Showing 21001 words to 24000 words out of 39674 words
Chapter 8 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf
gaishe da Inna,ya kuma tambayi jikin Hauwa. Inna
ta ce cikin damuwa,
ai tun bayan tafiyar ka jiya zazzabi ya rufe Kuluwa, ko tashi bata iya yi, sallah ma sai na
taimaka mata take iya yi daga zaune, ta dauki damuwar duniya ta dorawa kanta a banza akan
abinda Allah ya kaddara mata. Dr. Sarham ya ce,
ashsha! Kakata jiki bai yi dadi ba ashe, ki barta Inna, dole ne ta damu, amma a hankali
damuwar zata bi jikin ta in sha Allah, bari to in koma in samo mata magani.
Har ya mike zai saka takalmin sa sai ya dubi Hauwa dake zaune a kan tabarma daga gefe, ta
jingina da filo, ga idanuwan tarr a bude kal dasu, amma shi a iya dan ilmin likitancin ido da Allah
ya bashi, da abinda ya karanta, ya san wadannan idanun na Hauwa’u in ba wani babban
kudurar Allah ba sun tafi kenan, wato sun tashi aiki sai ko wani ikon Allah, wanda ya fi gaban
ilminsu su likitocin fidar idon.
Ya matsa gaban tabarmar ya russuna yace sannu Kakus, ina yake miki ciwo? Don in san irin
maganin da zan karbo? Ko allura kike so?” Hauwa ta bata rai sosai saboda sunan da ya kira ta
da shi kamar wata tsohuwa, haka mafa a asibiti yace mata Kululu bata ce masa don me ba,
yanzu kuma yace mata kuskus, ta dan fiddo manyan idanun kamar tana ganin sa irin warning
look dinnan, ta yi fuska sosai ta ce masa, sunana Hauwau Bilyaminu ba kuskus sunana ba,
kuma ni ai bana tsoron allura inda a hannu za’a yimin, ba sai na kwaye zani ba”, Inna ta ce an
ce miki Kuskus din, ke da baki san wasa ba. Yayi murmushi ya sake cewa.
Kakus, idan na ce miki sunan Kakata gare ki, wadda ta haifi mahaifina zaki yarda? I mean
you have my Grandmas name, Hajiya Kulu Shanono”.
Anan kuma sai tayi shiru, don ta san ba karya yake ba, ba kuma zolaya a maganar sa ta
yanzu, ta zuba masa gululun idanunta kawai kamar tana ganin sa, yace to sunan ki daya da
Kakata Hajiya Kulu (Hajiyar Gadon kaya), ni kuma Kakus nake kiran ta, idan ban kira ki Kakata
ba bazan iya cewa Hauwa ba, don in ta ji na fadi sunan ta haka gatsau, ba sakayawa, sai tayi
kuli-kulin kubra da ni.
Hauwa bata san sanda ta yi dan murmushi ba, sabida yadda Sarham ya fadi kuli-kulin
kuburar ya bata dariya matuka.
Ya ce daga yau ni da kaina zan saka miki sunan da ya dace da kyakkyawar diyar Inna kamar
ki, kin ga daga Hauwa, har Hauwau, har Kulu, zuwa Kuluwa duk na tsofaffi ne Inna ta lika miki,
don haka ki lamunce min daga yau in kira ki da MAIJIDDAH!.
Ai kuwa nan da nan Hauwa ta washe baki, fararen hakoranta suka bayyana, batun yau take
so a kirata da Maijidda ba amma ba mai kiranta da hakan. Dr. Sarham ya ce, amma bisa
yarjejeniyar banni arawa kowa sunan nan, nawa ne nikadai, ni na saka miki, don haka nikadai
zan kira ki da shi, ke ko wani kika ji ya kira ki da shi ki gaya masa ba nasa bane nawa ne, ban
yarda ko Inna ta kwaikwayar mun ba.
Inna tayi dariya tana cin goro ta ji Sarham ya kara burgeta, ko ba komai yau ya saka Hauwa
murmushi don ta manta rabon Hauwa’u da murmushi (ear to ear) irin haka, watakila tun kafin ta
fara ciwon idon yayi na apolo.
Yadda Sarham yayi ta yi musu hira sai da zazzabin Hauwa ya sauka a take, ba tare da
sun san lokacin da ya sauka ba, ko dama damuwa ce ta sanya a ranta ta hanata sukuni har ta
saukar mata da zafin jiki, amma duk da haka Sarham bai kyale ta ba saida ya fita chemist din
Lamco ya samo mata magunguna da first aid kala-kala ya dawo, har da gorar locozade da
daurin gasassar kaza da biredi. Ga kayan shayi ya sayo musu makil, tun daga kan sukari, milo
da madara har da lipton.
