Showing 36001 words to 39000 words out of 43117 words

Chapter 13 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf


danne-dannen da basu san me yake yi ba a ciki, ya samu jirgi mai tashi zuwa Qatar a gobe,
don haka yayi maza ya yi booking, ya san dai Nenne bazata hanashi komawa bakin aikinsa ba
tunda ta san yanke komai yayi ya taho sabida lafiyarta ba don yana cikin hutu ba. Nenne ta juya tayiwa Murjanatu kallon disappointment, tace a sanyaye “Maman Kiki, ina
tsarabar ‘yar uwarki kika baiwa kowa banda ita?”.
Aunty Murja ta juyo tana kallon Nenne, idonta na bidar tambaya, Nenne tace cikin lallashi
“Kada ku manta she is now part of the family, in zakuyi irin wannan zaman na zumunci a

gabanmu da rabon kaya kona menene ku dinga hadawa da ita”.
Har suna hada baki wajen cewa “toh Nenne ai bamu ce kada tazo nan ta zauna ba?” Nenne
tace “kun kirata cikin sakewa ta ki zuwa? Aishatu-Siddiqah bata da saurin sabo sai a hankali
nikaina ta saba dani, ita kadai ce ‘ya a gidansu da mahaifiyarta kadai ta saba, zata saba daku
idan kuna janta a jiki!”. Ta fada a hankali cikin lallamin ‘ya’yan nata idonta na kallon reaction dinsa. Prince, wanda
har lokacin fuskarsa take expressionless, kansa na bisa wayarsa.
Mikewa ma yayi daga bisani fuskarsa a sake yana fadin “I booked my flight back tomorrow
Nenne, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai albarka, ina son ganin ku hakannan
complete family, I am missing this!”.
Nenne ta bishi da ido tana mamaki, kamar bai yi noticing maganar aurensa ba? Kamar bata
gaya masa zancen aurensa da Siddiqah ba? Ko kuwa iya shege ne abun irin na su na diyan
yarbawa?
Zai kuwa ga iya shege albarka Annabijo (da albarkar Annabi).
Sai kawai ta bi shi da adduar data saba yi masa wato.
“Allah hokku sa’a Hammansu ko a yahi dabuttugo albarka Annabijo”.
Kuma ko a fuskarta babu bacin rai. Watakila Prince harda auren aljana a tare da shi ta ke
gayawa kanta.
Namijin da zai ga mace tamkar Aisha-Siddiqah a matsayin halalinsa amma zuciyarsa bata ko
motsa ba, manhood bai motsa masa ba.
Sannan bai yi wani action ko kankani da zai nuna cewa ya san da wanzuwarta ba, alhalin ko
jiya tana jin yadda Dade ya zaunar da shi kusan awanni uku yana labarta masa yadda aurensa
da Siddiqah ya wakana, tun daga haduwar Nenne da Hajiya Zainab a filin Munna ya dauko
masa labarin har kawo zuwa yau. Har Dade yayi yagama tana jin su daga kwancen da take uffan wannan Prince Abdulrasheed
Kehinde bai ce ba.
Dade da saurin hassala a lokacin taji yace da shi “ka samu lalurar ji ne ko Kehinde?”
Dan murmushi ya yi cikin kasaitarsa yace “Dade, kunnena ras suke. Banida abin cewa ne,
banda Allah yasa hakan shi yafi alkhairi a gareni daku da yarinyar bakidaya”.
Wannan ne yasa Nenne bata kara yi masa zancen Aisha ba ita, koba komai he is now aware
of it. His I don’t care attitude ne ya bata mata rai ta fasa ce masa ya tafi tare da Aisha. Aisha tafi
karfin ta cusa ta wajen namiji, ta barwa Allah wannan ikon nasa. Su dai sun sauke nauyin dake
kansu da addini da al’ada suka dora musu sauran ya rage nasa. Yarinya dai data dauko daga gaban uwarta da ubanta zata kula da ita kamar koma fiyeda
tana gabansu.
Don haka bayan barin sa wurin Nenne ta cigaba da yiwa Aunty Taiwo ciwon bakin tayi rabon
tsaraba ta manta da ‘yar uwarta.
Murjanatu-Taiwo, nan ta hau babbaka dariyar shakiyanci nan ta maida Nenne Kakarta, tana
cewa “Nenne mai ‘yar fingi-fingi, kamar kazar mayu, ina ganin sai kin hada da addu’a fa, naga
Kehinde yarinyar nan bata masa ba”. Ta kara babbako dariya tace.
“Allah na tuba Nenne, wadanne irin matane Kehinde bai gani a kasashen duniya? Wadanne
irin mata ne basa bibiyarsa kamar su bashi ransu har gida da ofis, Kehinde da in mata dari
yakeso a rana zai aura, sai kece mai idon gano masa macen aure Nennenmu?

