Showing 33001 words to 36000 words out of 39674 words

Chapter 12 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf

nana ta da kasa.
​ Salele dake tsallakowa titi akan idon sa mota ta kwashe Hauwa. Ya dora hannu a ka ya
rafsa ihu yayi kanta a tsakiyar titin yana fadin na shiga uku, Hauwa ban ce ki jira ni ba?
Hauwa!!!”
Mai motar ya gangara gefen titi ya tsaya, ko kafin ya fito daga motar jamaa sun taru a kan
Hauwa ana salati. Da yake na kirki ne sai bai gudu ba, ya taimaka aka saka Hauwa a motarsa,
tareda wani dattijo da Salele da ya ce ai Yayar sa ce, suka nufi asibiti da ita jini nata disa a
motar, amma mai motar nan bai damu ba ta ran Hauwa yake, yana rokon Allah yasa abun ya zo
da sauki kada diyya ta hau kansa.
Hauwa bata san inda kanta yake ba har suka shiga babban asibiti.
Asibitin Malam suka kai Hauwa, a ka karbe ta a imajensi likitoci uku suka rufu akan ta suna
kokarin ceto ranta. Sai bayan an samu an yi treating raunukan da ta ji, an kuma daure karayar
da ta samu a hannu sannan aka basu daki kwanciya. Wanda ya kade ta duk shi ya biya komai,
kuma ya tsaya har aka kai su dakin kwanciya din na mata inda aka basu gado. A lokacin ne ma ya samu damar da ya kalli Hauwa tana barci, duk da ta kara girma sosai, ta
zama budurwa sai yaga kamar ya santa. Ya tambayi Salele gidan su, don aje azo da iyayen ta,
Salele ya ce zai je shi kadai ya zo da Innar ta.
Don haka saurayin ya ja kujera gaban gadon Hauwa ya zauna bayan fitar Salele, ya dau
wata jarida a kan lokar gadon ta asibitin yana dubawa yana satar kallon Hauwa yana fadi a
ransa yau tsautsayi ne ya fito da shi daga wajen aikinsa ba tare da lokacin tashin sa yayi ba,
tsautsayi da baya wuce ranar sa, banda haka shi baya wani fita cin abinci har cikin bankin a ke
kai musu su biya, daga yaje ya ci abincin rana a restaurant ya koma office zuwa lokacin tashi
tsautsayin nan ya ritsa da shi?
​ Ya sake kai duban sa ga Hauwa a karo na sau ba adadi, sosai take masa kama da wata
fuska da ya jima da sani, amma ya kasa tuna inda ya san fuskar ba.
​ Har saida Inna tayi sallama a gigice ta fado dakin asibitin kamar an turo ta, Salele ya
biyo ta a baya da buta da bokiti da tabarma da bargo, nan ne mutumin ya gane ta sarai. A
tsorace ya mike tsaye, ita kuwa Inna bata ma lura da shi ba kan Hauwa tayi tana salati tana
godewa Ubangiji. Bayan ta dan nutsu ne Jamilu ya matsa gaban ta ya tsugunna, ya sadda kan sa kasa cikin
kaduwa da mamaki da tsoron kada Inna tace da gayya ya kade Hauwa, yace Inna Safiya kiyi
hakuri, ni na kade ta ban sani ba, ashe Hauwa-Kulu ce ma, kanwata.
Wallahi ina cikin tafiya kawai na ganta a gabana a tsakiyar titi, nayi kokari in kauce ta sake
dawowa daya barin da ba yadda zan iya kauce mata.