Lokacin da ya dawo ya tsugunna gaban Inna yana nuna mata komai kasa magana ta yi ta ce
dan nan ya da wahala haka? Ya murmusa yace kada ki damu Inna, na neman albarka ne.
Inna ko ta shiga shi masa albarka kwando kwando sannan shi da kan sa ya dau
kunshin naman ya isa gaban Hauwa, ya bude ya tura mata gabanta, kamshin kazar nan wadda
taji kayan kamshi na gargajiya har cikin kwakwalwar Hauwa wadda rabon ta da abinci dama tun
kokon safe da ta dan kurba, don ta rasa ‘appetite’ dinta gabadaya, yace kanwata ci nama ko
zazzabi ya idasa tafiya sosai yana ganin yadda ta hadiye miyau, mukut, a makoshin ta, amma
don karfin hali da ki-fadi irin na Hauwa sai tayi fuska, ta ce ita ta koshi, sai ya ce “to in ni ne baki
so in ga lomar ki, bari in tafi, Inna zan wuce gida sai an kwana biyu, kin san na zama dan ki
yanzu, zuwa gidan mu sai kin gaji kin kore ni.
Inna tace wane mutum ya kori mai kaunar sa, likita Allah ya jikan mahaifan ka, idan suna
raye kuma Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana mai albarka.
Wannan addua tafi komai dadi da ga Sarham, da sauri Dr. Sarham yake amsawa da
Amin-amin ya rabbi Inna, Abba da Mama duk suna lafiya, cikin koshin lafiya. Allah ya karawa
kanwata Maijidda lafiya, da Yakanar karbar kaddarar ta.
Tun daga wannan ranar gidan su Hauwa ya zama wajen zuwan Dr. Sarham hira, wato tsakar
ginan Inna ma tsafta da wadatar iska ya zama dakalin hirar sa, kusan kullum ya taso aiki sai ya
je, su yi hira su yi dariya shi da Inna, hirar duniya iri-iri haka suke yini yin ta suna nishadantuwa
da daukewa kai damuwar duniya. Inna tayi girkin ta mai dadi ta zubo masa, tuwo ne, dambu ne
ko danwake ko dafadukan alkama da ire-iren su, ko gudun kurna da miyar taushe, sai ka ga Dr.
Sarham ya mike kafa a kofar dakin Inna ya nade hannun riga ko yayi loosing tie din suit din jikin
sa yana kwasar girkin Inna na gargajiya irin wanda baya ci sam a gidan su koda sadaka zaa
hadashi, musamman da ya fahimci irin tsaftar Inna, har yan gidan su saida suka gane ya daina
cin abincin ranar sa yanzu a dining. Ballde ya zana ya ci abinci tare dasu. In sun yi magana ya
ce ya ci wajen wata Innarsa ne. Ga Inna da jin radio komai ta ji a radio sai ta kwashe ta gayawa
likita Sarham, shikuma da yake ba maabocin sauraron radion bane sosai yake jin dadin labaran
duniya daga radio mai jini wato Inna, sam Hauwa bata iya saka musu baki don ta fahimci daga
Innar har Sarham maganannu ne na karshe (talkatives), ita kuma Allah bai halicce ta da yawan
magana ba, ciwon kai take saka ta, don haka sau tari haushi sosai suke bata.
A wani hutun karshen mako wato ranar wata lahadi Sarham ya zo gidan, Hauwa na
duke gindin famfo wai wankin kayanta take yi, ba yadda Inna bata yi da ita ba kan ta bar su zata
saka Salele ya wanke mata in ya shigo, Hauwa ta ki, wai wankin Salele baya fita, Inna ta ce
cikin subul da baka, “da wanne idon zaki ga wankin har ki san ya fita ko bai fita ba?
Ai kuwa Hauwa ta fashe da kuka sosai, wai Inna ta yi mata gorin ido. Ta tattara kayan
wankinta ta yi bakin famfo tana ta dirzar su kamar Allah ya aiko ta tana kuka wurjanjan. A haka
Dr. Sarham yayi sallama a gidan.
Inna ta amsa daga dakin ta, ya shigo har dakin nata don yanzu ba bakon sa bane,
dardumar Sallahr ta ta shimfida masa tace Lale Maraba da Da na Sarhamu yayi dariya yana
kokarin zama ya ce Inna kema sunan bakin Abban mu zaki koyi lika min, don a ce ni din wani
tsoho ne ko? Bayan ko talatin ban rufa ba, ina cikin twentieth dina? Inna ta ce kai da Kuluwa
ban san waya fi wani son yarinta da gudun tsufa ba, ita ta hana a kira ta Kulu, kai ma kace
Sarhamu tsoho ne, bayan ainahin sunayen kenan kuke bata maanar su da zamananci. Sarham
yace by calling Hauwau da Maijiddah, ai baa bata maanar sunan ba Inna, tunda inkiyarta ce ta
hakika. Inna ta ce “hakane kuma, duk inda Hauwa take, Jidda ce.
