Showing 33001 words to 36000 words out of 43117 words

Chapter 12 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

Ko lura da ita bai yi ba, don gabadaya hankalinsa yana kan Mamansa.
“Here comes THE PRINCE!” Zuciyar Siddiqah ta ta gaya mata cikin whisper. Alhalin har
yatsun kafarta kakkauran takalminsa ya dan taka mata kuma ta ji zafi da radadi, amma da yake
hankalinsa baya jikinsa bai lura ba, kacokam hankalinsa ya dauku kan mahaifiyarsa dake
kwance saman gado, baima kula da ya dan taka yatsun mutum ba, yama dauka inuwar daya
cikin twins ce a zaune gaban Nenne.
Sai ga Nenne ta bude ido a hankali bayan ta shaki turarensa, kamar tana jiran isowarsa kafin
ta bude ido, sai idanunta cikin na Abdulrasheed.
Prince yasa tausasan yatsunshi ya damke hannun Nennensa sosai, yana fadin "Nenne
please don’t leave us..... gani nazo. My Nenne get well soon I beg you, duk abinda kikeso zan
yi, koda barin Polo ne dungurungum, na rantse in har yanzu ba kya so daga yau na daina! Na
kuma dawo gida kenan!!". Nenne ta lumshe ido ta bude, ta tabbatar Abdulrasheed ne a gabanta, ba cikin mafarkinsa
take ba, yadda yayi ya zo haka cikin gaggawa shikadai ya sani. Ta damke hannunsa itama cikin
nata, ta nemi ciwon da take ji ta rasa, tana kokarin juyawa idanunta suka fada kan
Aisha-Siddiqah. Wadda ta ja can gefe ta tsaya duk ta sha jinin jikinta cewa Prince Abdulrasheed ne.
Siddiqah ta sunkuyar da kai, lokacin da Nenne ke yafitota da hannunta da Prince bai rike ba,
ko dagowa kasa yi tayi, don jikinta ya gama bata. Hamman gidan ne ya iso.
In ka lura zaka ga yadda jikin Aisha ya dan dauki rawa da ‘yar karkarwa. Nenne ta juyo saitin
da take tace Siddiqah matso nan kusa dani. Ga Hammanku kingan shi ya zo!"
Da hanzari Siddiqah ta dago, anyi sa’a shima Prince ya dan cira ido ya dubeta. Suka hada
ido. Siddiqah taji gabanta ya fadi, shima kuma Prince haka yaji. Saboda nauyin igiyar aure ba
wasa bane. Amma dai Prince ya dake ya cije faduwar gaban data sameshi a lokacin tunda
baima santa ba. Da kailula Siddiqah ta iya cira kafa ta isa ga Nenne, ta tsaya a gefen Prince suka jeru gaban
Nenne, jikinta har lokacin bai daina bari ba.
Abdulrasheed ya juyo gefensa a hankali yana kallon bakuwar fuskar mai jinyar mahaifiyarsa
wadda Nenne ta kira da suna Siddiqah.
Wadda da farko sabida rudun da yazo a ciki, tun dazu ya dauka Firdausi ce a zaune a

gefensa.
Sai ya juyo gareta sosai, ya bude manyan maganansa masu salki da haske da wani irin sheki
na musamman a cikinsu, yana kallon bafullatanar yarinyar.
A idonsa bata fice sa'ar Kiki ba. Idonsa ya gano masa tarin kuruciya da innocent looks irinna
Kiki a fuskarta. Amma cikin dangin Nenne kaf bai santa ba.
Nenne bata bashi damar gama tunanin inda ta samo yarinyar ba ta soma shaquwar dake
bukatar ruwan Sha, irin na wadanda aka yiwa CS.
Don haka da hanzari da zafin nama Prince ya durfafi firjin dakin da saurinsa.
