Showing 66001 words to 69000 words out of 99941 words

Chapter 23 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1534

Meenah fushi takeyi dani ban damuwa domin nasan gata Mai
Martaba yayi mata kaidin dama kaine ka dace da ita Hukuncin Allah ne yabawa Rasheed da
Kuma rabon Sarki junior Kuma ma ai tanasonka tun a baya kawai yanayin da take cikine yasa
zakaga kamar batasonka"
Murmushi yayi yace “hakane Mom na gde am Dr yace zamu iya tafiya gda nikam zanfi samun
nutsuwa tana tare dani" batason jayayya dashi shiyasa ta aminta su tafi din ta shiga dakin ta
fara hada musu kayansu Meenah na kallonta harta gama ta dubeta tace “mu tafi mijinki ya
matsa saidai mu tafi gabadaya" daqyar Mom tasha kanta ta miqe suka tafi baya ta shiga yana
kallonta yayi murmushi sai Mom ce ta shiga gaba suka nufi Katsina da suka isa Daura ta samu
ta fita a mota tayi wuf ta shige dakin da take ta fada gado ta rushe da sabon kuka tana tuna wai
yau ita ce matar Kareem bata Rasheed ba meyesa qaddararta kullum ita baibai ce a fili tace “lkc
yayi da zan nemawa kaina gata dole na nemi su Baffa Ribado ko zasu kasheni su fitomin da
dangin mahaifiyata"




Qwanqwasa qofar taji anayi ta miqe ta bude qofar ganin Kareem ne tayi saurin mayarwa ta
datse yaja baya da sauri tare da cije lebe ya juya a kasalce ya fice daga gdan ya nufi gdansa
babu kowa kamar yanda ya tsammata yayi murmushi ya nufi gdansu Zahrah acan ya tarar da
yan karbar gaisuwar bai wani zauna ya dade ba ya nufi gidansa ya kwanta a gado Yana saqawa
da warwarewa akwai aiki a gabansa.
Meenah batashi takeyi ba baya a lissafinta ga Addah Abulle ta takura masa da Kira har takai
baya daga wayarta saboda yariga yasan mgnrta bata wucce akan qiyayyar aurensa da Meenah
tana qara tuna masa tun tana budurwa an hanashi sai yanzu data zama saura ragowa sannan
ga rashin asali kalma daya yake fada mata Babu komai Addah inasonta a haka ba meenah ce
ta qini ba a farko fin qarfinta akayi saboda hska nima bazan qita ba" idan ya Fadi haka Adda ji
takeyi kamar ta kasheshi shima gashi Mai Martaba yaqi sauraronta balle yaji kokenta hasali ma
fushi yakeyi da ita wannan tasa ta zare hannunta daga lamarin Kareem din ta zubansa ido tare
da cin alwashin indai itace ta haifeshi to Meenah ta gama kwanciyar hankali a duniyarta saisun
takurata sun azabtar da ita ita da yan'uwanta babban abinda yake daganta hankali Zahrah yar

wanta ce ta nemawa Kareem aurenta don huce haushi yanzun Kuma ya samu abinda ransa
yakeso bayama ta ita tunkan tafiyar tayi nisa.




Wadannan dalilan suka hadu sukayiwa zuciyar Kareem yawa abinka da mara isasshiyar lfy
nandanan zazzabi ya rufeshi shi kadai a gda yayita murqususun ciwo yana dafe qirjinsa
wayarsa ma ya kasa dauka ya kira wani, baa Ankara ba Saida ya kwana shidda yana fama da
ciwo shi kadai a gda sannan ubangiji ya kawo masa sassauci a galabaice ya lalubi wayarsa ya
Kira layin Zahrah bugu yafi biyar tana gani taqi dagawa ya hqr ya Kira na Meenah itanma yayi
mata misscall yafi goma tana kallon wayar taqi ta daga qarshe ma ta kasheta gabadaya ya
jinjina kai cikin azabar ciwo ya Kira layin Mom dan yasan idan ya Kira na Addah ma itanma
kamar yanda matansa Basu saurareshi ba itama ba saurararsa zatayi ba.
Bugu daya Mom ta daga tace “dan halak kaqi ambato Ina ka shigene inata nemanka bana
samunka....." Nishin da taji yanayi ya fadar mata da gaba tace “ya salam kardai bakada lfy
ciwon ne ya tashi Kareem....." Cikin rawar murya yace “Mom....ki....ki taimaka ki kawomin
Aminatuh don Allah kada ta zamo silar ajalina sonta zai kasheni...." A gigice tace “o.... Ok ganinan don Allah kada ka mutu Kareem mukam mun shiga uku da
wannan masifa" kashe wayar tayi ta zari mayafinta ta fice a kidime ta nufi dakin Meenah tana
zaune tana koyawa Sarki Homework ta dago ta dubi Mom tace “Lfy Mom?" Sharce gumi tayi
tace ”taso ki rakani unguwa"



