Showing 30001 words to 33000 words out of 99941 words

Chapter 11 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1532

ta tashi tayi karatu da dare tana kwanciya kuwa bacci ya
dauketa.
Da safe ta riga kowa tashi tayi wanka tayi brush ta shirya dake alhamis ce azumi ta tashi dashi
suka fita domin tafiya makarantar lkcn shima ya fito zai fita tun daga nesa ya zubanta ido yanda
take tafiya a nutse yana karyar da zuciyarsa bata lura dashi ba Muntaz ne tagani yana training a
harabar gdan ta dauke fuska hakanan takejin tsanar Muntaz don ta fahimci shima ba qaunarta
yakeyi ba driver ya gama saita motarsa domin kaisu yaji an kirashi ya juya da ladabi cikin isarsa
da izzarsa ta jini yace “kaje kayi abinda ke gabanka zan saukesu" jinjina kai Mal Wada yayi
Kareem dake fitowa yace “Ya kabari kawai zan kaisu....." Dagowa yayi ya sauke idanunsa masu
firgita mazan gaske akansa bai samu arziqin Amsa ba yace.

“Ku shiga" Gabadaya Juhud a firgice take da yanayinsa suka bude baya suka shiga dukkansu
yaqi tashin motar ya dora qafarsa saman sitiyarin ya kashe A.c ya kwantar dakansa saman
kujerar ya lumshe idanunsa shi kadai yasan irin azabar da zuciyarsa takeyi masa game da
yartasa yanajin tsoron yin abin kunya a tunaninsa kamarshi ya bude baki yace yanason Meenah
matsayinsa da darajarsa ta fado bawai don bata isa ba aa kawai shi tsarinsa ne hakan babu
macen data isa yace yanasonta a duniyarsa Yana ganin hakan matsayin raini da rashin aji.
Amrah ce tayi qarfin halin cewa “yaya takwas zamu fara paper fah Kuma yanzun bakwai da
arba'in" batare daya dago ba ya furzar da iska yace “Meenah!" Yanda ya ambaci sunan ba itaba
hatta su Ya'isha Saida sukaji yar a jikinsu suka dubeta ta dago a kasalce tace “na...na'am" ajiyar
zuciya yayi yace “idansu qanne nane ke meyece a gurina?" Tambayar tazo mata a bazata, cikin
rawar murya tace “ya" ya miqe ya zubawa fuskarta ido ta cikin mirrow yace “kuma kikeso na
zama driven ki" bata fahimci abinda yake nufi ba Ya'isha tace “ki koma gaba don Allah mu samu
yakaimu" sai yanzun ta fahimta ta bude motar ta fita ta bude gaban ta shiga ta rufe ya juyo ya
kalleta ya dauke kai ya tada motar suka bar gidan"




Tunda suka taho babu me cewa qala har suka isa makarantar yayi parking suka bude zasu fita
ya riqo hannunta ta zauna ta juyo suka fuskanci juna ta sunkuyar da kanta yace “ina kwana" da
sauri ta rufe idonta kunyarsa ta lullubeta yayi murmushi yace “nawa zanke siyan gaisuwarki ne
Meenah?" Dariya tayi ya kafeta da ido nandanan ta shiga hankalinta yace “idan kun tashi ku
jirani kar wacce ta tafi" jinjina kai tayi ya bude mata ta fita yace “ki kulamin da kanki" sake jinjina
masa kai tayi ta nufi cikin makarantar yabita da ido baija motar ba Saida ya daina ganinta
sannan ya tafi.




