Showing 18001 words to 21000 words out of 43117 words

Chapter 7 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf

California itada kawarta Badriyya.
“Amma Kiki ban hanaki bin kawaye yawo ba? Ban ce daga makaranta sai makaranta ba?
wato har kallon ball kike zuwa?”
“Kayi hakuri Uncle AK, wallahi ba inda nake zuwa banda shopping, ranar ma Badriyyah ta
matsa muje ne don taga AbdulNasir a fili, tana matukar son wasansa, na gaya mata ka hanani
zuwa ko’ina, tace daga ranar bazasu kara zuwa yin wasa Los-Angeles ba, and she don’t want
to miss seeing her favourite footballer in reality (bataso ta rasa ganin dan ball din data fi so a
fili), sai na yarda muka je, tun a ranar ya nuna kaunarshi gareni muke waya, ban taba gayawa
kowa ba sai Mama, shine ta bani waccan amsar cewa bazan taba sauraron kowa ba sai kayi
aure”.
Abdulrasheed yayi ajiyar zuciya ya ce “Kiki count me out kinji? Bani lambar yaron kuma ki bar
ni da Taiwo”.
Kiki ta dage itafa bata so itama, in Abdulrasheed naso tayi aure ko ta saurari maso sonta to
ya barta ta hada masa lefe.
Dariya yake yi a yanzu. Yace “Kiki! Daga hada lefe sai me? Na baki dama kiyi tayi. Kudi ne
dake. Ki sayi kome kike son saya kiyita tarawa gaibu, amma bada kudina ba bana cikin shirme
kinji?”
“Yo dama Uncle ai ban ce ka turomin ko sisin kwabonka ba. Zai zama cewa tawa
gudunmuwar kenan ta aurenka, saya maka akwatin (undies and night wears) dinta. Kawai cewa
nayi ka gayamin frontward and backward size din matar ka”. Kan Abdulrasheed ya shiga duhu
da shirmen Kiki, yace “meye kuma front and back?” Kiki ta hau dariyar shakiyanci sabida yadda
Uncle Prince yayi maganar cikin yamutsa fuska dole ya baka dariya tace “brazier da panty dinta
nake nufi, gani gaban wasu masu azabar kyau, amma bansan size dinta ba”. Da karfi Prince
yace “Kiki! If I don catch you….” tayi maza ta kashe wayar don kamar zai fasa kunnenta da ihu.
Itama ta san da a kusa suke yau ko Taiwo bata isa kwatarta hannun Uncle ba, in ya murde
kunnenta.
Ya kashe wayarsa yana fadin “Oh my God! Kiki ta girma, har ta fara raina shi, don ya maida
kansa abokinta.
Ya koma ya kishingida, amma barcin da yake so yayi yaki zuwa sam. Sai juyi yake gefeda
gefe akan sofa-bed, maganar Kiki ta jefashi cikin wani yanayi na begen yayi auren don yasan
yana missing wata rayuwa da bait aba shiga ba har shekarun girma suka riskeshi, sai kuma
bacin rai ya biyo baya da wani tsohon tunani y gilma masa… A can baya shekaru masu dama da suka gabata ya taba sayawa Haseena brazier da Panty
da hannunsa, itace da bakinta ta gaya masa size tace ya sayo mata, a lokacin ne ma ya taba
sanin wani abu brazier, da wannan tunanin dana kadaitacciyar rayuwarsa wadda bai nemi
komai ya rasa a cikinta ba sai macen aure kadai, alhalin yanada tabbacin cikakkiyar lafiya ta
kowanne dan adam a tare dashi, idan kuma by now ya rasa mazantakarsa ne duk ba mamaki,
watakila yawan shekarunsa yasa ya rasa feeling na manhood dinma gabadaya, har gashi ‘yar
da ya haifa ta isa aure, da wannan tunanin mara dadi kuma mai sosa zuciya barci mai nauyi ya

dauke shi.
Yana fadawa ransa da zuciyarsa cikin barcin da ya debe shi mara dadi, mai wani irin nauyi;
hatta matan aljannah (hurul eeni) in aka bashi zai ce baya so! Ko kuwa yace ya yafe!! He is not
destined to experience that kind of life!!
**** **** ****


