Showing 78001 words to 81000 words out of 99941 words
Chapter 27 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf
da sauri tana cewa “Ya Allah Mai Martaba yaushe akaga Baffa'am dina
Amma aka boyemin meye yasa akayimin haka ashe akwai abinda zaa iya boyemin game da
Baffana....."
Tana mgnr tana nufarsa shikam ya saki baki ne Yana kallonta zuciyarsa na wani irin bugawa da
mugun qarfi qara waro idanunsa yakeyi yanason ya ganeta ya kasa tana Shirin kai hannunta
jikinsa taji yace da Mai Martaba “mai Martaba itan wacece?!" Ba itaba shi kansa Mai Martaba
Saida tambayar ta dakeshi ya dubeta yaga tayi mutuwar tsaye hawaye nabin kuncinta bakinta
yana rawa alama ta magana takeson yi ta kasa kama hannun Meenah Mai Martaba yayi yace
“ki nutsu Meenah Rasheed fah ba qalau yakeba duk duniya Babu wanda yake ganewa" zubawa
Mai Martaba ido tayi tace “meyesa aka boyemin bayyanarsa?" Murmushi Mai Martaba yayi yace
“akwai hikima cikin hakan yanzun ma banso kikasan da bayyanarsa ba so dandai ya matsa ne
saiya biyoni"
Zubewa tayi ta rushe da kuka tace “Allah na gde maka daka bayyanamin shi a raye Mai
Martaba Amma ya gane Sarki junior ko?" Murmushi yayi yace “ni kaina da zan fita na dawo
saiya tambayeki waye ni" zubawa Rasheed ido tayi da yake bin dakin da kallo yace “Mai
Martaba shima wannan dakin bansanshi ba shikuma wannan da bashi da lfy waye?" Yana
mgnr yanakai hannunsa ga Kareem dake kwance kamar gawa riqe hannunsa Mai Martaba yayi
yace “bakasanshi ba?" Daga kai yayi yayi murmushi yace “wani qaninka ne Kareem ja tunasa?"
Dafe kansa yayi kamar zai tuno ya dago yace “ok shine wannan wanda mukayi yaqin tare dashi
aka sacemu tare aka kaimu Sudan kace sunan gurin ko?" Murmushi Mai Martaba yayi ya dubi
Juhud data kwantar da kanta a jikin gadon tana kallon ikon Allah.
Likitan ne ya shigo suka gaisa da Mai Martaba suka fita suka barta ita da Rasheed abin yana
tsuma jikinta da ruhinta wai gata ga Baffa'am dinta Amma baiko kallonta harkar gabansa kawai
yakeyi ta miqe tanajan tsohon cikinta me watanni takwas ta matsa bayansa ta sassauta
muryarta tace “Abdulrasheed" juyowa yayi ya zubanta ido tare da dibanta ya watsar hawaye ya
sake tsiyayo mata tace “wai da gaske baka ganeni ba?" Daina latsa wayar yayi ya sunkuya ya
ciro takalminsa duka biyun ya miqa mata yace “nasan sune sukayi miki kyau to gasunan na
baki" noqewa tayi taqi karba tace “meyesa zaka mantani tsayin shekara shidda nakasa cireka a
Raina na kasa karbar kowa bayan kai Rasheed ni ban cancanci ka mantani ba....."
Saurin ja baya tayi lkcn daya fara kwance tazugen wandonsa gabanta ya fadi tana kallonsa
tanajin ninkin faduwar gaba gani tayi ya zare wandon ya kuma cire rigar ya rage dagashi sai
singlet da boxes ya nufeta Yana murmushi yace “nifa kinganni banida rowa idan kinason
wadannan dinma zan iya baki wlh Meenah ta tafimin duk abinda na mallaka a duniya Kuma
kinsan Meenah ta mutu Ina zuwa kogin maliya zan fada ciki na tsunduma tsundum na mutu
nima kowa ya huta yawwa ai kema kinsan zan hadu da Meenah acan ko?"