Amma ko kafin ya juyo... Siddiqa sarkin zafin nama ta rigashi da nata irin zafin naman, ta
dauko robar ruwan Faro akan lokar gado ta bude ta kafa ma Nennne a baki. Saida ta sha sosai
ta koshi shakuwar ta lafa mata sannan ta dauke robar daga bakinta, Nenne ta koma ta kwanta
ta rufe idanunta a hankali ta barsu. Dade ya murdo kofa ya shigo dakin. Ya tadda Prince da Aisha sun kafa ma Nenne ido,
kowanne da gorar ruwan Faro a hannu. Siddiqah ta manta yadda ake gaisuwa sakamakon
nauyin igiyar aure na wannan bafillacen sardidin bayerabe dake tsaye gefenta da yazo nan take
yayi mata dabaibayi, ta san dai ana gaida babba a ko’ina aka ganshi, Ummanta tayi mata
wannan tarbiyyar, amma ta rasa dalilinta na kasa gaida Hamma Prince.
Shigowar Dade dakin ne ya ceceta domin ya bata damar shaqar numfashin da ya kasa ratsa
huhunta yadda ya kamata tun dazu, sakamakon inner feelings na wanzuwar Prince a wurin da
take ji a ilahirin jikinta.
Aisha tayi ta maza ta amsa sallamar Dade idonta a kasa, muryarta na dan shakewa. Sai taga
kawai bari tayi amfani da wannan damar ta fice daga dakin, zai fi mata sauki fiyeda cigaba da
tsayuwar rashin sakewa kusa da Prince, ta kama tafiya ta nufi kofa da zummar fita reception na
asibitin ta zauna, ko ta samu damar jan numfashi ta koshi, kuma ta basu dama su gaisa sosai
shi da mahaifansa.
Amma sai Dade yace “yaki Aisha, zo nan ki gaida Yayanku Abdulrasheed kinji, sai kije Seun
yana waje ya kaiki gida ki yi wanka da sallah ki huta, ki ci abinci don nasan rabonki da abinci
tun jiya, tunda ga Abdulrasheed ya zo, shi sai ya karbe ki jinyar.
Zuwa dare sai Seun ya dawo dake ki kwana shi ya koma.
In kuma su Fatima ma sun iso kan magariba kina iya zamanki a gida sai gobe da safe kya
dawo”.
Daga bakin kofar da take tsaye ta russuna da irin durkuson yarbawa ga manya ta soma
gaisheshi, wani irin innocently bewildered, ba tareda ta dawo cikin dakin ba, muryarta na fita a
nitse, a ladabce, tana kuma dan shaking haka, cikin fadin,
“Barka da zuwa HAMMA ABDUL. Yaya hanya? Allah ya huta gajiya ya baima Nenne lafiya”.
Prince AbdulRasheed dai ya rasa a yanayin da gaisuwar tata ta riskeshi, yana cikin wani hali
ne na juyayin halin da mahaifiyarsa ke ciki, tunanin halin da Nenne ke ciki yasa baya fahimtar
komai sosai yanzu. A halin da yake ciki yanzu bashi dako muhallin da zai iya amsa wata
gaisuwa daga kowa in har ba ya ga Nenne ta mike akan kafafunta ba. Don haka bai amsawa Aisha ba. Ya bita da kallo kawai da manyan maganansa da suka dan
kada.
Sai Aisha tayi amfani da shirun nasa tayi ficewarta. Kallon idanun Prince kadai ya nuna mata
bai santa ba sai yau, kamar yadda itama yau ne ta ganshi gani na farko, bayan auren watanni

akalla hudu, kuma ganin nasa ya hargitsa nutsuwarta da tunaninta, don yadda ta zace shi ba
haka ta ganshi ba.
Tayi tsammanin ganin irin katon bakin bayerabe. Sai taga ba haka ba, wani sardidin matashi
ta gani tsaye a gabanta mai wadatar lafiyar jinin jiki da koshin lafiya da kuzari, ingarman jiki
gareshi irin dai na ‘ya’yan sarakunan Najeriya.