Sai ya dubi inda Hauwa ke wanki bata kula shi ba yau, duk da dama ba wai kula shi ta ke
sosai idan ya zo ba, amma akalla ta kan ce masa sannu da zuwa, tacigaba da sabgar gabanta
ta manta dasu, ta hanyar kame bakin ta, amma yau kam ko uffan bata ce masa ba, bata kuma
kai hankalin ta kan su ba, sai wanki take dirka lokaci zuwa lokaci ta na tsane ido da habar zanin
ta.
Inna me ya samu autar ki haka? Wa ya taba miki Maijiddah? Kamar kuka haikan naga
tana yi? Inna tace “ai tana jin ka, tambaye ta mana. Waka a bakin mai ita tafi dadi.
Wai daga cewa ta bar wakinnan Salele yayi mata, shikenan ta maida abun tashin hankali.
Sarham ya ji wani iri, ganin kukan Hauwa’u ya karu da maganar da Inna tayi, kamar ta kara
kunna ta, amma duk da haka bata fasa wankin da take faman yi ba kamar na dole, har da kara
karfin sheshshekar kukan ta, Sarham ya mike daga kan dardumar da yake zaune ya matsa har
inda Hauwa take wankin a gindin famfo ya russunna a gaban ta yace. Maijidda yaya haka zaki tadawa Inna hankali? Kinsan bata son kukan ki.
Hauwa tayi sharbe, hannu a bayan ido, ta ce bayan gorin ido tayi min?!
Gorin ido kamar yaya?
Ta fashe da kuka ta ce cewa fa tayi wai da wanne ido zan san kaya na sun fita ko basu fita
ba, menene wannan in ba gorin ido ba?
Sarham yayi kokarin danne dariyar sa ya ce easy Maijidda, ko kowa zai miki gorin ido, ai
banda Inna. Ke dai kin fassara maganar ta ba daidai ba sabida dama akan tsini kike, amma ba
haka Inna take nufi ba, kin ji?
Ta gyada kai tana share hawaye. Ya ce to tashi ki bar wankin haka, in ya zo sai ya
karasa ai har na gama dauraya nake yi, sai shanya. Yace to dinga daurayewa kina bani ina
shanya miki Hauwa ta zaro ido ta ce. Lah! Likita da kai, zan saka ka shanya ka jika jikin ka?
Sarham ya ce likita bazai taimaki kanwar sa ba? Shi dama ai mai taimakon alumma ne tun
asalin sa da haka ta yarda, ta ke dauraye su daya bayan daya tana miko masa, yana karba
yana shanyawa akan igiyar shanyar su, nan da nan suka gama.
Dr. Sarham ya ce da Inna zai tafi gida, ba zai jima ba yau, dama ya leko ne kawai ya gansu
ya wuce saboda Mama ta aike shi Dakata. Suka yi sallama shi da Inna.
Har ya kai bakin kofa ya tuna abinda ya kawo shi yau, kukan Hauwa yasa ya manta, sai ya
dawo ya ce “Inna kiyi wa Maijidda shirin tafiya makaranta gobe, amma ba tata ta da zata koma
ba.
Na nema mata makaranta wadda tayi daidai da masu irin lalurar ta (special school), yadda
zaa yi ta dinga zuwa tana dawowa kullum shine ban sani ba, inata tunani a kai har yanzu.
Inna taji idon ta har kwalla ta taru, wato shi Da nagari wanda ya samu tarbiyyar iyayen kwarai
daban yake, ba sai wanda ka haifa ne kawai zai iya zame maka Da ba, da gaske akwai yayan
mutane yan albarka fal a duniya wadanda baku hada kowacce irin alaqa ta jini ba, don dama
damuwar ta kenan tun bayan makancewar Hauwa cewa itada karatun sakandire yaya zasu
karke?
Gashi tun ba’aje koina ba likita Sarhamu yayi musu maganin wannnan damuwar. Ya
share musu wannan hawayen. Me zata yiwa wannan bawan Allah banda duk sallahr farillar ta
ta roka masa rahmar Ubangiji da gafara ga iyayen sa ba don sun mutu ba? da gamawa dasu
lafiya. Godiya sosai Inna tayi masa, ta shi masa albarka iyaka, sannan tace kai ta da daukota
wannan ba damuwa bane Salele zata yiwa magana ya dinga kaita kullum yana zuwa ya dawo
da ita in sun tashi”. Sarham ya ce shi kuma ya saka masa albashin hakan, don kada yau da
gobe ya gaji.
A yammacin ranar Sarham ya kawowa Hauwa uniform na Special School ta Kano, littafai,
jakar makaranta da takalmi sau ciki da socks. Ita da kanta Hauwa saida ta rasa ta inda zata
godewa Dr. Sarham.
