Showing 63001 words to 66000 words out of 99941 words
Chapter 22 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf
WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/6, 10:48 AM] Oum Hairan: *0029* A gdan Ya'isha suka shantake sunata fira Basu suka baro
gdanba sai gefin magrib suna shiga gdan gaban Juhud ya fadi batare da tasan dalili ba suka
nufi parlourn da sallamarsu a tsaitsaye suka tarar da Addah Abulle da Fadila Juhud na Shirin
mgn taji an shaqeta ta baya batare da sanin waye ba suka rinqa kokawa daqyar Mom da
Muntaz suka rabasu Fadila na huci ta nuna Juhud da ta zubanta ido tace “muguwa azzaluma Ni
dama tunda akace kinje barka nasan ba Alkhairi ne yakaiki ba ace daga zuwanki jaririya ta
kama cuta kwana uku da haihuwarta batayi ba sai yanzu da kikaje to wlh ki sakar Mana kurwar
yarinya ko mu aikaki lahira shegiya baqar kadara"
Cafewa Addah Abulle tayi da cewa “to waima meye yakaita barkar waye yace Yana buqatar
barkarta gsky nikam wannan lamarin na gdannan ya isheni Abu ya wucce kan wadanda suka
jajuboki ya dawo kanmu shekara uku dayin auren nan baa haihu ba shine daga kinji an haihu
zaki lashe musu ya tab wlh bazai yuwu ba dole ma Mai Martaba ya zaba a gdannan ko mu da
muke dolensa ko Kuma ita da suka liqawa mutane" tunda suka fara mgn ta fahimci inda suka
dosa jikinta yake rawa hawaye ya kasa tsayawa a idanunta mgn takeson yi Amma bakinta ya
sarqe zuciyarta wani zafi takeyi hakanan takejin a ranta yau ko zata fita a kasheta sai tabar
gidan lamarin ya fara wucce yanda zuciyarta zata dauka. Juyawa tayi ta shiga dakin da take
taja akwatu ta fara hade takardunta tana wani irin kuka me ciwo itakam tagaji da wannan
quntattaciyar rayuwar shekaru ashirin da biyar na rayuwarta ta qaresu a qunci shekaru tara
Mom na hadiyar baqin ciki akanta meye yasa bazata gushe ba kota samu salama da sanyin
ruhi suma masoyanta su samu?
Tanayi tana jan zuciya tana tunano yanzu hakanan zata fice tabar gudan jininta daya tal a
duniya meye makomar rayuwar Sarki idan ta tafi ta barsa? Dagowa tayi bayan ta gama hada
kayan ta zuge ZIP din trolley din ta miqe ta dauki hijjab dinta ta zura taja akwatin takai hannunta
zata bude qofar Mom ta bude ta shigo idanunta na tsiyayar da hawaye tace “duk wani abu daya
kamata nayi miki Meenah nayi miki domin Allah meye yasa qaramin Abu yakesaki jin tafiya
kibarni shine mafita? Me kikeso nacewa Rasheed idan Allah ya bayyanashi yaji abinda kika
aikata? Haba Meenah nidai Ina ganin indai kika yanke barina to tabbas baki biyani haqqina ba
Kuma kin basu damar yimin dariya ne......."
Wani kuka ta saki me ciwo tare da durqushewa ta kifa kanta jikin akwatin tanayinsa babu furuci
kalma batada ita a bakinta da zata iya furtawa zama Mom tayi tana bata baki tana rarrashinta
Amma kamar tana zugata, aka bude qofar aka shigo Mai Martaba ne ya shigo fuskarsa Babu
alamun wasa yace “ke Aisha tashi ki bani guri inason mgn da ita" miqewa Mom tayi ta fita tana
kallon Meenah data dunqule tanata aikin kuka ta girgiza kai ta fice daga dakin ya nemi guri ya
zauna Yana nazarin yarinyar da yanda duk jikinta ke rawa jikinsa yayi sanyi shi kansa yanajin
kunyar kansa irin biyayyar da yarinyar takeyi masa bata cancanci haka daga gareshi ba ta
daukeshi kamar mahaifi tanayi masa biyayya fiye da yanda yayan daya Haifa sukeyi masa to
waima meye yasa yake yarda da jita jita akanta ne?"