Nenne a shawarce ki maida yarinyar nan ga iyayenta, ki basu hakuri kawai. An daina irin
wannan auren yanzu”.
Nenne tace da kakkausan lafazi, “Murjanatu! Shin ke kika haifa min yaron nan ko ni na haife
shi?
To in har ba ke kika haife shi ba, baki kuma shayar dashi ba, sannan baki tayani jegonsa da
rainon cikinsa ba daga yau na cire ki daga sha’anin auren sa.
Shiyasa dama tun farko ni ban saka ki ba don nasan dama tunaninki akan Abdulrasheed
ragagge ne sai abinda yakeso kike bi, ba abinda zaifi masa alkhairi ba. Shiyasa tun farko kika
biye masa akan waccan yarinyar.
Na yarda har yanzu da sauranki Murjanatu a sanin baiwar da Allah yayiwa 'ya'ya mata,
yawan shekaru da zurfin ilmi ko cikar jiki basu ne ba. Haka naki shekarun basu yi miki amfani
ba, tunda har kike tunani akwai namijin da yafi karfin wata bafullatar mace don kawai bata da
wayewa irin ta kabilunku. Murjanatu ta rage dariya ganin Nenne ta hassala sosai, gashi bata da lafiya, tace “Nenne ni
dai ba ruwana fa kiyi hakuri, I rest my case akan maganar nan, shawara ce dama na bayar
sabida saninda na yiwa Kehinde, amma kiyi hakuri ga ku ga Kehinde”.
Nenne tace "ki yi fatan alkhairi ko ki fita daga sabgar da ba'a saka ki ba tun farko".
Ai kuwa a washegari tunda asubah Prince ya tashi zuwa Qatar ko Dade sai a masallaci
sukayi sallama da shi.
Dade yaso yace dashi Siddiqah fa? Yaga cewa wannan ba wurin da ya dace suyi maganarta
bane, amma ya sha mamaki da cikin daren Nenne tace masa gobe AbdulRasheed zai koma har
yayi mata Sallama, ta rokeshi kada ya takura masa kan tafiya da Aisha wato yace sai sun koma
tare, ya zuba masa Ido, ita bazata cusa masa ita ba don saya mata martaba a wurinsa don ta
lura kawai shida Taiwo basuyi na'am da zabinsu ba. Dama kullum bakinsu daya.
Kasancewar bata da koshin lafiya sai bai cikata da magana ba kawai ya gyada kai. Sukayi
sallama da Dan nasa yadda suka saba yasa masa albarka ya kuma yi masa addu’ar da ya saba
yi masa. Seun, ya wuce dashi zuwa filin jirgi.
Kwanansa daya da tafiya itama Murjanatu ta koma gidanta a Ilorin.
Gidan ya koma yadda yake wato su ya su. Sai lokacin da Firdausi ta tabbatar mata Hamma
ya koma, Auntynsu Murja ma ta wuce gidan mijinta, sannan Siddiqah ta soma fitowa falo cikin
su yadda ta saba ta sake.
Nenne ta yankewa kanta shawarar bazata sawa ranta damuwar komai ba, cututtukan nan na
zamani na zuciya da hawan jini ba karya bane. Ta samu ta sha da kyar daga cyst and renal
stones. Bari ta maida hakali kan abinda zai fishsheta da ibadarta ta gama da damuwar
Abdulrasheed kuma. Ya rage nasa ya gama da yazo ya dauki matarsa a sanda ya shirya ko ya cigaba da
rayuwarsa a jirkice yadda yake yinta.
Ita dai ta san ba zata kwari yarinya ba idan ya shekara bai dauketa ba, zata mayarwa
iyayenta dake ganin mutuncinta ta ce musu ta gane bashi da lafiyar iya yin aure, wanda
mutuncin ne yasa aka bashi ba wani abu nasa ba. Bazata yi sanadin da zumuncin ta da Haj.
Zainab wanda sun ginashi ne saboda Allah zai lalace akan ‘ya’ya ba. Allah ya gani wahalar da ta sha a baya akan damuwar rashin auren Abdulrasheed, bazata
kara maimaitata a yanzu ba. Ta cimma shekaru na girma da take bukatar tattalin lafiyarta.

