Showing 9001 words to 12000 words out of 39674 words

Chapter 4 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf

su. Amma bata yarda ta tafi ba, duk da sun kore ta. sun kuma
tabbatar mata bazasu mika katin nata ba. Sai suka rabu da ita suka koma hirar da ta shafe su,
suka manta da su a wurin. Lokaci lokaci suna kiran sunan marasa lafiya suna shiga ofishin likita
amma basu kara bi ta kan su Hauwa ba, don a wurin su sun gama da babin su. ​ Hirarrakin da suke yi duk a kan matashin likitan su ne, wanda aka kawo musu ya maye
gurbin kwararren tsohon likitan ido wato Dr. Barde Abba, wanda shi kowa ya san kwararre ne.
Inna na ganin hirar tasu a matsayin cin naman abokin aikin su.
Don a cikin hirar tasu ta ji suna fadin.
“Ai tsautsayi ne kadai zai sa mutum ya fada hannun sa, da sunan wai yayi masa aikin fidar
ido, yayi yarinta kwarai da gaske da zama likitan ido, a ganin su baa taba yin yaron likita a
tsangayar ido mai kananan shekaru, kuma mai jarumtar hali da karfin hali kamar sa ba, a dai
tarihin asibitin Murtala bakidaya da suka jima da sani, don sun dade suna aiki anan. Dayar tace ai hatta sauran likitocin duka asibitocin da ke cikin kwaryar birnin Kano a yanzu,
bata jin akwai karamin yaro kamar wannan da kwalin likitanci, bama na MBBS kadai ba, wai har
consultancy ya gama, wanda bai wuce ace masa saurayi dan tashen balaga ba, watakila dai
zuqen karatu aka yi tayi masa, saboda yana da uwa a gindin murhu, tunda Baban sa wato
mahaifin sa Farfesa ne (Prof.) na tsangayar likitancin ido, a jami’ar koyarwa ta Abdullahi
Bayero.
​ Gulma tayi dadi sosai a tsakanin su. Daya daga cikin su kuma ta ce,
aah fah, ku daina Magana akan abinda baku da tabbas, ai an ce baa jamiar Bayero yayi
karatun likitancin nasa ba, a can Jeddah ne, ta kasar Saudi-Arabia.
Wato alumnae ne na Jamiar Sarki Abdulaziz. Can kuma kun san baa dadewa ana karatun
likitanci kamar yadda ake dadewa a nan Kano da sauran garuruwan Arewacin Najeriya, idan
muka auna a hankali, a bisa maauni na adalci, zamu ga cewa in har ya bar sakandire a shekaru
goma sha shidda, ya shiga jamia a shekarar da ya bar sakandire zai iya yin MBBS na tsahon
shekaru biyar acan, ya kuma dora da consultancy shima na shekaru biyar zuwa shidda, zaku ga
cewa babu zuke cikin ilmin sa har kuwa da hidimar kasa”, inji mai dan hankalin cikin su.
Ta kare zancen ta da cewa.
​ Don haka ba abun mamaki bane don ya zama likitan fidar ido a shekaru ashirin da
bakwai zuwa da takwas da haihuwa, in dai har da gaske ya fara karatun da wuri, ya kuma gama
karatun sakandire a shekaru akalla 16-17, kuma dai yana da gatan sa a fannin karatun nan
kowa ya sani”. “Sai shegen iyayi da uban tsayi kamar karan raken takanda, dan sirit da shi kamar ka bushe
shi ya fadi amma sai iyayi, ga dan banzan manyance kamar gyambo a kafa.

Karambanin irin su ya wuce shekarun su, don ko ni nan na tabbata na girme mishi wallahi”.
In ji wadda ta fi sauran rashin ta ido wai ita Nos Saratu. Duk suka sa dariyar maganar tata,
Nos Maria har da kyalkyalawa da sukuyawa da rike ciki, irin ta wadanda dariyar gulma tayiwa
dadi.

