Showing 6001 words to 9000 words out of 43117 words

Chapter 3 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

abinci (food warmers) sun
ajiye masa nasa.
Amma Siddiqah ko loma uku kwarara ta kasa, kuma ko sha'awa abincin bai bata ba, duk
haduwar abincin da bajintar Femi wajen iya abincin yarbawa na alfarma, itafa komai na
bayerabe bai burgeta, a wani bangarenma kyankyami abincin ya bata. Ba dadewa tun ba’aje
ko’ina ba Nenne ta gama karanto matsalar Aisha-Siddiqah da zaman gidan (kabilanci) ne da ita,
da belief din cewa kabilarta sama take data kowa, abinda masana zamantakewar dan adam ke
kira ethnocentrism (feeling na cewa kabilarka tafi ta kowa daraja) irin wanda itama tayi fama da
shi a farkon zuwanta cikin zuri'ar Emir Abdulrasheed Akanni, wato royal family na masarautar
Ilorin.
​ Banbancinta da Aisha-Siddiqah ita ko a lokacin data zo bata kyamaci abincin Yoruba ba,
dagewa tayi ta koyi ci, kai komai nasu ma kokari take tayi adopting cikin dan lokaci with great
passion, saboda soyayyar mijinta Engnr. Idris Akanni data yi wuf da ita lokaci daya, sabida
karamcinsa da bala’in iya tattalin mace da nuna soyayyarsa karara gareta. Murmushi Nenne ta yi. Zuciyarta tayi tsalle ta tafi ga hasko mata ranar da za’a kai Siddiqah
gidan Prince Abdulrasheed a matsayin matarsa. Ashe kuwa kallo na gaba, in dai haka Siddiqah
ta dorawa kanta kabilancin kabilar Yoruba babu gaira babu dalili. Ko yaya Siddiqah zata ji ranar
da aka sanar da ita Bayerabe dinne abokin rayuwarta na har abada toh? Bayeraben ma jikan
sarkin Yarbawa, shi ne zai mallaki komai nata da take tinkaho na Fulani ne? Murmushi sosai
Nenne tayi a lokacin, tana hangowa idanunta Siddiqah da Abdulrasheed a matsayin mata da
miji.
​ A cikin ranta tace “Aishatu-Indo Siddiqah! Ina jiye miki ranar karyata kai. Ai saidai Allah
ya taroki tunda kin fado komar auren Bayeraben mutum. Tuni zaki mance da shirmenki da
ethonocentrism dinki, domin su din maza ne na daban da suka fi kowacce kabilar Najeriya son
matansu, iya soyayya da iya kula da bukatunsu da tattalin macen da suke aure. Ba jimawa na
tabbata zaki manta da kabilancin, da zarar kin fada hannun Bayeraben miji.
Nayi fin wanda kikayi a baya, kuma gashi na cika masa gida da zaratan ‘ya’ya na soyayya.
Ta san dai nan bada jimawa ba komai zai kasance tsakaninsu cikin yardar Ubangiji wato
tsakanin Prince da Aisha tunda har Dade yayi na’am da Siddiqah. Dama shikadai take fargabar
amincewarsa. As long as ana tare da ita kuma, yau da gobe, koda bayan auren ta da Prince da
kadan zai goge mata hadda, Siddiqa zata kai ga fahimtar babu mutane masu dadin mu’amalar

aure da tsafta da gayu da son uniqueness da iya tafiyar da mace irin Bayeraben Najeriya!
Don haka koda ta tsame hannu tace ta koshi, Nenne bata ce komai ba, ta tashi a hanzarce ta
koma dakin da aka sauketa duk suka bita da kallo, kai tsaye toilet ta nufa ta tofar da aman da
ya cika mata baki ta wanko bakinta ta fito, nan ta tarar an kawo mata kayanta da aka wanko aka
gogo dukkansu, da wasu ma da a saninta ba nata bane, a rashin saninta dakin hutun Kiki ne
dake daura dana su Fatima aka gyara mata.
