Showing 27001 words to 30000 words out of 39674 words

Chapter 10 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf

mahaifiyar ta, mun yi da kai kafin ka tafi ko sau
daya ne za kaje ku gaisa da ita Sadiya din, amma har yau ban ji ka kara tada zancen ba, gashi
har zaka tafi.
Kasan dai yadda nake da Barr. Hannatu, babu wasa ko rainin hankali tsakanina da ita, bana
so ka je ka shantake a Jeddah babu aure, so nake da ka samu good two or three years ka
dawo gida kayi auren ka in ya so in ma komawar zaka yi ka koma da matar sai hankali na yafi
kwanciya da zaman ka a koina ne, tunda na fahimci kafi son rayuwar Jeddah banda haka da ka
zauna ka cigaba da aikin ka kawai.
Duk da nasan baka da matsala Sarham, tarbiyyah ta Allah bazan ce ni na baka ita ba, amma
Allah ya yi maka tarbiyyar da kowacce uwa zata yi alfahari da ita, saidai kwanciyar hankalin
iyaye a kullum shine ace yaran su sun yi aure a lokacin da ya dace.
Sarham ya nisa, ya ajiye rigar da zai saka a cikin trolley a gefe, kafin yace cikin lallashi Mama
bana so kisa ran ki a irin wannan hade-haden auren na favouritism domin ki dadadawa wasu,
wanda a karshe maimakon ku gyara zumunci sai dai ku kai ga lalata shi, saboda ni gaskiya
Mama bana raayin macen da iyayen ta ke nemo mata miji daga yayan kawaye. Yau da a ce ke da kan ki kika yi wannan raayin, zan iya bi, koda kuwa bana so, amma daga

sanda kika gaya min Barr. Hannatu ce ta nemi alfarmar nace a raina yar ta ta rasa miji ne take
nema mata, gashi ni ba rasa mata nayi ba, na tabbata lokaci ne.
Mama kin san da labarin “Madinah” ba tun yau ba, to wallahi Mama har gobe tana raina, don
nina gan ta naji ina so saboda wasu dalilai, amma na gwammace in hakura da ita tunda ubanta
baya kaunata, kuma daga kanta bana jin zan kara son wata ya mace, daga kanta kuma na tsani
soyayyar bakidayanta. Mama weve had a wonderful time together nida Madinah, for as long as four years muna tare
cikin kauna da fahitar juna, mun yi wa juna alkawura masu yawa amma Madinah ta saka kafa ta
take su tayi fatali dasu rana daya, don haka daga kanta na daina bata lokaci na a kan yammata
wallahi. Duk marasa amana ne. Madinah ta dusar da hasken sauran mata daga idanuna Mama, ba wadda nake ganin farin
ta. In fact, Mama bani da niyyar aure nan kusa.
Ban san me kaddara ta tanadar min gobe ba!.
Mama ta ce in uban Madina baya son ka sabida ya raina ajin uban ka, su wadannan uwa da
uban duka sun zo da kan su sun ce ka yi musu, suna son hada jini da ni, saboda sun san
darajar mu da martabar mu, ni kuwa bana tulawa masoyi na kasa a ido. Amma ban isa in maka
dole ba. Duk abinda uban Madina ke takama da shi na tarin arziki da ilmi da har yake ganin baka isa
auren diyar sa ba, uban Sadiya ya mallaki goman sa,
Da sauri Sarham yace ko ita Madinah ba dalilin da yasa na so ta ba kenan Mama, na rantse
ban taba sanin waye ubanta ba har sai bayan ya yanke alaqar mu.
Na so Madinah ne akan wani dalili Mama. dalilin kuma shine. kokarin ta a karatu. zai fara
bata labarin irin kokarin Madinah da yadda take ‘excelling with high grades a kowacce
jarrabawa Mama ta katse shi da karfi, inda tace bana bukatar ji, na gaji da zancen Madinah
Attahiru Sarham tunda ba itace autar mata ba. Ka karbi masu son ka, ka rabu da tsammanin warabbuka.
In dai labarin nan ne ka bani shi yafi sau shurin masaki, yafi cikin carbi, har na riga na
haddace shi, kana son Madina saboda kokarin ta akan karatu, na gaji da jin wannan, abinda
baka sani ba, Madina ba itace karshen masu kokari ba, Sadiya ma tana da irin nata domin kuwa
Quantity Surveyor ce. Kuma uwarta ta tabbatar min tana son ka sosai, ba wai ita ta ga dacewar
abin ba Sadiyar ce da kanta tace tana son ka.
“Ahap! Anzo wurin. Mama ta bare ta gabadaya. Sarham ya fada kasa kasa su Mama an kara
bare ta, to ai ni Mama bazan taba auren macen da ta ganni wai ta ce na yi mata ba, komai
lalacewar zamani akwai mata masu aji, wadda ba ni na ce ina son ta ba in the first place
hankalina bazai taba kwanciya da ita ba”. Duk ta inda Mama ta bullo don Sarham ya karbi tayin yar aminiyar ta Sadiya Sarham sai ya
zuqe, amma fa cikin lallami da dabara yake bin Mama don su yi rabuwar salama. Ya san kan
Maman sa sarai, yana yi yana dariya da hilatar ta yadda bazai bata mata rai ba.
A karshe Mama ta gaji da jainjar, ta sakar masa inda ta ce Sarham! Na baka shekara daya ka
kawo min matar da kake so ka aura, mai kokari irin Madinah wadda hankalin ka zai kwanta da
ita din, tunda kai dai a kan Madina kowa dakiki ne, to ka nemo mai kokari irin nata, kafin
shekara daya, amma ni wannan Madinar ko zancenta bana son ji. Sarham idan shekara ta zagayo baka kawomin mata ba na rantse Sadiya zan aura maka,