Zaka yi mamaki in ka ji cewa kusan duk wannan gulmar tasa da zunden nasa da suke yi,
wato shi sabon likitan nasu, yana sauka ne reras, kuma tiryan-tiryan a cikin kunnen sa kamar an
kunna radio yana sauraren su. Bai san sanda ya ajiye biron hannun sa ba don ya kasa cigaba
da rubutun, ba wai haushi yaji ba don sun aibata halittar sa, aah, kawai abin ya bashi tsoro, cin
naman mutum haka a kan kunnen sa da tsakar rana babu ko shakka, ya fiddo ido warwaje ya
kuma kara sakin kunnuwa yana sauraren su da alajabi da mamaki. Mata sun kware da gulma
ya sani, amma ta wadannan ta bashi mamaki kasancewar su Nosis ne dake karkashin sa.
Shima ya yarda kamar yadda mahaifiyar sa ke yawan fada wato shi “SARHAM” mutum ne
mai karfin JI. Wato jin sa yana da karfi, kamar yadda ganin sa yake da karfi yadda baa zato.
Kusan komai na halittar sa ma mai karfi ne Ubangiji ya yi masa, idanun sa basa bukatar
madubin kara karfin gani (medicated glass) da yawancin likitoci ke amfani da shi. Sarham hatta takun tafiyar sa wato (gait) din sa shima mai karfin gaske ne, gab-gab-gab…
haka zaka ji takunsa in ya dumfaro ko ya durkako inda kake. Kafin ya iso sautin takunsa zai
gaya maka isowar sa. Baban sa kan ce, shi din, wato Sarham, “DAN BAIWA NE KUMA NA
MUSAMMAN A CIKIN DUKA YAYAN SA. Komai nisan zance in dai yana gefe aka yi shi, to kuwa tabbas Sarham zai jiyo shi tsaf.
Wannan wata baiwa ce da Ubangiji ya yi masa da ba kowa yake yiwa ba, wadda a kullum yake
gode masa a kanta, wato baiwar kyakkyawan ji da gamsashshen gani, da suka banbanta dana
sauran mutane da yawa, shiyasa a kullum kunnuwan sa suke zuko masa abinda baa zaci ya ji
ba.
Ga shi dai da gaske siriri din ne shi, kuma dogon mutum a halitta, kamar dai yadda suka
gulmanta, shima ya san hakan, don har wasu na yawan fadin wai yana dieting ne saboda
sirantar sa mai yawa ce a matsayin sa na namiji, amma kuma a zahiri kakkarfa ne ta cikin
kasusuwansa, zaka gane hakan ko daga fadin kirjin sa da kaurin kwanjin sa, wanda ke nuna
duk safiya yana motsa jikin shi da kyau da hanyoyin motsa jiki irin na bature, ko daga kaurin
tsokar damatsan hannun sa.
Kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham ka fahimci yana matukar kula da lafiyar sa kwarai da
gaske, ta hanyar kula da abinda yake ci, da motsa jini (exercise) bada wasa ba a duk safiyar
Ubangiji. Shi yasa yake dan shafal da shi mai dogon hanci.
Sannan tsayin sa bai wuce kima ba kamar yadda Nosis dinsa suka kintata shi a gulmar tasu,
kuma kaurin jikin sa ya wuce ace masa kamar na karan-raken takanda, kai shi bai taba jin wani
ya kushe halittar sa ba banda wadannan magulmatan matan, iyakaci ana cewa yana ‘dieting’
baya cin abinci saboda kwalisa, amma shima ya san shi dogon ne saidai ba kamar karan-rake
kamar yadda yaji suna cin naman sa ba.
Don haka ba tantama in aka yi laakari da kalaman bakinsu, da bayanin da mai dan hankalin
cikin nasu tayi a kan karatun sa, zaa fahimci tabbas sun yi masa farin sani ba kirkirowa suka yi
suka fada ba, har da abinda ya bashi mamaki cikin zunden nasu, wai a Baban sa Farfesa ne na
tsangayar ido, kasancewar bai dade da zuwa Murtala ba, kuma shi dai ya san bai taba abota da

kowa a asibitin nan ba, balle su maaikatan jinya mata wadanda a karkashin sa suke.
Sai yayi dan murmushi kawai wanda ya motsa gefen kuncin sa na dama, ya cigaba da
rubuce-rubucen da yake yi a cikin wani fayal na mara lafiyar da ya kammala dubawa ya fita,
yace a ran sa.

A zauna a kafa tebur saboda kai, ana rage maka zunubi haka ai ka isa ne, wanda bai isa ba
ko kallon sa ba mai tada kai yayi.

Yana cigaba da rubutu yana murmushi cikin mamakin gulma ta rashin aikin yi irin na mata
musamman maaikatan jinya.

Dr. Sarham Abbas Shanono kenan. Siririn wankan tarwadan matashin likitan da bai fi ace a
bana ya gama makarantar sakandire ba, sabida duka-duka bai fi shekaru ashirin da takwas ba.