Nenne ko ta ji ba dadi da abinda Sidiqah take yi bazaka gane hakan a fuskarta ba,
kasancewarta mai iya zama da mutum da duk wani halinsa da tafiyar dashi da halinsa, bin
bayanta tayi bayan ta dauki madarar shanu (fresh milk) mai sanyi a firji da sinkin shawarma mai
zafi da aka gama gasawa yanzu-yanzu ta bita dasu har dakin Kikin. Tun daga bakin kofa Nenne ta hangota ta shige cikin bargo ta takure ta kudundune, ta san
yunwa take ji, yarinya sai kafirin kabilanci. Watakila kuma AC da aka kunna ce ta matsa mata
ba kadan ba, don haka sai jijjiga take yi a ita kadai cikin bargo. Nenne ta tsorata, data tuna
Siddiqah nada (Mild Asthma), da sauri ta karasa ta kashe iya kwandishin din, tana yi tana fada
“wa ya ce a kunnama Indo AC?” Ta zauna a daidai kanta ta dora hannun ta saman goshin Aisha
da har ya soma daukar zafi. Cikin dabara irin ta iuyaye da son nuna bata san halin da take ciki
ba take magana.
“Aisha lafiya kuwa? Meyasa baki ci abinci ba? Ina kula fa tun isowarmu baki ci komai ba sai
ruwa, so kike in maida ke gida da ulcer kuma nida na dauko ki neman lafiya daga wata cutar?”
Kasancewar Siddiqah frank, irin yarannan ne dasu ba za'a kirasu 'yan fari ba don wauta,
sannan su ba auta ba sabida rashin iya rufe maganar dake cin ransu, a zahiri Siddiqa bata iya
boyewa Ummanta abinda ke damunta komai girmansa, sai ta ke ma Nenne kyakkyawan zato
na cewa in taji damuwarta zata fahimce ta, zata yi mata uzuri tunda ita `babba ce kuma
bafullatana ‘yar uwarta, ta kuma lura Nenne nada kulawa a kanta, ga yunwa ta gama jigata ta
don hanjin cikinta rawa yake amma bazata iya cin abinci mai qaguwa ba, don haka tsakaninta
da Allah tace.
“Umman Lagos wallahi bana iya cin abincin Yarbawa. Inada kyankyami, nayi kokari inci na
kasa”.
Wannan magana sai ta sauka a kunnen Princess Fatima data doso dakin neman Nenne, abin
ya daure mata kai ya kuma bata mamaki sai ta dakata kadan don son ta fahimci me Aisha ke
nufi, duk da ba halinsu bane labe, amma maganar ta doketa, me yarinyar ke nufi da abincin
kabilar yarbawa din? Ita bata taba jin maganar da bata yi mata dadi makamanciyar wannan ba. Nenne tayi murmushi mai tafe da dariya tace “Siddiqah ho!” Duk da taji ba dadi a ranta
musamman da burinta akan Siddiqah din na ta tallafi rayuwar Prince ya fado mata a rai, da irin
alherin data keson kullawa a tsakaninsu, sai kuma gashi Siddiqah data zaba masa matsayin
mata ta nuna kiri-kiri a matsayinta na Hausa-fulani kyamar kabilarsa take yi gabadaya, (which
means) har shima bazai tsira ba daga wannan kyamar da kyankyamin ba kenan.
Ta tuna yadda akayi ta kace-nace a danginsu lokacin da marigayi mahaifinta Sarki Ahmadu
Umar Jalloh ya kawo batun aurar da ita ga Dan sarkin Ilorin, ba karamin opposition aka samu
ba a lokacin don dai Sarki mai magana daya ne kuma ya isa da kowa dake karkashinsa amma
hatta mahaifiyarta Nani Oummana bata so, bazata manta da statement din Oummana a lokacin
ba “ka rasa wanda zaka baiwa Sappa sai Bayerabe?” ta rasa wane irin kabilanci
bahaushe/bafullace ke da shi akan Yarbawa. Wanda su yarbawan a garesu ba haka bane suna

girmama kabilar Hausa-fulani. Nenne sai ta wayance cikin lallashi da tsokanar Siddiqah tace,
“Ha’an, kamar yaya ba kya iya cin abincin Yarbawa Aisha-Siddiqah?!” cikin hawaye dake
tsatstsafowa tace “saboda qaguwa (shrimps) da aka zuba a miyar” “haka ya kamata kice, ba
kya iya cin shrimps, amma ba bakya iya cin abincin yarbawa ba, this is sheer discrimination!
