Showing 36001 words to 39000 words out of 39674 words
Chapter 13 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf
Kofar Na’isa.
Gidan ai ba zai taba bace masa ba, tunda kuwa gidan gadon su ne, Bilyaminu yayi
masa karfa-karfa ya raba shi da shi, don haka kai tsaye ya tuna hanya, bayan tsayin shekarun
da ba zai iya tuna yawan su ba rabon sa da ko bin hanyar.
Zakari ya yi sallama a zauren Inna, da katotuwar murya mai razana wanda ake yimawa.
Ta na tsakiyar dabbobin ta tana zuba musu dussa, ta ji muryar sa yana kwada sallama kamar
zai tada gidan Safiya, ina Safiyar ne? Diyar masu Danjangabo?.
Nan da nan zuciyarta tace mata ZAKARI!. Don shikadai yake kirata diyar masu Danjangabo
don sanaar mahaifiyarta kenan. Inna ta dago kai cikin mamaki ta tako ta iso soron ta yi tsaye a
gaban sa, bazata iya tuna rana ta farko da ya tako kafar sa gidan su ba tun bayan rigimar
mallakar gidan, da a karshe ya sayarwa Malam Bilyaminu. Ai bai kamata kiyi mamakin gani na yau ba, tunda ke kika takalo ni, kuma kin sanni farin
sani kamar kashi nake, sai an kula ni nake doyi”. Zakari ya fada cikin gyara murya da gyara
tsayuwa. Inna tace,
dole in yi mamaki mana tunda dai na san banza bata kai zomo kasuwa yo daman ina kuwa
zata kai shi? Sai ya ji wuta!
Zuwa nayi in ja kunnen ki, in sake ja, da kwantareriyar murya, in kin ji kin dauka, ki zauna
lafiya, in kin ki ji ba kya ki gani ba.
Ki saki kurwar Da na Jamilu ta shakata, don shi ba nakasashshe bane, haka kawai kin
ga yaro da maikon sa shine zaki bi dare ki bi rana ki lika masa makauniya ko? Yo Allah na tuba
ko Kulu idon ta hudu kinga ta dace da Jamilu yaro son kowa dan gata dan asali, mai ilmi, mai
nasaba, Uwar Bilya kuwa ki bincika tarihi kiji inda uban mu ya samo ta, can ne cikin zuriar su
barbushe da tsimbirbira.
Inna Safiya ta yi tsaki ta ce kana tunanin ko Hauwa ta rasa miji saboda makanta, ko tana
yawo tsirara saboda talauci, zan dauketa na baiwa dan ka ko shugaban kasa ya zama?
Ai ni martabar diyata da kake gani, duk da take marar ido, miskiniya, wallahi tafi karfin gidan
ka, wulakantaccen gida na rashin tarbiyyah, gidan da daga yan daba sai yan shaye-shaye, sai
sauta ga wawa rututu. Uba daya uwa kowa da tasa, kurwar ya ta kurr da shiga irin wannan
laanannen gidan na Allah wadai, in sha Allahu. Zakari ya kyabe baki duk da ya ji mugun ciwon maganganunta, ya ce ni dai na gaya
miki, kuma aure-aure ai arziki ne, idan fitsari banza ne kaza tayi mana, shi bai iya ya kara ko
daya ba saboda talaucin da yasa shi barin gida, ke da aka gudu aka bari bakin jini yasa ba
wanda ya taba zuwa ya sunsuna ki da sunan aure, a haka zaki mutu gwauruwa, da makauniyar
ya a gaban ki kina mata tsarkin kashi.
Daga yau zan zuba C.I.D a kofar gidan nan, aka kara gaya min an ga Jamilu ya shigo, duk
abinda ya same ki ke da makauniyar yar taki ku kuka da kanku, ke kika saya muku da kudin ku,
lakadan.
Ya juya ya tafi, ya bar Inna tana tsaki. Juyawar nan da zata yi sai taga Kulu a bayan ta
curko-curko da ita, manyan idanun ta kamar sa fado kasa don tashin hankali, tayo waje dasu
bakidaya. Inna tayi kwafa tace,
gara da kika ji da kunnen ki, irin tijarar ubansa, marar lissafi, gobe ki kara tankwashe kafa
kina hira da Jamilu da sautin murya kamar na gyare, a zo a ci mutuncina ban ji ba ban gani ba.
Jamilun da kin riga kin san waye ubansa, ko wanene Zakari ba bakon ki bane ba.
Jamilun bai san an yi haka ba a washegari ya zo wa Hauwa sallama zai wuce wani
workshop’ da banki ya tura su na sati daya a jihar Delta.
A take kuwa aka kira Alhaji Zakari a waya aka gaya masa, ga Jamilu nan ya sake zuwa.