Babu musu ta miqe ta dauki mayafin doguwar rigarta ta sanya ta kama hannun Sarki suka fito
ita kejan motar Mom na fada mata inda zasu tana fahimtar gidan Kareem suka nufa hasken
fuskarta ya dauke ta hade rai donma Mom tafi qarfin musu ne a gurinta shiyasa tayi shiru har
suka isa gdan suka Mai gadi ya bude musu sukayi parking Mom ta fito itakam gyara zamanta
tayi Mom ta dakanta tsawa tace “bafa nason sakarci Meenah ki fito mu shiga nace"
Tana qunquni ta fito suka shiga cikin tun daga falon taji gabanta na faduwa komai a hargitse tabi
falon da kallo taja tsaki Mom ta haura saman tabi bayanta tana kallon tsarin gdan bude wata
qofa Mom ta Kuma yi qofofi ne guda biyu suna kallon juna ga mamakinta nan dinma falo ne sai
wasu qofofin biyu tsayawa Mom tayi tana tunanin wacce zata bude Sarki yace “Mom ga dakin
Uncle nan" Yana mgnr Yana murda qofar suka shiga a tare itakam guri ta samu ta zauna a falon
tana hura hanci.
Yanayin da Mom ta isheshi yayi mugun tada mata da hankali ta saki wani kuka tace “innanillahi
wa Inna ilaihir raji'un Abdulkareem meye hakan kashe kanka zakayi a gda kai kadai" gaban
Meenah ya sake faduwa lkcn da Mom ta qwala mata Kira ta miqe a razane ta shiga dakin tare
da zaro ido Yana kwance a qasa magashiyan cikin wani mawuyacin yanayi ya bude idonsa ya
saukesu akan Juhud tare da sauke ajiyar zuciya ya fara yunqurin miqewa Yana cewa “Am....
Ami...na...tuh zo... matso gareni please...." Janyewa tayi tayi baya idanunta na kansa Mom ta

tura ta fada jikinsa ya lumshe idonsa tare da sanya hannunsa ya zagayeta yaja wata ajiyar
zuciya me qarfi tana qoqarin qwacewa ya bude bakinsa yace “na...na gode Mom ke kadai kike
tausayina a duniya Mom Meenah bata sona...." Juyawa Mom tayi ta fice saboda yanda taga
Yana qara matse matarsa a jikinsa abin yabata tausayi da kunya ta lura da Rasheed da Kareem
tafiyarsu daya Basu da kunya akan abinda sukeso.......




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane kada ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan
account din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton
katin ko digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*

