Showing 21001 words to 24000 words out of 43117 words

Chapter 8 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

nashi wannan ya cafe.
Baba Barau yafi kowa zafi, shi baya hadawa da lallashin ma. Cewa yake ta kara fadin Kalmar
yarbawa ko bayerabe yanzu ya kumbura mata baki. Malam Yunus shi ke lallashinta, yana gaya
mata kaddadar kenan data hado Hajiya Zainab da Hajiya Sappa a aikin Hajji, wato kaddarar
aure a tsakanin ‘ya’yansu.
Kaddara mai kyau, wadda aka kullata a gaban Ubangiji a dakin Allah kan dutsen Arfah mai
alfarma.
Domin Umma ta gaya musu addu’ar data ji Haj. Sappa nayi a kan dutsen arfah. Ta ce tun a
lokacin ta fada a ranta baiwar Allah inama zai amince da Petel dina! Ko ba komi addu’arta da
tsarkin zuciya tayi ta, kuma sai ta riga ni furtawa kafin ni in furta nawa fatan.
Ina kara fada miki cewa ban ganshi ba, ban taba ganinsa ba ko a hoto ban kuma taba jin
muryarsa ba, amma shi na zaba miki a matsayin miji Petel”.
Aisha ta saka kuka tana cewa “Umma karatuna, Umma makarantata shikenan bazan gama
aji shidda ba?”

Malam Yunus yace “Aishatu ni malamin makaranta ne kin fi kowa sani, na san muhimmancin
ilmin diya mace, ko bana raye bazan bari a aurar dake a inda za’a tauye ki ta fannin ilmi ba. Ki
bari ki samu lafiya ki barwa Allah komai, shi zai iya miki kinji ko?”
Har dare suna kanta, kuka da sheshsheka har da jijjiga don kuka. Hawaye ya hade da
majina. Saida likita Umar yayi mata allurar barci suka samu lafiyarta.
Washegari da safe data tashi nurses suka bata maganin ciwon jiki da Panadol ta sha. Umma
ta hada mata tea mai zafi da kauri shima ta sha. Wajejem karfe sha biyu na rana yace zasu iya
tafiya gida sannan yace da Siddiqah ita kadai.
“Babanki ya bani tausayi Aisha, ki duba yadda ya damu da halin da kike ciki, jiya ya sameni a
ofis ya gayamin yafiso yayimiki abinda kikeso amma yana ganin kimar wannan baiwar Allah, kiyi
hakuri kiyi masa biyayya kinji bazaki tabe ba”.
Ya kara da cewa “one more albishir, Yarbawa fa sun fi Fulani iya soyayya Siddiqah”.
Siddiqah ta harareshi sannan ta gyada kai, tana tsane hawayen idonta, Umma kuma na can
tana tattara ‘yan kayansu batasan me Dr. Umar ke fadawa Siddiqah ba wanda shi fisabilillahi an
yi masa riga malam masallaci ne tuntuni yana matukar son Siddiqah, amma da yaji ko
sakandire bata gama ba shiyasa ya dakata, don shi kadai take gani a matsayin likita duk sanda
tazo FMC. Umma tazo inda suke sukayi sallama da likita ta kamata ta sakko daga gadon suka
wuce zuwa mota inda malam Yunus ke zaune cikin motar shi Toyota Corolla yana jiransu.
Ko kafin su iso gida, an sauke buhunhuna da katon katon na kayan abinci daga gidan Sarkin
Gombe. Siddiqah ta wuce uwar dakin Ummanta ta kule a karshen gadon Umma bata ko kula
kannen iyayenta dake tsokanarta ba, wai ciwon aure take yi ai normal ne. Addar Kumo da yake
mijinta bai jima da rasuwa ba, tabi Siddiqah har dakin Umma tace da ita, “to ni ki bar min
Bayeraben mana? Shashasha jikan uban kasar Gombe ne ta fannin uwa, ni inasonsa tunda ba
wani tsufa nayi ba”. ta kara da cewa (cikin jin takaicinta) “Su Indo! An tako arziki ana kokarin
fatali da shi da gangan”.
