Showing 39001 words to 39674 words out of 39674 words

Chapter 14 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf

me yake nufi kuwa banda su koma yin bara bisa titi da kwana
a kasan gada? Matattarar duk wani abin cutarwa a matsayin su na mata ba maza ba. Inna ta
rasa yadda zata yi da Kulu, don kukan nata har da gunji da majina ita atafau bata barin Kano
saboda Zakari. Inna ta ce,
“to Kuluwa sai ki gaya min ina zamu je in muka zauna a Kanon, gida dai kina gani akan idon
ki aka rushe shi, takardun gidan na hannun su, don haka ni banida sauran buri a zaman kasar
Kano da cikin BADALOLInta”.
Hauwa-Kulu tace ko kan dutsen Dala da Gwauron dutse ne mu hau mu zauna, ai dai muna
cikin Kano, kuma can babu mai rushewa, sannan idan gari yaw aye zan iya zuwa makaranta
komai nisan dutsen in dawo in tadda ke anan. Inna ta ce cikin takaici, to “huda-huda, mungu

Park uwar yan boko, ana ta makwanci da abinda zaaci ma babu, kina ta zancen wata
makaranta?
Da idon uban wa zaki je makarantar daga kan dutsen Gwauron Dutsen?”
Da ace cikin nutsuwarta ta ke, da kuwa ta tada ballin Inna ta mata gorin ido.
Amma da yake babu nutsuwar ko ta kwabo a tare da ita bata tuna wannan ba, Hauwa tace
da mahaifiyarta Inna.
Inna kada ki manta kin yi ma DAN KI SARHAMU alkawarin duk runtsi ba zaki raba ni da
makaranta ba, kin masa alkawarin cika masa burin sa in kammala sakandire, alkawari abu ne
mai girma Inna, in ban je makaranta ba Inna ba abinda zai raba ni da BARA watarana. a
matsayina na makauniya-miskiniya- musaka!. Ai jin furucin Hauwa haka wanda ya taso ya fito kai tsaye daka kasan zuciyarta da jijiyoyin
wuyanta da suka mimmike. Inna taji kamar Hauwa ta bata vibe, ta zuba mata allurar karfi da
kuzari daga sarewar data fara yi. Sai ta samu kanta da tare abin hawa (ba tare da tunani na
biyu ba) ba kuma da ta san inda zasu nufa ba ta dai yarda bazasu bar Kano ba, zama daram!
Domin ta yarda HAUWA-KULUnta ta fita gaskiya kuma ruhin HAUWA shine GIDANSU NA
BADALA!!!

**** **** ****
MURFIN LITTAFI NA DAYA

Abin tambayar anan shine; shin jarumar cikin BADALA (HAUWA-KULU) zata koma da
rayuwar ta cikin BADALAR KOFAR NAISA inda ruhinta dana iyayenta yake, ko kuwa ta fito
wajen gari kenan tana walagigi???

Shin burin masoyin su na hakika (DR. SARHAM ABBAS SHANONO) zai cika akan
HAUWA-KULU na ta samu koda ilmin sakandire ne ba tareda nakasar ido ta zame mata shinge
(barrier) ba, ganin cewa tun baaje koina ba a bayan tafiyar sa, rayuwa ta juyawa Hauwa da
Innarta upside-down???
Wanene PACE-SETTER din Barr. H. Bilyaminu kuma sai yaushe zai bayyana a rayuwar yar
cikin Badala Hauwa-Kulu???

Shin Hauwa-Kulu zata yi rayuwar aure da tara iyali kamar kowacce mace, ko kuwa nakasar
ido zata zame mata shinge (barrier) ga cikar farin ciki da dan adamtaka, kamar yadda take
zamewa mafi yawan akasarin masu lalurar idanu irin nata???

​ Ina labarin mahifinta Malam Bilyaminu? A mace yake ko a raye???
​ Amsoshin duka wadannan tambayoyin in sha Allahu suna cikin littafin HAUWA-KULU
kashi na biyu.


Daga taku har abada;
Sumayyah Abdulkadir

(Takori).
2/09/2023

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login