Showing 3001 words to 6000 words out of 39674 words

Chapter 2 - HAUWA KULU Yar Cikin Badala Part 1 BY TAKORI.pdf

shan surfe da dakau da tukin tuwo, sakamakon hakan kasusuwansu
suka yi karfi sosai, gashi bata wasa da shan magungunan gargajiya masu kara koshin lafiya da
cire kananan cututtuka irin su shawara (jante) dasu basir.
Girman tsakar gidan zai isa a gina wani dakin guda, ba tare da daya ya gogi sauran dakunan
ba, amma mahaifina wato Malam Bilyaminu ya barwa iyalin sa filin su yi amfani da shi don
hidimar gida ta yau da kullum da hutawar su, don ya fahimci yadda rayuwar mu tafi bada karfi a
zaman tsakar gidan. Kowa ya san yadda babu wanda ya kai mutanen dake cikin gari da badalolin nan na jihar
Kano jin dadin alfarmar dake tattare cikin zaman kwaryar birnin Kano, da kuma jin dadin
rayuwar birni gabadayanta. Mutanen cikin Badala, na da rayuwa ta tsaro ga junan su, da hadin
kai, da taimakekeniya a tsakani, don suna kaunar juna ne kamar jini guda suka fito, ga kula da
hakkin makwabtaka.
A irin wadannan unguwannin na cikin Kano, a tsakanin 1970s, 1980s da 1990s zaki samu
akwai saukin rayuwa na ban mamaki, misali arhar kayan masarufi dana abinci, makwabci baya
iya cin abinci shi kadai a gidan sa ba tare da ya zuba an kaiwa makwabcin sa ba, ko ya fito da
shi majalisa ayi ciyayya don inganta hakkin makwabtaka da zaman tare, da karfafa taimakon
juna da zumuncin Allah.
To a unguwarmu ma, wato Kofar Naisa, irin rayuwar da su Babanmu ke yi kenan kullum, shi
da makwabcinsa Malam Isa, kullum bayan sallahr ishaI kowa zai fito da abincin gidan sa su
shimfida katuwar tabarmar kaba a kofar gidan Malam Bilyaminu, su sallaci magriba da isha tare,
sannan su zauna zaman cin abincin a kwano guda, da hannayen su dana kawo musu ruwa
suka wanke.
Akwai wadatar shaguna na kayan masarufi da abubuwan bukatar yau da kullum a kowanne
lungu da kowanne kwana na unguwannin Badala, babu abinda baa sayarwa.
Iyaye na dorawa yaran su talla ba tare da fargabar wani abu ba, akwai abincin sayarwa iri-iri
kuma mai arha mai tsabta da a ke yi a gidaje, ga rijiyoyin burtsatse a koina da rijiyoyin amfani a
cikin gidaje, don haka babu batun wahalar ruwa a lokacin, kai duk iya talaucin ka zaka rayu ne
cikin jin dadi ba tare da ka sayi ruwan amfani ba a unguwannin cikin Badala.

A hakikanin gaskiya sai kana zaune a irin gidajen nan namu dake cikin Kofofi da Badalolin
Kano, shine kadai kake samun duka wadannan alfarmomin masu tarin yawa, kuma shine zai sa
a kira ka da cikakken Ba-Kano, ko ka kira kanka da Bakano, ba dan wajen gari ba ko bakon
haure a Kano. **** **** ****