Shin Siddiqah Bayerabe ba musulmi bane? To idan Allah yayi ikonsa kika auri Bayeraben
mutum fa, kamar yadda nima na aura tun ina kankanuwa ba tare dana shirya kona zaba ba?
Yaya zakiyi idan hakan ta faru dake tunda aure babu inda baya kai mace?”
Saddiqah ta zaro ido cikin tsoro da firgicin maganar Nenne abin gwanin ban dariya ga wanda
ya gani, sannan ta saki hawayen data ke maqalewa suka dirgo akan kuncinta tace “kuma kika
yarda kina bafullata aka aura miki Bayerabe?” Wannan Magana ta kara rikita Princess Fatima
dake tsaye tana jinsu. Aisha bata yi shiru daga wannan ba ta kara da cewa “Ni dai Umman
Lagos ki tofar da miyaun bakinki, Umman Lagos kada kiyi min baki, indai akaina ne kinyi
babban sabo kada Allah ya hada ni da miji bayerabe….. (iya abinda Princess Fatima ta iya jure
ji kenan ta juya da sauri zuwa dakinta. Tun daga wannan ranar kiyayyar Siddiqah ta fara
darsuwa a ran Fatimah.
Aisha ta cigaba da gayawa Nenne cikin rufe ido da bayan hannnunta tana ‘yar dariya
“Umman Lagos kada kice nayi rashin kunya. Allah ya riga ya bani miji bafulatani dan uwana fa
ba tun yanzu ba, ki tambayi Ummana zata gaya miki Ishaq dan Gombe ne, haihuwar Nafada,
tun ina karama muke tare yake riko na Umma tun ban san wani Kalmar so ba”. Nenne Sappa taji wani iri a ranta, Aisha wace irin yarinya ce haka mara kara da sakayawa
akan abinda ta yardarwa kanta bata so? Ta dan yi murmushi cikin rashin jin dadi, sannan ta
gyada kai tace.
“naji Siddiqah, kuma Abbanki ma ya gaya min zancensa. Amma Siddiqah mace budurwa a
addinance da al'adarmu ta Fulani musamman a zamaninmu na baya bata zabarwa kanta mijin
aure, biyayya muke yi ga duk abinda iyayen mu suka zartar akanmu, sai muga alheri mai
dimbin yawa ya biyo bayan hakan, ni da aka aura min Babansu Fatima ban ma ganshi ba har
saida aka kaini Ilorin. Kuma a haka nayi biyayya yau na tashi da alkhairi da riba mai yawa.
Ki dinga neman zabin Allah akan aurenki kin ji ko Aisha-Siddiqah?
Ki yi kokari ki cire kabilanci daga ranki don bashi da kyau ga zuciyar mumini, shi din lahani
ne ga Imani, tunda Allah da kansa yace “Innna akramakum indallahi atqakum”.
Don haka (ethnocentrism) abu ne da bashi da amfani ko kadan a addinance, tunda
dukkanninmu addinin musulunci muke bi, kuma mun yarda da Allah da Manzonsa to mun zama
daya, dukkanmu musulmai ne da muka hadu akan kalmar LA’ILAHA
ILLAH-MUHAMMADUR-RASULULLAH, wannan ce tsintsiyar data hada mu ta daure duka
kabilun duniya ta mayar abu guda, ba iya ‘yan Najeriya kadai ba, mu duka al’ummar Annabi
Muhammad SAW ne, dake kwadayin tashi karkashin inuwarsa ranar da babu inuwa sai tasa. In
hakane kuwa ai kai bawa baka da ikon banbance kabilar da zata shiga karkashin wannan
inuwar a cikin musulman duniya”.
Haka Nenne tayi ta yiwa Siddiqah nasiha mai shiga jiki akan ta daina wariyar launin fata
akankabilun da ba na arewa ba, tace ba Yarbawa kadai ba, dama kowanne yare in dai musulmi
ne, har a karshe tacema Aisha cikin zolaya ganin ta kasa sakin ranta.