Inna ta kai duban ta ga saurayin, nan da nan ta gane shi duk da girma da cika idon da yayi,
Jamilu ne dan wajen Zakari, Inna ta ce.
Jamilu dan wajen Rumanatu? Yace ni ne Inna Inna tayi kwafa ta ce to babu komai, kana iya
tafiya, mun gode.
Jamilu ya ji babu dadi a ransa, yace Inna Safiya wallahi tsautsayi ne, ba inda zani sai taji
sauki, zan kasance tare da ku har Allah ya bata lafiya.
Inna bata sake komawa ta kansa ba, ta maida hankali kan gyarawa Hauwa kwanciya, har ya
karaci durkuson sa ya tashi, ya tafi cikin damuwa.
Bayan fitarsa Inna ta tambayi Salele yadda aka yi ma ya rabu da Hauwa har ta hau titi bisa
ita kadai, cikin kokarin boye bacin ran ta, Salele duk rashin gaskiya ya bayyana a fuskar sa ya
ce Inna daga nace ta tsaya in je ni tsallake in dawo Inna tace ka dai fadi gaskiya, kai dai wallahi
a kan kalle-kalle ko bakauye nan ya ganka ya barka. Allah ya kiyaye gaba”. Can kuma tace. “Oh
ni Safiya, Hauwa-Kulu harda karaya? Idon ta ya kawo ruwa, tasa habar zaninta ta share tana
sake gyarawa Hauwa kwanciya, an sakale hannun da aka gyara a jikin karfen gadon.
Ba jimawa da fitarsa Jamilu ya sake dawowa niki-niki da ledoji a hannayensa, yayi sallama
akan su, dakin irin dogon dakin nan ne na kwantar da marasa lafiya mata zallah, suna daga
gadon tsakiya da wasu a gefeda gefen su, Inna ta juya ta dube shi ta amsa sallamar sa, fuska
kadaran-kadahan ta ce wani abu ka manta ne kuma? Ya ce aah Inna, ai na dinga zuwa kenan
har sai an sallame ku, in sha Allah. Ya ajiye mata ledojin da ya shigo dasu a gaban ta cikin
matsanancin ladabi, sai Inna ta rasa me zata ce, yaushe yayan Zakari suke da hankali balle su
yi halin da yake yi a gabanta yanzu?
Koda yake ko dama can shi daban yake a cikin su ta san wannan, saboda uwarsa ta masa
tarbiyya daidai gwargwado, bayan Zakari ya saketa da shi ta tafi tayi aure a wani gidan, ba laifi
yana gaida mutane duk inda ya gan su ba kamar kannen sa ba da sau dubu zasu wuce ta ko
kallo bata ishe su ba. In zata iya tunawa rabon ta da Zakari da wani da ya shafe shi tun batan
Malam Bilyaminu, shekaru hudu baya da ta je neman sa yayi mata korar kare. Wani cikin su shi
ko yayan sa bai kara neman su ba, yau kuma sai ga Jamilu ya kade Hauwa.
Inna ta nisa, ta kasa ce masa ya kwashe tsiyar sa, don sosai taga damuwa a tare da shi na
irin karbar da take masa. Haka suka zauna shi da ita zugum-zugum, ba mai iya ce da kowa
uffan, daga baya yayi mata sallama ya tafi. Yace sai gobe in sha Allah kafin ya tafi wajen aiki zai
leko ya ga jikin Kulun. ​ Inna tayi masa godiya, amma sai ta ce “don Allah ba sai ka dawo ba Jamilu, taimakon
da kayi mata ma an gode sosai, madallah. Allah yayi albarka.
Jamilu bai ce komai ba ya juya ya fita don ya san tabbas Inna ta kullace su duka ahalin
gidansu daga su har mahaifin su, don ma dai tana da kai zuciya nesa.
​ To bayan fitar sa kuma ta samu kanta da bude ledojin da ya aje musu, ta farko kayan
shayi ne a ciki, da katon biredi (Laziz) sabon gashi, sai kayan marmari shake a daya ledar
harda Tuffa da Inabi, daya ledar kuma gasashshen naman rago ne mai zafi sosai a ciki.
A lokacin Hauwa ta farka tun bayan kawo ta asibitin da kyar ta iya ta dan motsa, sai ta ji ta
kamar a daddaure, koina na jikin ta ciwo, bata san me ya faru da ita ba, ta kai hannun ta da baa
daure ba kan goshin ta tace wash! Inna tace sannu Kulu kin ji, tsautsayi ne da baya wuce ranar
sa, mota ta buge ki, Allah dai ya dada kiyaye gaba. Nosis suka zo suka bata magungunan ta, suka ce a bata shayi mai zafi ta sha, kuma zata iya