kana so ko baka so, in kuma dauketa in bika da ita har inda kake.
Sarham ya ce to Mama addua zaki yi min Allah ya kawo mai kama da Madinah, fara kamar
balarabiya, doguwa siririya mai gashi yala-yala har gadon baya, sannan mai asalin kwanya a
karatu irin ta Madinah Sorondinki. Tsaki Mama tayi ta tashi ta bar masa dakin don haushi. Ta
sani daga Madina har iyayen ta babu wanda ya damu da shi shi, kadai yake kidan sa yake
rawar sa a kan ta.
Ita kuma bazata taba maraba da inda baa son nata ba.

Washegarin ranar Sarham ya ga cewa ya kamata ya je wa su Inna sallama, kai zai yi kewar
kawar sa Inna Safiyya… yadda baa zato, tsakanin itada Sumayyah bai san wa zai fi kewa ba.
Wata zuciyar a can kasan kirjinsa tayi whisphering a sace, inda tace masa MISKINIYA
KULU!” Da sauri Sarham ya kalubalanci zaciyar sa da cewa capital NO! he will never
HAUWA_KULU, zai yi kewar kowa tabbas, har Surayyah da basa jituwa, amma ko kadan ba zai
yi kewar Maijidda ba, ba don komai ba ko don halin koin kulan ta da miskilancin da take nuna
masa, da rashin maganar ta da sakewa da mutane wanda baya bari ayi sabo mai shiga jiki da
ita irin wanda har zaayi kewar ta don an daina ganin ta a wuri.
Shin wai kodai shi kadai Maijidda take nunawa halin koin kula, da shariya, da miskilanci, da
rashin walwala wani lokacin ma sai ya ga kamar sad face a tare da ita idan taji muryarsa a
gidan su???

Ya isa gidan ana kiran sallahr Isha, Inna na alwalah Hauwa na cin tuwo. Yayi sallama Inna ta
amsa Kulu ko kamar yadda yayi tsammani a cikin cikinta ta amsa masa sannan bacin ran da
yake zargin gani ya dan bayyana kansa a kan fuskar ta. Sai Sarham ya lallaba ya dauke
kwanon tuwon daga gaban ta ba tare da yayi magana ba, ta shafa gabanta don kara kai loma
sai taji wayam, babu kwanon, amma bai sani ba kamshin turaren sa da ya nashi hancinta (Oud
Abyad) ya tabbatar mata shine a wurin ya dauke kwanon.
Baya jan ta da wasa amma yau da yake sallama ya zo, shiyasa ya ke son ko yaya ta kula shi.
Dan murmushi tayi, wani basakkwacen murmushi ta share shi, ta janye hannu ta koma gefe, ai
kuma ta mike don wanko hannu, tana tafe kanta tsaye zuwa famfo kamar ba mara ido ba, ba
tare da ta nemi Inna tayi mata jagora ba. sai data kai bakin famfon ta kunna sannan tace ka
hutar ni dauke kwanon, dama na koshi ai. Mamaki yasa Sarham rufe baki yana dariya yace.
Inna ashe idon mu ya bude! Inna tace fata nagari lamiri, me yasa aka ce muyi fatan alkhairi
akan komai? Ai don bamu san tasirin bakunan mu ba, mai yuwuwa Allah ya biye bakin ka
watarana Likita”.
Sarham ya ce haka yake Inna, amma shi ya san da kamar wuya wai gurguwa da auren
nesa, sai dai duk wani mumini yayi amanna da cewa ba abinda ya gagari Allah, suma likitocin
lalube suke yi a cikin duhu. Sanin gaibu sai Allah. Ya russuna har kasa ya gaida Inna, ta kawo
masa darduma ta shimfida, sai ya ce, “tunda sallah za kuyi, muyi jami gaba daya kawai, ban taba jan ku sallah ba Inna. Maijidda
dauro alwallah.
Daga inda take tsaye a jikin famfo tayi dan sakale! Bata ce toh ko aah ba, don jiya ta fara
ganin jinin alada a rayuwar ta, itama bata sani ba, Inna ce ta gani a jikin zanin ta ta gaya mata,
ta kuma taimaka mata wajen kunzugu, ta koya mata yadda zata dinga killace kanta da