Amma me? Bata ga wani gurbi a fuskarshi na ya santa a matsayin matar shi ba. Gashinan
dai emotionless. Ba wani reaction da ya nuna mai nuna ya santa ko sanayyar miji zuwa ga
matarsa, wani abu data dade tana tambayar kanta “anya Hamma dinma ya santa?” yau dai ta
yarda ko a fuska bai santa ba shima. Itama bata ji komai game dashi a ranta ba bayan ‘yar faduwar gaban data samu daga
ganinsa na farko yana shigowa, Hamma ya bayyana sabani ga tunaninta. Fuskarsa kadaran –
kadahan, wato ba yabo ba fallasa a lokacin da suka hada ido, wato dai kallon da kake yiwa
wani da ka fara gani yau aka nuna maka ya sanka kafin ka ganshi, amma bayan wannan babu
abinda Siddiqah ta iya ta fahimta a tare da facial expression dinsa.
Dade kuwa binsu yayi da kallo a sace su duka biyun yana kokarin karantarsu, har Aisha ta
fice daga dakin asibitin da ‘yar sassarfa, dogon maroon kala hijabinta, yana binta yana jan kasa.
Seun, ya daukota sai gida. Ta bude ta shige dakinta har da tuntube, ta kulle kanta ta fada
toilet ta sakarwa kanta shawa mai dumi tayi wanka sosai, daga bisani ta daura alwallah ta dauro
towel a kirjinta wanda ya sauko har saman cinyoyinta ta fito.
Tana idar da sallah Princess Fatima da Princess Firdausi suka shigo dakinta a tare, suna
tambayarta ina Nenne. Saukarsu kenan daga filin jirgi suka biyo taxi suka iso gida.
Siddiqah ta gaya musu Nenne na asibiti babu lafiya yanzu ta dawo daga can, Seun yana
waje ai, shi ya dawo da ita, tace su je ya kai su ya san dakin da Nenne take. Don ita Dade yace
ta dawo gida tayi wanka sai dare zata koma in ta girka abincin Nenne.
A firgice Fatima ta dubi ‘yar uwarta Firdausi, itama ta dubeta, sai suka juya da gudu cikin
razani, da sauri suka fice.
Saddiqah ta cewa ranta tunda dai duk ‘ya’yan Nenne sun hallara akanta, to komawarta
asibitin a daren yau bashi da amfani kada ta takura musu, musamman zasu so su sake da
Yayansu da ya jima baya nan, a ganinta presence dinta a wurin zai iya rage musu jin dadin
haduwa da juna ko ta hanasu sakewa yadda suka saba. Don haka bata koma asibitin a daren ba. Seun ta shiryawa abinda Nenne zata iya ci ya tafi
dashi, faten dankalin turawa ne tayi mata mara yawa da yaji ganyen alayyahu da hanta da
koda.
Sai washegari da safe ta sake shirya karin kumallon mara lafiya, ta yi wanka ta shirya tsaf
cikin ruwan goron atamfa mai glitter din silver da ratsin baki ta dauki abincin a Kwando ta tafiwa
da Nenne. Seun ya dauketa sai asibitin.
Lokacin Fatima da Firdausi kadai ta tarar a dakin. Prince ya je gida yin wanka shima don
anan asibitin ya kwana. Don haka sosai ta sake cikinsu Fatima suka gaisa ta tambayi mai jikin
da gajiyarsu ta biki a Ilorin, daga nan ta karbi komai a hannunta na kula da Nenne. Su kuma
suka sakar mata suka fara shirin tahowa gida, dama Nenne tafison Aisha tayi mata komai, ta
kan ce ai ta fisu zafin nama.
Aunty Murjanatu ma daren ranar ta baro UK zuwa Lagos don duba jikin Nanne.