Siddiqah kasa shiru tayi tace “Adda wallahi Allah na bar miki bayeraben dari bisa dari kuma
da zuciya daya, koda Ishaq ba zai aureni ba ai na fi karfin auren bayerabe jikan oduduwa”. Sai
jikake gab! Umma data shigo ta gabje bakin nata.
“Inace dazunnan Babanki Barau yace kada a kara jin kalmar nan ta kabilanci daga bakinki?”
Siddiqah kuka ya koma sabo, bazata iya tuna (when last) Umma ta kai hannu jikinta ba sai
yau. Itace ta fari itace auta tsakanin ta da Umma sai soyayya. Sai yau akan Bayerabe dan
kawarta. Tayi kuka-tayi kuka ta gode Allah bata kara tankawa kowa a gidan ba. Daga bisani
kuma barci ya dauketa. Data farka da la’asar da kyar Addar Kumo tasa ta tayi wanka shima duk rabi ita ta cuda mata
baya Siddiqah na rufe kirjinta wai kada Adda ta gani. Wannan abu ya kara kular da Siddiqah
don tayi tayi Addar ta fita ta bata wuri tayi wankan da kanta taki, tace na san biji-biji zaki yi, gara
in cuda ki da kaina, da aka haife ki ma ni dinnan nina cude ki, har yaushe kika yi girman? Ina
abin yake da zan gani wai maye ya ci jinjiri kirji kamar ‘ya’yan goriba? Haka in kin haifo mana
jikan Uban Kasa ni zani har kasar Yarbawa in sake wanke ki fes da runhu da ganyen darbejiya”.
Kabakin abinci iri-iri aka dinga fiddawa daga gidan su Siddiqah da soyayyen naman Sa
zuqu-zuqu akai, wanda aka saka cikin abincin ya wadata. Lemuka (soft drinks) kamar a wanke
tsakar gidansu Aisha dasu. Surutu iri-iri a Jeka da fari, don basu bayyana neman auren ba sai
bayan daurin auren aka bayyana kowa yaji.

Wasu ma sun ce Uban kasa ne da kansa wato Yayan Nenne Sarki mai ci a yanzu Abdul
Yasar Jalloh Umar ya auri Aisha-Siddiqah. Duk kuwa da cewa ana kishin-kishin wai sarkin Ilorin
ne da kansa ko babban dansa. Shaci fadi iri iri musamman daga gidansu Ishaq. A lokacin shi
Ishaq yana can Abia state yana bautar kasa babu wanda ya sanar dashi daga gidan su. A kwana biyun Aisha ta dan kwantar da hankalinta, amma bata fitowa daga daki. Adda tayi
mata kwalliya amma iyakata uwar dakin Umma. Ko falo bata zama. Musamman da Malam
Yunus jiya da daddare yazo har dakin Umma ya sameta, ya bata kunshin balangun da ya shigo
mata dashi mai zafi da ruwa-ruwa, don yasan ko abinci ba sosai take iya ci ba, sai Umma ta
zauna ta bata a baki, shima loma uku take yi tace ta ko shi.
Malam Yunus ya zauna a gefen gadon da Aishah take kwance, yace da ita “kwantar da
hankankalin ki kin ji Indo?
Dazu nayi Magana da Hajiya Sappa kan makarantarki, ko zasu mana alfarma su bari ki
karasa kafin ki tare, tunda term biyu kadai ya rage miki? Tace kada in damu, gtana sane da
wannan, zasu wuce dake gidanta a Lagos ne daga Ilorin, in an kai ki kin ga dangin mahaifinsa,
Kakansa ya ganki yasa albarka, amma a gidanta zaki zauna har sai kin zana WAEC da NECO
zaki bari ki tare a gidan mijinki”.
Wannan albishir ya dan faranta ran Siddiqah.
