Showing 42001 words to 43117 words out of 43117 words
Chapter 15 - Aisha Saddiqa part 2 Hausa Novels by Takori .pdf
kalmar shafa labari shuni ke nufi ba, ta san yana nufin dai kamar ta
faye surutu ko fadi ba’a tambayeki ba. Ta hau dariya tana cewa “da gaske nake duk abinda na
gaya miki ni bana karya, ke nafi ganin dacewar Uncle ya aura kuma zan je har Qatar in sameshi
akan hakan”. Siddiqah tace da karfi “Kiki! Ni nace miki banida wanda nake so toh? Ba kyau cin naman
mutane ki daina zancen wata budurwarsu. Is better you mind your business Kiki, ki rabu da sa
damuwar kowa a ranki. In Allah yayi matarsa ce tunda Mum naso, sai kiga anyi”.
Kiki tayi maza tace “ba amin ba! Because my Uncle has a pure heart, I assure you he’s pure
and clean, with a golden heart! Allah bazai bashi mace wadda ba mai tsarkin nasaba ba. Bazai
taba auren mara asali ko lalatacciya ba in sha Allah”.
Amma ko bayan gama wayar su da Kiki, Aisha sai tayi jimm! Tana jin maganganun a ranta.
Ashe shiyasa bata samu reception a wurin Aunty Taiwo ba, akwai wadda ta dade da yiwa dan
uwanta tanadi.
Banda haka bata ga me tayi mata ba da ko gaisuwarta sama-sama ta amsa kuma a
shaqare.
“Umh! Su suka sani” inji Aisha. Babu wani Bayerabe data saka a ranta balle damuwarsu ta
dameta.
Sati biyu bayan nan su Aisha suka fara zana WAEC, wadda zata dauke su tsayi sati hudu
suna zanawa.
Watarana Siddiqah ta fito dakin jarrabawa ta tadda Seun yana jiranta zai dauketa zuwa gida,
suka kamo hanyar gida, sai taga Seun ya karkace kan motarsa ya tafi wani wurin da ita. Saida
suka isa wurin ta fahimci ko’ina ne, wata ma’aikata ce ta shige da fice a jihar Lagos (immigration
office). Da ta tambayeshi ko’ina zasu je yace “tayi hakuri Dade zai dauka. Suna isa ta hango dade a
nesa yana jiransu, sai ya karaso jikin motar tana kokarin fitowa cikin girmamawa don ta gayar
dashi, yace ta biyoshi zuwa ciki.
Tare suka shiga ciki yasa aka mata hoto da finger-print. Seun ya dauko su zuwa gida
gabadaya. A kan hanya Dade na tambayarta yaya jarrabawar tana gaya masa ita bata da
matsala har suka iso gida.
**** **** ****
BAYAN SATI HUDU
MURFIN LITTAFI NA BIYU
“Dade har ka kwanta ne?”
Nenne dake karasowa gabansa ta tambaya, ganin shi a kwance, ido a lumshe kamar baya jin
dadi, sai ta zauna gefensa ta dora hannu akan goshinsa, zafi rau.
Dade ya bude ido da suka kada yayi mata murmushi, kafin yace “masassara ke son rufe ni
tun dazu” “sannu Dade, to tashi ka sha magani”. Ya yunkura ya mike zaune akan gadon ita
kuma jiki na rawa ta doshi (first aid box) dinsu don dauko maganin.
Dattijan biyu na matukar kula da junansu, kullum kamar sabon aure haka suke mu’amalarsu,
ta ballo maganin kan hannayenta ta bashi ya kora da ruwa sai ya koma ya sake kishingida.
Nenne ta yi amfani da wannan damar ta zauna a jikinshi ta soma magana.
“Dade nace dama gobe ne Aisha zata zana final paper, ina so jibi in maida ita Gombe in Allah
ya kaimu”.
A kishingide Dade yake, amma bai san lokacin da ya taso zaune ba, yace “zata je ganin gida
ne? Har yaushe aka yi auren Hajiya Sappa? Ko dai Nani Ummana zaku je ganowa?” Girgiza kai
Nenne tayi, tace “Dade, in ta tafi ta tafi kenan, Allah ya gani na yi nadamar hada wannan auren,
na bata muhimmin lokacina a kansa, don zuwa yanzu na yarda da gaske Abdulrasheed baya
bukatar mace a rayuwarsa.
Na yi nadamar rabo yarinya da iyayenta. Da na san in ya ganta bazai karbeta ba da koda
wasa ban fara ba”.
“Dama ana nadamar aikata alkhairi ne ga haularka Hajiya Sappa?”
Dade ya tambaya idonsa a kanta. Ba tareda ya jira amsarta ba ya cigaba.
“Kada ki karaya, kada ki sare tun yanzu kada ki maida alkhairinki baya. Wanda zashi sama
ya taka tsauni ai yayi kokarin azo a yaba.
You truly made it my dear. Tunda har kin aura masa ya san da zancenta ya kuma ganta ganin
idanunsa, ya kuma san tana zamansa. To kin gama naki, ki barni inyi nawa nikuma.
Da wannan Dade ya lallashi Nenne kan kada ta mayar da Aisha gida, ya soma yi mata
bayanin abinda ya dade yana shiryawa wanda shima Emir ne ya bashi idea din hakan.
“Yana hutun karshen shekara (Annual Leave) a gidan sa na kasar Argentina currently”.
Mu karasa a littafi na uku.
Tare suke.
Taku har abada SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORIN TAKORITES).
10/04/2024
(MASOYA LITTAFAN TAKORI INA FARIN CIKIN TALLATA MUKU JAKADIYAR KAYAN
KAMSHI NA ORIGLAME HAJIYA AISHA LAME (ORIGINAL ORIFLAME AMBASSADOR)
Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai? Kinason mayuka da zasu dace da launin fatarki a
wannan lokacin na zafi kona sanyi? Kinason kamshi na alfarma? Kinason supplements
ingantattu na wellness and meal replacement ga masu bukatar weight loss and weight control?
Kayan kwalliya na kerewa sa’a? Kina bukatar zama Dawisu sarkin ado? Kawai tuntubi AISHA
LAME a lambar waya 07036662633 zaki samu duka wadannan cikin farashi mai inganci da
kyakkyawar mu’amala. Aisha lame karshe ce wajen baiwa faat hakkinta ku tuntubi Aisha ku zo
ku bani labari.
-Takori Sumayyah Abdulkadir
April, 2024