Showing 24001 words to 27000 words out of 39674 words

Chapter 9 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf

kalar dana ke so na koma (kasancewar
Sumayyah fara ce tas).
Sarham ya juya ya galla mata harara don ya ji ta sarai. Yace wallahi zaki koma yanzunnan in
baki yi min shiru ba”. Inna ta leko jin maganganun su tana maraba da bakuwa, nan da nan ta
saki fara tace Sumayyatu ce ko?
Sumayyah ta washe baki jin farad daya Inna ta kama sunan ta, ko da wannan ta san tana da
matsayi mai girma a gun Bhaiya, tunda har wadanda yake muamala da su sun san da zaman
ta.
Ta ce ni ce Inna ina wuni?
Inna ta bata shimfidar karaunin ta ta zauna, inda Hauwa ta tashi, a lokacin ta gama alwalarta
ta juyo tana tafe zuwa inda suke kanta tsaye babu ko lalube, tsabar ta dade da sanin kowanne
lungu da kowanne sako na gidan su. Sumayyah ta kamo hannunta ta zaunar da ita a kusa da
ita, cikin girmamawa Hauwa tace da Sarham Ina wuni likita, yaya aiki? Ya dan dubeta kadan
kafin yace an gode Allah Maijidda, ga Yayarki Sumayyah na kawo miki Sumayyah ta saka
hannunta cikin na Hauwa, sai Hauwata rike hannayen nata sosai a cikin nata tana murmushi
tace sannu da zuwa.
Basu jima suna hira ba Inna ta kammala girkin ta na dambun shinkafa da yaji zogale da
soyayyen mangyada ta zubo musu a kwano guda, sannan ta zubawa Sarham yadda ta saba
zuba masa a kwanon sa da ta ware masa na samira wanda sabida shi ta dauko shi daga cikin
samirunta, shikadai take zubawa abinci a ciki. Ga yaji da yaji tafarnuwa a gefen abincin. Kamar
ta san shi da son tafarnuwa, Sumayya ta hadiyi miyau tun kan ta kai loma abincin ya gama yi
mata, sannan tsaftar masu gidan ta gamshe ta.
Hauwa kasa cin abincin tayi da Inna ta hada musu itada Sumayyah don bata sakewa da baki
amma Sumayyah sosai take kai loma, nan da nan ta tashi da dambunnan. Shima Sarham tuni
ya tada nasa sai kwanuka aka direwa Inna.
A ranta Sumayya ta ce eh, wato dole Bhaiya yayiwa abincin gidan su kaura, yana nan an
gargajiyantar da shi da wannan girki mai motsa kunnuwa. Basu jima ba sosai don zasu gidan
Hajiya Kulu, Sumayya ta baiwa Hauwa sayayyar a hannun ta inda ta saka mata ledojin a cikin
hannun ta ta ce, ga nan gift dinki ne inji Bhaiya, ki cigaba da dauko na daya kin ji Hauwan Inna, shi kuma yayi
ta kawo additional gift, duk karshen shekara.

Murmushi Hauwa tayi, tana shafa kayan da ledojin, murmushin na karuwa a fuskar ta, kanta
a kasa ta ce kice masa nagode, Allah ya saka da alkhairi, kema na gode da ziyara Anti
Sumayyah.
Bayan fitar su da kadan itada Inna shiru suka yi. Hauwa tace Inna ni bazan taba komai ba,
don bana son abinda zaa zo ace muna kwadayi. Inna tace to ban ki ta taki ba Kulu, amma
shima ya san bamu kwadayin komai nasa tunda baki roke shi ba kuma ba yau ya fara ba, saidai
na yau nima ya tsorata ni, don kayan sun ci kudi da yawa da alama. “To Inna ki ajiye ni dai
bazan taba ba Inna tace “tsahon shekara guda kenan muna tare da yaron nan, in da wata
manufa a tare da shi ko da wani hali nasa mara kyau zuwa yanzu ya kamata in sani, to ban
taba gani ba sai tarin alkhairi da nagarta a tare da shi.
Alheri da kyauta wannan na lura halin sa ne na halitta kawai. Don haka ni mahaifiyar ki Safiya
na ce ko bayan raina duk abinda Sarhamu ya dauka ya baki da hannun sa ki karba da godiya,
ki kuma yi amfani da shi da zuciya daya, wannan yaron bashi da wata manufa akan mu sai
zumuncin Allah da ya saka kansa tsakanin sa da mu, don bazan ce wani ne ya saka shi ba ko
don neman wani abu daga gare mu”.
​ **** **** ****

