Showing 27001 words to 30000 words out of 43117 words
Chapter 10 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf
A satinnan an dinka mata sittiru iri-iri sun kai hamsin daidai jikinta, sittiru masu daraja da zata
dade tana mora.
Firdausi kuma tana tare da Aisha koyaushe tana kara koyar da ita tsaftar jiki yadda ya
kamata da matar aure, don ta raina tsaftar Aisha.
A gidan Nenne ne Siddiqah ta san cewa in za’a kwanta sai an yi wanka da brush na
barci. Don a Gombe bata yinsu take barcinta abinta.
Princess Firdausi Ta koyar da ita yin shaving akai-akai. Tace duk sati biyu ya kamat tayi ba
sai gashi ya taru ba.
Hatta manner din cin abinci tareda jama’ar gida bisa tebir, Nenne bata yin shiru in ta ga
Aisha tayi wani abu ba daidai da su ba, wanda a wurinsu kauyanci ne ko Arewanci, sai ta gyara
mata (in a nice way) yadda bazata ji ta muzanta ba, mostly in suna girki a kitchen suna hira,
bata yimata gyara a gaban su Firdausi. Ta wannan hanyar tunani na farko da ya dade da samun muhalli a tareda Siddiqa ya
goge na cewa duka Yarbawa kazamai ne. Ya Ilahy, ashe a rashin saninta, wasu yarbawan dai
har sun fi wasu hausawa da Fulanin tsafta, kudin goro hausawa ke musu na isgilanci da iya
shege da suke kiransu masu kashi a kwano ko masu tukin tuwo da Duwawu. A hutun karshen makonnan baki suke tayi a gidan yawanci danginsu ne dake zaune a
Lagos da family friends, masu zuwa ganin amaryar Prince, manyan mutane sosai ke zuwa suna
tafiya, ‘yan kasuwa, ‘yan siyasa da ‘yan sarauta da manyan ma’aikatan gwamnati dake da alaqa
dasu Nenne. A zahiri suna mamaki in suka ga ‘yar ficikar yarinyar da aka aurawa Prince
Abdulrasheed da bata ko kai shekaru ashirin ba, in suka fita sai sun gulmanta, Bayerabe da son
tsegumi, kuma babu wayewa irinta kabilu ko ‘yan bokon arewa a tareda ita, (typical Gombe
Fulani girl).
Wasu basa iya shiru ko a gaban Nenne sai sun tanka, cewa “Prince shi ya zabi little
fulani girl haka?” Nenne saidai tayi murmushi tayi shiru bata cewa komai. Jikin Aisha da ake
yawan yiwa ba’ar siranta a wurinta harda sakacin Haj. Zainab ga irin abincin da ta bar Siddiqah
tana ci. Ire-iren abincin da Aisha ke ci duk na kwalam ne, tafi ganewa mai da yaji da kayan
kwalam su agwaluma, dinya, kanya, magarya wanda babu wani sinadarin gina jiki a cikinsu.
In kuma abinci zata ci sai ta shirbineshi da barkono yayi jajir Nenne kan ce Allah ya so ta
bata da ulcer, suma Yoruba na son yaji amma na Aisha is over ace ko abinci aka yi da miya da
nama ita sai ta dibi fara ta sa mata mai da yaji zata ci. Duk wannan enne na kokarin rabata
dasu yanzu. Kai hatta yadda zata dinga dukawa ta gaida Emir da sauran Baffanninsa in taje Ilorin ko sun
hadu Nenne bata barta haka ba sai da ta koya mata dukawar gaisuwarsu ta al’ada, ta maida
kanta TUTOR ga Siddiqah ba Uwar miji ba.
Duk da dai Siddiqah bata nuna wani interest akan abubuwan al’adar Yoruba da Nenne
kullum ke kokarin dorata a kai. A wurin Nenne aure abu ne mai broad perspectives, wanda
cikinsu ya hada da rungumar al’adun juna (embracing each others’ cultures and traditions) don
samun karuwar soyayyar juna, wanda ita Siddiqa a tunaninta bai zame mata dole ba ai, since
she has her own culture data riga ta girma cikinta.