KANAWAN DABO

A
lummar Kano su akewa kirari da laqabi da KANAWAN DABO. Ni Hauwa-Kulu ina alfahari da
kasancewata (yar asalin cikin BADALAr Kano), don haka ne na dauko muku labari na tun daga
tushe, wato na fara da baku shimfidar labarina daga inda na taso, kuma inda aka haifeni, wato
cikin kwaryar BADALA. Garin Kano gari ne da ake ma kirari da Ta-Dabo Tumbin Giwa (Yaro ko da me ka zo an fi ka).
Mun samo wannan lakabin ne daga masarautar Kano (Dabon Kano) ta Sarki Abdullahi
Bayero, Kano garin Sarki Ado, Kano mai Mata mai Mota, mai Ganuwoyi da Badaloli da wasu
irin kofofi wuri-wuri lungu-lungu na tarihi, suna nan birjik bila adadin zagaye damu.
A takaice tarihin birnin Kano tarihi ne mai dogon zango kuma mai zaman kansa, wanda in
aka ce zaa bada shi saidai a dauko shi tun daga tushe, wato tun daga lokacin zuwan Habe, har
zuwa shigowar Turawan mulkin mallaka, da rayuwar Mai-Tatsine a Kano, data sarakunan Kano
da suka gabata. Don haka ba zai takaitu a shafi guda na gabatarwar/shimfidar littafi ba, sai dai I can boldly
say; Kano ta zarta kowacce jiha a arewa kyakkyawan tarihi na sarauta, da ilmin addini dana
boko da rike kasuwanci da muhimmanci.
Abinda kowa ya sani ne Ba-kanon mutum bai yarda da zaman banza ko zaman kashe wando
ba. Haka kuma bai yarda da zama cikin jahilci ba komai yawan shekarunsa; wato dai Gemu
baya hana Ba-Kano neman ilmi.
Saboda zaka ga daga yara har manya a Kano kowa dalibi ne, matan aure ma a wancan
zamanin duka da suna dakin miji dalibai ne a gidan auren su, da zarar an yi sallahr isha, zaka
ga suna firfitowa daga gidajen su cikin lullubi da shigar mutunci don tafiya makarantar dare ta
matan aure, haka da safe akwai masu halartar makarantun manya (adult education schools) irin
su Gidan Galadima, ko makarantar Gidan Makama, don haka akasari a Kano maza da mata
bakidaya kusan kowa yana da abin yinsa daga neman ilmi zuwa sanaar da ta karbe shi, ko
kuma wadda ya gada daga iyayensa.
Zauna gari banza ga Bakanon mutum mace ko namiji sai mu ce sai dai abinda bazaa rasa
ba, don hatta maaikatan gwamnati baka raba su da kodago a kasuwar kantin Kwari, ko Bata
(Sabon gari), ko kofar Wambai, kasuwar Singa, ko kasuwar Kurmi, manyan kasuwannin birnin
Kano kenan. Mafi yawan jamaar Kanon kuma da kasuwancin kacokam suka dogara, basu damu da aikin
gwamnati ba, koda sun dan yi karatun zamani kuwa, balle wadanda basu samu yin mai zurfi ba,
kamar mahaifina, wanda akafi sani da suna “Malam Bilyaminu dan Kofar Naisa”.
Sanaar Babana Malam Bilyaminu itace sayar da kayan yara na gwanjo a kasuwar kofar
Wambai. Da wannan sanaa muke rayuwa kuma da ita ya dogara, sannan kuma ta rufa masa

asiri ya rike iyalin sa daidai gwargwado da kulawa irin ta Bakanon mutum, mai zucciyar kula da
iyali, wato Mallam mutum ne har mutum wanda ya san ciwon iyalinsa.
Malam Bilyamin ya taba yin sakandire ya kuma yi aikin masinja a wata maaikata daga baya
ya bari ya kama kasuwar gwanjo sadidan.
Duk wanda ya san Malam Bilyaminu, (kafin a neme shi a rasa rana daya), ya san cewa
mutum ne da ya dogara da sanaar sa ta gwanjo, ya kuma bata muhimmanci sosai, sannan
kuma shi din mai kula da iyali ne fiyeda kima da duk abinda Allah ya hore masa a lokacin da
yake tare damu, bai yarda ya tara komai ba, in dai iyalin sa bazasu nemi komai su rasa ba. Kafin ni Hauwa, Innarmu Safiya da Babanmu Malam Bilyaminu sun haifi Yayana Zulkifilu,
wanda ya jima da rasuwa tun yana saurayi dan shekaru sha biyar da haihuwa, ya rasu ne a
sanadin wankan cikin rafi (wankan kogi) na samari irinsa marassa ji da fitina, sai ni kanwar sa
Hauwau, Hauwa – Kulu, ko kuma ace Kuluwa” duk babu wanda bana amsawa sai Kuluwa. Mahaifiyar mu wato Inna ita kadai take kirana “Hauwa” ko ta ce Kulu”. In kuma ta bushi iska
ko in ta so ganin zumburo bakina, sai ta ce Kuluwa din.
Malam Bilyaminu Ya kasance mutum mai kyakkyawar muamala da makwabta da abokan
sanaarsa a kasuwa, kai dama duk wadanda suka zauna tare da shi a unguwar Kofar Naisa da
Wambai sun yi masa kyakkyawar shaida.
Shiyasa alamarin bacewarsa rana daya ya girgiza duk wanda ya san shi.
Ni kadai ce yar sa a raye a duniya yanzu, a yayan da ya Haifa wajen guda biyar, wasu sun
mutu a ciki, wato wasu an haifesu stillbirth, daga kaina kuma ni Hauwa-Kulu, ko batan wata
Innata bata sake yi ba, ni nasan Inna tana matukar so na, watakila don ni kenan guda da Allah
ya bar mata. Tun daga wata fitar Babana kasuwa bai dawo gida ba, babu inda Inna bata je neman sa ba,
haka ba inda bata turani ba data san yana zuwa. Har gidan kanin sa Zakari ta je neman sa, duk
da ta san ba wajen zuwan sa bane, masu iya magana suka ce “in abinka ya bata, duba har inda
baka tsammanin shigar sa”. Wannan ne dalilin ta na zuwa Dan agundi gidan Baba Zakari cigiyar mijin ta Malam
Bilyaminu.
Baba Zakari da ya fito sai ya gyara tsayuwar sa a kofar gidan sa yana gyatsa, sannan ya
dubi Innar Hauwa da wani kallo a tsiyace, irin na kashi wannan ya fi ku daraja a ido na, yace
cikin gatse,
“Halan kin yi batan kai ne? To yana inda kika bani ajiyar sa a kuryar daki na ko, in banda
neman jidali yaushe rabo na da matsiyacin mijin ki da bai san hakkin zumunci ba, yo banda
neman magana irin naku na mata me zai zo yayi min? Ko ya gaya miki akwai wata sauran
kadara tsakanina da shi ne bayan ta yan ubancin da ke tsakaninmu? Don haka sawun ta a likkafa ta bar kofar gidan Zakari. Bayan ya caccaba mata bakaken
maganganun da gobe koda sadaka aka hadata bazata yarda ta sake tako kafafun ta kofar gidan
sa ba.
Tun ana maganar batan nasa kadan-kadan, har Innar Hauwa ta tabbatar mijin ta wani abu
mara dadi da bazata ce ko meye ba watakila ya same shi, ko daga irin muggan mafarkan data
ke yi a kan sa, ko dai ya bata, ko ya mutu a wani wuri inda baa san shi ba, don bai taba kwana
a wani waje tun sanin ta da shi da ba a gidan sa cikin iyalin sa ba. Batan mahaifina ya faru ne tun ina yar shekaru goma, wannan alamari ya sanya mu cikin