A ranar, duk da Inna na cikin bacin rai, haka ta hadiye shi, ta zaunar da Jamilu a
gabanta, cikin lalama ta roke shi Allah Annabi ya rabu da Hauwa-Kulu, kada ya kara zuwa gidan
su.
Ta warware musu shi da Hauwan irin tsohuwar gabar da ke tsakanin iyayen su maza tun
kafin a haife su, a sanadin yan ubanci kawai, ba wani kwakkwaran dalili. Ta kuma gaya masa ita
a yanzu girma ya cimmata, bata fama da ciwukan zamani ko guda daya, don haka bata son
abinda zai tada hankalin ta. Ta ce masa Hauwa kuma ka gani nakasa ta same ta, wadda tasa bazan iya yi mata aure ba
sam-sam, balle na kai ta cikin iyalin Zakari, zai iya hura wuta ya babbaka min ita, a karshe Inna
tace.
“Jamilu daga ni sai kuma Allah kadai muka ragewa Hauwa-Kulu, ni kadai ce karfin ta a
yanzu, don haka ina tattalin rayuwar ta ne bazan iya kaita inda bazata taba samun kwanciyar
hankali ba, koda zan mata auren, balle in kaita gidan ku. Balle kuma bazan taba yi mata aure
ba in ba idanun ta ne suka dawo ba. Don haka na roke ka Allah da Manzonsa kan a bar zancen
nan daga yau, anan inda zamu ajiye shi.
Jamilu na yarda kai mutumin kirki ne, zuciyarka ba irin ta mahaifinka bace, kai daya ne cikin
dubu a gidanku, kuma kai mai nufin Hauwa da alheri da soyayya ne, duk da lalurarta ka amince
ta zamo maka uwar iyali a haka, babu wata kauna da taimako da soyayya da wani dan adam
zai nuna ma Hauwa a duniya da ya wuce wannan a doron kasa. Hakika mun yaba maka, mun
kuma gode maka, domin ka so kayi jihadi ne kuma Allah zai baka ladan niyya.
Amma komai zamuyi sai da yardar iyaye zai yi albarka Jamilu ka sani, ina kuma tabbatar
maka ba zaka taba samun albarkar mahaifin ka ba in kana tare da Hauwa-Kulu”.
Jamilu Zakari, yasa hankaci yana tsane tulin hawayen idon sa, ya fahimci Inna sosai,
yau kam ya fahimci bata kinsa da Hauwa kamar yadda yake zato a baya, ya fahimci abinda ada
ya kasa fahimta, wato su iyayen Hauwa da nasa mahaifin, bazasu taba zama a inuwa guda ba,
a sanyaye Jamilu yace. “Inna na ji ki, na kuma fahimce ki, amma ku sani daga ke har Babana; Hauwa yar uwa ta ce
ta jini, baa raba hanta da jini, ni kadai na rage mata matsayin Uba kuma dan uwa a yanzu.
Maganar aure tsakanin mu na bar ta har abada! Amma ni Jamilu daga yau nine Yayan
HAUWA-KULU na halali kuma Uban ta na jini, daga nan har karshen rayuwar ta, ko kuma ranar
da mahaifin ta ya dawo na damka masa yar sa a hannunsa.
Kiyi min alfarmar cigaba da zumunci da ita, da kula da ita, tunda na hakura da maganar
aurenta, ba don komai ba sai don samar muku kwanciyar hankali amma ba don na daina sonta
ba, don ni da kaina na san Babana hatsabibi ne”.
Inna ta rasa kuma me zata ce. Ta rasa Jamilu kowanne irin mutum ne da baya gane
abinda zaa shekara ana ganar da shi.
Da zai tafi ya kawo kudi masu yawa ya baiwa Inna, shi kan sa baisan adadin su ba, yace
su yi amfani da su kafin Allah yayi masa dawowa daga tafiyar da ta same shi zuwa Delta.
Jamilu ya tafi Delta da kwana biyu aka yi sallama da Inna a zaure, maza ne magidanta
su uku, nan suka gaya mata yaya har yanzu bata tashi daga gidan ba?
Inna ta ce wane gidan? Sai suka hau mata bayanin wannan data ke ciki yanzu, saboda mai
gidan yana so zai rushe shi, zai mayar da wajen kamfanin buga ruwan leda, ko ba a gaya mata
an bata notice din tashi na kwana uku ba?
Inna tayi musu kallon banza ta ce ban gane ba? Anya nan gidan kuke nema? Nan dai gidan
Malam Bilyaminu Kofar Na’isa ne, wanda ya gada daga tsohon sa.
Ya gada ko suka gada?.