Kehinde ba shikadai ta haifa ba. Amma shikadai matsalarsa ke wahalar da ita, bazata taba
lafiyarta dake reto saboda shi ba, alhalin shi yana can cikin jin dadin rayuwarsa. Tunda ta
wanke masa ‘labelling’ na rashin aure (tambari) wanda addini da al'ada ya dora musu sauran
hukuncin na rayuwa da matar ko a'ah nasa ne ba nata ba. Nenne ta sha mamaki da Aisha Siddiqah ta koma rayuwar walwalarta cikin gidan bayan barin
Taiwo da Kehinde gidan. Wato itama ta gane Taiwo bata yin ta kenan. Allah sarki! Yo aka ce
shimfidar fuska tafi ta tabarma, sannan ido ba mudu ba amma ya san mai maraba dashi, kai
tsaye Aunty Murjanatu bata boyewa kowa ba matar Kehinde bata yi mata ba, including
iyayennasu da suka hada auren bata yi musu alkunya ko Karar ganin ido ba wajen nuna musu
basu yi zabin da ya dace ba.
A wurin Siddiqah gidan har wani fili ya kara da iska mai dadi da Hamman su Firdausi ya bar
shi. Wanda iya hangenta na kushe dan adam ko kabilan da ba nata ba data saba kushewa ta
kasa hango ta ina zata iya kushe Prince Abdulrasheed (Kehinde) Idris Akanni.
He's perfect, duk da ana cewa duk mutum tara yake bai cika goma ba.
Gani uku ko hudu ta yi masa cikin gidan kuma ba wai ta masa kallon kurilla bane ko a
asibitin. Amma tashin farko ta gane shi din ko cikin mazan Yoruba kyakkyawa ne na gaske
ashe. Classique. Jinin fulanin Gombe ya wanke shi tas! Akwai abinda ya burgeta guda daya a
tare dashi wanda shi kadai ta rike a kamanninsa, “Tabon Sallah_shaidar Sujjadah” wanda ke
shimfide can farkon saman goshinsa.
He didn’t give her a second look either… Iya abinda ta hango a tare dashi kenan, bata hango
maraba ko rashin maraba da ita a tare Abdulrasheed ba. Kai ko kai ne Sigmund Freud ko
Wilhelm Wundt wurin karantar dan adam bazaka karanci komai akan Siddiqah a tare da shi ba.
Nenne na kara jin karfin jikinta, ta koma harkokinta na cikin gida, aka maida Aisha
makarantar su Kiki ta jeka ka dawo.
***** **** ****
Malamar da aka daukowa Siddiqa ma Bayerabiya ce mai suna Mrs Yemisi.
Ana saura kwana biyu ta fara zuwa makaranta wato asabar malamar ta fara zuwa suka soma
karatun bita. Muhimmin abinda zata koya mata shine Lissafi da Ingilishi.
Siddiqah ta fara karatu daga takardar transfer da Babanta ya karbo mata daga FGC Billiri, ya
aikowa Dade, ta fara ne daga (first term) na aji shidda inda daga shi sai zango na biyu sai zana
jarrabawa
Ranar data fara zuwa a darare take, ba abinda take tsammani a makarantar sai yaran
yarabawa zasu yi mata “Atule bahaushiya!” Irin wanda take yiwa Bisola. Tunda ta gama
saddaqarwa alhaki kwikwiyo na Bisola keta walagigi da ita a cikin Yarbawa.
Amma akasi ga tunaninta daliban kowacce harkar gabanta take yi babu wadda ta lura da ita
balle su kula cewa ita din bahaushiya ce, har saida form master din ajin ya gabatar da ita ga
sauran dalibai a matsayin sabuwar daliba daga Gombe suka ji sunanta na hausawa ne.
Tun yinin rana ta farko a makaranta Siddiqah ta san cewa makaranta tazo, wadda ta amsa
sunan makaranta, ta ko’ina ta zarta Billiri zafin karatu, ba hadi ko kusa. Turancin makarantar har
yaso yafi karfinta.
Don haka Siddiqah ta dan ture kabilancin nata a gefe ta soma karatu tareda ‘yammata
Yarabawa da sauran kabilu, amma yorubawa sun fi yawa. Har bada jimawa ba ta soma tsinttar
wasu kalmomi na yarbanci irin su “Zo” (Wa) “Jeka” “bari” “good morning” (Ekaaro) da sauransu.