cin wani abu, Inna tace basu zo da ruwan zafi ba, sai suka bata aron karamar heater ta jona ta
hada mata shayi mai kauri da kayan shayin da Jamilu ya kawo.
​ Ta taimaka mata ta zauna a jikin filo tana bata shayin a baki har ta koshi, ta debo naman
da zafin sa a faranti irin gasashshen naman nan ne na babbar tukuba mai ruwa-ruwa wanda da
kasa a bakin ka ka tauna zaka ji ya baje tsabar laushin sa, wanda yaji yajin citta, Hauwa duk da
jikin ta na ciwo taji dadin cin naman nan, don baza ta iya tuna yaushe rabon ta da cin nama ba,
tun zamanin Likita Sarham na zuwa gidan su! Balle mai dadi da laushi irin wannnan ai sai
zamanin Dr. Sarham.
Daga nan ta koma barci har dare bata tashi ba, Inna ta sallami Salele ya tafi gida bayan ta
masa sautun abubuwan bukata da zai zo musu da su washegari har da filas din ruwan zafin su
da hita.
​ Washegari yan dubiya fululu daga kofar Naisa, Salele ya barabada musu mota ta kade
Hauwar Inna. Hauwar Inna mai jamaa kowa na son ta, koda makanta ta same ta jamaar
unguwar su kowa kokari yake ya kyautata musu, musamman da aka san mahaifin ta ya bata,
kuma Innar ta bata da matallafi sai Allah. Makwabta na ta tururuwar zuwa duba Hauwa kullum, koda Inna ta aika Salele don ya fada a
makarantar su Hauwa kada aga bata zuwa, sai ga Malaman su Hauwa sun yo kungiya a motar
makarantar su a washegari daga ‘special school Kano’, suka zo suka duba ta da kayan dubiya
niki-niki, kasan yaro mai kokari da shiga ran malamai. Don haka a wannan jinya su Hauwa sun
samu alheri sosai, don Jamilu ma kullum yana tafe, abin arzikin da zai kawo na yau daban na
gobe daban.
​ Tun Inna na daure masa fuska tana korar sa a wayance, har ta fara gane Jamilu neman
shiri yake yi sosai dasu, rannan ya kawo dafaffen abinci yace mata inji Hajiyar sa, da yake bata
gidan mahaifin sa ita kuma tare suka yi yanmatanci da Inna, kusan lokaci daya Bilyaminu da
Zakari suka aure su. Ta manta rabon ta da Rumanatu don tun Jamilu na yaro Zakari ya aunata gaba.
Daga baya ma ya dauko Innar tasa ya kawo dubiya, nan suka baje ita da Inna a kan tabarma
ana labarin yaushe gamo da tuna baya. A bakin Hajiya Rumanatu Inna ta ji cewa Jamilu yayi
karatun shi mai zurfi har digiri a hannun ita mahaifiyar shi a boye, ba tareda Baabnsa ya san
yana yi ba, tace yanzu haka Jamilu aikin Banki yake da bankin Afrika (United Bank of Africa) da
akafi sani da UBA. Kuma da wannan aikin har yana taimakawa kannensa sosai da suke garari
da gararramba a gari, matan yawanci an sako su suna gidan uban suna zawarci, tace yayan
Zakari mata basa jimawa a gidan miji zaki ji an sako su, uban duk kudin da ya tara baya iya
saya musu ko gasarar koko, sai dai ya je tukubar mai shayi a lafta masa kwai da shayi mai
kauri, ta ce ai ita kam Allah ya cece ta da ya raba ta da gidan su Jamilu.
Ta shiga lissafo wa Inna yawan matan da Zakari ya aura bayan ita yana shika musamman
bayan yayi kudi abun babu ko dadin ji.
​ Tace bayan rabuwar ta da Zakari ta yi aure ta haifi wasu yayan mata guda biyu Hansatu
da Lami, duk ta aurar dasu. Shekarar baya Allah ya yiwa mijin ta rasuwa wanda ya rike mata
Jamilu kaamr shi ya haife shi.
​ Har yamma kafin Jamilu ya zo daukar Hajiyar sa, suna tafe a hanya Hajiyarsa na bashi
labarin irin mutuncin Inna Safiya tun suna yammata. Jamilu ya sosa kai, da damuwa yace.
Hajiyata ina da magana, tuntuni, amma ina shakka, kin ga ba don halin Baban mu ba da illar da