Gyaran murya yayi yace “ina kike Shirin tafiya yanzu?" Cikin kuka tace “inda ubangiji ya kaini
don girman Allah karka hanani Mai Martaba na gaji wlh na gaji da qaddarorin nan masu wahalar
dauka inaji a jikina banida wani rabo na farin ciki a rayuwata Mai Martaba idan ka hanani zan
rasa kaina zuciyata zata buga....." Jinjina kai yayi cike da tausayawa yace “meye yasa kika
yanke wannan hukuncin?" Dagowa tayi idanunta akansa bakinta ba rawa tace “Baffa'am shine
mutum na farko dayayimin gata ya zabi farin cikina akan komansa Mom ta dora sunci baqin ciki
akaina sunama kan ci wlh koda bana tare da mijina inaji a jikina duk inda yake hankalinsa yana
gareni Mai Martaba bazan zama silar bacewar da na zama silar macewar uwa ba idan naci
gaba da zama da Mom baqin cikin abinda ke faruwa Dani zai iya taba tata rayuwar nikam na
riga na zaba na yankewa kauna da samun wani jin dadin rayuwa kubarni naje na rayuwa ni
kadai abinda kukayi a baya na gde....."
Daganta hannu yayi yaja zuciya yace “naji Meenah ki cire wannan tunanin a ranki Babu inda
zakije kinanan" miqewa yayi ya fita daga dakin yana fita ta koma ta kwantar da kanta jikin gado
tana wani kuka me ciwo, tana jiyo hayaniya da fadan Mai Martaba a falo saidai bata fahimtar
meye yake cewa sama sama taji yana cewa “ni na haifi Rasheed na haifi Kareem dukkansu
ikona ne duk da qaddara tasa Meenah bata zama mallakin Kareem a farko ba hakan bazai
zama hujja ta cin mutumcinta ba wlh tallahi Zainab duk ranar da wani abu makamancin wannan
ya Kuma faruwa zakisha mamaki na Kuma babu wanda ya isa hanani zartar da abinda nayi
niyyah a gobe juma'a zan yanke abinda nayi niyyah kai nama fasa yau dinnan idan da Wanda
ya isa ya Hana"
Bata fahimci komai ba Amma sosai taji wata faduwar gaba ta darsar mata ta miqe ta shiga
bathroom ta watsa ruwa ta dawo ta kwanta damuwa tasa zazzabinta na qa'ida ya dirar mata
wanda likitoci sukayi ittifaqin zai iya haifar mata da ciwon zuciya saboda Yana yawan kumbura
zuciyar tata. Bacci ne ya dan dauketa sama sama kasantuwar ba sallah zatayi ba tanaji ana Kiran sallar Isha
a masallacin Fada ta sake gyara kwanciyarta bacci me nauyi ya dauketa batasan meye yake
faruwa ba sai ji tayi ana yiwa qofar bugu na hauka ta miqe zunbur tana son tantance dalilin
bugun taji muryar Addah Abulle tana cewa “billahil lazi la'ilaha illahuwa indai nice na haifi
Kareem bazai taba zama da wannan tsinanniyar yarinyar ba matsayin mata wlh Allah saidai
idan na kasheta nima a kasheni"
Muryar Mai Martaba taji Yana cewa “bazama takai ga kisan ba kizo ke ki fita a gdannan ki tafi
gdan naki uban aure ne na daurashi Babu dalilin fasashi" bude qofar taji anyi ta sake zabura ta
zubawa me shigowar ido Kareem ne ya shigo idanunsa akanta itanma shi take kallo ido cikin
ido ya mayar da qofar ya rufe ya nufota taja baya da sauri yaja ya tsaya Yana kallonta ya dan
saki fuskarsa batare data tsammata ba taga wasu hawaye sun kwaranyo daga idanunsa ya
daga hannu sama yace “Alhmdllh Meenah duk da banyi tsammanin zuwan wannan lkc da wuri
ba Ina tayamu murnar samun kanmu a sabuwar rayuwa matsayin da naso samunsa a farko
ubangiji bai amince ba wato ma'aurata.........."