Ta ga cewa ma akwai hausawa tsilli-tsilli a ajinnasu, wadanda galiban aiki ya kawo iyayensu
jihar Lagos, don taji ana kiran jakadiyar ajin (class monitress) din da suna Maijidda Sulaiman
Yabo.
Cikin sati daya Aisha Siddiqah ta saki jikin ta a makaranta. Mrs Yemisi kuma na kokari da ita
a gida, don ganin cewa ta haye Ingilishi daa Lissafi a yayin zana jarrabawarta ta kammala
sakandire.
**** ***** ****
KIKI
A karshen wannan watan da ake ciki ne Kiki ta kusa kammala course din da take yi a LA
tazo Lagos hutu don gaida Kakanninta.
Da shigowarta babban falon gidan ba wanda idonta yayi tozali da shi sai Aisha-Siddiqah,
a lokacin tana zanawa Firdausi lalle a kafafunta.
Sha’awar abun ya kama Kiki ba kadan ba, don Kiki akwai son abubuwan hausawa amma
bata da kawaye hausawa, Aisha sai kallon Kiki take tana admiring komai na Kiki a ranta; ga
tsayi, ga kiba kamar Aunty Murja, don ita Siddiqah duk wani mutum mai cikakken jiki sha’awa
yake bata, ta kasa gane cewa jikin ta ma abinso ne musamman ga wadanda ke neman weight
loss. A shirye suke dasu biya makudan kudade in zasu samu irin jikin ta.
A ganinta Kiki komai ta hada, ga iya ado sannan ga kibar, ga hutu yabi jikinta, ya hadu da
iyayi da rawar kan wayewar 'yammatan zamani masu yawo a duniya, duk wannan ya nuna a
tare da Kiki.
Ita kadai amma duk ta ishi gidan da karadi.
“Nenne bakuwa kukayi ne, halan daga Gombe? So Pretty and Georgeous!”
Nenne ta sha mamaki da Taiwo bata gayawa Kiki maganar Siddiqah ba, sannan shima duk
yadda yake da Kikin ace bai mata zancen ba. wannan kadai zai nuna maka (how uncared they
are) da zancen Aisha daga Taiwo din har Kehinde dinnata.
“Umh!” in ji Nenne cikin takaicin Murjanatu, tafi takaicinta fiye da Kehinde saboda da ace ta
karbi Aisha 100% da kyakkyawar fahimta akan zabin da ita Nenne tayi da komai zai zo da
sauki, don ita kadai ce zata iya convincing din shi ya kalli Aisha da idanun rahma, har ya fahimci
alkhairin dake tare da ita don da farko shi da bakinsa ya yabe ta kafin yaji maganar aure a
tsakaninsu, Taiwo da taga dama zata iya taimakawa kwarai Kehinde ya bude zuciyarsa ya
samar ma Aisha gurbi ko yaya, ya manta da komai da ya jima da sakawa ransa a kan mata.
Amma har gobe tana kan bakanta na bazata cusa Aisha ga Prince ba, ta ma fara tunanin da
Aisha ta gama karatun data sa aka katse mata a garinsu ta karbi sakamakonta na WAEC sai ta
maida ita Gombe hannun iyayenta cikin salama.
Ta san Aisha akan dole take zaune tare dasu don ba yadda zata yi ne amma zuciyarta tun fil
azal bata son mu’amala da yarbawa balle alaqa mai girma ta aure.
Fin karfinta iyayenta suka yi, sai kuma kirki da karamcinsu iyayen Abdulrasheed din a gareta
ya taimaka wajen kwantar mata da hankali ta zauna. Amma Prince da al’amarinshi basa
gabanta. Har Nenne ta soma ganin laifin kanta ta dinga tunanin anya bata dauki alhakin Aisha
ba, data hada wannan auren? Ita dai tasan manufarta kyakkyawa ce akai, ta kwadaitu da hada
tsatso da kyakkyawan iri ne, mai addini mai albarka, sauran kuma Allah shine shaida amma
bata da wata manufa cikin hada auren Siddiqah da Prince. Bata san ya zata yi ta fahimtar da
Taiwo da Kehide hakan ba. Idan Taiwo bata yi na’am ba, mawuyaci ne ya zama Kehinde zai

taba yin na’am, because they share each others’ feelings.
A tunanin Nenne Taiwo da Kehinde sun hada baki ne akan su yi wa Aisha kora da hali,
wanda aka ce yafi kora da sanda, akan wannnan gallafirar Haseenah din rainon Taiwo.
Ita kuma zata kyale su suyi abinda suka ga dama. A rayuwarta bata matsawa kowa yayi
abinda ba ra’ayinsa ba, ta dauka farat daya Murjanatu in taga Aisha zata karbeta da hannu
bibbiyu da zuciya daya, ta zamar mata uwar daki a cikin su, shikenan ta Kehinde zai zamo mai
sauki, amma har gara shi din, bai kushe ba amma bai ce komai ba. Ita kuwa Taiwo muraran ta kushe Aisha har tace a mayar da ita ga iyayenta kai tsaye. ‘Ya’yan
yanzu ne ba’a tuka su, musamman a shekaru irin nasu shida Murjanatun, babu karamin yaro a
cikin su da zata tankwara ta karfi akan dole yayi abunda take so, musamman Abdulrasheed
yadda yake gudun bacin ranta da gudun zuciyarta yake iya kokarinsa wajen kyautata mata da
‘yan uwansa, itama bazata yi abinda zai takura shi ba, duk da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login