Hayaniyar Malaman jinyar sa, da ta dattijuwa Innar Hauwa data dage bazata tafi ba sai yar ta
Hauwau ta ga likita, koda kuwa dukan ta zasu yi karewar rashin kunya, tace ban haife ku ba? ta
kuma ce ai asibitin ba nasu bane na gwabnati ne, don haka basu isa ba da zasu hana ta ganin
likita, inji dattijuwar, don sun kure hakurin ta, wannan hayaniyar ta hana shi fuskantar rubutun
ma da yake yi yadda ya kamata. Gashi kuma a kofar ofishin sa ake ta wannan taqaddamar.
Su Nosis din sun dage da rashin mutuncin tunda ta bari sai da ido ya rube zata zo asibiti, to
ta je ta nemi sandar yi wa yar ta jagora zuwa bara. Amma bazata batawa likita lokaci ba, a
lokacin da ba abunda zai iya tabukawa wadannan idanun da hakiya ta gama canyewa murus.
Innar Hauwa har da kukan ta, don taga alamar fada ba zai bi da su ba, tana rokon su da
muryar ban tausayi su bar yar ta ta gan shi kada ta makance, ta yarda ta yi laifi amma a
taimaka musu su ga likita don Allah, ta tuba. Kuskure ne ta riga ta yi. Nan gaba zata kiyaye.
Amma maaikaciyar jinyar nan ko a jikin ta, ta dora kafa daya kan daya akan kujera tana
karkadawa ta hana su shiga ta yi rantsuwa da Jesus din ta, ba zata bari su batawa likita lokaci a
kan idonnan da sun riga sun kashe shi a banza ba.
Me ke faruwa haka? Hayaniyar me kuke yi mata haka? Ke Maria, meye haka kike yi?
Wannan ya dace da maaikacin jinya? Sister Saratu wannan matar bata girme ku ba?”
Dakusassar muryar DR. SARHAM, irin ta mai fama da sabuwar mura, ta karade wurin, yana
maganar yana furzar da dan tari, don sosai yake fama da mura daga jiya zuwa yau da ya dan
sha ruwan sanyi, jikin sa baya son sanyi ko kadan.
Muryar tasa ta dira a kunnen su da sigar tambaya daga inda yake tsaye a jikin kofar ofishin
sa, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun bakar Jacket din sa, yana dan yamutsa fuska cikin
gajiya da alamun jin yunwa, don tun safe yake aikin duba marassa lafiya har zuwa yanzu da
agogo ya buga karfe biyun rana, wato lokacin cin abincin ranar sa kenan da zuwa yin sallahr
azuhur, lokacin tafiyar sa gida yayi kenan. Don haka ya fito ne don tafiya gida.
Yana sanye da bakaken ‘suit’ da ya zanzare kugun sa a cikin su, ya dora bakar jacket a kan
su, wadda ta sauko har zuwa gwiwar sa, ta bada suurar cikakken dan gayun likita kuma dan
kwalisa dashi na wancan zamanin, masu yawan yin zanzaro da belt.
Bafullatanin Shanono mai kakkaifar murya, amma a halin yanzu ta dushe, ta dakushe da
alama yana fama da ‘Catarrh’.

Yanayinsa na Kanawan usli ne, amma yanayin zubin jikin sa na Fulani ne, sabida sirantar sa
da ta zabge masa cika ido kai bazaka ce yayi shekaru ashirin da takwas din da yake da su
bama.
Sister Saratu ta hau raba ido tsakanin Innar Hauwa da Likita Sarham, ta ki cewa komai, don
a dan zamansa da su na dan gajeren lokacin da bai wuce sati biyu ba da aka yi masa transfer
daga asibitin Abdullahi Wase (Nassarawa hospital) zuwa nan wajen su, sun fahimci halinsa na
kirki yayi yawa a kan marassa lafiyan sa, (hes very compassionate and caring to his patients),
shi yasa a halin rashin mutunci irin nasu suke cewa ya fiya iyayi da kidifiri.
Ilai kuwa ya fahimci komai tun ma kafin su bashi amsa, don ya san ba yau suka fara ba,
wulakanta marassa lafiyan da suka rainawa ajawali halin maaikatan su ne, daga zuwan sa
zuwa yanzu ya gama shaidar hakan, kuma yana cikin sahun likitocin da suka san darajar dan
adam, basa yarda da hakan, sai dai in an yi ne a bayan idon su. A fusace ya soma fadin wato Metron Maria, Sister Saratu, Nos Mairo ba zaku daina
wulakanta bayin Allah ba ko? Shin anya kun san aikin ku? Wannan ba shine halin da aka san
maaikacin jinya na hakika da shi ba, hakan cin amanar aiki ne babba, kuma tozarta dan adam
ne. Ina humanity din ku da aka hore ku da shi matsayin ku na maaikatan jinya, dana kiwon
lafiya?
A gaskiya na gaji da halin ku, ko jiya na raba ku fada da patient. Idan baku yi hankali kun yi
aikin da ya kawo ku yadda ya kamata ba wallahi duk sai na yi reporting din ku.
Ya dubi Innar Hauwa data sunkuyar da kai kasa tana tsane ido, yace.
Baiwar Allah me ya faru? Waye babu lafiyan?
Innar Hauwa ta ji dan kwarin guiwa ya shige ta, saboda a cikin muryar sa mai dushewa da
rashin karsashi saboda mura, akwai (caring) wato kulawa da darajja dan Adam, ta rausayar da
kai gefe ta ce,
dama yarinya ce na kawo tana ciwon ido, to sun ce ban zo da wuri bane shiyasa bazan ga
likita ba, shine dalilin da nake ta basu hakuri”.
Tausayin matar ya kama shi, ya dubi yarinyar da take rike da hannun ta, yadda hakiya ta
cinye rabin idon sai da tsigar jikin sa ta tashi, zuciyar sa ta tashi, ga kwantsa babu kyawun gani,
da sauri ya dauke idon sa daga kallon yarinyar, ga kafafun su futu-futu da kura tabbacin sun sha
tafiyar kasa mai nisa kafin su iso asibiti, sai ya karbi katin su daga hannun maaikaciyar jinyar da
katin ke hannun ta wato Nos Maria, ya kuma yiwa Inna umarnin su biyo shi a baya zuwa cikin
ofis din.
Sai lokacin Inna ta gane shine likitan da ake musu rowar gani.
“Iya yaya aka yi aka bar idon yaci hakiya sosai har haka?
Dr. Sarham ya tambayi Innar Hauwa, yana haska cikin idanun Hauwa da yar tocilan din sa
mai tsananin haske, yana magana cikin tsantsar damuwar da ta kasa boyuwa a muryar sa,
yana cigaba da haska cikin idanun bayan ya gwale su sosai, Inna bata iya ta ce komai ba
amma guilt ya bayyana akan dattijiyar fuskar ta ainun. Dr. Sarham ya gama duba idon Hauwa da tocilan din sa, ya kuma gama nazarin sa gabadaya
duk cikin dan lokaci, sai ya koma ya zauna a bakar kujerar sa mai juyawa, itama yace ta zauna
a kan kujerar zaman maras lafiya da ke fuskantar sa, ya bude mata fayil a take don ya gama
gano Hauwa na bukatar aikin ido na gaggawa kawai, don a cire hakiyar. Ya sunkuyar da kai