Ba’a tashi drama da Siddiqah ba sai a washegari da ‘yan daukar amarya suka iso da hantsi
ido na ganin ido daga masarautar Gombe, tareda hamshakan dangin Abdulrasheed mata daga
Ilorin. Matan Baffanninsa ne su duka tara da dangin marigayiya kakarsa Olori Murjanatu, wadda
ta haifi Waziri Idrisu, su uku suka zo daban, suka hade da mutanen Ilorin suka taho Jeka da fari
a manyan motoci Hummer Jeep bakake wuluk masu tinted.
Raba Aisha da Ummanta kadai abin kallo ne domin wani ‘show’ ya koma, don saida aka boye
Umman aka iya fitarda Aisha daga gidansu zuwa fadar Gombe, tare da Goggonninta su Addar
Kumo, da Baba Barau da kansa a gidan gaban motar a matsayin uban aurenta kamar yadda
yake a al’adar su dole a yi mata uban aure. Nasiha iri iri babu wadda iyaye da ‘yan uwa da baba Barau basu yiwa Aisha-Siddiqah tun
daren jiya ba. ko ta dauka ko bata dauka ba dai ta ji su.
A gidan Sarkin Gombe a dakin Nani Ummana wato Kakar Abdulrasheed data haifi Nenne
Sappa aka kai amarya da iyayenta, Nani duk da ta tsufa sosai amma kasancewar 'ya'ya na kula
da ita ga rike ibadah tsufa baisa ta rikice ba, tsaf take, cikin nutsuwarta, ita ta amshi amarya da
iyayenta inda aka wadatasu da nau’I nau’I na kayan abinci na alfarma da abin sha gwargwado.
Daga bangaren matan Sarki na yanzu wato Yayan Nenne Uban Kasa Abdulyassar wanda shi
ya gaji mahaifinsu duk an kawo kabakin abinci iri-iri na sarauta.
Da daddare ne aka kai Aisha har turakar uban kasa yayi musu addu’a mai tsayi, inda yace da
ita suna mata maraba da shigowa masarautar Gombe. Suna mata fatan alkhairi mai yawa da
fatan bada jimawa ba ta cika musu gida da 'ya'ya.
Sun kwana a gidan Sarki karkashin kulawar Nani Ummana da hadimanta sai washegari
Nenne da wasu daga ‘yan uwanta da iyayen Abdulrasheed mata da suka zo daga ilorin suka
dauki amarya suka wuce Ilorin da ita ta jirgin sama, don a kaita ga Emir, da kuma dangin
mahaifin sa da da yawa basu ma san da zancen auren ba. Abinda zai baka mamaki hatta Taiwo
bata san komai ba. Nenne da Dade suna ta boyewa, Taiwo itace kunnen Abdulrasheed shiyasa
suka boye mata kada su bata musu shiri, kuma cikin ikon Allah babu wanda ya kira ta a kan

maganar don ta tafi UK tare da mijinta bayan y agama hutunsa.
Da yawa cikin family din su ma basu sani ba, banda matan baffaninnsu da suka je Gombe
dauko amarya.
Princess Fatima da Princess Firdausi kuwa suna can gida Lagos, basu san meke gudana ba,
sun dauka Nenne ta tafi mayar da Aisha wajen iyayenta ne kawai, daga nan zata ga gida ta
dawo, basu san ana can ana bidirin auren Hamma (Prince) da Aisha a Gombe ba tare dasu ba.
Duk abubuwa na al’adar su na karbar amarya an yi wa Aisha-Siddiqah a Ilorin, aka kuma
kaita ga Emir. Sarki Abdulrasheed dan Abdullataeef Akanni, ya dade yana musu addu’a itada
Kehinde ya kuma baiwa Aisha kyautar zoben zinare mai daraja a cikin battarsa, kyauta ce ta
bajinta da sarki ya dade baiyiwa kowa ba. domin kuwa zoben na marigayiya Olori Murjanatu ne
da ya gada.
