Showing 30001 words to 33000 words out of 39674 words
Chapter 11 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf
sai da ta kasa rike hawayen nata a wannan karon, da ya ajiye mata kudi masu
dama a gabanta, tace. Dan nan shekara uku ba kwana uku ba. Allah yasa ka same ni a raye,
rayuwar nan da bata da tabbas. Allah yasa muna da rabon sake ganawa, Allah ya hada
fuskokinmu da alkhairi. Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ilmin da zaka je nema, ya kuma
baka dukkanin abinda kake nema a cikin samunsa, ya huwwace maka saukin sa, ya kuma baka
albarkar sa.
Amin- amin Inna, nagode kwarai da gaske da wannan addua mai dadi daga bakinki, na ji
dadin zama da ke Inna, zan kuma yi kewar ki ba dan kadan ba!.
Sai da ya tashi tafiya yaga Hauwa ba tace masa komai ba, koda kuwa adduar fatar baki ce,
ta sunkuyar da kai kawai. Wannan karon kam ya kufula da wannan mugun hali nata, ya ce
Kuluwa!!!”. (Sunan da ya san ta tsana, kuma yana kular da ita), ta dago manyan idanun nan tayi
harrr! Dasu a saitin da ta jiyo tashin muryar sa, ga mamakinsa hawaye ya gani ya kwanta
dankam a cikin su, ya basu wata irin kala kamar na mai jin barcin da ke hamma, ya sake cewa,
ko ba da Hauwa-Kulu-AKA-Kuluwa nake magana ba?.
Hauwa ta tsuke baki, sannan ta sosa hanci cikin jin haushi, bata amsa ba, sai can data mula
taga damar magana don kanta sannan tace,
amma dai saboda Allah in mutum ya nuna baya son suna, bai kamata a dinga kiran sa da
shi ba, har raina bana son suna KULUWA! an ce miki Kuluwar, Kulun Majadun, Hauwa-Kulu,
Kululu, da wasu idanuwanki kamar na Kuliya (mage/mussa).
Ke kam baki ji dadin halin ki ba, wallahi ba don Inna ta tabbatar min a gida ta haife ki ba, da
na yi rantsuwa an canja mata ke a asibiti.
Don Inna ba sumumu-kasau bace, bakin ta baya shiru don ya cutar da ita, ki fada kar ta
kashe ki, mai yuwuwa kafin shekara ukun na mutu! Ko ke kin mutu! Ko dukkan mu mun mutu!
Don haka fadi abinda ke ran ki yau da nazo yi muku sallama, ba tare da mun san ranar sake
haduwa da juna ba. Hauwa zan iya rantsuwa kan ban taba jin kin yi min magana da ta wuce sentence biyu ba, a
tsayin shekaru biyun da nayi da sanin ki. Ga wani ‘sadness’ da nake gani akan fuskarki a duk
lokacin da kika ji sallamata a gidan ku. Me nayi miki haka? Meye dalili? Na rantse gaisuwa ma
akan dole kike yi min ita. Kulu baki dauke ni dan uwa kamar yadda na dauke ki ba.. Hauwa-Kulu sai ta fara hawayen babu gaira babu dalili, ko da yake dama sun cika idon
tuntuni suna so su zubo ne, tana fin karfin su. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki.
Ta ce dama kullace kake da ni haka duk tsayin lokacinnan ban sani ba?. Nake kullace da ke?
Ko kike kullace da ni?. Inna bata san me yasa ta kasa sauraron takaddamar tasu ba, ko don cikin zafin rai kowanne
yake furucinsa, sai ta tashi salin alin ta saka takalmanta ta dau buta da niyyar ta zagaya bayan
gida, ba tare da tana jin fitsari ko kashi ba, kawai ta kasa jure ganin hawayen Hauwa shi kuma
ta kasa jure ganin bacin ran sa karara yau, don bata taba ganin sa cikin bacin rai ba, shi
Sarham ta fahimci kullum mai kirki ne, mai fara ne, mai walwala ne kuma mai farin-ciki da
kowanne yanayi (jovial person).
Kasancewar bai taba nuna bacin rai a kan share shin da halin koin kulan da Hauwa-Kulu ke
nuna masa ba sai yau, wanda itama ta sha yi mata fada a kan bata kula shi, bata kyautata
muamala da shi, bata masa fara kamar bata so yake zuwa gidan su, amma Hauwa sai ta ce,
to Inna me kike so in dinga ce masa? Magana ba sai ta dauro ake yin ta ba? To ni ban da
wata magana da shi banda gaisuwar da ta zame min dole, kuma ina gaida shi”.