Nenne kuwa ta yarda da cewa in ka auri mutum ka aure shi ne da shi da danginsa da
kabilarsa da iyayensa da dabi’unsa bakidaya, wato dai ba shikadai ka aura ba. shiyasa ta dage
wajen koyar da ita abubuwanda watarana su zasu taimaketa a zama da Prince da danginsa.
Duk da haka Aisha na jin dadin girke-girkennan data ke koyo daga Nenne, don wani ilmi
ne na daban yazo mata, sannan yana keeping dinta busy a gidan har bata zama tunanin gida.
Nenne ta gaya mata in zata maida kai ta dinga cin abincinsu ta maida, shine zai gina mata jiki ta
zama mace. Ta gaya mata cewa Yoruba na amfani da komai na abincinsu (fresh veggies) ne
masu kara lafiya, duka abincinsu kyakkyawan vegetables ne da protein, basa cin abinci saida
isashshen nama da kifi da korran ganyayyaki iri-iri, shiyasa take ganinsu healthy cike da kuzari,
ga su Firdausi nan masha Allah dasu, bul-bul, cif-cif, kamar ka taba jini yayi tsartuwa.
Siddiqa gani take jikinsu Fatima kamar da an soka tsinke zai bule don laushi da kyau.
Kirjinsu tantsan da dukiyar Fulani, bayansu cike da mazauna kamar balan-balan, har bata son
kallon kanta a mudubi a gidan don sai taga kanta kamar kwancen yunwa, har bata son duba
mudubi. Ta maida hankali ga cin ire-iren girke-girken da Nenne yiwa Dade kullum, musamman
da yake tare suke yi ba Femi ke yi ba. Nenne tace mata Hammansu Fatima ma abinda yake ci
kenan mostly wato Brown Amala da Ewedu Soup.
Ta taba gaya mata Hamma baya cin Igbin saboda snails da ake sakawa a ciki. Inda abincin
Yoruba guda daya da baya so a duniya to Igbin ne, don baya cin snails tun yana yaro. Amma
Gbegiri ma yana sonta sosai.
Ta gaya mata shi din ne ma’abocin cin korran ganyayyaki ne a cikin abinci, sannan yana
matukar son WARA.
In ka gansu a kitchen sun hada kai itada Nenne suna hada girke-girke akan cooker
kamar kanwarta dake mata zaman daki, don jikin Nenne baya nuna shekarunta sam. Kullum
tana nan fit and healthy don akan ce jikinta na Fulani Prince ya samu mai boye shekaru da
rashin mummunar kiba. Bata da kiba, kuma sannan bata da rama sam. Jikinta daidai ita kamar
ita ta zabawa kanta.
Da farkon zuwanta tana dan jin kunyar Nenne, daga baya da taga bata da wadda ta fita a
gidan ga sakewar fuska irin na Nenne Sappa sai ta ware ta maida ita kamar Yayarta. Kai
bazaka ce wai danta ne aka aura mata ba kwanaki kadan da suka gabata, ko watakila don ita
kanta Siddiqar bata shaida hakan bane a zahiri, wato bata yarda tana auren dan Nenne ba,
tunda kuwa da idonta bata ganshi ba, sannan da kunnenta bata taba jin muryarsa ba ko
inuwarsa bata sani ba. Don har gayawa Nenne take tanaso tayi kiba da cika irinna su Firdausi.
Nenne tace “good, ai siranta ba abin so bace, haka itama kiba, amma taki kam akwai rashin
‘good nutrition’, to daga yau sai ki cire kabilancinki ki dage da cin su Gbegiri, Oka/Amala, yam
flour/ponded yam, da miyar Ewedu.