Tashin hankali Yana matsarta tana matsawa ya damqo hannunta ta rintse idonta ya damqa
mata kayan yace “ki riqe nabaki sadaka idan kinason agogon ma da zoben duk na cire miki Ni
dama na daina kwalliya takaba nakeyi Kuma bazan qarason wata mace ba a duniya tunda na
rasa Meenah"
Girgiza masa kai takeyi tana kuka me gunji ya dora hannunsa a bakinsa yashe “dallah malama
kiyi shiru Meenah batason kuka" gumtse bakinta tayi ya juya zai fita Mai Martaba ya budo qofar
ya shigo yaja ya tsaya da sauri yace “ya subhanallah Rasheed meye hakan?" Murmushi yayi ya
sosa sumarsa yace “ai harkai zan iya kyautarka indai akan Meenah ne" zaro ido Mai Martaba
yayi yace “nidin Rasheed" dariya yayi harda riqe ciki yace “kaidin har wata daraja ce dakai ta
musamman da zatasa naqi fansar dakai akan Meenah?"
Girgiza kai Mai Martaba yayi yace “naji banida ita Sanya kayan naka muje masauki" juyawa yayi
ya kalli Juhud ya tsugunna yace “don Allah mamana kibani aro Allah niba barawo bane zan
dawo miki dasu yau dinnan aidai bake kika sani ba nine nasa kaina nabaki kyautarsu ko?" Miqa
masa tayi yace “aafah Hajiya in kinsan ba tsakani da Allah kika baniba bar kayanki" Dauke qwallah Mai Martaba yayi yace “karbi tsakani da Allah tabaka" yasa hannu ya karba
Yana sawa Yana waqarsa “Meenal Aso kin matar da zuciyata ta mace! ki tausaya karki sani
bangare na yaudara!! Ina gudun duniya!!!"
Da wannan ya fice Mai Martaba ya dubeta yace “likitana ya tabbatar min da zai samu sauqi fah
karki damu" ficewa sukayi suka barta da kallon Kareem dake kwance kamar gawa ta juya itama
ta fice kamar mahaukaciya ta nufi block nasu ta fada gado domin tabawa zuciyarta hutu daga
sabon tashin hankalin daya tunkarota ga Baffa'am dinta a gabanta Amma yakasa ganeta to
waima meye asalin dalilin sukurkucewarsa ne haka Shiba Mai mgn ba Amma surutai rarrara
kamar Wanda ya qone a qeya miqewa tayi tare da cewa “tabbas lkc yayi da zan sakawa Mafi
cancanta Alkhairinsa....."
Tunaninta ne ya tsaya cak da tunawa da Kareem shikuma da yake cikin halin ni yasu dora
hannu tayi akanta daidai lkcn da wayarta tayi ring ta wawurota Ya'isha tace “na dade inason
tsegumta miki watanni biyu baya anga Big Cele a Tanzania to tsoron jagula wannan
dofanannen auren naki da Ya Kareem yasa Mom ta Hanani fada miki wai Kuma yau sainaji me
kankat ankawo mikishi har qasarku"
Cikin kuka tace “shine me gata ko rashin galihu yasa kukaki fadamin labari mafi soyuwa a
duniyata Ya'isha ko ku fada ko karku fada Rana irin wannan zatazo gashi tazo Baffa'am ya
dawo zamana da Kareem ya qare....." Da qaraji Ya'isha ta katseta da cewa bakida hankali ne
karki soma wlh Kareem yafi kowa buqatar taimakonki kinaganin fa a halin da yake" jan zuciya
tayi tace “meye ribata dama uwarsa ta rantse indai na haihu saiya sakeni to kafin ma na haihu
zanbar mata gidan danta nima a dole nake zaune don halacci" magana Ya'isha keson yi mata ta
kashe wayarta can Mom ta kirata tace “idan kin kwantar da hankalinki akwai labari me dadin
dadi da nakeson baki"
Muryarta harta dashe tace “kun boyemin abinda na cancanci nasani Mom meyesa" murmushi
tayi tace “saboda kada muyi mahaukata biyu a dangi shiyasa Meenah kifa nutsu motsi kadan
zakiyi ki fada rami mijinki yafi kowa buqatarki to kibi sannu kada santsi ya debeki"haka Mom ta
rinqa bata kalamai wai ita a dole saita kwantar mata da hankali batasan qara tashin hankalinta
takeyi ba suna kashe wayar Dr Khazeem yazo ta dubeshi yace “ya naki jikin batason hayaniya
hakan yasa tace “naji sauqi so ganin yanayinta yasashi ficewa ta koma ta kwanta kamar bazata
koma asibitin ba saidai taji zucciyarta taqi natsuwa dole ta shirya ta nufi asibitin ga mamakinta
saita isheshi a zaune shida Mai Martaba ta dubesu suka gaisa da Mai Martaba yace “kema kina
buqatar hutu ya kamata ki koma gda ki haihu acan" jinjina kai Kareem yayi yace “dama inada
burin hakan sai na kwanta jinyar nan" da wannan sukaci gaba da tattaunawarsu hankalin
Kareem na kanta Mai Martaba yace “ki koma masaukinku ki huta zan kwana dashi muga abinda
hali zaiyi".......