[8/7, 7:18 PM] Oum Hairan: *0031* Da qyar ta samu ta janye daga jikinsa idanunsa suna
lumshe hawaye yake zubarwa ya riqe hannunta yace “Nayi tunanin kedin me yarda da qaddara
ce da hukuncin ubangiji Meenah ashe ba haka bane Meenah ko bazakiji tausayina ki daina
azabtar da ruhina don na cancanta ba ya kamata kiji qaina don qaunar da nakeyi miki inasonki
ne Meenah da jinina da rayuwata" Yana mgnr numfashinsa ba kakkatsewa hakanan taji bazata
iya jure cigaba da kallonsa a wannan yanayin ba ta miqe zata fice ya Kira sunanta ta tsaya ya
dauki wayarsa ya miqa mata yace “idan tafiya zakiyi ki kiramin Amrah ko Urwat ko Muntaz wani
cikinsu yazo ya zauna dani Ina cikin yanayin da komai zai iya faruwa dani"
Harararsa tayi ta fice a ranta tana cewa “badai ni ka zaba ba wlh saidai ka mutu yanda uwarka
da yan'uwanka ke qina haka nima nakeji game daku ban shirya zama da wannan ahlin ba
abarni na rayu da zabina koda baya tare dani nasan Ina kwance a zuciyarsa" sauka tayi qasan
ta tarar da Mom da Dr Razaq suka dubeta tare sukace “ya me jikin" a gajarce tace “yana ciki" ta
juya ta fice ta shige mota shiru dogon lkc ya wucce basu fito ba can taga mota ta shigo Mai
Martaba ne da Arman suka shiga suka daukoshi suka fito dashi. A mota suka sanyashi suka
fice Mom ta shiga mota Juhud taja suka fita sosai ta qular da Mom da halin ko in kula din data
nuna akan mijin nata bata taba tunanin zuciyarta tayi soyewar haka ba.

Saida sukaje gda ta juya zata shiga dakinta Momy tace “bantaba tunanin hakan daga gareki ba
Meenah mijinki zabinki a baya banga zafin da rayuwa tayi tsakaninki dashi ba da zaki zabi
azabtar dashi Meenah koda a yanzu baki zabeshi ba cancanta aka duba aka zabanki shi kada
kiyi wasa da damarki inaji a jikina Kareem zai sharenki hawaye don Allah Meenah indai da
gaske kin daukeni matsayin uwa a gareki kiyima mijinki biyayya ki rintse idonki ki ninka hqrnki
akan wanda kikayi a baya. Tabbas akwai qalubale cikin zamanku to Amma qaddara ta riga fata
haka Allah ya shirya mana addu'a Rasheed yake buqata kawai daga gareki"
Sunkuyar da kanta tayi tana sauraron Mom harta gama fadar abinda zata fada
Ta juya ta fita ta kwanta rigingine zuciyarta na hasaso mata abubuwa da dama da suka faru a
baya lkc zuwa lkc tana dauke hawaye a fuskarta itadai batasan sanda bacci ya dauketa ba
wajen biyun dare ta farka tayi alwala ta tayar da nafila tana roqon Allah ya shiga lamuran
Rasheed a duk inda yake ya tsareshi da tsarewarsa ya bayyana shi cikin aminci da salama
bayan ta idar ta zauna tana lazumi taji wayarta tana ring takai hannu ta dauka lambar Kareem
ce taja tsaki ta katse wayar ya Kuma Kira ta dauka zata kashe maganganun Mom suka rinqa
dawo mata tayi qarfin halin dorawa a kunnenta




Ajiyar zuciya ya sauke lkcn da tayi masa sallama ya Amsa cikin wata irin murya me tsananin
sanyi shiru taci gaba da wanzuwa wadda harta sabbaba mata tunanin kashe wayar can taji ya
sake jan zuciya yace “nayiwa Mai Martaba mgn game da tariyarki yace nayi miki mgn shiyasa
na kiraki a wannan lkcn me kike shiryawa meye plan dinki?" Shiru tayi kamar bazata ce komi ba
shikuma yayi kasaqe Yana jiran jin cewarta alamar da yaga na ba mgnr zatayi ba yasashi cewa
“ok bakida wani tsari ga dukkan alamu ni inadashi yau Litinin na baki zuwa juma'a ki gama
komanki zaki tare a gdanki kici gaba da ibada kamar kowacce mace, ki duba account dinki na
tura miki wasu yan canjika Basu da yawa kiyi hqr dasu idan basu isheki shirye²nki ba zanyi
qoqarin qara miki insha Allahu"
Katse wayar yayi daga haka tabi wayar da kallo cikin mamaki lallai ma Kareem dinnan yana
fama da kansa yana fama da bala'i shikam dama ya hqr ya barta anan inda take da yafi musu
kwanciyar hankali dukkansu. Qwafa taja ta duba alerting din da akayi mata dazun ta zare ido
tare da cewa “wht? Me zanyi da kudaden nan ni Aminatuh 2 millions ta meye ce?" Komawa tayi
ta kwanta baccin da bata koma ba kenan washegare wayewar Litinin ta fara shiri don komawa
makarata Mom na kallonta batace mata komai ba harta gama shiryawa ta dauki jakarta ta saba
tace “mom zan koma school" murmushi tayi tace “da izinin wa?" Kallon Mom tayi da sauri tace
“izini Kuma?" Daganta kai tayi tace “mijinki ya kirani da asuba yace kada ki koma makaranta kiyi
shirye²nki juma'a zaki tare a gdanki Litinin me zuwa zaku tafi Saudi zai koma can da zama
abinda yayi saura na karatunki yayiwa H.O.D na department dinku mgn zaayi bakin qoqari"
zama tayi dabar a gurin gumi na karyo mata tace “ni Kuma Mom in bisa Saudi haba Mom don
Allah kice masa aa inada abubuwan da sukafi binnasa muhimmaci anan Mom inason in nemi
dangina su hadani da dangin mahaifiyata idan naci gaba da zama a haka akwai matsala please