Ga kuma kunun farar shinkafa, garin gero, cukwi da aya da dabino dana sa aka niko, zan ke
dama miki kullum kiyi ta sha.
Nina gaya miki har sai kinfi Firdausi cikar ido da cikar kirji, wadannan ‘yan kirgen dangin naki
da aka rasa size din braziyar da zata yi musu daidai, suma su cicciko suyi gwanin ban sha’awa,
gasu dama ‘yan kanana da basa bukatar rigar mama”.
Kunya sosai ta kama Aisha ta kare fuska da tafukan hannunta tana dariya, hakan da Nenne
ta fada ya tuna mata wani abu da ya faru da jimawa sanda Ummanta ta sa muciya ta buge
kirgen dangin data soma, wato ta mayar da nonon, lokacin da ya fara fitowa cikin wata hikima ta
iyayen da. Nan ta hau dariya ita kadai, tace.
“Nenne, ni fa na san dalilin da yasa har gobe ni banida manyan nono, zan baki labari, amma
kada ki gayawa Ummana na gaya miki”.
Nenne tace “umh, I am all ears, amma ‘yar shekaru kusan sha takwas haka bata saka ‘bra’ ai
da mamaki, to ina jinki” ta dakata da abinda take yi ta bada hankalinta tana sauraron Aisha.
Rufe ido Siddiqah tayi da fararen tafin hannunta tana kyalkyala dariyar maganar da Nenne ta
gama yanzunnan, kafin tace.
“Ai wato Nenne sun fito fa da farko, tun ina 13 years, Ummace ta bige su da muciya, lokacin
da suka fara fitowa ta samu muciya ta karanta addu’ar da bansan me ta karanta ba tace "Ya
Allah ba yanzu ba, sai ta kara girma", sai ta buge su da bakin muciyar, daga lokacin suka
koma”. Nenne ta kasa rike dariyarta, don ita bata taba jin inda akai haka ba, kai Hajiya Zainab
sai a barta, saida ta gama dariya mai isarta kafin tace.
“to ita kuwa Umma meyasa tayi hakan ai girma dole ne ga diya mace, fatan dai shine Allah
ya taya mu akan tarbiyyarku, har mu mika ku gidan mazajenku. Fara kirgen dangi da wuri ba
abinda zaisa ba abinda zai hana in lokacin aure ya zo wa mace. Sabida shi aure lokaci ne dashi
ga kowacce mace ba sai sanda ta shirya ba”. Siddiqah tace “ai Ummana bata so ayi min aure da wuri, ga Babana yayi alkawarin da wuri
zai min aure, saboda ya samu jikoki da wuri tuda shi bashi da’ya’ya da yawa, ita kuma Umma
tunda nikadai ke gareta, sai bata son auren wuri gareni, shine dalilin data komar da kirgen
dangin lokacin da ya soma fitowa, tace itama Goggonta Allah ya jikan rai haka tayi mata kuma
suka koma, don in Abbana ya gani zai ce ai kawai na isa aure”. Kai yau cikin Nenne har kullewa
yayi don dariyar da Aisha ke bata, tace “kuma sai gashi hakan bai hana auren yazo miki da wuri
ba, Allah kenan! Mai yin yadda yaso a lokacin da yaso”.
Ita kuwa Siddiqah sai yanzu take jin takaicin abinnan da Umma tayi mata, da yanzu tana
cancada gayu kamar su Fatima, don gani take ko kwalliya tayi bata kyau kamar yadda su
Firdausi ke cika idon mai kallonsu, suna juya jikinsu yadda ransu yake so.
Tun daga ranar Siddiqah ta cire kyankyamin abincin yarbawa, ta bude ciki tana cin ire-iren
abincin da akeyi a gidan, irinsu ‘Afang Soup’ da ‘Ewedu Soup’ da ‘Oka (brown amala), ga Iyan
(yam flour/pounded yam) da 'ékuru' da akeyi da wake’. Duka abinciccika ne masu gina jiki da
kara kuzari. A gefe kuma ga kamun da Nenne ke yi mata da kanta kullum da yamma bata
mantawa har cikin dan lokaci ya fara bin jikin Siddiqah.