Mutumin ya gyara mata zance cikin gatse. Kafin ta bashi amsa yace to ai shi Zakari ya riga
ya sayar mai da gidan a gaban wadannan shaidun”, ya nuna mutanen da suke tare, wadan da
yan unguwar ne abokan Zakari, sannan ya fiddo ainahin takardun gidan ya nuna mata,
wadanda Innar bata san ina aka je aka samo su ba. Suka ce lallai suna son gidan su zuwa gobe, don zaa zo a rushe shi goben, da sauran
gidajen da aka saya na makwabtan su.
Da fadin haka Inna ta rasa abinda zata yi, sai kawai ta saka kuka tana cewa su koma su
gaya wa Zakari ta sallami dan sa Jamilu in dai a kan sa ne zai mata wannan tozarcin. Ko
sauraron ta basu yi ba suka tafi.
Har washegari Inna ta kasa gayawa Hauwa maganar nan, tana ta fama da ita a kirjin ta
dake faman zabalbala, zuwa yamma kuwa wasu tsagerun samari suka shigo suka soma fatali
da kayan Inna suna jefo komai waje. Suka ce suma saka su aka yi. Ga masu rusau nan zuwa,
in sun ki fita ta arziki zaa rushe har da su suna ciki. Yadda ake jifa da kayan Inna a unguwar ya janyo hankalin daukacin jamaar unguwa, suka
taru don neman baasi, amma ba wani bayani sai na maigidan ya sayar da shi, ita kuma Inna an
ce ta fita ta laluma taki fita. Inna na kuka, Hauwa kuwa don taurin da zuciyar ta tayi idon ta ko
kyallin hawaye babu, amma ya kada ya yi jajir, jakar makarantar ta lalubo da gilashin ta da
Sarham yayi mata ta sakaya idanunta, ta goya jakar ta mai dauke da komai nata na makaranta
ta kama hannun Inna, kamar itace mai idon ba Inna ba, Hauwa tace.
Kada ki damu Inna muje, Baba Zakari ya kara arziki da gidannan don Allah, in don ni ko a
tashar mota da karkashin gada zan iya kwana, in dai idan gari ya waye zan je makaranta, ba
kuma zaki bar ni in yi “bara” don bana gani ba.
Inna ta kasa magana sai kuka, a haka ta yafa mayafin ta ta kulle kayan ta da zata iya
dauka a bakko, ta kama hannun Hauwa suka fice daga gidan.
Gidan su mai tsohon tarihi! Gidan da tayi dukkan rayuwarta da yaya da mijinta, sama da
shekaru talatin. Gidan da ba abinda take so a rayuwarta sama da shi.
Ga Hauwa kuwa wannan gidan na bayan Badala shine farin cikin ta, da shi kadai take tuna ta
rayu tare da mahaifinta.
Ko minti goma basu yi da fita ba, masu rusau din suka iso, cikin dan lokaci suka hau rushe
gidan Malam Bilyaminu. Kafin dare sai kasar gidan da duwarwatsu, Dabbobin Inna kam tuni sun
yo waje da suka ji su a bude babu turke. Sai Malam Isa da ya dawo kasuwa ya ga dabbobin a
kofar gidansa aka kuma gaya masa abinda ke faruwa wato Zakari ya kwace gidan ya sayar su
kuma wadanda suka saya sun rusa, Hauwa da Inna suna tsaye a kofar gidan sa ake ta rushe
gidansu akan idon su, sai ya tattara dabbobin ya kora su wani kango na gidan sa ya rufe su.
Jamaar unguwa suka yi dafifi suka hana Inna barin unguwar suka ce tunda dare yayi ta
shiga gidan Malam Isa zuwa gobe, dattijan unguwa sun ce ta zauna gobe a shigar da karar
Zakari a kotu. Don mai unguwa ya dade da rasuwa.
Saidai cikin daren, a gidan Malam Isa, inda aka baiwa su Inna mafaka, Inna ta canza
shawara, ba ita ba shiga kotu a rayuwarta saboda abun duniya, a wurin mutanen da shiga kotu
na nufin karshen tozarci ga mutuncin su kenan, meye abun duniya wanda duka mutuwa zaayi a
bar shi a inda yake? A gidan Malam Isa suka kwana dakin matar sa Mai kosai, da asubahi ta kama hannun
Hauwa ta dora kayan su a kanta, suka faki idon kowa suka bar gidan Malam Isa. A lokacin shi
yana masallaci sallahr asubahi, matar sa kuma tana daka tana jan rago (munshari).