A kofar fitowarsu daga turakar Emir ne mayafin Siddiqah ya dan zame, fuskarta ta bayyana
sai a idon Bisola. Bisola ta cika da mamaki, wannan kamar abokiyar fadanta Siddiqah Yunus. Ta
tambayi ta kusa da ita aka tabbatar mata daga Gombe aka aurota. Bisola sai da ta san yadda
tayi ta kutsa cikin mutane ta isa har jikin Siddiqah wadda ke rike cikin hannun Adda Magajiya, ta
sunkuya daidai kunnenta ta ce “an fadi ba nauyi. Aisha Sadiqqah! Kece kuma kika bige da
auren dan sarkin yarabawa?”
A firgice Siddiqah ta dago sai taga Bisola Akanbi. Bisola ta kyabe baki ta ce “dama an ce
mutum bai san inda ranarsa zata fadi ba. Sai a koyi kiyaye harshe acan gaba”. Ta murguda baki
ta kada ido ta wuce cikin ‘yan kallo.
Kafin su wuce Lagos kusan duk masarautar Ilorin sun samu labarin auren. Masu mamaki
nayi masu jin haushi da takaicin an rasa wadda za’a baiwa Prince duk cika da batsewar
masarautarsu sai diyar fulanin arewa na yi, kuma wai ba ‘yar sarauta bace diyar malamin
sakandire ce, ko daga nan Aisha Siddiqah bata samu wani maraba sosai daga dangin mahaifin
Prince ba.
Musamman da ba wani shahararren biki aka yi mata ba irin wanda aka saba yi a gidan, ba
kuma angon, kuma babu danginta masu yawa da suka nuna ita mai yawan dangi ce, sannan
kowa ya tabbata Prince Kehinde, bai san ma ana yi ba. Rabonshi da kasar shi an doshi watanni
uku kwarara yanzu. Sai bayan sun koma gida Lagos ne an kai Aisha dakinta na da, an kai mata duk abinda zata
bukata sannan Nenne ta samu nutsuwar zama ta kira babbar diyarta Taiwo a waya, dake
Lancashire a lokacin tare da maigidanta.
Bata san cewa kafin ta kira ta tuni Fatima ta kira Aunty Taiwo din cikin tsegumi da mamaki,
wai Anti Bisi (matar Uncle dinsu Malami Uban Doma) ta gaya mata sunje Gombe dauko
amaryar Hamma Prince, amma meyasa Nenne bata saka su a ciki ba. Me hakan ke nufi?”
Taiwo (was like) irin bata yard aba wasa ake yi, hakan ba mai yuwuwa bane a yiwa Kehinde
dinta aure babu saninta. Wane irin aure ga Prince haka bagatatan kamar wasan yara? Ita din ai
daga mahaifiyarsu wato Nenne, sai ita a mutane masu matsayi cikin rayuwar Prince, kuma ta ya
za’ayi masa aure babu sani da amincewarsa sai kace wai saurayi ko karamin yaro? Don ko jiya
sunyi waya dashi lafiya-lafiyar Allah sukayi sallama bai ce mata komai ba, mai nuna ya san
zancen.
Tana kashe wayar Fatima don tsananin haushi ta kasa cewa komai, sai ga kiran Nenne na
shigowa, kamar jira take Fatima ta gama tseguminta sannan ita kuma ta kira.

Taiwo ta amsa wayar mahaifiyarsu ba tareda ta nuna jin haushinta na tsameta da tayi daga
al’amarin ba. Nenne ta kwashe komai ta gayawa Taiwo, tun haduwarta da Hajiya Zainab a
tafiyar filin Munna, da yadda taji sha’awar karbawa Abulrasheed auren diyarta bai ko sani ba, ba
don komai ba sai don ita kadai taga ta dace dashi. Yarinya ‘yar masu mutunci sannan mai
addini da tsarkin nasaba. Amma ina! Hankalin Taiwo yana kan Haseenah da labarin data zo har
UK ta bata akan abinda ya faru tsakanin ta da Tokumbo, cewa daga baya ta gane magani
Tokumbo yasa mata a lemo a gidan Prince, yayi raping dinta a dakinsa shine har Prince ya zo
ya gansu basu sani ba. Da sauran maganganu very sensitive na kare kai, da yasa ta daina
ganin laifin Haseenah kwatakwata.