Ko don taron dangin da iyalin Engnr. sukayi a asibitin yasa dole likita ya baiwa Nenne

sallama a washegari, musamman da ya kasance surgery din da aka yi mata na zamani ne
kuma yayi kyau sosai baya bukatar doguwar jinya, in yaso ta cigaba da shan magani da ganin
likitanta a gida.
Sun dawo gidan dukkansu a tare, a mota guda, in ka cire Prince da ya biyo motar Dade. Nan
gida ya kacame da hidima, masu aiki sai shige da fice suke yi suna kaiwa da komowa don
wadata al’ummar gidan da abinci da abubuwan bukata da tsaftace shi.
Prince tun daren jiya ya zama curious sosai akan bafullatanar yarinyar dake jinyar Nenne a
asibiti, yana hankalce da duk irin kyakkyawar kulawar da take baima Nennensa da dukkan
nutsuwarta da attention dinta in tana gaban Nenne itace kawai a gabanta, ko uwarta ce sai
haka, kuma yaji dadi sosai a ransa. Ya cika da son sanin ko wacece yarinyar. Kwana biyu kacal da dawowarsu Nenne ta kara warwarewa, duk da bata bar gado ba amma
tana iya cin komai da Siddiqah ta sarrafa musamman don ita.
Yau da kansa ya tambayi Nenne bayan fitar Aisha daga dakinta, bayan ta gama bata
maganin safe. Tana kokarin fitowa shikuma yana shigowa. Sai ta rabe cikin ladabi ta bashi
hanya ya wuce ciki, ta gaisheshi a gajarce yana amsawa yana karasawa ciki.
Prince ya zauna a gefen kafafun Nenne, suka gaisa yadda suka saba, ya tambayeta ina ke
mata ciwo yanzu Nenne tace babu sai bayanta, shima din saboda yawan kwanciya ne. Yau dai
Prince ya kasa shiru har ta kai da ya tambayeta.
“Ni Nenne ‘yar waye wannan kika samu haka mai kokari a kanki da nutsuwa, sannan ga
hankali da ladabi haka?”
Nenne taji dadin furucinsa, a lokaci taga ya kamata tayi masa bayanin kome ke akwai, don a
yanzu taji karfin jikinta zata iya daukar reaction dinsa.
Tayi sassanyar ajiyar zuciya tace. "Abdulrasheed Aisha matar ka ce fa. Itace matar dana
zabar maka a duniya da lahira. Cikakken sunanta “Aishah-Siddiqah Yunus”. Ita muka zaba
maka nida mahaifinka da albarkar Kakanka Emir.
Itace matar da muka aura maka baka nan, kusan watanni hudu kenan tana tare dani tana
jiran zuwanka.
Kayi min biyayya yadda Aisha-Siddiqa ta yiwa iyayenta, ka zauna da ita cikin kauna da
amana ko bayan raina".
Nan Nenne ta koro masa labarin asalin haduwarta da Haj Zainab da yadda komai ya wakana.
​ Abdulrasheed ya rasa tsakanin mafarki da ido biyu wanne yake ciki. Don jin abinda
Nenne ke fadi yake kamar almara mara yuwuwa. Prince Abdulrashheed ya yi shiru yana jin
bugun zuciya na wani lokaci kamar ruwa ya cinyeshi.
“Aure? Aure? Aure? Mata? Gareshi shi Abdulrasheed Idris Akanni Kehinde din? Ko kuwa dai
wani ne daban da ya sani mai irin sunansa Nenne ke nufi?” amma a yadda tayi maganar nan
she seriously mean it.
Ba shiri ya yiwa Nenne sallama yace zai je yayi sallahr walha, ba tareda ya tofa komai akan
muhimmin zancen Aisha data gama yi masa yanzu ba.
Ai kuwa tun daga lokacin Prince ya daukewa Aisha wuta, 'yar gaisuwar ta da yake amsawa a
mutumce da karsashi in ya zo ya tadda ta tare da Nenne ya koma baya amsawa ma.