Kai tsaye Inna da Hauwa suka naushi hanyar fita daga BADALAR Kofar Naisa, ba don
sun san inda suke nausa kafafun su ba, ko suna da wurin zuwa, burin Inna kawai su yi nisa da
kusa da duk wata Badala ko Kofa da Zakari yake ciki ba kofar Naisa da Kofar Dan agundi kadai
ba, kasancewar kofofin biyu suna makwabtaka da juna. In haka ne kuwa sai dai su bar duka
kwaryar BADALOLIN KANO bakidayansu, kafin su iya yin nisa da Zakari, in ba haka bata
tabbata zai sake biyo su ne ya batar da ita itama in ta tsaya shariah dahi a kotu, kamar yadda
take da kyakkyawan zargin shi ya batar da dan uwan sa mijinta Malam Bilyaminu!
Hanyar da ya bi ya batar da shi dinne bata sani ba har gobe. Ta san dai ko don ya ganewa
idon sa irin tagayyarar MISKINIYAR yar dan uwan sa a rayuwa da ya hana dan sa mai lafiya ya
aura ta tabbata Zakari zai sake biyo su. Don haka dole ta dauke HAUWA-KULU suyi nisa da
BADALOLIN KANO bakidaya, don dai ta nisance shi, ta kuma kare Hauwa daga kiyayyarsa da
zalincinsa da hassadarsa.
Daga yau tayi kudurin zamewa Hauwa GARKUWA daga dukkan abinda zai cutar da ita
musamman kanin Uban nan nata, Zakari, wanda yau ta kara tabbatarwa baya nufin su da
alheri. Tayi kudurin cika burin masoyin su na hakika wato “Dr. Sarham” akan Hauwa, na ta
tsayawa Hauwa komai runtsi ta samu rabauta daga ko ilmin sakandire ne, ba tare da ‘makanta’
ta zame mata shinge (barrier) ga neman ilmi da cigaban rayuwa ba.
Tayi kudurin in har tana raye, da yardar Ubangiji sai Zakari ya ci arzikin dan uwansa
Bilyaminu a rayuwa. Idan kuma malam Bilyaminu baya raye, ita SAFIYA UWAR HAUWA tana
raye! Aka ce Uwa mafi Uba… koda uban Sarki ne.
**** **** ****
Tafiya suke ba tare da sun san inda suke jefa kafafun su ba, tsabar bacin rai yasa Inna
bata ko gajiya da tafiyar da suke dirka, amma Hauwa tun baa yi nisa ba ta sare, tace “Inna na
gaji”, Inna tace daure Hauwa, bana so makwabtan mu su biyo bayan mu su cimmana, bazan
zame wa kowa nauyi ba, ba kuma zan zauna cin arzikin kowa ba sai na Ubangiji, don haka
bazan zauna a gidan makwabta in hada su fada da iyalin su ba, musamman Malam Isa, kin dai
san halin Mai kosai ba taso a rabe shi.
Hauwa ta daure suka cigaba da tafiya har suka yi wa kofar Nasarawa fintinkau, ita kanta
Inna bata san ina suke jefa kafa ba, kofofin cikin gari kawai take so su bari, sai da garin ya Allah
ya waye rana ta fito, yunwa da gajiya suka sa Hauwa ta ce to Inna dan tsaya in huta ko na minti
biyu ne. Suka tsaya a daidai sakateriyar gwamnati ta Audu Bako, suka zauna suna hutawa. Sai
lokacin Inna ta tuna da kudin da Jamilu ya bata, cikin kunshin kayan ta, saboda yawan kudin ta
san ba cikin hayyacin sa ya bata su ba, domin sun kai naira dubu biyu. Ta saka hannu cikin
bakkon su, ta tabbatar suna nan, sai ta ce, “tashi Kulu mu hau abin hawa zuwa tasha, na tuna akwai kudi cikin kayanmu”.
Kulu ta kwalalo manyan idanun ta waje, ta ce tasha Inna? Kano zamu bari? Kanon Dabon?
Gari ba Kano ba dajin Allah Inna.
Ai ni da kike gani na nan Inna, ban iya zuwa koina in bar mahaifata KANO saboda wani
Kawu Zakari. In muka yi hakan ai ya ci galaba a kan mu kenan, ya raba mu da KANO farin cikin
mu, tushenmu, tsatson mu, cibiyar mu, jihar mu ta gado.
Ni dai Inna ko a karkashin gada ne zan dinga kwana in dai ina cikin kwaryar Kano, ruhina
yana Kano, zuciyata tana mahaifata, in muka bar Kano Baba ya dawo ina zai gan mu? Kuma
makaranta ta fa Inna?
Sai ta fashe da kuka cike da tsoron, halin da karatunta zai shiga. A da kam, bata karaya ba,
amma yanzu ta fara karairayewa, karfin halin ta ya kare, kuzarin jikin ta ya kau, data fara hango
illar da Zakari ke son yiwa rayuwar su tunda muhalli shine rayuwa, ta san yanzu itada karatun
sai wani babban ikon Allah, a lokacin da ya zo gangara tunda basu da matsuguni, bata san me
Zakari ke nufi da su ba sai yanzu,