Hudu saura suka fito daga exam din Ya'isha da Amrah suna Shirin kiran driver Kira ya shigo
wayar Ya'isha ta daga da sallama jin muryar yayan nasu yasasu shiga taitayinsu yace kuzo Ina
jiranku inda na saukeku, Basu so ba donsu nufinsu ba gda sukayi ba gdan Aunty Hamida zasu
wucce ganin babu hali yasasu nufar inda yayi parking suka bude suka shiga. Hudu saura suka fito daga exam din Ya'isha da Amrah suna Shirin kiran driver Kira ya shigo
wayar Ya'isha ta daga da sallama jin muryar yayan nasu yasasu shiga taitayinsu yace kuzo Ina
jiranku inda na saukeku, Basu so ba donsu nufinsu ba gda sukayi ba gdan Aunty Hamida zasu
wucce ganin babu hali yasasu nufar inda yayi parking suka bude suka shiga, Yana driving din yana satar kallonta inda ita Kuma gabadaya hankalinta yake akan titin har suka
isa gdan babu me cewa qala suna zuwa ta bude motar ta riga kowa fita saboda kanta da yake
ciwo “idan kun shiga kuce ta kawomin abinci" abinda ya fada kenan suka fita shima ya fito ta
baya yabi ya shiga bangarensa ya zauna a falo kallo yakeyi Amma hankalinsa baya gane komai
tsayin lkc yaji ana qwanqwasa qofar yabada izinin shigowa ta murda ta shigo da sallamarta ya
Amsa mata idanunsa akanta wasu riga da skirt ne na atamfa sunyi mugun karbar jikinta ta ajiye

abincin ta dago tace “barka da hutawa Baffa'am"
Lumshe idonsa yayi ya bude akanta yace “kamar wani abu na damunki ko?" Dagansa kai tayi
ya gyara zamansa yace “meye shi?" Sunkuyar dakai tayi tace, kaina ke ciwo sosai" sake
quranta ido yayi yace “kinsha magani?" Girgiza masa kai tayi ya miqe ya bude bedside drower
ya dauko magani ya miqa mata ta karba ya tsiyaya mata ruwa a cup ya bata tasha ya sauke
numfashi yace “ki gyaramin dakin nan" miqewa tayi ta fara gyara dakin ta wanko bathroom din
ta fito Yana zaune inda tabarshi ta rusuna tace, na gama" jinjina kai yayi ya nuna mata abincin
ta zuba masa ta miqa masa ya karba ya faraci kamar bason cin yakeyi ba itadai tana zaune so
take yabata damar tafiya saboda shima kallonsa ya fara takurata sosai ta kasa sakewa
maimakon hakama sai ce mata yayi “wacce paper kukayi yau?"





A gajarce tace “English" yaja gemunsa yace Kuma kina ganewa?" Daga masa kai tayi ya dauki
wayarsa ya kunna wata waqa ya miqa mata yace “inason ki saurari waqar nan sosai ki fadamin
meye kika fahimta game da ita?" Sauraron waqar takeyi cikin nutsuwa a hankali ta kwantar da
kanta saman dayar kujerar tanajin kalaman baitocin da mawaqin yakewa masoyiyarsa suna
ratsata musamman wani baiti da yake cewa “kece ta farko, kece ta qarshe kece kike samin
nishadi! idan na waiga ke zana hanga kada ki kasa cikan muradi!! sonki na kama bani nadama
kyawun hawan doki da sirdi!!! in kika yarda dani bazani yarda ki wahala ba Rahma!!!" Akwai
dalili zanyi misali sunnarki yau na cika buri! nayi su'ali nakwance qulli kedayace zan baiwa sirri!!
Samun halali boye da fili,,, shine yakesa rai sururi inda na shaqu dake aso bazaiyi na makara
ba!!!......."
Sakkowa yayi ya karbe wayar yasa hannu ya dago kanta idanunta suna lumshe yace “me kika
fahimta?" Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke tace “baitukan sun kashemin jiki Baffa'am
Amma ban fahimci komai ba" iska ya furzar yace “bakisan soba ko Meenah?" Daga masa kai
tayi ya zuba mata ido Yana lasar lips dinsa yace “nikuma Yana wahalar dani sosai Meenah son
wata yarinya Yana neman tarwatsamin zuciya abin takaicin ni jarumi ne a filin daga na iya riqe
kunamar bindaga da sakin ruwan harsashe Amma a gabanta matsoraci nake zama na kasa
fada mata Meenah"




Cikin yanayin tausayi ta dago tace “Allah sarki Baffa'am meye yasa bazaka fada mata ba to
babu wani abin tsoro a lamarin soyayya Kuma ma fah zai iya yuwuwa itama tanasonka bazata
iya fada maka bane" tunda ta fara mgnr yake kallon bakinta har tayi shiru yaja zuciya ya dafe
kuncinsa yace “idan tanasona me yasa bazata fadamin ba ita tunda ni nakasa?" Murmushi tayi
daya qara bayyanar da sihirtaccen kyaunta tace “kaima dai Baffa'am to kaima namiji da aka
sanka da jarumta akan muradinsa ka kasa tararta ka fada mata sai ita da take mace da aka
sani da yakana da kunya kaima kasan bame yuwuwa bane ai"