Rannan da Inna ta hau ta da fadan ya zo har ya fita ranar ko gaisuwar ma bata yi masa ba,
Hauwa ta zaro manyan idanunta waje (ta manta da wa take magana) ta ce,
Inna! Idan kin manta ni ban manta ba, daga gyaran ido ya karasa makanta ni, ni duk wannan
kirkin nasa gare mu ta baya ta raggo, ido fa na rasa a hannun sa, Inna! Wani abu zai min ya
biya ni?”
A ranar Inna ta sha mamaki ta kuma tsorata, ta ce au, dama dalilin ki na kin girmama
alamarin likita kenan?. Hauwa ta yi shiru, sai can ta kama hawaye. Tace Inna dalili na kenan,
amma ba wai na rike shi a raina bane na san kaddara ta ce, amma kullum na tuna shi yasa idon
ya karasa macewa saboda careless na aikin sa sai naji tsanar sa ta darsu min, tunda Inna ba
abinda zai yi ya biya ni ido na, ba kuma abinda zai min da zan yi farin ciki da shi idan ba
idanuna ne suka dawo min ba!”.
Inna ta kai hannu zata mari Hauwa, ko me ta tuna? Malam Bilyaminu! Ya taba rokonta ko me
Hauwa zata yi nasiha ta kasance tsakaninsu ba duka ko zagi ba, duka baya biyar da yaro yayi
abinda kake so saidai ya kara kangarar da shi musamman mautum mai riko irin Hauwa-Kulu.
Sai Inna ta rike hannun nata da daya hannun, ta hana shi isa ga fuskar Hauwa. Cikin tashin
hankali tace mata na rasa me zan ce miki, Baban ki ya sha gaya min kina da kullata ban taba
yarda ba sai yau, amma ina so ki sani Allah ne ya dora miki makanta ba Likita Sarhamu ba, su
kawai masu taimakawa ne a samu lafiya amma suma basu hada sani da Allah ba, lalube suke
cikin abinda suka karanta don su taimaki alumma kawai.
Inaso ki sani Hauwa-Kulu, komai na rayuwar dan adam a rubuce yake a Lauhul Mahfuz, tun
kafin halittar sa balle haihuwar sa.
Ban so kika saka wannan mummunan tunanin a ranki ba Hauwa-Kulu, domin ya zama
rashin yarda da kaddara, ya nuna baki dauki kaddararki da kyakyawar zuciya ba kenan, wanda
yana cikin sharuddan imanin mumini.
Yi maza ki ce “astagfirullah domin wani Likita duk kwarewarsa ko akasinta, bai isa yayi
abinda Allah bai yi ba, kuma shi ba Allah bane da zai bayar da lafiya ko ya hana.
Banda son zuciya irin naki, in ma tuhumar ne ni ya kamata ki tuhuma, ni da tun farko ban kai
ki asibiti ba tun ciwon yana apolonsa, sai da idanun suka kusa tashi aiki.
Haka Inna tayi ta mata waazi mai shiga jiki a lokacin, amma Hauwa-Kulu bata kara tankawa
ba saboda miskilancin ta, don haka yanzun ma da Inna ta shige bayi ta bar su a nufin su gama
fadan sannan ta dawo, Sarham ya ce wai ta fadi abinda ke ranta yau, kada ta bar shi a ranta ya
kashe ta, sai taji kuka ya kwace mata ba kakkautawa a gaban sa. Sarham sai gashi jabar! Ya koma ya zauna dabas a kasa, akan rairayin tsakar gidan su
Hauwa. Taja gefen hijabinta ta rufe fuska cikin kakabi da fushi da muryar kuka ta ce, babu
komai a raina, sai fatan alkhairi ga kowa”. Sarham ya ce karya kike yi, kuma ni bana shiri da mai
karya. Ko amon muryarki ya karyata ki, ya karyata abinda kika fada. Fatan Alkhairi ne a ranki game da kowa? Amma banda a kaina ni Sarham ko? Wa na kashe
miki? Ko me nayi miki haka da zafi da kika kullace ni?. Hauwa ta rasa yadda zata yi da shi, don
ba zata iya ce masa tana jin maqaqin sa a ranta ba, da cewa bai iya aiki bane ko kuma
carelessness dinsa ga aikin sa ne yasa ta makance gabadaya. Sai ta samu bakin ta ya bige da cewa cikin rawar murya da rishin kuka.
Ina dakace ne na cewa, inama ina gani! Inama in ga fuskar ka a zahiri in san kamannunka!
Rashin idona yana hanani farin ciki da kowa da komai”.
Mamaki ya kashe Sarham daga zaunen da yake na yadda nan da nan ta kirkiri karya don
kaucewa tunanin ta na hakika, ya dube ta sosai cikin manayan idanun ta kamar tana ganin sa,
zai so ace a lokacin da zai fadi abinda zai fada yanzu sun hada ido, yace cikin wata irin murya
mai rauni.