wani hali na damuwa da dimuwa mai tsanani, wanda ya kusa haukata Innar Hauwa,
kasancewar mahaifiyata wato Innar Hauwa, irin matan nan ne da miji ya gatanta ta hanyar
dauke musu nauyin komai na rayuwar yau da gobe, don haka bata sanaar komai sai kiwon
dabbobin ta, duk abinda zasu ci shi yake kawowa, hatta omon wanki da sabulun wanka Malam
Bilyaminu ya daukewa iyalin sa.
Don haka batan sa ran daya ya daga hankalin ta dana duk wani mai kaunar mu kamar
Malam Isa, kada tilon yar sa wato ni Hauwa in ji labari, domin na saba da shi kusan har fiye da
yadda na saba da Inna don shi kam Baba ba kwaba ne ba hantara ba kamar Innata ba.
Daga baya da watanni suka mika baa gan shi ba, kuma babu labarin sa, sai aka tattaro duka
kayan sayarwarsa na gwanjo da ke rumfar da yake ajiyewa a kasuwa aka kawo mana gida.
Daga wannan lokacin rayuwa ta sauya mana nida Innata, takalihun rayuwata ni Hauwa ya
koma kan Innata kacokam, kasancewar bamu da tabbacin Malam na raye ko mutuwa yayi ya fi
komai daga mana hankula, sannan a wancan lokacin baa satar mutane balle a yi tunanin ko an
yi garkuwa da shi ne mu jira kira. Daga baya daga ni har Innar Hauwa muka ga babu mafita banda addua agare shi, sai Inna ta
maida komai ga Allah ta kuma saka nima na koma yi masa addua kan Allah yasa a koina yake
ya fada a hannu nagari, hannun da ba zai taba cutar dashi ba.
A duk sallahr farillar Inna tana rokon Allah idan Baban Hauwa yana raye, Allah ya bayyana
mana shi cikin koshin lafiya, idan mutuwa ya yi, Allah ya bayyanar da hakan a gare mu hankalin
mu ya kwanta, ta maida hankalin ta kacokam! Kan kula da rayuwar tilon yar ta wato ni
(Hauwa-Kulu). Ganin cewa yanzu bamu da mai taimaka mana ta fuskar ciyarwa sai Allah sai makwabta da
muka saba ciyar da junan mu, musamman gidan malam Isa, komai na gidan da Malam ya ajiye
mana a rumbun abinci a hankali ya kare tas, sai hakan ya sa Innar Hauwa ta fara tunanin
sanaar yi, daga karshe ta tsayar da sanaar da ta fi yawa ga matan cikin Badala wato sanaar
dafa abincin sayarwa a cikin gida don nemar mana na batarwa dana cefane da bukatun yau da
kullum.
A kullu yaumin Inna ta kan dafa shinkafa da wake tiya daya, dahuwa mai kyau, ta soya
mankulin ta da albasa, ta daka yajin maggi, bata dora min talla a dalilin tana cikin masu adawa
da tallan yara mata, ta fi yarda da in je makaranta fiye da in nemar mata kudi, don haka tun
Baba yana nan ina zuwa makarantar boko da safe, da ta allo da yamma. A rashinsa kuma ban
fasa zuwa ba.
Da aka gane tsaftar abincin ta a hankali har gida ake zuwa a saya, kuma akwai wani yaro
anan makwabtanmu wai shi Saleleh, yaron ya saba da Inna ya shiga jikinta don shi yake
zamarwa Babana a shago in zashi wani wuri, bayan batan sa ya cigaba da shigowa gun Inna
tana bashi abinci da haka har suka saba don haka shi ta roka yake zuwa ya fitar mata da
abincin makarantar bokon da nake zuwa, wato makarantar firamare ta gwamnati ta Kofar Naisa,
wadda bata da nisa da gidanmu. Ita kuma tana bashi abincin data dafa da naira goma daga
cikin cinikin kullum ya dawo.
Kafin sha biyun rana Saleleh zai dawo da kudin ta a kulle a leda cif. An sayar da wake da
shinkafan, har ana neman kari, sabida dadi da tsaftar abincin Innar Hauwa.
Sai mu yi cefanen abincin gobe kuma, mu kuma yi amfani da ribar da muka samu. Idan
shekara ta zagayo Innar Hauwa na fitar da ragunan data kiwata ta sayar a kasuwar Raguna duk