yana rubuce-rubuce a cikin fayil din ta, kafin ya gama ya dago ya dubi Inna.
A hankali kuma cikin tsanaki, Dr. Sarham Abbas Shanono, ya shiga yiwa Innar Hauwa
bayanin amfanin zuwa asibiti da wuri, da zarar an ga alamun ciwo, ba sai ciwo ya ci ya cinye
ba, cikin tausasawa da lallashi da fasahar harshe irin nasa yake mata magana, ya gaya mata
yanzu ba abinda zaa iya yiwa Hauwa a ceci idanun ta illa cataract surgery watau (fida don cire
hakiya) ta gaggawa.
Likitan ya saka musu ranar aiki jibi-jibin nan, ya kuma fada musu kudin aikin. Duk da Innar
Hauwa ta tsorata da yawan kudaden bata nuna ba ko a fuska. Duk da ta san kuwa bata da su a
ajiye.
Da suka koma gida Inna ta shiga cikin matsananciyar damuwa, na farko bata da kudin da
likita ya bukata a yanzu, ko jarin wake da shinkafar ta ba zai yi kwatan su ba, abu na biyu tana
ganin bazata iya bari a farkawa Hauwan ta ido ba haka kawai. A je garin neman gira a rasa ido.
Ko a jangwalo wani abun da yafi karfin su. Amma Hauwa ta dagewa Inna ita dai tana so ayi mata aikin nan. Inna ta gaya mata abinda
take tsoro da kuma rashin kudin aikin a hannu, nan Hauwa ta dinga magiya har da kuka, tana
rokon Inna ta amince in yaso ko dan taure daya ne cikin dabbobin ta a sayar a biya. Komai ya
faru daga Allah ne. Haka kan dole Inna ta amince da shawarar ta, don bata son kukan Hauwa ko bacin ranta. Ta
fidda Akuya budurwa aka sayarwa mahauci. Washegari, wato ranar da aka basu, da sassafe
suka koma asibitin Murtala.
​ Likita da abokan shiga tiyatar sa suka gama shirin yi wa Hauwa aiki, aka nemi Inna da ta
saka hannu, Inna ta saka hannu amma da ganin ta zaka fahimci a matukar firgice take, gani
take kamar aka shiga da Hauwa tiyatar nan bazata fito a raye ba, Inna ta soma hawaye tana
sharewa da habar zanin ta, tana kankame da hannayen Hauwa. Ganin haka Dr. Sarham ya shiga yi wa Innar Hauwa maganganu na kwantar da rai yana
cewa kada ki damu Innar mu, lafiya zan maido miki ita, da iznin Ubangiji, da kiyayewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login