**** ***** ****
THEPRINCE
Bayan ya koma Qatar baifi da sati biyu ba aka turashi consultation na aiki a Abu-Dhabi
Kamfaninsu ‘Qatar Refinery’ ne ya tura Engnr. Abdulrasheed consulting wani aiki na sati biyu a
(Abu-Dhabee National Oil Company) don haka yau da safe ya kira Nenne a waya, don ya sanar
da ita, yaso kwarai a satin da za’a shiga suzo masa hutu Qatar yadda ya riga ya tsara tunda
farko, lokacin da Abdulrasheed ya kirata ko fitowa Nenne bata kai ga yi daga dakin barcinta ba
don safiya ce sosai a wurinsu Dade kuma ya jima da fita jogging.
Bayan sun gaisa yadda suka saba shi da mahaifiyarsa, kasancewar baya yiwa Nenne
kowanne yare sai fulatanci, don yasan shi tafi so su dinga yi mata musamman in shi da ita ne,
yarbanci wannan saisu Fatima, sam basu cika yin fulatanci ba sai harshensu na gado. Aunty
Taiwo kuwa dama maganarta duka rabi turanci ne ita saboda mijinta Toufeeq da yaranta su Kiki
shi suka fi yi a junansu.
Yace da Nenne cikin fulatanci “Nenne inata dokin son ku zo wannan watan
gabadayanku keda twins, har Hakeem, muyi hutun Easter dinnan tare duk da babu Kiki. Itama
naso ince ta samemu anan don ta kusa Hutu.
Amma tafiyar aiki ta sameni unexpextedly zuwa Abu-Dhabee sai suka rushe min plan, sai
idan na dawo in sha Allah sai kuzo”.
Nenne tace “to sarkin kanne Uban Hakeem da Kiki. Sune kawai ababen kulawarka iyali
ko oho. ‘Allah hokku sa’a ko ayahi dabbutugo Albarka Annabijo" wato (Allah ya bada sa’ar
abinda aka je nema albarkar Annabi), Ya kuma dafa muku”, sannan ta nisa tace.
“Hammansu bazamu zo ba wannan Easter Holiday din, saidai kai kazo. Am not feeling fine
da zan iya hawa jirgi nan kusa”.
Amma Prince ya riga ya sakawa ransa nan kusa shikam nan kusa bai zuwa Lagos ko Ilorin,
ba don komai ba sai don gujewa fushin Baffanninsa.
Yayiwa Nenne alkawarin zai zo amma sai bayan wani lokaci. Yayi mamaki da bata yi masa
korafin Baffanninsa sun bude mata wuta akan rashin zuwansa ba yadda ta saba.
Sunyi waya da Aunty Murja ma duka a ranar, wadda ke can cikin bacin ran Nenne ta hanata
sanar dashi maganar aurensa har yanzu, balle ta san yadda ya karbi al’amarin ta bangarensa.
Da yake bakinta nata kaikayi saida tace masa “Kehinde!” Yace “Na’am” ta sake cewa “Prince!
Sau nawa na kiraka?” Yana dariya yace “Taiwo! Kin kirani sau biyu, wani abu?”.
“Ka daure kaje gida immediately daka gama aikin da zaka je dinnan”.
Ya nemi karin bayani dalilin kalmar immediately din, don yaji seriousness sosai a kan
muryarta, sai kawai ta kashe wayarta ba tare data bashi amsa ba.
To haka su Fatima ma baki nata kaikayi, kamar sun ci bawon Doya, musamman Princess
Fatima uwar tsegumin gidan bakidaya, komai a bakinta Taiwo ke ji. Har hotunan Siddiqah ta
tura mata.