1/RABI’UL THANI HIJRIYYAH
P
rince Abdurrasheed Idris Akanni, yana wannan barcin mara dadi agareshi kife da ciki (rub da
ciki) akan ‘sofa-bed’, irin kwanciyar da bai san ma yayi ba don tun suna kanana Nenne ke gaya
musu bata da kyau ga musulmi, mafarkai barkatai masu alaqa da aure da ‘ya’ya na ratsawa ta
cikin barcin nasa mara dadi. Daidai lokacin da Turaki of Ilorin (mai bin mahaifinsa a haihuwa) ya
mikawa Malam Barau Hamza (madaurin aure Aisha-Siddiqah) wato wan mahaifinta sadakin
Abdurrasheed na dankwala-dankwalan sarkokin zinare a cikin battarsu, ga “Aisha-Siddiqah
Yunus”.
Aka daura auren nan da nan, bisa tsari da koyarwa irin na addinin musulunci, bayan an shafa
fatiha, kalilan din shaidu kuma sun shaidah, masarautar Gombe data Ilorin da dangin Uwa da
na Uban Siddiqah duk sun shaida domin kowanne bangare ya bada wakilai da suka shaida, aka
fara musabiha a tsakanin iyayen wadanda suka kasance Yoruba da fulanis, daga kowanne
bangare na farin ciki bayan kam]mala daurin auren mai albarka.
Abinda zai baka mamaki shine ko a kafar sadarwa daya ba’a sanar da wannan daurin auren
na Prince ba, wannan kuma ya faru ne bisa umarnin Emir, daga nan aka wuce fadar Uban
kasar Gombe inda za’ayi reception na bayan daurin aure tsakanin dangin Siddiqah maza,
dangin Nenne da kuma Akanni’s dake nan har lokacin. Sun kwashe akalla sati guda kenan a garin Gombe suna gudanar da komai cikin nutsuwa har
alkawarin Allah ya tabbata a yau Juma’ah daya ga watan Rabi’ul Thaani da Siddiqah ta tabbata
matar Abdurrasheed.
**** **** ****

An daura!”.
Dade ya gayawa Nenne, fuskarsa fal murmushi kamar tana kallon shi, ya kara da cewa “sai ki
daukota ki dawo da ita Gombe toh, kin kama musu ‘ya kin rike daga zuwa asibiti, at least tayi
sallama da iyayenta ko, in yaso su kawo ta da kansu”.
“Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Alhamdulillah!
Kawai Nenne ke maimaitawa a fili.
Nenne ta shigo dakin da Siddiqah take da wani irin annuri a kyakkyawar fuskarta irin wanda
Siddiqah ko wani dan adam ko ‘ya’yanta babu wanda ya taba gani a tare da ita, zuwa yanzu
alamu na raunin ciwo sun dade da bayyana a tare da ita, tana dai daurewa ne tana kuma
karfafa jikinta da son ayi biki a gama lafiya kafin ta tafi Morocco ayi mata surgery, sai ta tadda
Siddiqah tana hada kayanta a trolley dinta hajaran majaran, fuskarta fal damuwa da ci da zuci.

“Siddiqan Nenne yaya dai? Kayan menene haka aka dannawa a jaka ba ko ninki? Ko mun
miki laifi ne za’a yi mana kaura?”
Cikin damuwa Aisha-Siddiqah ta dago ta dubi Nenne tace “Gida nakeso zan tafi, baku yimin
komai ba Nenne sai alkhairi, na duba date ne a kalanda naga gobe za’a koma makaranta
shiyasa nake hada kaya na, kinga har na cinye hutun ma a nan, ban ma Ummana ko kadan
ba”. Nenne ta karaso cikin dakin ta dafa kanta cikin tausayi da wata sabuwar kaunarta, tace