sallar layya, sai ta sayi wasu kanana ta kara kiwatawa zuwa shekara ta gaba.
Da wadannan sanaoin guda biyu ni Hauwa da Inna ta muke rayuwa har tsayin shekaru biyu
da batan Malam, muna cikin alhinin rashinsa.
Duk da cewa ni Hauwa ba wata kyakkyawa bace acan-acan, gani nan dai kalar Kanawan
usli, wankan tarwada kuma makimanciya ga kyau, banda idanuna farare manya dasu masu
kama da zagayen kwan zabo, ba abinda zaka ce mai bayyannnen kyau ne a halitta ta.
Na farko bani da tsayi, kuma bani da rama, amma bazaka kira ni mai kiba ba, gani nan dai
yar duma-duma haka, lubu-lubu mai jiki (luscious) tubus-tubus kamar na kulba, na kasance
yarinya mai zafin nama tun ina karama da kwazon taya Inna aiki, sannan da tsananin son
Uwa-mahaifiya da tausaya mata, musamman dana wayi gari babu Baba tare da ita, na fahimci
ita kadai take buga-buga da kulle-kulle don ganin ban rasa komai ba.
Hakika na saka son Inna ta da yawa a raina, da tausayinta tun ina kankanuwa mai cikar
lafiya, ga Inna da kujuba-kujuba a cikin gida tayi wannna ta koma ta yi wancan, shiyasa nima
bana kyuya wajen taya Innata aikin abinci da ayyukan cikin gida tunda na soma kawo karfi, ni
dai bar ni da shiru-shiruna na rashin son magana da rashin son hayaniya, sai manyan idanuwa
tubarkallah masu yiwa wanda duk na harara barazana, farare kal dasu, masu haske da sheki da
wani kwantaccen ruwa a kasan su, inna juya ido sai ka ga kamar hawaye ya kwanta.
A kaina akwai tarin sumar hausawa baka mai karfi irin cunkus dinnan, wadda bata taba
ganin man shamfo ba (relaxer) ko na Danjangabo da ake amfani da shi a lokacin domin motsa
gashi. Ni Hauwa tun ina kwailata akwai son wanka da yawan shafa turaren ‘Binta-Sudan’ ko
‘Dan Duala’ wanda na Inna ta ne da take yawan siya don amfaninta, kullum tayi wanka su take
shafawa, sai nima na ara na yafa.
Lokaci-lokaci Inna kan sai min maina na shafawa na musamman (Dela-Maigurguwa), can
gaba da zamani ya kara sabuntawa wato ‘cream’ ya shigo, sai ta koma saya min ‘TonyMontana’
don nima in jera da yammata, a lokacin a shekaru goma sha biyun da nake dasu sune matakin
farko na fara zama budurci, duk da ko kirgen dangi ban fara ba. Komai nawa dai-dai misali ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login