Amma wane mutum a gidannan Nenne tayi umarni yayi fatali dashi? Ko tasa kara mutum ya
tsallaka? Ko basa so zasu bi. Don kowa na gudun bacin ran Nenne Sappa.
Da wuya tayi bacin rai a cikin iyalinta amma in tayi shi basa ji da dadi, don bata sauka ta
sauki sai kowa yaji a jikinsa.
Yau da ba don Nenne uwarsu bace kuma itace da kanta ta hada auren nan na Prince da
Aisha, da Murjanatu tace an kwari Kehinde dinta, an zubar masa da class a inda bazai kwasu
ba, da aka aura masa Aisha.
Ta fadi hakan ne lokacin data ga hoton Aisha Siddiqa a wayarta.
Ba wai Siddiqah din ba kyakkyawa bace, a'ah don kyau Masha Allah ko makiyinta ya san ta
kere sa'o'inta a kyawun sura. Amma a ganin Aunty Murja kyawun ba shi Prince yake bukata a
halin yanzu ba da shekarun girma suka riskeshi.
A yadda Prince ya kwashe shekarun kuruciyarsa babu aure a ganin ta cikakkiyar mace kuma
kilalliya wayayya preferably ‘yar kabilar Yoruba ce ta dace dashi in har ba Haseenah ba, mace
'yar shekaru akalla Talatin wadda zata kula da komai nasa, ta tarairayeshi ba hijabin kunya,
sannan ta jiyar dashi dadin aure da ya jima bai sani ba, amma ba dai shi Prince a halin yanzu
yayi zaman rainon ‘teen’ ba.
A yadda Fatima ke fasalta mata abubuwan da Siddiqa keyi a gidansu na kauyanci da kuma
hotonta data gani ba maraba da ‘yan tallan nono a kasuwar Gombe. Don haka zamu iya cewa,
from Day 1, Aunty Taiwo bata yi na’am da dacewar Siddiqah da Prince ba a matsayinta na mafi
kusanci dashi data fi kowa sanin likes and dislikes dinsa. Ko dalilinta ya isa dalili? Ko kuma na son zuciyarta ne bazan iya cewa ba.
Dan adam din kenan, har kullum halinsa sai shi. Marar godiyar Allah marar tuna baya. In
banda haka sai muce ko dai Aunty Murjanatu ta mance yawan shekarun dan uwanta Prince
Abdulrasheed dinne? Da dadewarshi yana Polo babu aure, kuma har gobe bashi da niyyar yi?
Maimakon Taiwo tace dan uwanta ya tsinci dami akala, na samun yarinya danya sharaf (in
her teens) wadda bazai sha wahalar tankwarawa zuwa duk yadda yake so ba. A ganina,
Aisha-Siddiqah ce za’a ce ta kwaru da auren Prince Kehinde, wanda a haife sai mu ce ya
haifeta, ko mu ce ya kusa haifarta da yayi aure a farkon samartakarsa, amma ba Prince za’a ce
an kwara ba a logical reasoning. Taiwo-Murjanatu, bata duba duk wannan ba, ji tayi kamar ta
fashe don haushi da taji cewa matar da aka aurawa Prince ma wai ko sakandire bata gama ba,
sannan ba ‘yar kowa bace a Gombe, kawai haduwar kan titi ne ita da Nenne. Sai taji fit! Matar
Prince bata da muhallin kima a gunta. Wani abunda zai baka mamaki a lokacin ma sai
Haseenah ta dawo ranta. Wadda a lokacin suna tare a gidanta ta kawo mata ziyara har
Lancashire. Wannan ba shine zuwan Haseenah na farko gun Aunty Murja ba. Don haka a wurin
Aunty Taiwo ma kamar danginsu na Ilorin, zamu iya cewa Siddiqah bata samu maraba ba,
amma ba yadda zasu yi tunda zabin iyayensu ce.
Taso kwarai ace da Prince bai auri Haseenah ba, to zama ya