_Yau fah saidai hqr da qarancin page din_
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/12, 8:08 PM] Oum Hairan: Duban juna Juhud da Kareem sukayi yayi mata qaramin murmushi
ya shafa sajensa tare da nuna mata hanya yace kije ki huta heart kinyi qoqari fah na gde Allah
yabada lada" sunkuyar da kanta tayi tare da daukar wayarta tayi musu Saida safe ta fice ta nufi
masaukin nasu zuciyarta na kaikawo tsakanin qirjinta da duniyar Rasheed, tana zuwa wanka
kawai tayi tayi sallah ta kwanta itakam wannan dare barawon ma kasa satarta yayi gabadaya ta
rasa nutsuwarta batajin daidai saina tunanin Rasheed, da asuba tayi sallah ta zauna tanayima
iyayenta da Rasheed addu'a tare da fatan sauqi da sassauci cikin wannan jarabawa da suka
tsinci kansu a ciki ciwon tabuwar qwaqwalwa a Rasheed abin Babu kyau.
Data tashi da ciwon mara ta tashi hakan yasa bata koma asibitin da wuri ba Saida Tasha
magani ta dan samu relief sannan ta fita ta nufi hospital din a qofar dakin da Kareem yake ta
ishe Rasheed Yana tsaye yana danna waya kamar ance ya dago suka hada ido ya lumshe
idanunsa qirjinsa Yana bugawa itama haka ta matsa gabansa tace “barka da sfy Baffa'am" ja
tayi da baya lkcn daya kece da dariya yace “shegiya ashe kinsan sunana ai Meenah ce take
kirana da wannan sunan" lumshe idonta tayi hawaye ya ciko ijiyarta ta bude akansa ta girgiza
kai tare da cewa “ka manta kowa da komai ka manta kamannin Meenah a zahiri Amma baka
manta sunanta ba Baffa'am ya akayi hakan?"
Yarfa hannu yayi yace “nima to nasani kawai dai kema kinsan idan na kama Wanda ya
kashemin Meenah a gabana saina dirmeshi da alburushi ke barima kiji fah koda yake na daina
kulaki Meenah kishine gareta batason a hadata da wata a mafarki Ina ganinta kullum Kuma fah
tana dan kama dake kadan Amma bakikai kyaunta ba" Mai Martaba ne yajiyo mgnr ta Rasheed
tayi yawa ya leqo yaga ashe shida Meenah ne tasashi a gaba sai hawaye takeyi ya qwala mata
Kira tayi saurin goge hawayen tace “ok ganinan" ta juya zata tafi ya riqota yace “shifa Wannan
mutumin dan raini ne ya rainani yama zaayi Ina mgn da mutum ka kirashi to kaima ka kiyayeni
kafin na qundumeka" zaro ido sukayi dukkansu ya dora hannunsa a bakinsa yace “lalalah ashe
fah sabo nakeyi kayyy ke haihuwa zakiyi me zaki Haifa?"
Ganin batada niyyar tahowa ne Mai Martaba ya fito yaja hannunta yace “idan kika biyewa
wannan saiku raba Rana da dare yanayi miki soki burutsunsa" sosai sautin kukanta yake fita
batare da tasan kalmar ta subuce ba tace “ta Ina zan fara taimakonsa?"
Dubanta Kareem yayi ya kawar dakai yanajin wani abu nayi masa yawo a qirji da sauri ta share
zancen da cewa “Mai Martaba ya jikin nasa?" A gajarce yace da sauqi sosai dama lkcn hutunsa
yayi zamu tafi gabadaya daku saboda dukkanku kuna buqatar kulawa" jinjina kai tayi tabbas
tana buqatar kulawa sosai Kuma taji dadin hakan domin itace damarta ta fuzgo yancinta
zuciyarta na raya mata dolene Kuma wajibi akanta ta qwaci kanta domin Baffa'am dinta.