Sake sanya hankali yayi akanta yace “ta yaya zan gane idan tanasona Meenah ita yarinyar ta
kasance tana matuqar ganin girmana fiye da kowa tana mutumtani batason bacin raina batason
damuwata har tana kirana da babanta........ Dagowa tayi da sauri yayi murmushi yace “haka
nake nufi sunan babanta ne dani babana haka take kirana a gaban kowa Meenah wlh inason
Aminatuh fiye da son da nakewa kaina banjin zan iya rayuwar aure da wata mace ba Aminatuh
ba na Raina kaina ranar dana fahimci ba shaquwa ce tasa nake tsananin kishinta ba sone, nayi
qoqarin mayar da lamarin mafarki Amma ya faskara har takai zuwa yanzun duk wani fitar
numfashi nawa da tunaninta yake fita please ki bani shawara ya zanyi na fahimtar da Aminatuh
inasonta?".........




*Oum Hairan*
[7/21, 6:31 PM] Oum Hairan: *JH015- littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada
ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or
card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*
*Ga yan Niger da suke son wannan littafi basusan ya zasuyi ba ga number da zasu tuntuba
94775574 zasu tura katinsu daidai da kudin littafin sai suyimin mgn na gde*



Wani gwauron numfashi Meenah ta saki tace “idan har kace saika Bari ta gane da kanta to
kuwa da jan aiki a gabanka Baffa'am idan Irina ce me qarancin fasaha wajen gane abubuwa
hannunka Mai sanda bazai wadatar wajen fallasa mata sirrin zuciyarka ba misali kamar ni duk
da har yanzun ban karbi tayin qaunar Ya Kareem ba, Ganin nidin bame ganewa bace yasa ya
fito ya sanar dani abinda ke ransa ko banza nasan zai samu sauqi game da ciwon dake cin
zuciya balle ma ni......"
Dagowa tayi ta dubesa tsoro ya kamata ganin yanda lkc daya ya hargitse yanayinsa ya canza
daga na walwala zuwa matsananciyar damuwa, da sauri ta miqe tace “kayi hqr don Allah
Baffa'am kaine kace duk wani abu dake damuna na rinqa sanar dakai kafin na sanar da
kowa......" “Shut-up Meenah!" Abinda ya fada da qaraji kenan ya miqe jikinsa na rawa zuciyarsa
na motsawa da qarfin gaske maqwallatonsa kamar zai faso maqogwaransa tsabar bala'in dake
cinsa suka fara zagaya dakin cikin tashin hankali ganin guri ya qure matane ta zame a qasa
kawai ta saki kuka me sauti tace.
“Na shiga uku ni Aminatuh Baffa'am meye laifina ne don naso Ya Kareem wlh ko zaka kasheni
saina fada maka inasonsa saboda yanada cikar Kamala da nagartar da tayi qarancin a samarin
zamanin nan inasonsa saboda zuciyata tana fadamin shine ya dace da maraici na Baffa'am Ya
Kareem baitaba sani dole ba baitaba hanani dole ba saidai akan aya da hadisin ma'aiki (S.A.W)
baitaba takuramin akan nasoshi ba saidai ya roqi alfarmata duk da kasancewar banida alfarmar
shine yake da ita domin a cikin da'irar arziqinsu nake rayuwa, Ya Kareem baitaba nuna yanason

jikina ba hasali ma yaqi yakeyi da duk abinda zai tarwatsa mutumcina Kuma, Ya Kareem ya
fadamin cewa Allah Yana maraba da bayinsa da sukayi soyayya dominsa wannan dalilin yasa
naji inasonsa domin Allah Kuma zan rayu das......"