Ai daga jin Nenne tace daga Gombe ne ta karbawa Hamma aure, nan take Taiwo ta tuna da
zancen yarinyar nan ‘yar siririya da Fatima ke bata labari kullum, wadda tace Nenne ta dauko a
Jeka da fari tana zuba musu fi’ili a gida har da kyamar abincinsu.
Babban abinda ya bata ran Taiwo da aka yi abinnan babu sanin ta, ba kuma ita ta tsara
komai ba. ba karamin buri ta ciwa auren Kehinde dinta ba duk ranar da yazo. Amma wai an yi
an gama babu ko saninta.
Taiwo nada son girma, wannan halin a ciki jininta ne, wanda ta tashi dashi a matsayinta na
babbar Yayarsu tun suna yara tanada son seniority. Hakannan tanada son duk wani sha’ani in
dai ya shafi Prince Kehinde ya kasance kacokam a hannunta. Kuma wai yarinyar da aka ce
kyamar kabilarshi ma take yi, koba itace akace wai bata iya cin abincin gidansu ba. Me
Kehinde zai yi da karamar yarinya haka (teen) mara exposure? Ai ko Haseenah da ya so ta
baiwa shekaru 22 baya a lokacin, kuma tana ajina uku a jami’a a turai, duk da shi ya saka ta. Ta
tabbata Prince ba zai taba yarda da wannan zabin ba ita kuma har kullum tana bayan abinda
yake so ne.
Ita a wurinta Prince har gobe yana son Haseena bacin rai ne da kishi, wanda tayi alkawarin
sulhunta su. Nenne bata taba yin wani hukunci da ya bata ran Taiwo irin na wannan lokacin ba.
Don ta katse duk wani hanzarinta na shirin sulhunta Haseenah da Kehinde. Kafin Taiwo tace
komai, Nenne ta soma gargadinta kan cewa bata yarda Hammansu Fatima ya ji komai akan
maganar auren shi daga bakinta ba, ta kyaleshi har zuwa ranar da yayi niyyar zuwa don kansa,
bata yi mishi aure don ta takura shi ba, ita da kanta zata sanar dashi ta hanyar da zai fahimceta,
don yanzu makaranta ma zata mayar da Aisha abin bana gaggawa bane, zata ta zana WAEC
da NECO kafin lokacin da yaga damar zuwa don radin kansa.
Taiwo was speechless. Har suka gama magana da Nenne, bata yarda ta ce uffan ba don
bacin rai, ita bata yarda bama ba’a mafarki taji zancennan ba. Wasa kawai ake yi hakan ba mai
yuwuwa bane Haseenah da Kehinde zasu komawa juna da taimakonta. Don a halin yanzu ma
suna tare da Haseenah a UK, wadda tayi tattaki ta sameta har gidanta a Lancashire ta gaya
mata komai na hanyoyin da Tokumbo yabi ya yaudareta ya rabata da Prince.
Ita kuma kamar wata Rakumi da Akala duk tabi ta hau kai ta zauna. Ita ta san zuciyar Prince
har gobe Haseenah take so, don soyayyar da yayi mata irinta ce ake kira soyayya ta gaskiya da
babu material attachement, tunda kuwa a kanta ne ya guji dukkan ‘ya’ya mata.
Haseenah ta gaya mata cewa ta dade da barin kasar Japan, wato bayan kammala karatun
digirinta, tana aiki da bankin Barclays a yanzu haka a garin Leicester. Har gobe aure ya
gagareta, ba don batada masoya ba, a cewarta sai don Prince kadai take jira ya huce.
Yadda Nenne ta sanar da Taiwo haka ta gayawa Firdausi da Fatima, cewa kada su sake su

sanar da shi sai ya zo don gigin kansa.
Taiwo ta rasa me yasa ta yarda da duk abinda Haseenah ta gaya mata, har hakan yasa
kwanannan take jin kewar rashin Haseenah cikinsu a ranta, ji take babu macen da ta kwanta
mata a matsayin partner ga dan uwan nata irin rainonta HASEENAH AMBURSA! Yo waye yake
sama da aikata kuskure ma? Haseenah ‘yar adam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login