tsaftataccen tsumma, dankwalin sabuwar atamfarta mai tsafta ta dauko ta tsaga shi gida biyar
ta koya mata amfani da shi, ta kuma gaya mata baa sallah da komai na ibada sai an samu
tsarki, koda yake duk ta sani a makaranta tun kafin ta fara din
Duk da cewa ta tsorata da Inna ta gaya mata ta fara alada, ta kuma tabbatar mata yanzu ta
girma dole ta kula da kanta da tsare mutuncin ta daga wannan lokacin, da kuma koyon yadda
zata ke muamala da maza daga yanzu.
Inna ta zaunar da ita ta ja kunnen ta sosai, ta gaya mata yanzu da girman nan ya hau kan ta
ko hannun ta namiji ya kama cikin shege ne zai shiga jikin ta kuma haramun ne. ta tsoratar da
ita sosai akan maza ko yaya take dasu. Yinin jiya zungur laccar da Inna ta wuni tana yi mata
kenan. Sarham ya gaji da jiran Kulu ta zo su tada sallah, don tunda ta shige daki ta ki fitowa ya
dauka hijabi zata shiga ta dauko amma shiru kake ji. Sai Inna ce ta sadda kai ta ce,
ja mu sallahr ka ji! Kuluwa girma ya zo!.
Sarham cikin rashin fahimta ya tambayeta girma kamar yaya?.
Duk surutun Inna da yadda ta ke sakewa da Sarham wannan karon kasa fada masa Hauwa
ta fara alada tayi, ta hau inda-inda, har ya gaji ya tada sallah, amma daga karshe a matsayin sa
na likita malamin kiwon lafiya sai ya dago su.
Abu daya zai hana mace sallah uwarta ta bi bayan ta shine idan tana fashin sallah.
Ikon Allah, har nawa Hauwa-Kulu take? Maiyuwuwa kuma irin jikin ta kenan. Irin su kuma
sune masu haihuwar wurwuri. Koda yake kanwarsa Sumayyah ma haka ta fara da wuri, kuma
shi ta fara gayawa tana kuka, don ta kasa gayawa Mama da Surayyah, tana ganin wani mugun
abu ne ya faru da ita, ba zai manta ba shi ya fara saiwa Sumayya always pad ko Mama sai da
Sumayya tayi wajen sau uku kafin ta sani.
Bayan sun idar da sallah shi da Inna, kasa gaya mata tafiyar sa Saudi yayi, saboda sabo, da
wata irin kewar su da tazo ta rufe shi, Inna kuwa tana ta hidimar hada masa tuwon masara
miyar kuka da manshanu, ga yajin daddawa a gefe, ta kawo ta aje masa da ruwan randar ta
mai sanyin dadi. Taga yayi shiru ya kasa cin abincin da doki kamar yadda ya saba, cikin kulawa
Inna ta ce, likita ya dai? Jikin ko garin?” Ya nisa, kafin yayi kundumbala ya ce babu ko daya.
Inna sallama na zo muku, zan bar kasar nan!.
Ba Inna kadai ba hatta Kulu da ke daki fitowa tayi da sauri daga uwar dakin data je ta boye jin
abinda Dr. Sarham yake cewa.
Tafiya ta same ni zuwa kasa mai tsarki, zan tafi karo karatu na akalla shekaru uku, Inna ina
fatan zaki cigaba da tayani kula da karatun Maijidda har ta kammala, alkawari ne na dauka
tsakanina da Ubangiji sai na ga ta kammala sakandire hankali na zai kwanta, to amma ga
yadda Allah ya tsara min. Ina fatan kafin in dawo Inna zaki tsaya akan karatun ta na sakandire har Allah ya cika min
wannan burin nawa”.
Inna gaba dayan jikin ta ya mutu. Bata san ta saba da Sarham ba sai yau da yake maganar
barin kasar mu baki daya, bata san dimbin alkhairin sa mai yawa bane a gare su, sai yau da zai
bar su. Kokari take ta mai da hawayen da suka kawo mata cafka, don kada ta kara karya masa
guiwa da tata karayar, don hatta yadda yake maganar kadai zaka san ya fi ta shiga damuwa da
kewa, ya karaya.
Hauwa dai ba tace komai ba, amma a cikin ranta wani irin ‘dakace’ take yi, cewa take
inamainama! Inama na ga fuskar sa yau, inama nayi masa kallon karshe yau kafin ya barmu,