Bata iya qarasa kalamin nata ba saboda wani gigitaccen mari daya sanyata kifawa ya nunata
da yatsa zuciyarsa na tuquqi yanason yayi mgn Amma harshensa ya sarqe a hankali ya janye
ya koma ya zauna yana furta “Innanillahi wa innah ilaihir raji'un" ya maimata ta takai sau goma
kafin yaji nutsuwa ta fara saukar masa ya dago idanunsa da suka kada sukayi jawur kamar
garwashi bakinsa da jikinsa har yanzu rawa yakeyi yace “kina sonsa ko Meenah?" Dagowa tayi
idanunta shabe² da hawaye yace “bakiyi qarya ba duk gdannan babu wanda ya tara wadannan
suffofin da kika lissafa sai Kareem nima shaida ne saboda haka ya cancanci kisoshi tabbas
Amma Kuma yanzu ya zakiyi da wanda ya daukoki tun baki cika mutum ba yajaki jikinsa ya
mayar dake mutum ya bata darensa da ranarsa dominki ya Hana kansa farin ciki sai yaganki
cikin farin ciki yake shiga damuwa da damuwarki koda kuwa bakwa tare motsinki ya zama nasa
lfyrki tasa ciwonki nasa Aminah ya zakiyi dashi wanne halacci zakiyi masa da zaiji a ransa kin
saka masa da kwatankwacin tausayinsa da qaunarsa gareki?"





Tunda ya fara mgnr ta kafesa da idanunta da yake tsiyayar da hawayen tashin hankali tasowa
yayi ya matso gabanta ya miqar da ita yace “idan ya kasance kin kasa saka wancan Alkhairin
da abu mafi daraja wato qaunar da wannan mutumin yake nema a gurinki to tabbas ke ba yar
halak bace domin dan halak shine yake jiran gabar saka Alkhairi da komansa koda kuwa gurin
bai cancanci sakayya ba shidai burinsa yaji a ransa babu bashi tsakaninsa da wannan
mutumin"
Sakinta yayi ya juya zai shiga bathroom har ya bude ya juyo yayi mata murmushi yace “kije kiyi
tunani akan kalamai na" a mugum kasalce ta bude qofar ta fito ta nufi cikin gdan zuciyarta na
kai kawo akan kalamansa tana shiga dakinsu ta zube a bakin qofar tana mayar da numfashi
Amrah dake fitowa daga bathroom taja ta tsaya sake da baki ganin yanda ta cure jikinta tanata
rera kuka takaici yasa Ya'isha miqewa tace “dallah malama ke baki rabo da kukane meye Kuma
akayi miki" dagowa tayi ta kwantar da kanta jikin Amrah tace “nikam Ina ganin rayuwa Amrah
don Allah meye wadannan kalaman suke nufi......"
Zayyane musu komai tayi ta qarashe da cewa “bansan meye yasa qwaqwalwata bata gane
abubuwa ba" numfashi Amrah da Ya'isha suka saki tare Amrah tace “kan ubancan lallai akwai
qura a gdannan Juhud bafa wani abu Big Cele yake nufi ba kece yakeso kece Aminan da yake
baki lbr ke kadai ce me wannan siffar daya suffanta" Ya'isha ce tayi murmushi tace “ke saiyau
kika fahimta ai dake da Aminah dukkanku kallonku nakeyi Amma wlh batun yanzu ba na fahimci
Big Cele son Juhud yakeyi tsabar miskilanci ne da girman kai ya hanashi bayyanawa yake wani

bada fadi da hura hanci kamar kyankyaso aikin banza na dade da gano damuwarsa kekam ta
bakin naki kina ganin rayuwa ga Mai Martaba yayima Ya Kareem alqawarin aurenki" cikin
mutuwar jiki ta dago tace “nikam ya zanyi wlh da gaske bantaba daukar wannan gundumemen
lamarin zai fadomin ba banyi masa muhalli a bangarena ba bantabajin Baffa'am zaice yanasona
ba kai bama abinda yake nufi ba kenan babu abinda zaiyi dani"




Dariya sukayi dukkansu ta zubansu idanu Amrah tace “waima to shi ya gani wlh yarinya tun
wuri ki takansa birki inba hakaba zakisha wahala Big Cele bashida mutumci gashi da ganinsa
zaiyi wuta babban tashin hankalin ma mgnr aurensa da Zulaihat tayi mugun nisa harma fah
ankai kudin tambaya sa rana kawai zaayi anasa rana Kuma raqashewa zamuyi Kinga kenan
bakida gurbi kawai batankin gomanki zaiyi dayanki bata gyaru ba"
Tagaji dajin wadannan kalaman hakanne yasata miqewa ta shiga bathroom ta sakarwa kanta
ruwa ta fito taji ana kiran magrib ta dauki dabino ta tauna ta fita ta dauko ruwa tana dawowa
Amrah ta miqa mata waya ta Amsa ganin number Kareem ta Kara a kunnenta tace “nasha ruwa
lfy Habiby kaifa?" Murmushi yayi yace “yanda kikasha Luv ya exams?" Kwanciya tayi tana
lumshe ido tace “inajin dadin exams din da taimakonka" hirarsu sukaci gaba dayi tama manta
da batun Shan ruwa saida yace “kije kisha ruwanki zan kiraki anjima" ta aje wayar ta tayar da
sallah tayi buda bakin.