Ai bai rufe bakinsa ba ya tsinceta a qasa warwas yayi kukan kura ya isa gareta Yana jijjigata
Addah Abulle ta danno qofar tayo kansu da wuqa tsirara a hannunta ya miqe da sauri ya tareta
Mai Martaba da Muntaz suka tayashi riqeta ya damqe kaifin wuqar da hannunsa tana wani kuka
me cin zuciya tana cewa “wlh saina kasheta mayya cikin zuri'a ta bazan taba lamunta ba......"
Abinda Mai Martaba baitaba yiba yau shine yayi mata allurar yan maza ta motsa abinka da
tsohon soja baisan sanda ya saketa ba yayi bal da ita taje ta daki gini ta dawo qasa tana
qoqarin tashi ya sake nufarta Kareem da hannunsa keta zubar jini saboda riqon da yayima
wuqar ya nufeshi da sauri shida Muntaz suka riqeshi daidai lkcn da Arman ya shigo shima yayi
kan Mai Martaba Mom ce da Salman sukayi ta Juhud suka kimkimeta Kareem ya saki Mai
Martaba har yanzu kuka yakeyi yace “don Allah Mai Martaba kada kayi abinda kayi niyya ka
qyaleta tayi duk abinda da tayi niyya aurena da Meenah ne Allah ya riga ya daurashi babu
abinda zai kwanceshi saidai mutuwa ko qaddarar data raba auren Rasheed da ita"
Fita yayi da sauri ya shiga motarsa yabi bayan tasu Mom suka nufi asibiti sukayi emergency da
ita likitoci suka rufu akanta numfashinta suketa qoqarin saqalowa abin ya gagara faduwar da
tayi taja mata shiga doguwar suma, ranar daga Kareem harsu mom Babu Wanda ya koma gda
anan suka kwana gurinta gabadaya ya rude hankalinsa yaqi kwanciya Yama manta da lissafin
yar jaririyar yarsa da take asibitin itama ta Juhud din kawai yakeyi Muntaz ya tafi gda suka dawo
da Hamida da Mai Martaba Addah Abulle bata gdan hankali ma baya kanta balle asan Ina ta
nufa.
Mom da Hamida ke jinyarta tsayin kwanakin biyar batasan waye akanta ba Kareem ya canza
mata asibiti yakai uku qarshe Asibitin Mal Aminu Kano ya mayar da ita acanne suka samu ta
fara motsa gabbanta sai lkcn ya samu nutsuwar tunawa da iyalinsa har zuciyarsa nutsuwarsa ta
rabasa da tunanin komai sai lfyr Meenah babban tashin hankalinsa da likita yace masa
zuciyarta ce take barazanar daina aiki saboda ta cunkusa mata damuwar da tafi qarfinta
tunaninsa ta yanda zai fara nasa aikin ya goge mata duk wata damuwa dake buwayar
rayuwarta ya sanyata farin ciki kamar yanda ya shirya yi a farko Allah bai amince masa ba
burinsa bai wucce Meenah ba cikin duniyarsa gata ya sameta Amma Kuma wasu abubuwan
sun danni soyayyarta gareshi tsabar qin da takeyi masa ne yasata shiga wannan yanayin dajin
cewa shine matsayin mijinta ko meye dalili?
Wadannan tunane²n sune suka sanyashi ramewa cikin kwanaki biyar din.
Ranar kwana biyar din ranar ta kama sunan Matarsa hakanan ya nufi Katsinan bashi da wani
kuzari dake yasan dama ba taron sunan akeyi ba har zuwa lkcn Zainab sunan yarinyar kenan
sunan mahaifiyarsa yasa mata tana asibiti ciwon gendis yayi mata kamun gaske anyi mata
juyen jini Amma duk da haka taqi lfy inda likitoci suka tabbatar da a cikin mahaifiyarta ta samu
matsala Amma su sun dauki alhakin ciwon kacokan sun dorawa Meenah musamman su Dada
Hanne da dangin Zahrah da sukayi tsalle suka dire suka dauke yarsu cewa bazata zauna da
Meenah ba shidai daya yakabo yaje ta qare masa,
Bai damu ba koda yaje gdan nasa ya tarar dashi a kulle domin ya riga ya shiryawa zuwan
wannan Rana a baqin kishi irin na Zahrah ba Meenah data tsans fiye da kowa a duniya ba ko
wacce mace ya auro sai anyi wannan rikicin shiyasa baisa abin a ransa ba taje tayita zamanta a
gdannasu idan ta gaji ta dawo. Kwanan Meenah bakwai a Kano ta bude idanunta tana kallon
kowa daidai a lkcn tunaninta bai dawo ba bama kowa take ganewa ba hakanan ta rinqa rarraba
ido kan mutane.