ya yiwa mutuncin mu gun Inna Safiya ba, me zai hana na auri Hauwa? Da ba sai kawai a yi yar
gida ba ni da Hauwau? Rai kwance hankali kwance?”
Hajiya Rumana ta ce cikin mamaki wai kana nufin kana son Hauwa din ne? Jamilu ya koma
sosa keya da hannun sa daya yace gaskiyar maganar kenan, Hajiyarmu tun ranar da na buge
ta, nake fama da zuciyata a kanta, zuciyata bata kara zama lafiya ba a kan tunanin yadda zan yi
na mallake ta, kullum tunani na shine yadda alamarin zai yiwu cikin sauki, amma na hanga na
duba ta bangaren Babanmu na tabbatar zan samu matsala sosai da shi.
Jiya na je gaishe shi, na same shi na gaya masa tsautsayin da ya gifta na kade Hauwa, cewa
yayi tun da na kaita asibiti na biya magani kada ya kara jin na koma inda suke.
​ Haj. Rumanatu ta ce umh, ni na rasa irin wannnan yan ubanci da yake yi wa dan uwan
sa, shikadai ya rage masa amma ya kasa kaunarsa, wallahi shi bai dauke shi haka ba
Bilyaminun, baka ga irin cin kashin da yake masa ba, haka yake masa tun suna yara saboda
bakin cikin ya fi shi samu a sanaar sa ta gwanjo. Kaima dai Yayan Hansatu banda kana son taro aradu da ka, ba zaka kaiwa mahaifin ka
wannan maganar ba.
Jamilu ya ce (with boldness) idan har Hauwa ta amince min in sha Allahu zan yi nasara a
kansa. Hakan ne kadai zai gyara wannangurbataccen zumuncin ya rage kiyayyar idan mun
haihu nida Hauwa. Ta ce “to idon ta fa? Zaka iya zama da makauniya Jamilu?
Ba wai ina kin Hauwa bane saboda lalurar ta, tunda kuwa yar uwar kace jininka ce, amma
akwai abun dubawa.
Tarbiyyar yaya, dawainiyar cikin gida, abubuwa ne da sai mai ido zai iya yin su. Da aikin
banki zaka ji, ko da kula da nakasassar mata a cikin gida musamman in ta fara haihuwa? Kaida
in ka fita tun sassafe wani zubin sai dare kake tasowa?
Don kuwa Hauwa, kasa a ranka in ka aure ta duk kai zaka yi mata wadannan abubuwan
dana fada a can baya tana daga zaune tana fama da kanta.
Jamilu ya nisa cikin jin karin kauna da soyayya da tausayin Hauwa, sannan ya ce Hajiyata, a
irin son da na samu raina yana yi mata, sam ban hango wadannan kalubalen ba, amma ni Jamil
Zakari naji na gani, na yarda in har zan samu auren Hauwa, zan hadasu duka ita da yayanta in
raine su in kula dasu har aikin bankin duka bazan kasa ko daya ba. Hajiya Rumanatu tausayi ya
cika ta, ta dade da sanin dan ta Jamilu mutum ne har mutum, mai kyakkyawar zuciya akasin ta
mahaifinsa, ta dade tana dakacen dama ace Bilyaminu ne ya haife shi, saboda halinsa na
yawan kirki da nagarta shiyasa ma mahaifin sa sam bai cika shiri da shi ba don komai nasu
Allah daya ne gari banban.
Sai ta ce Allah ya tabbatar da alkhari a tsakanin ku idan akwai, ya huwwace maka lamunin
mahaifin ka cikin sauki. Auren Hauwa hakika Jihadi ne babba zaka yi, na gyaran zumunci da
kuma na taimakon miskinin da baida maraba da maraya.
**** **** ****

An sallami su Inna daga gadon asibiti bayan an kwance karayar hannun Hauwa ranar wata
lahadi, ta dauka shikenan sun rabu da jelen Jamilu. Amma ina! Ashe wasa farin girki, lokacin
nema Jamilu ya maida gidan su wajen zuwansa. Aka ce in kaga kare na sunsunar takalmi.
​ Wani babban abinda yafi bata mata rai, duk shiru-shirun Hauwa da miskilancinta in da
Jamilu suke hira kaji ta har tana kyakyatawa tun daga soro, tana hira rai-rai-rai kamar kanari ita

da shi, ta sake da shi sosai abin ki da jini! Asabar da lahadi da baya zuwa aiki a gidan su yake
wuni, makale da Hauwa, Inna ta rasa yadda zata yi da Jamilu. Daga baya ya fito fili ya gaya
mata shi fa kamun kanwarsa yake yi, da zarar ta kare sakandire zai kawo sadakinsa.
​ Inna kam bata yi kasa a gwiwa ba ta ce Jamilu kana wasa! Kaima ka san wannna abu
ne da ba zai taba yuwuwa ba, don haka na roke ka daga yau kada ka kara tada wannan
maganar mara yuwuwa.
Ni bazan raba ka zumunci da yar uwarka ba, amma bana bayan wannan maganar wai auren
zumunci kai da ita.
​ Jikin sa a sanyaye ya koma gida ranar, kuma kai tsaye ya yanke shawarar tunkarar
mahaifin sa a kan maganar, a yi ta ta kare. Komai ta fanjama-fanjam.
​ Malam Zakari sai da ya bari Jamilu ya gama bayani kaf cikin kankan da kai, da tsananin
ladabi ga mahaifin nasa, sai ya ce masa, kai kai kai! Kai kuma ta nan ka bullo?
Auren makauniya? Diyar BILYAMINU jafai a cikin zuria ta? Toh ban shirya haifar jikan da zai
zo ya zama dan jagora ba. Ko ya gado makanta ya saka min a cikin zurria, ko babu makanta
haihata-haihata jinina ya gogi na Bilya jafai, jinin jaraba jinin masifa jinin tsiya da rashin arziki.
Idan ka kuskura ka sake zuwa inda suke, idan na ji labari, sai na tsine maka albarka.
​ A gigice Jamilu ya bar gaban Baban sa, o ganain gabansa baya yi, shi kuma Zakari
Jamilu na tafiya ya saka takalman sa ya fito ya rufo shagon atamfofin sa dake cikin Singa.
Da ya fafuri mota bai tsaya a koina ba sai a Badalar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login