Showing 9001 words to 12000 words out of 43117 words

Chapter 4 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

kaurinsa, don haka taci albarkacin ta fito daga tsatson kabilar
Nenne, keda ita duk abu daya ne, kinji Bongel?!"
Da haka Prince ya kashe bakinta ya lallasheta suka yi sallama a wayar, ko dama can haka
yake da son kannensa da kula da al’amarinsu, kome yake ciki in suka kira zai tsaya ya
sauraresu ya basu attention dinsa, amma duk da haka da Firdausi ta dawo saida ta gaya mata
komai data ji tsakanin Nenne da Aisha-Siddiqah, don abin ya kasa barin ranta, da abinda
Hamma Prince yace na hakan ba abunda zata damu bane, in dai akan hausawa da Fulani ne.
Princess Firdausi tace “I once heard something like that fah, Hausawa na da kabilanci akan
Yoruba food and Yoruba people in general, ba tun yau ba na sha jin wannan kisser ba, so ki

manta da yarinyar nan har nawa take, kin faya mita da kambama karamin abu Fatima”.
Nan suka hadu suna tattaunawa akan kabilancin da hausawa ke yi akan duk wani yare na
cewa ko kai musulmi ne in dai wani yare ne kai ba hausa Fulani ba kallon wani arne-arne suke
yi maka, basa maka kallon cikakken musulmi, meyasa? Kuma me ya janyo? Sannan saboda
me hausawa ke yiwa yare haka? Haka Suka maida abin ‘topic of discussion’ dinsu na ranar,
kamar masu yiwa juna (tutorial class). Su lallai suna son gano dalilin afkuwar hakan tun tali-tali.
Fatima har da hada ‘Imo’ ta kira Yayarsu Taiwo.
Suna shiga tattauna maganar tareda Aunty Taiwo dake Ilorin a lokacin. Amma Firdausi kare
Aisha take tayi, tana cewa ai yarinya ce da bata wuce sa’ar Kiki ba, kuma bata da wayewar kan
da har zata san sauran kabilu sun wuce haka yanzu a hannun hausa-fulani, tace ba wani
exposure keda yarinyar ba tunda daga cikin Gombe take, su yi mata uzuri. Allah kadai yasan
dalilin Nenne na son yarinyar alhalin bata da alaqa da su, kuma basu kai matsayin da Nenne
zata yi alaqa ta jiki dasu ba irin haka a matsayin su na talakawan gari.
Lafiyayyen dakin da aka baima Siddiqah ita kadai shimfide yake da sabon lafiyayyen zanin
gado hade da duvet mahadinsa, amma Aisha-Siddiqah tasa hannu ta cire zanin gadon nan ta
aje a gefe, ta yi kwanciyarta akan zanin atamfarta wai bata sani ba ko Yarbawa sun kwana a
kanshi, ita bata son jin warin jikin Yarbawa. Duk fadan da Umma tayi mata kafin su taho na shan magungunanta, ta bayan kunnenta yabi
ya fice. Tun saukarsu a Lagos bata kara shan maganinta ba, ta yi masa maboya cikin lokar jikin
gado ta manta dashi. Dama dai Siddiqah ba dai kin kwayar magani ba. Cikin dare kuwa Asma
ta tashi, sosai sosai, ita kadai tayi ta fama da inhaler ba wanda ya san me take ciki, ga yunwar
data dorawa kanta don haka kafin garin Allah ya waye Aisha-Siddiqah ta ji jiki, tayi zuru-zuru a
garin Ikko kamar ba gidan daula tazo ba.