Tun daga wannan ranar salon rayuwar gdan ta canza musamman tsakanin Juhud da Rasheed
duk inda tasan zasu hadu gujewa gurin takeyi saboda ita har cikin zuciyarta bataji a ranta zata
iya soyayya dashi ba bayan haka ma sannu a hankali Kareem ya gama siye zuciyarta da salon
qaunarsa me tsayawa a rai da wuyar gogewa kullum idan sunyi waya kalmarsa daya itace don
Allah Aminah ki kulamin da kanki nayi miki tanadin kaina na tsare kaina tsayin shekaru burina
ya kasance a halali na na fara shuka inason gonata tayi kyakkyawan yadon da yabanyarta zata
burge kowa idan amfanin ya nuna ya isa moro ya morawa duniya baki daya Aminah samawa
yayana uwa ta qwarai shine abinda na dade Ina addu'a nasani bazan taba danasani ba idan kin
kasance mata a gurina zaki bani farin cikin da zanyi alfahari dake a duniyata da lahirata"
Idan ya fada mata haka Yana kashenta jiki matuqa takanji kamar ya daureta da jijiyarta ne duk
saitaji wani shauqin qaunarsa Yana qara mamaye ruhinta wannan dalilin yasa ta qara qaimi
wajen tsare kanta tunda me bata kariyar bayanan gashi ya Daura mata nauyi Mai girma na
amanarkai.



Kwanci tashi lkc ya rinqa tafiya cike da matsaltsalu Rasheed mugun miskili da baa gane

matsalarsa Amma yanzu kusan kowa ya fahimci yanada damuwa gashi da baqin zurfin ciki ya
kasa furtawa kowa damuwarsa saidai yaje Garden yayi tagumi ko ya tusa waya a gaba yayita
kallo. Ranar da sukayi Candy suka hada qwarya²r party a gidan sarautar Juhud batada qawaye
su Ya'isha ne suka gayyato samarinsu da qawayensu Mai Martaba shine ya daure gindin partyn
harda dauko musu Dan Hausa yazo don qarawa abin armashi qarfe hudu suka fara caskalewa
samarinsu duk sunzo itace kadai saurayinta baizo ba baya qasar ma Amma yayi mata fatan
Alkhairi sun dauki wanka na tashin hankali sunyi kyau na bam mamaki dama dukkansu ba baya
ba wajen kyau Amma sukansu Saida suka sallamawa Juhud tayi kyau kamar wata amarya
suka fito daga gdan ana take musu baya suka fara hotuna anyi mata hoto yafi kati dari da shiga
daban² ta karbi wayar Ya'isha ta zagaya baya ta Kira layin Ya Kareem bugu daya ya daga tayi
ajiyar zuciya tace “rayuwata tana cike da kewar masoyi banajin komai yana tafiyar min daidai"
dariya yayi yace “kinajin abinda nakeji kuwa Aminah nifa inajin kamar zanyiwa Mai Martaba
mgn ne zanzo hutun azumi kawai a hada bikinmu dana Big Cele ayi a bani ke mu taho nan"




Juyowar da zatayi suka hada ido da Rasheed dake tsaye jikin swimming pool kallon da yake
mata ne yasata kama in...inar qarfi da yaji tace “am...in...." Ji tayi ya warce wayar ya duba yaga
number qanin nasa yana mgn Yana cewa “hello..... Luv....." Qit ya kashe wayar ya jefa a
aljihunsa ya juya yabar gurin daga Ya'isha dake qarasowa ta dafata tace “wai me kikeyi ne
anata nemanki" juyowa tayi idanunta ya ciko da qwallah tace “ya qwace wayar Amrah...." Binsa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login