Kwanaki biyu suka qara a asibitin aka sallamesu cikin kwanakin ta fahimci abubuwa da yawa
game da Baffa'am dinta hakanan wani lkcn sai yayi shiru yaqi yima kowa mgn ya rinqa kallon
kowa daidai idan Mai Martaba ya cika damunsa saiya tashi kawai yakoma jikin tagar dakin yana
hango waje yana cewa “kawai don anga Aminatuh batada gata sai a takurawa mijinta nifa idan
kunsan takurawa na Meenah nazakuyi to kubarni ko da qafa zan koma Tanzania harda Sudan
naje naci gaba da gadin kabarin Meenah ta"
Zantukan nasa a sukurkutacce suke ba kowa ke fahimtarsa ba Amma ita tana gane wani abu
cikin maganganunsa ta fahimci kamar akwai hoton abinda yake masa yawo a kwanya da yake
bashi gizon mutuwarta tunda dukkan wata kalma tasa mutuwa yake cewa Meenansa tayi to ya
akayi haka?" Abin da yafi komai bata al'ajabi ita daya yafi yiwa wannan soki burutsun zantukan
nasa marasa kan gado inda ta fahimci Kareem ko kadan bayason yaga Rasheed ya fiye mata
mgn shi kansa Mai martaba yana nuna alamun hakan wannan take sanyata cikin jimami domin
da tazo asibitin kafin sallamarsu zai tareta da cewa yawwa qawata zo na baki lbrn Meenah a
duk sanda ya fadi haka sai takanga fuskar Kareem tayi duhu inda ita Kuma takan shiga tunani
da zullumin wannan lamari.
Kwana uku suka qara komansu ya kammala suka dauki hanyar 9ja ko a cikin jirgin da Rasheed
ya fara mata mgn sai Mai Martaba ya katseshi da cewa kai wai meye yake damunka ne
Rasheed shikuma gashi ko yayi shiru baa minti biyar zai sake zungurota yace mata “yawwa
qawata akai kaza akai kaza" haka Mai martaba zai sake mata tsawa itadai ta kasa jurewa
ganinta wannan ai takura dan adam ne Kuma ma meye don ya zabeta matsayin abokiyar
hirarsa aikuwa tayi kicin kicin da fuska ta juya gabadaya gareshi ta kamo hannunsa tace
“labarin me kakeso ka bani Baffa'am?" Dago kansa yayi da yasa cikin cinyarsa ya dubi Mai
Martaba da Kareem yace “ai dama batun yanzu ba na fahimci wadannan Gayun basasona da
qawance dake Kuma na daina kulasu"
Murmushi tayi tace “to Kuma meye na kukan aini Inasonka da qawancen...." Ihu yayi yace “don
Allah da gaske?" Daga masa kai tayi yace “wayyoh dadi zan baki alawar madarar dana siyawa
Meenah zankai mata lahira idan munje gda" murmushi tayi me hade da hawaye tace “Baffa'am
ai wanda ya mutu baici baisha baya mgn fah" hannunsa yayi a baki yace “dallah ware sunguma
malohuwa ita Meenah an fada miki irin mutuwar kowa tayi ne ai ita kullum tare muke kwana da
asuba saita bace bana qara ganinta sai wani daren Kuma in fada miki kullum cemin takeyi
Inasonka Baffa'am dina bazan taba rayuwar farin ciki ba tare dakai ba kaji a ranka ko bana
duniyarka to Ina fadar zuciyarka daka bani nini kadai....."ba itaba dukkansu Saida suka kalleshi
sak muryar Juhud yayi amfani da ita wajen furucin tayi dariya sosai tace “Kana bani nishadi....."