A kwanaki biyun nan kullum zaka samu ‘ya’yanta sun zagayeta amma Siddiqah taki zama a
cikinsu musamman bayan zuwan Aunty Murjanatu (Taiwo), da irin tarbar data samu a wurin ta,
sannan da dauke mata wuta da Hamma yayi lokaci guda, ba tare data san ba’asin abin ba. Don

wani sabon daure fuska ya koma yi mata. in kuwa ta shigo dakin Nenne yana ciki to zai fita
yace ma Nenne yana zuwa. Hakan yasa duk ta takura, ta fara killace kanta a dakin ta zuciya
babu dadi.
Amma hakan baisa ta fasa zuwa ta yiwa Nenne hidimar data saba yi mata ba, ta bata
magungunan ta, ta gyara mata gado ta bata abinci ta killace mata daki. In ta gama sai ta bar
musu dakin, ta daina zama sam a dakin ko a falo ta koma nata dakin kawai, ko ka sameta a
kitchen tana taya Femi da sauran masu girkin gidan shirya abinci. Nenne ta fiso Siddiqa ta dinga zama a cikinsu, bata son ware kanta dinnan data soma yi
wanda ta lura saboda Prince ne, amma taga yaran nata kamar sunfi gamsuwa da hakan da
take yi musamman Aunty Taiwo wadda ko bude ido bata son yi taga Aisha a cikinsu, ba kuma ta
son yiwa kowannensu korafi akan Aisha don tserar da martabar Aisha din a idanun su kada su
rainata, amma dai ta gane babu wanda ya damu da zamanta cikin gidan banda Firdausi,
musamman bayan zuwan Aunty Murja duk sun kara ja baya da Aisha.
Kannenta sunata murnar zuwanta kamar me don Aunty Murjanatu ta dade batazo Lagos ba.
AbdulRasheed, Murjanatu, Fatima da Firdausi sun hadu yau sun saka Nenne a tsakiya kowa na
bata labaran da suka shafe shi da harshen da yafi so, masu yarbanci na yi haka masu turanci,
amma Nenne da fulatanci take mayar musu. Can na hango Prince AbdulRasheed a gefe yana cin “WARA” akan wani ‘royal plate’ mai
ruwan gold, wadda yasa Femi tayi masa, ya takaitawa kansa yawan magana a cikinsu yanzu,
ba don komai ba sai don tunanin yarinyar da aka kira matarsa ko tana inama? Baya son wani
dan adam ya shiga takura saboda shi, ya kuma lura zamansa a gidan ya takura Siddiqah din,
don haka ya sakawa ransa komawa da gaggawa ba tareda ya batawa kowa rai ba.
A rashin sanin dukkansu su suna hira ne, Prince kuwa yana danna waya yana yiwa kansa
booking flight tunda dai jikin Nenne masha Allah Alhamdulillah, bai ga zaman me zai yi ba
kuma.
Kwatakwata saboda shaukin haduwa da juna sun manta da wata Aisha kamar ma babu ita in
existence a gidansu, to basu saba da shigowar bare cikisu ba. Hatta Princess Firdausi mai dan
damuwa da Siddiqah yau ta manta cewa tana gidan sabida murnar zuwan Aunty Murjanatu da
tarin tsarabobin data kawo musu daga UK. Wannan abu ya damu Nenne, kuma ta lura itama Aisha din tafi son zaman dakinta yanzu ko
meyasa? Ko dai Hamma yace mata wani abu ne? Bata yarda ta zauna a cikinsu in Hamma da
Murja suna falo, tun dawowarsu gidan daga asibiti.
Nenne ta kasa shiru ganin sun gama rabon tsaraba a junansu ba wanda yace ga ta
Aisha-Siddiqah. Maganar Asoebi ma suka koma yi wanda zasu yi na bikin kawar Fatima yar
Sarkin Ibadan, suna rokon Hamma ya kawo kudi masu kauri.
Ko kula su bai yi ba domin hankalinsa ya dauku ga abinda yake yi a wayarsa yanata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login