Mom kisa baki don girman Allah"




Murmushi Mom tayi tace “wannan duk me sauqi ne ni na daukar miki alqawarin bibiyarsu har
zuwa lkcn da zaa dace kibani address nasu" sunkuyar da kanta tayi hawaye wani nabin wani
itadai bataso ba taso tayi komanta da kanta miqewa tayi ta koma dakinta ta kishingida zuciyarta
na zafi haka yinin ya kusan qarewa kiran duniya da yakeyi mata taqi dagawa itafa bayan zafin
tsanarsa saboda mahaifiyarsa da tayi harma da ganin rashin dacewar wannan auren nasu duk
da tasan ba haramci a ciki Amma wata halal din ta cancanci bari don kunya.
Da la'asar tana kwance Mom ta turo qofar ta shigo da sallamarta ita da wata mata Meenah dake
kwance ta miqe suka gaisa da matar Mom tace “wannan itace nakeyi miki mgn aurenta na farko
yazo a wani yanayi baayi mata komai ba so data haihu an gyarata Amma anja shekaru kusan
shekara antafi biyar shine yanzun nake buqatar ki qure fasaharki wajen gyarata ko nawa ne
mijinta yace zai biya" suna hirarsu wannan Hajiyan na fito da saiwoyi da magunguna tana yima
mom bayani tare da turaruka itadai tabe baki kawai takeyi bata yarda abin gaske ne ba Saida
taga an dauki wani qoqo an zuba wani ruwan tsumi an dauko wasu barbade barbade anyi an
gwamutsa da danyan madarar shanu wai sun miqo mata tasha.
Ta dubi Mom da idanunta daya kawo ruwa zatayi mgn ta kuwa daure fuska tace “aini dama
nasan ban isa dakeba Aminatuh nunamin bani na haifeki b...." Da sauri ta karbi qoqon maganin
jikinta na rawa ta kafa bakinta ta shanye daqyar tana kakarin amai matar tayi murmushi tace
“wannan shi kadai ma idan Tasha na kwana biyar ya wadatar bare zaa hada da wasu tun daga
wannan rana Juhud ta bani ta lalace da magunguna wasu tsarki wasu Sha wasu dafawa itadai
bakinta har daina tantance dandano yayi cikin kwanakin batada aikin daya wucce kuka.





