddiqah.
Satin Kiki biyu tare dasu ta koma gidan iyayenta a Ilorin, bata tafi ba sai da tayiwa Nenne
dadin bakin da yasa ta baiwa Aisha kan waya don a baya tace sai ta gama WAEC zata bata. A
cewar Kiki ta yaba da hankalin Aisha tana so zata dinga kiranta akai-akai don neman shawara.
Kuma bai dace a dinga hadata waya da Ummanta ta wayar Nenne ba a barta ta dinga kwana
tana hira da Ummanta tunda yanzu bata kukan. Kuma dai Aisha bata da `BF’ a cewar Kiki da
zai ke distracting karatunta da zancen soyayya.
Nenne ta kalli Kiki tana hararar ta wai bata da kunya, amma maganganun Kiki suka sa dole
ta baiwa Aisha waya tsadadda, ta yarda Kiki na son Aisha.
Su Siddiqah sun fara jarrabawar gwaji wato mock kusan kullum suna waya da Ummanta da
Abbanta suna binta da addu’ar samun nasara (albarkar Annabi).
**** **** ****
​ Watarana Kiki ta kirata tsakar dare daga Ilorin.
“Siddiqah ko kin san addu’ar rufe bakin mutum ya kasa magantuwa akan wani abu?” Dariya
sosai Aisha tayi tace “Kiki wa kuma za’a rufewa baki dungurungum? Wane mai tsautsayinne ya
shiga komar yar gatan Uncle dinta?” Kai tsaye Kiki tace
“Mamana! My Mum. Oh! My Mum is annoying.
​ Aisha tayi maza tace “akul! Kiki daina fadin haka gareta tun kafin mala’iku su rubuta” Kiki
tace “To ya zanyi da Mum dina? Tosin yace zai zo Ilorin, musamman don ya gabatar da kansa
gareta ya gaisheta ya kuma gaida Emir, amma ina tsoron gaya mata, don nasan bazata yarda
ba, yanzu zata hau cewa sai Uncle AK yayi aure, bayan Uncle da kansa ya bani go ahead, har
Tosin yaje ya sameshi a Qatar ya ganshi ya kuma amince da shi.
​ Amma ita sarkin tagwaitaka ta nace sai yayi aure zanyi, sabida Allah Aisha Mum bata
kwareni ba idan ta janyomin na rasa Tosin? Abinda na sani ina son AbdulNasir sosai. Kuma
Uncle din nawa ya amince dashi. Haka kawai Mum zata yimin sakiyar da babu ruwa. Bata san
yawan ‘yammatan dake son Tosin bane”. Muryar ta yanzu gwanin ban tausayi cikin damuwa.
Aisha ta san bayan wauta da gata da suka yiwa Kiki yawa, still da gaske tana neman shawara
da mai hankalin da zai sa ta a hanya.
Ta san ko ta girmi Kiki to da kadan ne, amma hankalinsu da wayonsu ba iri daya bane. She’s
so much infatuated akan Tosin AbdulNasir. Har tana ganin laifin mahaifiyarta akan saurayi.

Irin Kiki duk abinda wada suka yarda dashi ya fada musu dashi zasu yi amfani ba tareda wani
dogon tunani ba. Siddiqah ta nisa, a hankali tace da Kiki cikin kwantar da murya.
​ “Kiki ki dinga addu’ar neman zabin Allah kin ji? Don’t be obsessed with him, ki bi
mahaifiyarki akan duk abinda takeso wallahi zaki ga alfanu a gaba.
​ Kuma ko a kan son da kika ce min Uncle dinki na yi miki zaki iya yi masa solidarity ki
jikirta baiwa zuciyarki abinda take so kamar yadda Mum take so sabida shi, da gaske baza taso
ki yi aure ki haihu alhalin shi bai yi ba, baki son soyayyar twins ga junansu bane musamman in
opposite sex ne (mace da namiji). ​ Nima bana son zaman gidannan, bana son zaman Lagos at all, amma yana iya? Dole
na yiwa iyayena biyayya kuma ina kan yi. Na san ko bajima ko ba dade zan tsinci wannan
biyayyar dana yi musu a gaba ko a kan ‘ya’yana ne.​
​ Ke kinji dadi ma kina tare da ita har gobe (mahaifiyarki) an kuma barki kin gama karatu
kafin ayi miki aure kuma ga dukkan alamu wanda kikeso za’a barki ki aura …..”.
Sai bayan ta fadi hakan ta tuno cewa ta saki layi. Kiki bata san wacece itaba har yau a
gidannan. Bai kamata Kiki taji daga gareta cewa tana da auren Uncle dinta daga bakin ta ba,
idan har Nenne da Aunties dinta babu wanda ya ga dacewar ta sani din ita akan me zata fada?
Amma ina! Aka ce magana zarar bunu ce ta riga ta fita, ta kuma shiga kunnen Kiki-Ruqayyat.
Kiki tayi dan jim, kafin tace.
​ “Kina nufin kina da aure? Ko kin taba yi kenan sister Aisha?”
Ta girgiza kai da sauri tana cewa “Kiki chapter closed, kiyi ta istikhara kina addu’a idan Tosin
rabonki ne, kuma akwai alkhairi a tarayyarku, Allah ya kawo auren Uncle dinki kurkusa kamar
yadda Mum keso, idan hakan ne kwanciyar hankalinta. Kada kimanta kullum tafi Tosin
muhimmanci agareki”. ​ Kiki ta ja numfashi tace “Sister Aisha, my Mum is annoying, wadda take so Uncle ya
aura fa ba wata bace Aunty Haseenah ce, his ex Haseenah Ambursa, koda yake ya so ta acan
baya, amma wallahi yanzu baya sonta, ban dai san abinda ya raba su ba amma anfi ten years
da rabuwarsu, rana daya naga ta dawo jikin Mum dina sun koma shiri, ni nafi Mum sanin Uncle
dina, bakina da nasa yace min shi matansa Hurul eeni ne suna aljannah, me Uncle zai yi da
Haseenah yanzu? Don kawai ya taimaketa?
Tsintacciya ce fa as in ‘yar gidan marayu bata da iyaye shiyasa Nenne bata so.
“Ho Kiki! Shafa labari Shuni!”
Duk da Kiki bata san me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login