A tsarin rayuwa irin na Fatima da Firdausi, ba Siddiqah kadai ba ko wani wanda ya hada jini
dasu ne ya zo gidansu da sunan kwana, misali daga Ilorin cikin dangin Dade, kota fannin
dangin Nenne daga masarautar Gombe yarannan sam basa shiga sabgar bako, wasu irin
‘yammata ne masu halin ‘ya’yan sarakuna na halin girman kai da da wanda hali ne da ya sha
bambam dana mahaifiyarsu da mahaifinsu kansa, balle Siddiqa da tazo musu da wani al'amari
da ya bata ran su, wai kyamar Yorubawa take, Firdausi kadai ke mata uzuri, don haka Siddiqa
da Nenne ta kawo gidan Engnr. Idris Akanni don ta nema mata magani ita kuma tana rarraba
musu ido a tsorace wai tazo gidan Yarbawa in suna yarbanci, ita Siddiqah tsakaninta da Allah
da gaske ko yarbanci ake yi bata son ji a kunnenta, damunta yake yi, don jin yaren take kamar
fada-fada, ita kuma bata son fada da hayaniya, ta kuma kasa boyewa a ranta har ta kai ga
Fatima ta fahimta, itama kuma ta kasa boye jin haushin hakan har ta fahimtar da sauran ‘yan
uwanta, sai hakan yasa suka fara tsanar bakuntar Siddiqah, suka nesanta kansu da shiga
sabgar ta, suka barta da Nennen data kawo ta kadai kuma basu nunawa Nenne hakan ba.
Ga hudubar Aunty Taiwo na kada su sakar mata fuska ta samu damar zama dindindin a
gidansu, ita bata son jaye-jayennan na Nenne, ko na ‘ya’yan yan uwanta da take kawowa hutu
gidan Taiwo na yawan hanawa, musamman daga bangaren Gombe, Taiwo tafi son dangin
Babanta ba tun yau ba don a cikinsu take rayuwa jefi jefi take zuwa Gombe, Oummana kanta ta
sani Taiwo tafi son dangin Babansu, a cewar Taiwo bahaushe bashi da amana, gashi da butulci
da rama khairan da sharran. Firdausi dai bata tsananta ba, cikin mu’amalarta da bakuwar
Nenne Aishatu-Siddiqah, a kiyayyar da suka kafawa Siddiqah, ita tana yiwa Siddiqah uzuri da

kuruciya da rashin wayewar kai.
Fatima kuwa ta daina zaman gidan sabida Aisha-Siddiqah, ganinta kullum tareda Nenne cikin
gidan yana bata mata rai, in ta fita tun safe sai yamma, dama service (NYSC) suke yi a wurare
mabanbanta itada Firdausi.
Don haka a kwana biyunnan asabar da Lahadi ba karamin shiga takura Siddiqa tayi a gidan
Engnr. Idrees Akanni ba, na farko babu kawayenta na makaranta su Amintako, da Ramatu da
sauran ‘yan gang dinta masu kara mata karsashi, ba Ummanta data ke zubawa shawagwaba
kullum a gefe, sannan babu Babanta mai biyewa rikicinta sannan ba Ishaq masoyi mai sa ta
dariya da murmushi sabida iya soyayyarsa, a wurin Aisha-Siddiqah duk wani farin cikinta yana
tattare da kasantuwar wadannan mutanen data zayyano a sama a tare da ita. Don haka cikin
kwana biyunnan Aishah duk ta birkice da dacin rai, duk kokarin Nenne nata saki jiki tayi feeling
at home abun ya ci tura, Allah-Allah kawai take safiyar Litinin tazo, a kaita asibitin da aka ce don
shi aka kawota Ikko, a gama a maida ita gidan su a Jeka da Fari. Don Nenne tace sai litinin zata
kaita taga likitan Firdausi.
Yau Lahadi da Nenne ta ga taki cin dinner ta kuwa ce mata komawa Gombe ba rana tazo
gidan yarbawa kenan har abada. Musamman data lura da dabi’un Siddiqah na kabilanci basu
canza ba, duk da nasihar data bata lokaci tayi mata, shiyasa take so ta saba dasu tun yanzu,
tunda kuwa she is going to be part of them nan bada jimawa ba idan Allah ya so ya amince
kuma ya yarda, tanaso ta cirewa Siddiqah ethnocentrism din data likawa zuciyarta akan kabilar
Yarbawa. Don haka cikin serious ta gaya mata yau cewa komawarta Gombe fa ba rana in zata
bude ciki taci abinci ta ci, ko ta dinga dafawa da kanta.