Maijidda you are accusing me for being the cause of your blindness, (Maijidda kina tuhumata
da zamowa sanadin makancewar ki), hakane ko ba haka ne ba?!”
Hauwa ta cira ido a firgice, zuwa inda take jin tashin sautin sa, ya daga gira yace Yes, ba
wani son ganina da kike yi, karewa ma ba kya son gani na, you are just accusing me.
Ni kuma na san bani na makanta ki ba ALLAH ne ya tsara miki wannan jarrabawa domin ya
jarrabi imanin ki Maijidda. Nakaa ba komai bace face jarrabawar Ubangiji ga wasu kebabbun
bayinsa.
Unfortunately, kina neman faduwa jarrabawar ki Maijiddah, domin a zuciyar ki babu TAUHIDI
babu IKHLASI. So ya rage naki kiyi maza ki gyara, kiyi istgfari, ki yi kokarin cin jarrabawar ki, ko
ki bari shaidan ya ci nasara da galaba akan jarrabawar ki ya barki da biyu babu; ba ido ba
imani. Don ni, da ke duka mun san yarda da kaddara yana cikin cikar imani. Hauwa ta dan tsorata da bayanin nan da Sarham yayi mata, amma dai ko ta gamsu da
bayanin Sarham bazaka taba gane hakan akan Bakanuwar fuskar ta ba, mai iya boye abubuwa
iri-iri da ki-fadi, tace,
ta yaya zaka fadi abinda baka shiga zuciya ta ka gani ba? Saidai in dama kana tuhumar
kanka ne”. Sarham yayi dan murmushinsa mai ban shaawa domin yanzu ya gama gane
manufar ta, da abinda ke cikin ranta a kansa tuntuni da yake saka shi ganin sad expression
akan fuskarta, yace. Nayi laakari da maganar hausawa ne da suka ce labarin zuciya ai fuska ake tambaya, kuma
dai ‘Im older than you, and Im good at reading minds. Da babbar murya zan iya kiran kaina
‘behavioural analyst’, amma mu barshi a abinda kika fada din, watau kina son ganin fuskata ne,
me kike kissimawa akan fuskar tawa? Idan kuma ni din mummuna ne fa Maijidda? Irin munin da in an gani sai an rufe ido don
muninsa?
Hauwa bata san sanda tayi murmushi ba, alhalin ga hawaye face-face a fuskarta, ta ce
mummunan mutum ba mutum bane? Ai mummuna da kyan hali irin naka, sai yafi kyakkyawan
gaske nagarta da shiga ran mutum, bayan haka ma a hakikanin gaskiya ni ba wannan nake
kissimawa ba, ina kissima yadda fuskar zata yi dai-dai da irin kyawawan kalaman ka ne,
koyaushe kana magana wadda ta dace da muhallin ta, kana da tunani na ilmi (with abstract
reasoning)”.
Sarham wani irin kallon bakinta dake motsi a hankali yake yi, da murmushi yace ikon Allah.
Ya akayi ni ban sani ba? Kamar wadanne iri ne kalamai na masu kunshe da abstract
reasoning? Irin dai wadanda kake yawan yi cikin surutun ku kai da Inna, wani lokacin ina
saurara, nafi zama mai sauraro a hirar mutane fiye da mai contributing, ta nan nake fahimtar
yanayin zancen kowa, na fahimci maganganun naka duka a muhallin su kake yin su, kuma a
takaice, amma cike da tarin maanoni da alfanu, sannan duk wani cukurkudadden alamari ka
san ta yadda zaka bi ka warwareshi cikin hikima irin taka”. Sarham ya zura takalman sa, ya
mike idonsa akan Hauwa, yana sakin dariyar da bai shirya zuwanta ba, ya lura yau in zasu
kwana a haka, bazai gaji da sauraron dadadan furucin Maijidda gareshi ba, ya ce SAI
WATARANA Maijidda sai watarana, ina rokon ki, duk runtsi kada ki bar zuwa makaranta, koda
kin rasa dan jagora! Ina nufin against all odds, koda da rarrafe ne ki jure ki nemi ilmi, duk da
nasan ba zai zamo abu mai sauki gareki ba, dama duk masu lalura irin taki, amma ki sani Allah
ne gatan ki sai kuma shi (ilmin)”.
Idan na rasa dan jagora da wanne idon zani makarantar? Misali, idan Salele ya daina
kaini ko ya mutu?”