“baki sani ba ko akansu ranar ki zata fadi Siddiqah?”
Ta karasa da dariyar tsokanar Siddiqah, Aishah-Siddiqah ta sunkuyar da kai ta nutsu tana

sauraren wa’azin Nenne kamar da gaske nasihar da take matan na shigarta. Sai tace a ranta ai
tunda Babansu Firdausi Bayerabe ne, ko meye ma Nenne zata ce akan yarbawa din, dole kuma
ta so su tunda har zuri’a mai yawa ta shiga tsakani amma ita meye nata, ita bata ga dalilin da
zata yarda bayerabe da bafillace abune iri daya ba. A zuciyar Siddiqah tace “in Allah ya yarda a Nafada rana ta zata fadi, Ishaq Hassan Nafada,
mijin da Allah ya zabar min tuni, baida alaqa da Yarbawa ko any yare, ta kowanne bangare shi
hausa/Fulani ne ziryan”. Kenan nasihar Nenne ta shiga ta hagu, ta fita ta dama a kunnen
Siddiqa, nan kusa bata ga me zai sa ta yarda bafullatani/bahaushe daya yake da bayerabe ba. Watakila dai Umman Siddiqah wato Haj. Zainab ta manta da halin Petel dinta ne na rashin
wayewa da shiga jama’a da irin wautar ta na diyan fari ne ko auta za’a ce, wanda ta kan taba
lokaci-lokaci, gashi ita ba ‘yar fari ba ita baza’a kirata auta ba. Aisha-Siddiqah a dabi’arta bata
iya boye abinda ke ranta ga wanda ya girmeta musamman Ummanta da tafi kowa kula da
abinda zai dameta, kuma kallon kawar Umma take kamar tata uwar. Shiyasa kai tsaye ta
zayyano mata abinda ke ranta babu kwane-kwane, watakila Ummanta ta manta da hakan wato
rashin sakaya damuwa irinna Siddiqah, da maiyuwuwa bata barta ta biyo Nenne Sappa ba, ba
tare data sanar da ita Aisha nada tarin rashin wayewa ba.
A rayuwar Aisha Siddiqah Yunus, ita batasan wani abu kara ba, ko fuska biyu, sannan bata
san boye abinda bai yi mata daidai da ra’ayin taba, komai girmansa kiri-kiri zata nuna maka
abin nan bai mata ba. Ita ’yar keke-da-keke ce. Ba sakayawa.
Da kyar Nenne ta samu ta yarda ta sha fresh milk din data kawo mata, don tace mata a
firjinta ta dauko, amma sam ta ki cin shawarmar. Tace a ranta mai yuwuwa da naman dodon
kodi akayi shawarmar ma.
Princess Fatima ta koma da baya zuwa dakinta da bacin ran maganganun Siddiqah fal ranta,
taji bata son zaman Siddiqah a gidansu, nan da nan ta dauki waya ta dokawa aunty Taiwo, a
mamakance tana labarta mata irin yarinyar da Nenne ta kawo musu gida daga Gombe wai
kyamar Yoruba food take and Yoruba people. Taiwo tace “'yar waye haka?” Fatima ta labarta mata daga haduwa da uwarta a Saudiyya
Nenne ta makale musu harda dauko 'yarta wai zata kaita asibiti”. Taiwo da yake ta san halin
karamcin mahaifiyarsu sai bata yi mamaki ba, cewa Firdausi tayi “in kin bibiya hausawa ne,
sune most attimes masu raina kabilar Yoruba. They are more ethnocentric. Kuyi hakuri ita da
kanta zata maida ita inda ta daukota”.
Princess Fatima har lokacin ranta bai gamsu ba, haka curiosity na son sanin dalilin Siddiqah
na kyamarsu wai har abincinsu duk tsaftarsa ya ki ya barta. Sai ta kira Hamma (Prince).
Tana so a bata karin bayani akan me Siddiqa ke nufi da hakan? She was like irin me aka fi
su? Taiwo kuma kashe wayarta tayi bata yarda sun tattauna maganar ba don tana tareda
Toufeeq a lokacin ya zo musu annual leave.