Duk girman kulawar da Nenne ke baima Aishah-Siddiqah a gidanta, duk sonda take kokarin
gwada mata, da daular da ta tsinci kanta ciki rana daya, sama A/C kasa A/C kai har a kitchen
A/C ce da fitilu masu haske wadanda da dare sai ka dauka kamar rana ce a gidan Engnr. Idris
Akanni, ga cima ta alfarma wadda bata ko taba gani ko mafarkin ci ba, ga motoci na zamani
kullum a jere a parking lot suna jiran mai fita a gidan da direba, rayuwa ce irin wadda Siddiqah
bata taba ji ko gani ko a mafarki ba a gidan Haj. Sappa dake a Banana Island, Lagos, amma
duk wannan sabida kulafucin uwa irin na Siddiqah hankalinta bai taba kaiwa kansu ba balle tayi
appreciating. Kacokam! hankalinta yana gidan su a Jeka da fari.
A weekend dinnan kafin zuwan Litinin da zasu ganin likita, sau uku Aishah tana shiga toilet ta
kulle tayi kukan makon uwarta da kewar Gang members dinta na Billiri, a karshe ta goge
hawayenta ta fito, ita ba waya ba balle ta kira Umma ko Ishaq ta gaya musu kurkukun Yarbawa
Umma ta kawo ta. Ishaq ya sha gaya mata cewa sabon data yi dashi yafi son da take masa yawa, yau ta yarda
da cewar nan tasa it aba wani soyayyar namiji a ranta sai kauna da sabo na ‘yan uwantaka da
shakuwa tsakaninta dashi, don a baya in ya fadi irin hakan fushi take yi sosai, ta ce ya raina son
da take masa, ita ba wani sabo a ranta sai SO. Yau dai ta yarda Ishaq ya fita gaskiya ta saba da
shine kamar Yayan da suka fito ciki daya shima wani irin kewarsa da take daban ce.
Haka a daddafe Aisha Siddiqa Yunus ta kai safiyar Litinin a gidan Engnr. Idris Akanni, kafin
kwana biyun nan duk ta kara ramewa kamar kudin guzurin da ake diba kullum, Umman
Siddiqah ma tana can a Gombe amma hanakalinta yana Lagos, tana kewar Petel dinta duk da
ta saba da hakan in ta tafi makarantar kwana amma wannan kewar bata san meyasa ba ta
dabam ce, tasan dai Hajiya Sappa zata kula da ita har fiyeda kulawar da zata bata, don taga

tsantsar kaunar Siddiqah cikin idanun ta rana ta farko data fara ganinta a kwance a jikin gado a
asibitin FMC Gombe.
Komai na gidan a darare Aishah-Siddiqah take dashi, ta sanyawa ranta son komawa Gombe
a matsayin abinda zai bata kwanciyar hankali kadai. Nenne kuma tace ba rana.
Ko jiya data baiwa Nenne tausayi ganin yadda ta maida kanta daddawar daka, saida tace da
direban su Fatima in ya kaisu wajen saloon ya dawo ya dauki Siddiqah ya kaita yawo ta ga
garin Lagos, ta bata kudi tace ta sayi duk abinda take so in sun fita, madadin zaman daki data
ke tayi ta dankare a kuryar gado tun safe har yamma in har ba Nenne ta kirata falo ba. Amma
Siddiqah taki, harda rokon Femi da Nenne ta aiko kiran nata.
“Don Allah don Annabi a kyaleni kallo nake yi”. A ganinta gara ta zauna a gida tayi kallon
talbijin da bata san ma me ake yi a ciki ba sabida hankalinta da baya jikinta yana Gombe ya fiye
mata shiga cikin garin yarabawa, a ranta tace ta san duk garin Legas dinma Yarbawa ne, don
haka ita bata ga abun kallo a garin Lagos ba. Nenne dai tana ta kara fahimtar (negative attitude) din Siddiqah akan kabilar da ba tata ba,
duk wani motsinta a daki ne ko a falo akan idonta ne ba tareda Siddiqah ta sani ba, ta fahimci
irin kallon da Siddiqah ta ke yi jama’ar gidan bakidaya kallon (yare) bama musulmai ba,
musamman kabilar yarbawa da sukayi kaurin suna (ridiculously) a idanun hausawa wanda a
zahiri yake bukatar gyara, ta fahimci har zuwa lokacin Siddiqah ta kasa karbarsu a ranta.