Mafarin fara karatun Hauwa Bilyaminu a special school kenan, tare da sauran yaran
Kano da zagayen ta masu visual impairment’ (lalurar gani.) Dr. Sarham yayiwa Hauwa
photochromic glass baki saboda ta dinga sakaya kwayar idanunta cikin hasken rana kada (sun
exposure) yayi ma kwayar idon ta lahani wadanda kyawun su mai matukar ban mamaki ne,
kamar bayan makancewar tasu an kara musu wani (added beauty) a cikin su, da haske mai
daukar idon duk mai kallon ta.
Washegari litinin tun kafin ya tafi asibiti ya zo gidan don kai Hauwa makaranta da kansa, ya
kuma ce da Inna da Salele duk su tafi tare don su ga makarantar ya kuma gabatar da su ga
malaman makarantar. Hakan kuwa a ka yi.
**** **** ****
Hauwa-Kulu ta soma zuwa makaranta kullum tare da Saleleh da yake yi mata jagora, in
lokacin tashi yayi ya je ya taho da ita. Hauwa ta soma karatu tare da sauran yara irin ta ta
hanyar ‘Braille reading and writing’. Wanda ake koya musu tun a mataki na farko a matsayin
hanyar rubutu da karatun su. Hauwa’u an zama daliba, karatun data ke yi kullum ya dauke mata damuwar rashin idon
ta manta da komai, kafin shekara ta zagayo a yi canjin aji na gaba Hauwa tayi na daya har sau
uku a kowane zango, ta iya rubutu da braille sosai ta kuma iya karatu da braille din tiryan-tiryan.
Sabida har a gida karatun take yi bata hutawa yasa Inna ta dauke mata tayata da ayyukan gida,
ko tayi kokarin karba don ta taya ta Inna cewa take koma daki kiyi karatu kin ji Kulu na yafe
miki, ba nakasashshe sai kasahshe, nakasa ba kasawa ba, kiyi ta karatu da nakasa domin
kubuta daga bara da tozarta, aikin gida ba naki bane. Nawa ne, nida Allah ya baiwa lafiya.
Sarham ba sosai yake zuwa gidan su Inna yanzu ba, saboda yanayin ayyukan nasa sun
koma safe da yamma. Don haka sai karshen mako yake samun leko su Inna ya ji lafiyar su, ya
kawo musu sayayyar da yakan yi musu ta kayan masarufi idan ya dauki albashin sa, yana
matukar farin ciki da cigaban Hauwa ta fuskar karatu, da kokarin da take yi a ajin su kullum.
Don yakan je wajen malamanta ba tare da su Inna sun sani bama, don bincikar progress din ta,
ana kuma tabbatar masa da irin kokarin Hauwa bana wasa bane, gifted ce.
Don hatta lissafi (mathematics) da yake baiwa makafi wahala a braille ita Hauwa tsaf take
ganewa abinta.
A karshen shekarar har kyauta aka bata wato ranar hutun karshen shekara prize giving day
kasancewar a shekarar gabadaya ita ke daukar na daya, kuma tafi kowa zuwa makaranta akan
lokaci da kasancewa cikin tsaftar jiki data kayan makaranta.
Hakan yasa Sarham da kan sa kawowa Hauwa tasa kyautar ta musamman don kara mata
karfin gwiwa inda ya dauki Sumayya a motar sa suka je Levintis suka yo mata sayayyar kayan
kamun azumi rankatakaf. Kayan dadi na kwali dana gongoni iri-iri.
Wannan ne karon Sumayyah na farko da zuwa gidan su Hauwa, tunda jimawa Bhaiyan ta
Sarham ke bata labarin su, amma bai taba yarda ta biyo shi ba sai yau, yau din ma don ta taya
shi sayayya ne don ta iya provision na kayan kwalama, ta kuma taya shi da daukar kayan zuwa
cikin lungun.
Suka yi sallama Hauwa na gindin famfo tana alwalah Inna na daga kitchen, Inna ta
amsa musu don ta dau muryar Sarham tun daga madafi, amma Hauwa a cikin cikinta ta amsa,
zaka ga dai yadda bakin ta ya motsa alamar ta amsa, Sumayya ta tsaya daga nesa ta saka ma
Hauwa ido don jikin ta ya gama bata itace Maijiddan, Hauwa Kulun Badalar kofar Naisa da
Yayanta yake yawan bata labari kullum, wadda yake cewa ya makantar daga kuskuren aikin
ido. A kunnen sa yaji Sumayyah ta rada masa cewa.
Tabarakallah-masha Allah, Subhanallah Ahsanal Khaliqeen da wadannan idanuwa na
Hauwau. Bhaiya, ashe dai Hauwa-Jidda beauty ce, irin