wanda zai sa kullum nake tuna fuskar sa, in yi ta masa addua!.
Don duk tsayin lokacin nan da suka kasance da Sarham a cikin rayuwar su kusan koda
yaushe cikin wannan fatan take, ba don komai Hauwa take son ganin fuskar Sarham a rayuwar
ta ba, sai don ta yi quenching curiousity dinta a kan kamannin sa ta kuma yi matching din fuskar
da kyawawan kalaman bakin sa na kullum a kan su, wadanda a kullu yaumin masu maana ne
wadanda suke kara mata son ganin kamannin halittar sa, shi Sarham mutum ne mai fasahar
zance na ilmi, da girmamawa ga mutane, ba tare da laakari da matsayi ko ajin rayuwar su ko
nasa matsayin ba, kalaman Sarham har kullum masu tausasawa dan adam ne, a duk halin da
yake ciki ya san kalaman da ya dace yayi masa, wato koyaushe kalaman sa na tafiya ne da irin
yanayin da ya tarar da kai a ciki.
Alal misali, in ya lura kana cikin farin ciki zai taya ka da zolaya da tsokana yakara maka farin
ciki, haka in bakin ciki kake shima zai taya ka har a murya da zuciyarsa, daga yanayin kalaman
sa kadai zaka tabbatar (he feels what you are feeling) kuma yana tayaka. Sarham ta kwana da
sanin cewa shi din, wani kyautar Ubangiji ne koko tace (dauki) da Ubangiji ya kawo cikin
rayuwar su, ya hada su da shi, a lokacin da suke tsananin bukatar tsayawar namiji a rayuwar
su.
Ubangiji ya nufe shida shigowa rayuwar su ne don ya zame musu fitila mai haske kuma
sanyi daga kuncin da suka samu kan su rana daya na nakasar ta, wanda in ba hadin Allah ba,
ba abinda zai sa ya shigo cikin rayuwar su ya tsaya kamar Yayanta na jini. Domin ta kowacce
fuska babu ta inda rayuwar su ta zo daya. ​ Yau da yake cewa zai tafi, har tsayin shekaru uku sai taji cewa lallai zasu yi rashin da
baa mayarwa, zasu yi kewar da bata karewa, don shekara uku ba kwana uku bace, abu ce ta
mai yawan rai.
​ Inna ta cigaba da hana kanta kuka a gaban Sarham, tana gayawa kanta saboda su ba
zai fasa gina rayuwar sa ba. Yo fisabilillah don su aka halicce shi? Daga taimako? Kuma dai duk
wani abinda ya dace don kyautata rayuwar mutum Sarham ya gama yi musu shi, tunda yayi wa
Hauwa sanadin cigaba da karatu bayan iftilain da ya same ta. Sun koyi abubuwa da dama daga gare shi, irin su magungunan da ya dace da taimakon farko
na cikin gida (first aid), home hygiene, sanitation duk karshen wata, cin balance diet a
gargajiyance da irin abincin da suke da shi, sun koyi abubuwa masu yawan gaske da suka shafi
kiwon lafiya a bakin sa a dalilin zamansu tareda shi. Haka kuma ko yau bai yi shiru ba sai da ya ce da Inna ga kudi zai bar musu ta tabbata ta
sayawa Hauwa auduga mai yawa a chemist, bai yarda da kunzugun tsumma ba, yace ita ba ido
ba, don haka ba iya kula zata yi da kanta ba kada yaje ta dauki kwayoyin cuta.
​ Kunya duk ta kama Inna. Kulu kuwa da ace a da ne Dr. Sarham ya fadi haka da tuni ta
hau shan kunu da fushi da bacin rai na cewa an yi mata gorin ido, watakila harda su kuka,
amma da yake yau itama zuciyarta ta tabu da zancen tafiyar tasa ba tace ko uffan ba, saima
kunya da taji sosai itama kamar Innar. Inna har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login