Hauwa bata san sanda ta jefe shi da wannan tambayar ba, a lokacin har ya saka kai zai bar
tsakar gidan su. Amma jin yadda muryarta ke rawa da karkarwa kamar kuka zai kwace mata
yayin fadar hakan, a lokacin da take fadin hakan ma tuni hawaye ya ciko idonta, sai Sarham ya
juyo yana kallon Hauwa da wani irin expression a idanunsa, cikin wata irin karaya da kewa,
hasken farin wata ya haske masa fararen idanun ta suna jujjuyawa a cikin lalurar rashin gani. Ya
kamata ya bata amsar wannan tambayar ta yadda zata dade tana tuna ta, wato tayi ta shawagi
a kwakwalwarta, har ta zame mata tsani a rayuwa.
Ta hanyar sakawa ran ki cewa zaki iya komai da mai lafiyar ido zai iya, hankali ke gani
ido gululu ne, ki tuna kullum da karin maganar da Bahaushe ke cewa “ba nakasashshe sai
kasashshe”. Bature kuma yace
“theres ability in disability!”.
Sannan kullum kisa a ranki “nakasa ba komai bace face wata kankanuwar jarrabawar
imani ga wasu kebabbun bayin Allah na kwarai daga Azza wa Jallah”.
Wadannan kalaman nasa su suka zamewa Hauwa-Kulu a food for thought, har bayan
tafiyar Dr. Sarham daga rayuwar su, bata bar mayar dasu madubin ta na rayuwa ba, fitilar dake
haska mata duhun koina dake cikin nakasar ta, sannan jagoran ta a duk lokacin da ta rasa dan
jagora, wato kalaman sa ta saka a gaba suke saita mata hanya a duk inda ta nufa, don cimma
rayuwa mai amfani a cikin halin data ke ciki na nakasar idanu.
Watanni masu dama suka biyo baya suna cikin kewar sa mai yawa itada Inna. Cikin tuno
‘precious moments’ din su tare dashi. Ko na rana guda sun kasa mantawa da shi.
Sun kasa mantawa da tarin gudunmuwarsa ga rayuwar su, da lokutan da suka kasance tare
da shi cikin yanayi na zumunci da yan uwantaka. Zaman sa na dan lokaci cikin rayuwar su ya
dauke musu kewar Baban ta watau Malam Bilyaminu kaso 50% data dan uwanta mai rasuwa
wato Zulkifl, duk da a sanda yake zuwa wajen su din bata wani damu da shi ba, sai ma kullata
data biyo baya, duk da repentance dinsa gare su akan laifin da ba lallai a kira shi nashi ba,
amma bayan tafiyar sa, da irin emotional sallamar da suka yi mai zaunawa a rai, hakan yasa ta
yin kewar sa bad an kadan ba.
Guzurin kudi da ya bar musu har naira dubu daya sun dade suna cin moriyar su, kafin bayan
wasu watanni masu yawa su kare, duk da haka Inna bata bar sanaar ta ba ta sayar da wake da
shinkafa da juyen dabbobi a kasuwa duk shekarar sallahr layya.
A lokacin Hauwa ta shiga babbar sakandire aji biyu, watarana ta dawo daga makaranta
tare da Salele kafin su hawo motar bus da zata kawo su kofar Na’isa Salele ya hango ana
hawan kilisa a kan dawakai a tsallaken titi. Saleleh mayen dokuna ne na gani kashe ni, yana
matukar son wasan Polo da hawan angonci ko hawan sallah na sallah da sarki ke yi a Kano,
tuni suka kwashe hankalin sa daga kan Hauwa, ya bata jakar makarantar ta ya ja sandar da
suke kamawa shida ita a matsayin jagora tsakanin su, don ba hannun ta yake rikewa ba duk da
ta girme shi, yace.
Hauwa, zauna kan bencin can ki dan jira ni in ga wucewar masu kilisar can akan dokuna
Hauwa tace toh, amma don Allah kayi sauri Salele, ka san yanzu Inna tana duban hanyar mu,
kada ta ga mun dade ta damu.
Salele tunda ya nausa cikin yan kallo ya bace mata bat! Shiru shiru Hauwa na jiran Salele bai
dawo ba, karambani irin nata yasa taga cewa bari dai kawai tarabu da shi yau tayi kokarin kai
kanta gida kada hankalin Inna ya tashi. “Dr. Sarham” yace ba ido ke gani ba hankali ne ido
gululu ne kawai. Sai ta tashi da zummar ta tsallaka titi ta tari motar kofar Naisa, don daga yadda take jin karar
motoci ta san a bakin titi suke, tana tafiya a hankali abunta kanta a kasa ba tare da ta san ina
take saka kafa ba ai dai mutum ya gane da kansa bata gani shi ya kauce mata.
Ai kuwa bata jima tana tafiyar ba taji ‘horn’ din mota a tsakar kanta, wanda ya kidimata ta
diririce ta kwasa da gudu, motar kuwa bata yi kasa a gwiwa ba wajen kwasheta, ta yi sama da
ita sannan ta