Wata tsawa Kareem ya daka mata yace “yaci gaba da baki nishadi zan datse duk wata alaqa
dake tsakaninku kuwa muga qaryar baki nishadi" dama a qufule take dashi da Mai Martaba ta
kuwa hayayyaqo masa tace “zaka iya Kuma? Kanajin kanada qumaji da qwarin gwiwar raba
hanta da jini ne? To karka soma shidin bangare ne na rayuwata da bashida tamka wlh a
duniyata yafi iyayena domin na rasasu tun bansan dadinsu ba shine ya mayemin gurbinsu ya
zamemin uwa uba Yaya qani aboki qawa sannan ya........" Dauketa da mari taji anyi ta dafe
gurin da sauri kafin ta kanta ya gama juyawa taji qarar wani Marin ta bude idanunta da sauri
taga Kareem dafe da kunci Mai Martaba a tsakiyarsu Rasheed sai huci yakeyi yana hanqoro so
yake ya samu dama ya damqi Kareem Mai Martaba ya hanashi yace “kasheka zanyi in kashe
banza wlh don akan qawata Babu ruwana dakai qanina ne inma yayana ne saina aikaka inda
na aika Wanda ya kashemin Meenah"
Zama Kareem yayi Yana huci Yana cije lebe shima Rasheed ya zauna yace “saqagon banza
dashi dabai iya komai ba sai cin zali" shidai bai kulashi ba don ya fahimci idan yaci gaba da
kulashi mahaukata biyu zaayi Amma yaci alwashin ta qarfin tsiya saiya raba Meenah dashi
suna sauka a Kano Lado driver yazo ya daukesu suka nufi Katsina Mai Martaba motarsa daban
shida Rasheed shikuma shida Meenah ko a tafiyar babu me cewa wani qala har suka isa
Katsinan a yanda Mai Martaba ya tsara dole haka sukabi gdan sarautar suka nufa anan yace su
zauna harta haihu.
Yana qunci da cin magani suka shiga cikin gdan kai tsaye ya figi hannunta suka shige part din
nasa ya kulle qofar ya saki hannunta Yana huci ta juya ta nufi kujera ta zauna ko kallonsa batayi
ba ya gama kumburinsa ya nufi dakin baccinsa ta tabe baki a ranta tace “ka kuwa hadu da aiki"
batabi ta kansa ba itama ta shige dayan bangaren tayi wanka ta bude Jakarta ta dauki doguwar
riga ta sanya tasa mayafinta ta sulale tabar part din ta nufi cikin gdan ta matsu taga Mom tana
shiga falon Mom ta taso da gudu ta tareta da cewa “oyoyo oyoyo Aminah ta" dariya tayi suka
zube a kujera tace “ashe kema kinyi kewata Mom Ina Sarki" juyawa tayi inda suke zaune shida
babansa tace “au shine bazaka kulani ba" dariya yayi ya taso ya fado jikinta yace “kin tafi kin
barni inata kewanki Dad dina ya dawo inaso kizo ki ganshi kullum na saci wayan Mom na kiraki
sai najita a kashe"
Murmushi tayi me hade da hawaye tace “Allah Sarki My Son kana Raina ya kakeji game da
dawowar Dad dinka?" Kwantar dakai yayi jikinta yace “happy Mom kinsan me Dad dina fah
bashida lfy baya gane kowa harni" share masa hawayensa tayi tace “ka daina damuwa zai
ganeka zansa ya ganeka kaji" daganta kai yayi Rasheed dake zaune yace “kuma itace qawata
da nake baki lbr Mom Kinga ashema tasanku tasan wannan yaron da yaketa cemin Dad" tare
suka share hawaye da Mom Mom tace “hakanma mun gode Allah Meenah wai a hakan fah an
samu sauqi farkon lkcn da aka tsintoshi abin baa cewa komai sai gdyr Allah Amma yanzu yaji
dama"
Jinjina kai tayi ya taso ya dawo kusa da ita tayi saurin sanya Sarki a tsakiyarsu yace “dariya ma
kike bani" dukkansu sukayi dariya Daidai lkcn da Addah Abulle ta fito daga sashin Mai Martaba
idanunta akan Meenah sukayi kallon kallo taja baya da sauri tace “na shiga uku ni Zainabu wato
shegen yaron nan da yace sun zubar da cikinga ashe qarya yakeyi" murmushi Meenah tayi
zuwa yanzu zuciyarta ta fara tsikewa tace “sannu fah Addah ya gda mun sameku lfy?" Wata
uwar qwafa tayi ta nufi dakinta fuuuuu Meenah ta tabe baki ta mayar