​ A cikin mota suna kan hanyar zuwa gadon kaya, Sumayyah ta kasa shiru, abubuwa da
yawa sun tsaya mata a rai game da muamalar Sarham da gidan su Hauwa, babu tudu me ya
kawo gangare? Ta saci kallon Bhaiya, wanda ke tukinsa hankalin sa a kwance, ta ce,
Bhaiya, ina da tambaya, if you permit, may I ask? Tsakani da Allah son Hauwa kake yi?
Wani irin wawan burki da Sarham ya ci da motar, saida dukkan su suka wuntsulo gaba, suka
kusa ci da baka a gaban motar. Saura kadan ya kwadawa Sumayyah mari, domin ji yayi kamar
ta yi sabo, amma ya daure ya rike hannun sa yana cewa ba zai taba dukan mace a rayuwar sa
ba in sha Allah, balle Sumayyah, da yafi so duk gidan su, kowacce irin katobara zata yi masa
kuwa, ba shiri Sarham yayi parking motar a gefen titi.
​ Cikin matsanancin mamaki da fushin da yake so ya danne yake kallon kanwarsa, yace
da Sumayyah ke kuwa me ya kaiki wannan tunanin mai kama da sabo? Sumayya sakewa ta
dake har ta kai da ki raina ni irin haka?
A duniya mutum bazai yi wata kyakkyawar alakar mutunci da zumunci da mutanen da ya san
darajar su, suma suka san tasa ba, kuma yayi sanadin janyo musu lalurar da basu da yadda
zasu yi da ita sabida raunin su, da rashin namiji tsayayye a cikin rayuwar su, mutum bazai yi
tunanin taimaka musu da faranta musu domin Allah ba sai don wannan shirmen? Sumayyah idon ta ya raina fata da ganin bacin ran Sarham karara, ta ce kayi hakuri Bhaiya,
ba raini bane hasashe na ne dana kasa dannewa a rai na, na yi laakari ne da maganar
Hausawa da suka ce in kaga kare yana sunsunar takalmi… dauka zai yi.”.
Da sauri Sarham yace amma kuwa Allah wadaran wannan bahaushen da a wajen sa babu
kowacce alaqa ta mutunci da taimako a tsakanin alumma sai da manufa, babu kyautatawa
mara galihu sai a dalilin wani shirmen banza wai SO!”. Yana fadi yana tada motar, da gaske a
gareshi so shirme ne, don baiga ranar da so yayi masa ba. Yana tukin yana maida numfashi, fuskar MADINAH ATTAHIRU na gilmawa a idanun sa. Itace
silar bacin ran sa ba maganar Sumayyah ba, ita tayi fami ne akan gyambon da aka samu yayi
healing ba tare da ta sani ba.