“babu laifi Siddiqah munyi waya da Umman naki ma, tace goben dama zaki koma saboda
makaranta”. Siddiqah ta hau murna.
“Allah Nenne ba tsokanata kike ba gobe zan koma Gombe?”
Sai ga Siddiqa tana far’a tana dariya kamar ba itace yanzunnan cikin damuwar data sameta
ciki ba.
Nenne tace “wannan ‘mood swing’ haka Aisha ai sai kisa inyi tunanin mu din ba kya jin dadin
zama damu ne, ko nida ahalina bama kyautata miki a kan guiwa kike”. Siddiqah ta rufe ido tana
jin kunya, sai ta kara fadada far’arta, tana “a’ah Nenne ba haka bane, nayi kewar Umma na ne
da yawa, kin san ban taba zuwa ko’ina na kwana ba banda makaranta, sai nan, ko gidan ‘yan
uwanmu na Kumo muka je da sallah bana yarda in kwana”.
A washegarin ranar Nenne da kanta ta maida Aisha Gombe. Kai tsaye suka zarce zuwa
gidansu Aisha kafin ko’ina. Nenne bata ko jima ba tasha kunun zaqi da cincin da aka sauketa
dashi don basu samu Umman Siddiqah a gida ba sun fita da Baba Yunusa sayayyar wasu daga
kayan auren Siddiqah duk kuwa da Emir yace a gaya musu yarinya kadai zasu dauka zuwa
Ilorin. Sai ‘yan uwan Ummanta fal gidan. Ganin suna neman fallasawa a gabanta ta hanyar
kiran Siddiqah da “amarya oyoyo!” Da ake tayi don haka suna gaisawa aka sauke kayan
Siddiqah Nenne da direbanta suka juya a gurguje zuwa gidan Sarkin Gombe, suna tafe suna
waya itada Haj. Zainab. Inda Nenne tace da ita a shirya amarya gobe-gobe zasu dauketa su
wuce Ilorin bisa umarnin Maimartaba. Haj. Zainab ta kawo uzurin cewa a kara musu kwanakin
tarewa su gama shirinsu a nitse, Siddiqah tayi sallama da danginta su kuma samu su lallasheta
akai, tayi mata shirin aure kuma da ya dace. Nenne tace.
“Kada ki damu da wannan Zaynaba nima Uwa ce, uwar kuma ta ‘yaya mata, nasan me kike
nufi, in lokacin tarewar yayi zan yiwa Siddiqa abinda ko su Murjanatu ban yiwa lokacin aurar
dasu ba.
Zuwa yanzu dai Ilorin za’a isa da ita ga Emir da dangin mahaifin su. Kin gama mana alfarma
ai tunda kin bamu diya kun gama komai, ku dai yi kokarin sanar da ita da lallashinta daga yau
zuwa gobe”.
Da haka sukayi sallama Haj. Zainab da Nenne, itada direba suka karasa fadar Gombe.
Umman Siddiqah kuma ta gayawa Malam Yunus isowarsu bayan sun gama waya da Nenne,
don haka a gurguje suka karasa sayayyar abinda suke yi suka koma gida.
Kukan Petel tun daga soron farko shi ya fara bakuntar kunnuwansu.
Daidai lokacin da suka sawo kai tsakar gidan, sai suka ji muryar Addar Kumo, sarkin
kankanba wato kanwar Malam Yunus Magajiya da tazo daga Kumo tana ce da ita.
“Shin wai laifi ne don su Hasssilo sun kira ki amarya? To ko kina nufin baki san an daura
aurenki bane tun jiya, da Dan Sarkin Yarbawan Ilorin take ko Ibadan??”
“Sun jika mana aiki!” Inji Umma cikin bacin rai, tana karasawa cikin gidan da sauri har zanin