Nenne ta gama sawa a ranta ita kuma sai ta goge wannan negative perception din daga
kwakwalwar Siddiqah koda ba a lokaci daya ba. Tace “Siddiqah na bukatar thearapy, counseling
kai har da rehabilitation akan shin su waye kabilun Najeriya wadanda ba Hausa-Fulani ba???
Me yasa aka sanya mu karkashin tuta daya (gabas da yamma, kudu da arewa) muka amsa
GREEN WHITE GREEN???
A ganin Hajiya Sappa kabilancin dake zuciyar Siddiqah da idanunta ya wuce kima ya kintace
har ya zarce na musulunci ya zame mata wani abu daban kuma, domin kuwa yafi nata na can
baya tsanani, a lokacin da take da shekaru irin na Siddiqa sanda ta tsinci kanta a gidan aure
dumu-dumu a tsakiyar masarautar Ilorin, lokacin da aka kawota cikin dangin mijinta da babu
bahaushe ko daya a matsayin mata ga daya daga cikin zuri’ar Emir Abdulrasheed Akanni.
Siddiqah ta yi wa kabilanci da banbancin yare da al’ada tsakanin ta da da kabilar da ba tata ba
mummunar fassara wanda Nanne Sappa ke son ta rage ko bata yi nasarar cire mata shi duka
ba.
**** **** ****
Ranar litinin da safe Nenne ta shirya tsaf cikin koriyar laffaya tayi sharr sai tashin sassanyar
kamshin turarukan “Naseem” take, kyakkyawar bafullatana wadda bata kwalliyar fuska sam,
amma fatarta sumul-sumul kamar ta shiga injin wankan fata, daka ganta ka ga daya daga irin
matan manyan sarakuna ko masu arziki wanke hannu ka taba, kalarta harda jaja-jaja na samun
kula da samun daular rayuwar da kowanne dan adam ke buri, hannunta cike da bangles na
zinare hagu da dama ko yaya ta motsa sai sun motsa tamkar ba’indiya. Haka tasa Siddiqa a
gaban motarta ita kuma tana hakimce a gidan baya direbanta Ojotu ya ja mota zuwa asibitin da
zasu je.
Tuntuni dama tayi (booking appointment) na ganin likitan nasu, tafiyar mintuna kalilan a
manyan titunan garin Lagos daga Banana Island ta kawo su asibitin (Lagoon Hospital), da kanta
ta kai Aisha har gaban likita Ayoade wanda shine likitan Firdausi, Dr. Ayoade Khalil.

Dr Ayoade yayi mata kyakkyawan (check up) ya dorata akan sabon treatment da yafi wanda
take kai a FMC Gombe, ya kuma canza mata magani mai kyau, da ya auna jininta yace sai
yaga yadan hau, ga rashin nutsuwa a tare da ita da alamun akwana bukunnan data yi a Lagos
ko sau daya bata ci abinci cikin nutsuwa ta koshi ba, likitan yace da Nenne zai riketa two days
bed rest don ya ga jininta ya hau. Zai kuma sa mata drip. Nenne ta damu kwarai, yau tana
ganin ikon Allah a gun Siddiqah wannan makon gida nata har ina! Ta ce ma Aisha bayan
kaucewar likitan daga kusa dasu.
“Yanzu saboda Allah Siddiqah me na raga miki? Me Umman take baki wanda bana baki? Na
tabbata sabida baki son zama damu ne kika sawa ranki damuwa har ta kaiga bp?”