Sumayyah jikin ta har rawa yake ganin yadda jikinsa har tsuma yake, ta ce don Allah don
Annabi kayi hakuri Bhaiya, ni tambaya kawai nayi bansan ranka zai baci haka ba, kayi hakuri
bazan sake shiga abinda ba ruwa na ba.
Sai kawai ya fizgi motar ba tare da ya kara ce mata komai ba, amma ya fasa kaita gidan
Hajiyar Gadon kaya, kofar gida ya maida ita wato can gidan su, New Site.
Tun bai gama tsayawa ba da motar yace, fice min daga mota malama, daga yau bazan kara
fita da ke koina daya shafeni baba, uwar kaudi uwar tsugudidi, fadi baa tambaye ki ba.
Jikin ta nata bari ta bude kofar motar ta fita daga gaban motar, hawaye ya tsirgo mata, zata
cigaba da bashi hakuri ya fizgi motar sa ya bar harabar gidan su.
​ Sumayya ta dade tsaye a wurin, tana nadamar shegen surutun ta, da bata iya gani tayi
biris, daga karshe ta share hawayenta ta shiga gida.
Yinin ranar zungur, Sumayyah ta kasa sukuni idan ta tuna Bhaiya na fushi da ita, Aunty
Surayya na tambayar ta me aka yi mata take kulubi da hade rai? Sai ta ce a fusace ina ruwanki
dani? Ko ina shiga harkar ki? Mama tace ke ko! Ina laifin Yayan da ya damu da kai? Nifa rashin
kunyar ki ce take hada ni da ke Sumayyah ta tashi fuuu! Tayi dakinta ta bar musu falon.
Surayyah na fadin kyaleta Mama ta yi da yar halak.
Shikuma tunda ya sauketa asibitin Murtala ya koma. Ya shige ofishin sa ya kulle kan sa a
ciki.
Maganar da Sumayyah tayi kuskuren furtawa ta tuna masa da shekaru biyar a baya, abinda
ya dade da mantawa; ta tuna masa ‘first love affair din sa wato MADINAH ATTAHIRU
(MADINAH SORON DINKI), yar ajinsu, wadda bai sha da dadi a hannun ta ba dama iyayen ta
da sunan soyayya, shiyasa duk inda aka ambaci yana son mace, sai ran sa ya kai makura
wajen baci.
Ya so Madinah kamar rai, irin son da ake kira (love at first sight) tun bai gama sanin ciwon
kan sa ba, amma Baban ta ya wulakanta shi, don a cewar sa nawa yake a shekaru da matsayi?
Sune samarinnan masu hurewa yaran mutane kunne su hana su karatu, bai isa auren diyar sa
ba. Sannan Uban sa ma bai isa ba, tunda ba wani bane banda malamin makaranta, ina shi ina
auren diyar sa?
A lokacin ko part three na karatun sa bai hada ba. Soyayya ta rufe musu ido, soyayya ce irin
ta tashen balaga daga shi har Madinan, sun so juna shi da Madinah kamar daya bai iya rayuwa
ba tareda dan uwansa ba, sun yi alkawarin aure da zarar sun kammala MBBS sabuda yadda
suka zaku ga son mallakar juna, amma Baban ta sai ya canza mata makaranta ma, duk don ya
raba su, ya nesanta Madinah daga gareshi kwatakwata, don yace ya fahimci zai hana yar sa
karatun da ya kai ta ta yi a Jamiar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah ne kawai, shine dalilin da a
karshe ma ya dauke yar sa ya maida ita Jamiar Yamboa dake kusa da Madinatul Munawwara,
inda acan ne Madinah ta samu ta kammala nata karatun, shikuma ya kammala a King Abdul
Aziz University ya dawo kasar sa ta haihuwa, daga lokkacin basu kara haduwa ba shi da
Madina ko a hanya ko a waya ko a mafarki.
​ Baya ko son tuna wata kalma wai ita soyayya saboda abinda Baban Madinah yayi
masa, shi ya san tsakani da Allah ya so Madinah ya kuma yi niyyar auren ta da zarar sun
kammala karatun matakin farko na koyon likitanci, itama kuma sai ta baiwa mahaifin ta goyon
baya dari bisa dari, lokacin da ya maidata Yamboa sai bata kara nemansa ba koda kuwa a
email, ko a telephone, ko ta wasika da ake aikawa ta post office a lokacin.

**** ***** *****

HAUWA-KULU
Kusan shakuwar tafi yawa tsakanin Inna da Sarham maimakon Sarham da Hauwa, kasancewar
Hauwa bata da magana kuma taki sabawa da Sarham har gobe, duk kuwa da yadda yake
kyautata musu, kuma yake jan ta da wasa lokaci-lokaci, iyakaci in ta ji ya zo ta gaida shi, ta
shige daki ta bar su, in ya mata tambaya akan karatu ta bashi amsa a gajarce, kuma in an bata
sakamakon ta bata kasa a guiwa wajen nuna masa da zarar ya zo gidan.
Don ta yarda Dr. Sarham shine ginshikin karatun nata. Kuma ta kwana da sanin taimakon da
yake yi musu mai dimbin yawa ne, da yafi karfin a gode masa, don duk da Inna ta cigaba da
sanaar ta ta sayar da wake da shinkafa duk wata hidima ta karatun Hauwa shi yake yin ta
kamar biyan Salele albashin kaita makaranta da daukota, da basu kudin hawa hayis zuwa da
dawowa, sayen littatafai da kananan abubuwan da makaranta ke bukata kasancewar special
school makaranta ce ta gwamnati domin yara masu bukata ta musamman yasa babu bukatar
biyan kudin makaranta.
Daga baya kuma Sarham baya zuwa gidan Inna sosai saboda ayyuka da suka tarar masa
amma duk weekend baya fasa lekowa. Ya zama dan Inna, Inna ta zama uwar sa, ya zama dan
gidan Bilyaminu kofar Naisa, don ganin sa take ya maye mata gurbin Zulkifilu.
​ A yanzu hatta a weekend dinma Dr. Sarham baya samun zuwa hira wajen Inna kamar
da, domin yana shirye-shiryen komawar sa Jiddah, bayan kwashe shekaru biyu yana aikin
gwamnati, tun akan abinda ya faru da Hauwa yasa a ran sa zai koma zurfafa karatun sa, domin
ya ki yardarwa kansa har zuwa yanzu cewa ba rashin kwarewar sa bane ya janyo wa Hauwa’u
cataract blindness, yasa a ran sa yana bukatar kara zurfafa ilmin sa zuwa mataki na gaba. Sai
ya ga abinda ya turewa buzu nadi daga ilmin likitancin ido, akan dai specialization din sa na
ophthalmology a shirye yake har ya tsufa in dai da rai, bazai gushe ba kuma bazai gaji ba yana
karawa kansa kwasa-kwasai na fadada ilmin sa da zurfafa shi, don zama kwararren ophthalmic
surgeon din da zai zamowa kasar sa abin alfahari watarana da fiddawa kansa ‘inferiority
complex’ din da yake fama da shi tun akan aikin da yayiwa Hauwa-Kulu. Duk da cdewa bayan
nan yayi wasu ayyukan fidar da yawa kuma an yi nasara. Abba Prof. kuma ya lamunce masa ya
koma din, don a cewar sa gara ya gama karatun duk da zai yi cikin kuruciyar sa, kamar yadda
shima ya samu yayi nasa yake cin moriyar sat un da jimawa.
**** **** ****
Jikin kafatanin mutanen gidan yau a matukar sanyaye yake, wannan ya faru ne kasancewar
gobe da asubah ake saka ran in sha Allah, Bhaiya (Dr. Sarham Shanono), zai tashi zuwa kasar
da ya baro a can baya a karo na biyu wato kasar Saudi-Arabia don zurfafa karatun sa.
​ Sabo, wani abu ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar iyali, musamman irin wannan
wadanda suka gina tubalin rayuwar su akan tsari na (nuclear family) wanda akasari yan boko ke
yi, wato rayuwa ta daga su sai yayan su, kamar yadda yake a gidan Prof. Abbas Shanono.
Don haka ficewar daya daga cikin su rana daya zai haifar da wawakeken gibi ne a gidan,
musamman shi Sarham da yake jigon gidansu, sannan ‘personality’ din shi ya banbanta dana
kowa cikin gidan, shi mutum ne na kowa!
Likita mai farin jini da sakewa da mutane wanda kowa nasa ne, mai faram-faram da hidima
da kowa nasa, shi kadai ne Da namiji a cikin su, in ka cire mahaifin nasu.