ta na kuncewa. Siddiqah na ganin shigowar Ummanta ta hau ja da baya a firgice, idonta cikin
na Umma tana tambaya.
“Umma wai da gaske ne?”
Umman ta mika hannu zata rikota sai ta goce. Ido fal hawaye tace “ki gayamin Umma da
gaske suke? Wai an yimin aure bada Ishaq ba? Umma wai da Bayerabe? Shiyasa kika kaini
gidan Yarbawa na zauna dama Umma?
To makarantata kuma fa Umma? Don Allah kada kuyi min haka!”
Umma na isowa don ta rike Siddiqa dake kuka tana mazari sai gani tayi yiiip! Aisha-Siddiqah
ta fadi kasa ta mimmike mata.
Umma cewa take “ku bani inhaler”. Addar Kumo na fadin “ki nutsu Zaynaba, ki gane wannan
ba tashin Asma bane, shidewa ce (suma) ne”. Malam Yunus na karasowa bai ce komai ba, sai
kawai ya kinkimi Aisha a kafadarsa zuwa motarsa, sai asibitin da take da file wato FMC Gombe.
**** **** ****

A can gidan Sarkin Gombe kuma su Nani Oummana abin nema ya samu, shirin biki ya
kacame ka’in da na’in, bikin jikan da aka jima ana jiran zuwan ranar aurensa a zuri’arsu Nenne
Sappa, duk da Nenne tace bata son biki, sabida bata jin dadin jikinta. Uban kasa yaki
amincewa, yace ta kwanta a daki ta huta ta barsu suyi. Abdulrasheed ne, dole su yi biki kona
kwana uku ne, tunda dangin ubansa ma zasu yi irin nasu a Ilorin.
Yayinda can gidansu amarya hankula ba’a kwance suke ba suna asibiti tun faduwar Aisha
suke asibitin a hannun likita Umar. Ko a lokacin Haj. Zainab sunyi waya da Nenne ta gaya mata
ga akori-kurar kayan abinci nan an taho saukewa sabida bakin da suka zo biki, komai na al’adar
bikin gidan Sarkin gombe an hado musu dashi rankatakaf. Hajiya Zainab bata gaya mata Petel dinma tana asibiti ta rikice musu da sambatu ba. Don
kada hankalinta ya rabu biyu, ko daga jin muryarta ta fahimci Nenne bata da lafiya, sai Haj
Zainab ta roki alfaramar Nenne, tunda itama bata jin dadi kan cewa suna so a daga daukar
amarya zuwa kwana uku don a samu a sanar da ita ko me ake ciki a kuma samu a lallasheta. Nenne ta amince da hakan inda ta sanar da ita matan ‘yan uwan mijinta masu daukar amarya
zasu zo daga Ilorin, zasu hadu da nata ‘yan uwan su dauki amarya. Likita Umar shine likitan
asmar da Petel take gani tuntuni shi suka samu nasarar gani a hannunsa Siddiqah take, kuma
yana kula da ita yadda ya dace don dama sun saba sosai shi da ita, yace ba asma ce ta tashi
ba, suma tayi dan firgici, ya bata (bed-rest) na kwana daya don yanaso yayi counseling dinta
tunda Haj. Zainab ta gaya masa aure ne aka yi mata bagatatan.
Koda ta farfado ma bin su Ummanta take da ido ta dauka asma ce ta kawo ta asibiti ta manta
shaf da abinda ya faru din.
Duk yadda Likitan ya iya lallashin Siddiqa don ta gaya masa abinda ya firgitata da bakinta
yau Siddiqah shiru tayi masa, tace ya tambayi Umma don ita ta manta. Umma dake gefe tace.
“Likita ba abinda aka yi mata rigima ce irin tata daga dawowarta bata ko ganmu ba, ta tsinci
magana a wajen ‘yan uwanta shikenan ta fadi ta sume min. Umma ta kara da cewa “Petel dina, ai kinsan daga ni har Abbanki masu son farin cikinki ne,
ba abinda zai daga miki hankali ba”.
Sai a lokacin Siddiqah ta tuno exactly me ya faru daga shigowarta gidansu daga Lagos. Da
sauri Siddiqa ta katse Umma hawaye nan da nan ya cika idonta. “Umma! Kuna son farin ciki na

shine kuma aka aura min Bayerabe da ban ma san shi ba?
Umma kinfi kowa sanin yadda bana son yarbawa”. Dr. Umar wanda mahaifiyarsa ‘yar kabilar
Yoruba ce, bai san sanda ya kufula yace da Siddiqah.
“shi Bayerabe ba mutum bane Aisha?”
Ta yi maza ta sunkuyar da kai, hawaye ya zubo mata tace “amma ai inada miji, kuma ban
gama makaranta ba”.
Abban Siddiqah da Baba Barau tare suka shigo lokacin, suka ja kujera suka zauna ta gaban
gadon Siddiqah aka cigaba da lallashin tare dasu. Muryar Abbanta abin tausayi yace
“Aishah-Indo Siddiqah, to uban Ishaq din yace bazasu aureki ba tunda kinada cutar numfashi”.
Aisha ta zaro ido daga kwance, Baba Barau ya gyada kai ya gyada mata kai cikin tabbatarwa,
yace “to su kuma wadanda kikewa kabilancin son ki suke da asmar taki, da dukkan zuciyarsu
sun karbeki cikinzuri’arsu, Ubanki kin ganshi sabida ya faranta miki ya kuma fita hakkinku don
yasan kinason yaron nan shima yana sonki da gaske sai da ya yi tattaki ya isa ga mahaifin
Ishaqa, amma bawan Alllahn nan ya wulakanta mu, don haka ya rage naki ki nemawa kanki
mutunci kije inda ake son ki ko ki tsaya shirmen banza a inda ba’ayi dake saboda lalurarki.
Hajiya Sappa Uwa ce da kowane Da zai so ta za uwarsa. Ke ya kamata ki bada wannan
shaidar, kowadanne iyaye zasu so hada zurri’a da ita saboda karamcinta da girmama dana dam
da halin tawali’u, ai dai kin dan zauna da su zuwa yanzu ya ci ace kin san ko su su waye.
Inna kara jin Kalmar “Bayerabe” ta fito a bakin ki wallahi sai na kumbura miki shi, don dama
yayi miki kadan”.
Suka taru su duka har likita Umar suna tausarta, likita yace “Aisha kibi zabin mahaifinki nina
gaya miki in sha Allah bazaki nadama ba, a cikin biyayyar iyaye babu nadama kin ji?
I am a Yoruba man by maternal tribe, ina tabbatar miki mun iya rikon aure mun iya tattalin
matanmu da girmama su”. Umma tace “wallahi wallahi bamu yi miki zaben tumun dare ba duk
da ban san shi ba ban kuma ganshi ba ko a hoto, zuri’ar Hajiyar Lagos ba yarbawa ba ko
inyamurai ne zan basu ke albarkacin ta da addu’ar da naji tana yi a filin Arfah, tunda dai kalmar
shahada ta hada mu bakidaya.
Ni bansan ina kika koyo wannan kabilancin naki ba, ni dai baki taba jin na ce wani da ba
bahaushe ko bafillace ba daban yake da sauran mutane ba”.
Ko ta ina sun rufu a kanta basa ko bari ta ce uffan, wannan ya koro

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login