Aisha-Siddiqah dai dai bata ce komai ba, ta sunkuyar da kai tana wasa da siraran yatsunta,
amma gara mata zaman asibitin nan sau dubu akan gidansu Nenne, musamman data fahimci
Princess Fatima ta sauya mata fuska yanzu. Wani kallo ma take mata mai zafi cikin ido. Nenne
ta zuba madarar hollandia a tambulan mai tsaho ta mika mata, ba musu ta karba tana sha a
urunce ji kake mukut-mukut, hadidiye madarar kawai take yi don yunwa, mamaki da haushin
iskancin Aisha-Siddiqah ya ishi Nenne, ji dai yadda take shan madarar a yunwace mai nuna jiya
bata ci abincin dare ba ta shige daki ta kudundune ta kwana da yunwarta, duk da ta ce da Femi
abinda Aisha take so zata dafa, an kuma tambayeta tace tuwo, haka ta bar su da tuwon masara
da miyar kubewarsu ya kwana a dining wanda akayi saboda ita ta yi barcin wuri duk don kada
ta ci girkin Femi. Nenne Sappa ta nisa, sannan tayi kwafa tace.
“Aishah, nace me yayi zafi na yiwa kai horon yunwa? To kwantar da hankalinki ki sauke jinin
da kika dora a can sama, in sha Allah rana ita yau zan maida ke Gombe ince ko shikenan?
Amma na rantse miki na sake rantsewa tafiya ce mai dawowa. Zaki yi dawowar da babu
komawa sai dai da yawo in Allah ya yarda. In yaso in ga karshen kabilanci”. Siddiqah dai shan
madararta take har da murmushi don hankalinta ya kwanta, tunda Nenne ta yarda zata maidata
gida zance yak are, sauran zancen da tayi a karshe bata ji bama balle ta fassara shi da wata
manufa don hankalinta ya kwanta yanzu.
Shikuma Dade wato Engnr. Idris Akanni a ranar ya tashi zuwa Ilorin. Kafin Dade yaje Ilorin,
saida yasa ‘yan uwan Nenne na Gombe suka yi masa duk wani bincike akan Malam Yunus da
asalinsa, nasabarsa da sana’arsa, kuma duk abinda aka gaya masa din akan malam Yunusa
Hamza na kwarai ne na sam barka. Malam Yunus ya samu duk kyakkyawar shaidar da ake
nema ga mutumin kwarai mai kula da iyali da sadaukarwa akan su iyakar karfinsa. Haka
matarsa ta samu kyakkyawan yabo na kula da hakkin makwabtaka da tarbiyyar Siddiqah
kasancewar Allah bai bar mata ‘ya’yan da take ta Haifa ba sai Siddiqah din wadda suke tsaye
kan jiki kan karfi wajen ilmin ta na addini dana boko. Siddiqah na cikin yaran kwarai da ake
alfahari dasu a unguwar jeka da fari sannan tun tana shekaru 13 tayi haddar Alqur’ani a Tahfiz
dinsu.
Da wannan kyakkyawan albishir din Dade Engnr. yayi tattaki har Ilorin ya samu mahaifinsa
Emir Abdulrasheed dan Abdullateef Akanni da maganar zabin da Nenne ta yiwa Abdulrasheed.
Sarki da yake akan tsini shima, sai yaji kamar an masa allurar tuni da wani babban al’amari da
duk suka zuba ido akai, yaji kamar an zaburar dashi ga wani muhimmin abu da ya saka shiririta
a ciki, ya tuna cewa babban jikan nasa Prince Abdulrasheed ya wuce shekaru 40 a halin da ake
ciki yanzu, burin sa a lokacin kowa ya san na Prince Abdulrasheed yayi aure yana raye ne, har
in zai samu ganin ‘ya’yan jikan nasa zai yi farin ciki, amma meyasa ya biyewa gudun zuciyar

Abdulrasheed har yau bai yi wannan yunkurin ba sai yanzu da mahaifiyarsa Sappa ta gaji da
kawaicinta na fullata akan rashin auren dan nata tayi tattaki da kanta ta nemo masa aure da
kanta? Shi kansa ya san son da yake yiwa Prince Abdulrasheed yayi yawa, shiyasa har baya
iya tankwara shi akan duk abinda yace baya ra’ayi. Gaskiya ne duk wata kauna mara illah tabi
bayan ta uwa gad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login