"Hamma!"
Daga daya bangaren, Prince ne ya amsa, a lokacin yana tsaye kan Pareto ana yiwa
Dawakansa wanka, yaja gefe yana amsa wayar Fatima.
"Bongel!” (Sunan da Prince yake kiran kanwarsa Fatima) wanda kalma ce ta harshen
Fulatanci mai nufin “mai kyau”, ya kara da cewa “Bongel, yaya akayi ne?"
A fusace Princess Fatima tace "Ka roki Nenne ta sallami yarinyar data kawo mana gida daga
Gombe, kafin na yi mata ‘Ai lojuti’".

Ta bashi dariya sosai don tana nufin (kafin tayi mata rashin mutunci) da harshensu na
Yoruba. Da muryarshi ta girma da kasaita mai tafe da lallashi ga kanwar tasa Prince yace.
"Wace yarinya ce haka? Bansan Bongel na da rashin mutunci ba".
Nan Fatima ta gaya masa wata yarinya ce Nenne ta kawo bata fice sa'ar Kiki ba, sai mulki
da fi’ili take zuba musu a gida da shan kamshi da kyankyami sabida taga Nenne na nan-nan da
ita, wai bata iya cin abincin su sabida su Yarbawa ne".
Abin ya bashi dariya sosai yace "Bongel, haka Hausa-Fulani ke ma Yoruba people kabilanci
ai, tun iyaye da kakanninmu, tun muna yara munsan wannan irin kabilancin da hausawa ke
mana, muma kuma Yoruba kada ki manta haka muke musu kallon wadanda basu waye ba,
kauyawa, dakikai, muna ganinsu marasa ilmin boko da ko turanci basa ji duk ilminsu, kema ba
sai ki rama ba?
Hausawan da asalinsu maguzawa ne? Kice mata jikokin barbushe da tsimbirbira ‘yan kan
dutse, in kuma bafullatana ce bakida halin ramawa fa Bongel, for Nenne’s sake, for Nani’s sake
ki yafe mata. Saboda kema rabi itace, fullata, saidai kawai in kinje gidansu kema kada ki sha
fura da nono kada ki ci tuwo da miyar kuka, inace shikenan kin rama?". Kasancewar da yarbanci suke maganar harshen da Princess Fatima tafi jin shi sosai fiyeda
kowanne harshe da suke yi a junansu. Ganin Hamma yaki daukan zancen da muhimmanci ya
kara tunzura Fatima. Gabadaya Hamma ya maida zancen wasa. Tace "Hamma I am serious,
Nenne ta dauki yarinyar nan da muhimmanci wallahi, I am jealous of her, wata 'yar firit da ita,
sai shegen kyau irin na aljannu".
Wanna karon Hamman, couldn’t control his laughter akan wautar kanwar tasa, wadda daga
murmushin kasaita da yake yi yanzu ta zarce zuwa dariya mai kima, yace
"kada kice min kishin kyawun nata kuma kike yi Bongel?
Shin Bongel akwai wanda ya kai tagwayen Nenne (Fatima da Firdausi) kyau ne a Najeriya?
Kada ki manta sau biyu kuna dauko ‘beauty contest’ a makaranta in kin manta ni ban manta
ba”.
Fatima taji dadi, ta saki kasaitaccen murmushi (from ear to ear), ko ba komai Hamma Prince
yasa kanta ya kumbura, ta rage jin haushin Siddiqah, amma ta rasa ta yaya zatayi dashi ya
yarda bata son zaman Aisha-Siddiqah a gidansu, ganin ta kawai fadar mata da gaba yake yi,
don jinta take kamar (part of the family), alhalin ba abinda ya hada su. Sai ta nisa tace "Hamma!
Ni bana son zamanta damu kawai, Hamma bana son bare agidanmu, kai kadai zaka iya yiwa
Nenne magana ta ji, to take her back to her home, har akwai wata kabila da zata aibata Yoruba
a idanuna in so ta?"
Yace "in kuma bafullata ce fa, tunda kince daga Gombe ta dauko ta? Ai kema Fulani ce idan
anbi salsala, jinin Uwa ma da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login