Don haka shi din, tamkar wani bango ne a gidan su abin jingina. Gabakidayan su jamaar
gidan, in ka dubesu yau zaka fahimci tsantsar damuwar da suke ciki, kowa fuska ba annuri,
banda Abba Prof. da ke shi babba ne, ya boye tasa damuwar, maimakon hakan, sai ya rajaa
wajen lallashin su da karfafa musu gwiwa kan tafiyar Sarham din da cewa, menene abun damuwa don Sarhamu ya tafi? Tunda ga waya yanzu, ta fara zama abu mai
sauki, kuma dukkan ku zaku so ganin ranar da Sarhamu zai zamowa kasar sa abin alfahari
inace, wanda zai zo a dama da shi a harkar kiwon lafiya a Arewacin Najeriya”.
Amma fa shima Abban a ran sa ya fi kowa damuwa, ya fi su shiga kewar Sarhamu, tun ma
kafin ya tafi, saboda yadda Sarham yake tsaye kullum kan hidimar sa data gidan sa, wani abun
ko labari baya ji sai zance ya shigo da zance, Mama zata ce ai Sarham yayi kaza, kamar misali
cefanen gidan sa, yana dadewa bai yi ba. Haka maganin da kowa yake sha idan rashin lafiya ta
samu dayan su, Sarham da bai da iyali ya daukewa Abban su kananan abubuwa irin
wadannan, su petrol din tada janerato, har ila yau, yana matukar taimakawa shi kansa Abban
da nasa ayyukan ofis din kasancewar Allah yayiwa Sarham baiwar ilmi da sanin hikimar
koyarwa, kuma da yake a fanni guda suke shi da Abban. Don haka shima yana cikin kewar
Lelen Abba!
Shima Sarham din karfin hali yake yi, musamman in ya dubi Sumayyah, da kukan da take yi.
Sai Abba Prof. yace tayi hakuri yayi mata alkawarin bin bayan Sarham da zarar ta kammala
sakandire itama zata je ta yi MBBS a can inda yake.
​ Kasancewar Abba Prof. yana da hanyar tagomashin karatu a kasar Saudiyyah
(scholarship) na Jamiar KING ABDULAZEEZ UNIVERSITY domin akwai abokan karatun sa da
yawa da suke aiki a jamiar, tun bayan bude tsangayar likitanci a jamiar. Da an samu rarar gurbin
karatu su kan bashi. ​ Mama bayan Sarham ya shiga dakin sa yana hada kayan tafiyarsa, sai ta zare jiki ta
bishi a baya, kujerar karatunsa dake dakin guda daya ta samu ta zauna, Mama ta ce,
“Sarham haka muka yi da kai? Ya bar abinda yake yi ya bata hankalin sa ya ce akan me
Mama? Tace maganar diyar Barr. Hannatu da na gaya maka muna so muyi muku yar gida don
kara karfafa zumuncin dake tsakanin mu ni da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login