Wayar ma da Kareem ke kiranta ta jefashi a blacklist ko ya Kira baya samunta hakan tasa dole
ya qyaleta yasan duk inda yau takai da jimawa gobe tana tafe yanaji a jikinsa wataran wannan
qiyayyar zata shude tunda da babu ita daga baya ta wanzu to watarana itanma zaa nemeta a
rasa, da wannan tunanin ya tattarata ya zubanta ido akayita shirye²n tariyar tata shine da Mom
da Ya'isha da Aunty Hamida suketa digiminsu dakin uwar ango da yan'uwansa Babu me ko lale
da bikin hasali ma ko bangaren da ake shagalin basuyi itama amaryar haka saidai idan Mom
tayi mata dole sannan take dan motsawa hakana aketa kaiwa da komowa su Ya'isha sune yan
jeran amarya har zuwa lkcn Zahrah bata dawo ba aka gyarawa Juhud dayan bangaren kamar
yasan zaiyi mata biyu dama tsarin mace biyu yayiwa gidansa bayan sun gama gyarawa sun
zubanta duk wasu kayan alatun rayuwa suka kullo suka taho gda sunata yabawa da kudin da
Kareem ya narkar a furniture dinta lallai ba qaramin so yakeyiwa Meenah ba.
Ta dauki gyaran jiki na ban mamaki abinka da farar fata har wani yellow takeyi yanda Mom ke
rawar jiki a wannan bikin ko Rasheed ne ya dawo ba lallai tayi ba ko lalle da akayi mata dishi²

ya kama jikinta saboda tsabar gyara hatta gyaran gashi a gda akayishi yin duniya suje gurin
gyaran taqi tana maqale a daki kamar wata mara gsky ko yaushe cikin kukan rashin mijinta take
da anbarta da wannan damuwar ma da tafi mata fiye da wannan da aka qara mata




Ranar juma'ar Mom taga ikon Allah yini Meenah tayi tana kuka tana kiran Rasheed duk dauriyar
da Mom takeyi a wannan karon Saida ta kebe itama taci kuka ta gode Allah Mom bata qara
tsinkewa da lamarin Aminah ba Saida magrib da Kareem ya turo da motocin daukar masa
amarya tunda ta fice a sashin su Mom din aka nemeta aka rasa babu wanda hankalinsa bai
tashi ba amarya ta bace da aka fadawa Kareem neman zaucewa yayi ya nufo gdan afujajan
suka shiga nemanta lungu da saqo domin sun tabbatar da cewa tana cikin gdan kasancewar
masu tsaron qofofin gdan sunce Babu wacce ta fita gabadaya sun gama karade gdan babu
dalilinta sai a qarshe Mom tace aje bangaren Rasheed ko can tayi haka Kareem da Mai
Martaba suka nufi part din ga mamakinsu suka tarar dashi a bude suka kalli juna babu furuci
suka kutsa ciki yayi qura sosai part din haka suka rinqa dubawa can cikin wani daki suka rinqa
jiyo shassheqarta har rige² sukeyi wajen shiga dakin sukaja sukayi turus dukkansu ganinta
zaune gefen gado rungume da wani hoto a qirjinta sai kuka takeyi me ban tausayi.
Wani abu me nauyi ne yazo ya tokarewa Kareem maqoshi ya furzar da iska me zafi ya juya ya
fice daga dakin sai Mai Martaba ne ya qarasa shiga ya kamo hannunta Babu musu ta miqe
tanaci gaba da kukanta idonta lullube da alqyabba ya fito da ita harabar gdan Ya'isha ta nufosu
da sauri suka sanyata a mota tana qarawa kukanta sauti tana Kiran sunan Baffa'am Sarki junior
dukkan wanda yake a gurin hatta Mai Martaba Saida tasashi sharar hawaye.




Hakanan suka nufi unguwar da gidan nasa yake Mai gadi ya bude musu suka shiga sukayi
parking Aunty Hamida ce take riqe da hannunta har cikin gdan suka haura da ita saman itama
kamar dayan sashin dakuna biyu ne sai wani qarami da alamun local kitchen ne wanda koda
zaka buqaci wani abu da dare basai ka sauka ba, daya cikin dakunan suka bude suka shigar da
ita sosai Hajiya Kulsum aminiyar Mom ta qara yimata nasiha akan biyayya ga mijinta itadai
Babu abinda da takeyi sai kuka da rawar sanyi zazzabi ne yake neman rufeta Ya'isha ta matso
jikinta ta sunkuya tace “ke banza ce wlh Ni banga abin kuka ba to kukan mafita ya zame miki
kome?" Dagowa tayi ta sauke idanunta sa suka jima da komawa jajaye saboda kuka tace
“shi....shikenan da gaske na rasa Baffa'am dina Ya'isha Kuma akeso nayi rayuwar farin ciki....."
Muryarta ne ya kama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login