Mom sai sannu take jera mata tana binta da kallo da la'asar Kareem ya iso asibitin shida Ya'isha
tun daga harabar asibitin ya hadu da Lado drivern Mai Martaba yayi masa albishir din Juhud
wani farin ciki da murna daya dade baiyi irinsu ba suka cika zuciyarsa har gudun motarsa ya
qara don ya isa gareta yayi parking baikai ga rufe motar ba ya nufi ciki sai Ya'isha ce ta rufe
masa motar cikin tausayinsa ko lkcn da Meenah take matsayin matar Rasheed Kareem baya
zama cikin nutsuwa muddin tana guri Allah ya jarabceshi da qaunarta gashi Kuma yanzu tasan
ba qaramin rikici ya saukowa kansa ba don tabbas Meenan da ba itace yanzu ba batajin zai
samu kanta da sauqi duk wannan rawar qafar da yakeyi akanta ba gani zatayi ba tunda bashine
a zuciyarta ba hasali ma ita a lissafinta ma Babu aure.
Yana shiga bai saurari kowa ba ya nufi gadon da take kwance idanunta a lumshe yaja wata
ajiyar zuciya tare da binta da kallo me nuna tsantsar qauna da kulawa yace “Aminatuh" jin
saukar muryarsa tayi kamar muryar Rasheed ta kuwa juyo da sauri tare da bude idanunta ta
saukesu akansa yanayi mata gizo cancanzawa yakeyi daga Kareem ya koma Rasheed ta kasa
gane taqamaiman waye a gabanta.
Tun farkawarta bata iyayin furuci ba sai yanzu da bakinta ya bude da furta “Abdulrasheed....."
Daga haka ta sake lumshe idanunta ta kwantar da kanta a pillow kuka me ciwo ya qwace mata
daya Sanya Mom dake shigowa nufota da sauri tace “Subhanallahi waike yanzu Aminatuh
bazaki daina Sanya damuwar nan a ranki ba kenan kullum ke kenan cikin jinya" wata ajiyar
zuciya me qarfi Kareem ya sauke ya nemi guri ya zauna gumi na karyo masa Yana sharcewa
Ya'isha dake shigowa tace “ya Kareem motar taka baka rufeta ba ka barota" shafa sumarsa yayi
yace “wlh hankali nane baa jikina ba ince kin rufe" dagansa kai tayi ta nufi gadon da Meenah ke
kwance ta riqo hannunta tace “amaryar Ya Kareem sunqi Allah yaso meye yayi zafi da doguwar
jinya haka?" Zame hannunta tayi a na Ya'isha ta sake gyara kwanciyarta taci gaba da jan
zuciya abubuwan da suka sabbaba mata ciwon suna dawo mata a fili tace “Aure, Ni Mai
Martaba Ya Kareem Innanillahi wa Inna ilaihir raji'un Allahumma ajirni fih musibati wlh banaso
don Allah ku taimakeni ku rabani dash.........
_Nasani wannan page din ba kowa zatayima dadi ba so Amma a babin qaddara wannan daidai
ne shi ubangiji Yana zartar da hukuncin da yake daidai batare da la'akari da abinda Wanda ya
zartar da hukuncin akansa zai nazartawa zuciyarsa ba kada ku manta matar mutum kabarinsa
Kuma shi rabo ajali ne yakanyi kisa ma idan qarfinsa yakai._ _So kada kuga laifin alqalamina haka abin yake kamar yanda kuka ganshi a rubuce kada ki
manta 50% is true life story._
Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 viaí ½í±‰í ¼í¿¼ 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank
Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...
Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....
*Oum Hairan*
[8/6, 9:00 PM] Oum Hairan: *0030* Miqewa Kareem yayi ya fice daga dakin ya koma waje ya
rafsa tagumi jikinsa sai tsuma yakeyi Yana tausayin kansa Amma yafi tausayin Meenah saboda
tafisa shiga damuwa ya jima zaune a gurin kafin likitan ya iso suka shiga tare likitan ya dubata
ya sake bata kulawa ya fice daga dakin ya dubi Juhud datake zaune take shan tea yace mata
“sannu" bata ko dubesa ba ya nemi guri ya zauna Suna taba hira lkc zuwa lkc suna taba hira da
Ya'isha Mom tana Sanya musu baki itako ko kallo bai isheta ba hasali ma tunda ya zauna
takejin wani qunci aranta ji takeyi kamar ta fice daga dakin bata son ganinsa.
Kwanciya tayi taci gaba da saqa da warwara a ranta sai yamma Ya'isha tace zata tafi mijinta
yazo daukanta sukayi sallama suka tafi Mom ta tafi rakasu ya taso ya matso jikin gadon yace
“duk da nasan ni mai laifine a gurinki Meenah Allah ya sani inasonki tun kafin yanzu Amma
bantaba yimiki fatan ki dawo gareni ba Allah shine ya tsara hakan saboda haka na karba Kuma
nayi masa gdy kema inaso ki karba kiyi masa gdy......" Miqewa tayi zaune zuciyarta na tafasa
tace “akanme zanyi gdy akan abinda ba zabina ba bankuma nema ba? Why da zakace dole
saina karbeka? Kareem da zaka manta dani ka fice cikin rayuwata da mun taimaki kanmu wlh
banyi farin ciki da samunka matsayin miji ba kada kaji a ranka na karbeka bazan taba karbarka
ba Rasheed shine zabina shine rayuwata......"
Hannunsa ya dora bakinta yace “stop Meenah ya isheki don Allah kada ki fasamin zuciya da
kalamanki kiji a ranki wannan bayin kaina bane yin Allah ne..... Wayarsa ce tayi ring ya zaro a
aljihunsa number Zahrah ce yayi kamar ya kashe saidai zuciyarsa ta raya masa ya daga qila
wani abune Important yasata kiransa danna wayar yayi ya Kara a kunnensa ta cikin wayar
Meenah take jiyo gunjin kukanta tana cewa “Allah ya isa tsakanina dakai Kareem ka cutar dani
kaine wlh kaine sila tunda kaine ka rakitomin ita cikin rayuwata harta cutar dani, na dauki ciki
watanni tara na Haifa matarka ta kashemin yata wlh bazan yarda ba kaji na rantse maka
wayyoh Allah na Zainab ta mutu Aminah ta lashemin yata......"
Qit ya kashe wayar idanunsa ya ciko da hawaye ya dubi Juhud data zubawa TV idanu a
zahirinta ba TV take kallo ba kalaman na Zahrah ne sukeyi mata yawo a kwanya yace “kinji
sauqi likita yace zaki iya komawa gida zanyiwa Mom mgn ta shirya mu tafi Zainab ce ta rasu...."
Bata ko kallesa ba taci gaba da wasa da yatsunta yaja numfashi ya fice a dakin suka hade da
Mom a reception ya tsaya Yana dubanta da jajayen idanunsa da damuwa biyu tasa suka kada
tace “yanzu ake fadamin Zainab ta rasu ya kamata kazo ka tafi kaima tunda jikin nata da sauqi"
girgiza kai yayi yace “ban yarda da hankalin Meenah ba Mom zata iyayin komai Ina tsoron kada
na tafi tayi tunanin guduwa tabarni wlh mutuwa zanyi a wannan karon Mom ke shaida ce na
wahala a karon farko dana rasata don Allah ki tausheta ta soni koda kwatan Wanda nakeyi
matane ni basai yakai rabi ba inasonta a haka"
Murmushi Mom tayi me dauke da hawaye ta dafa kansa tace “Abdulkareem to Banda abinka
Meenah yanzu ai taka ce kasan dai ba cikakkiyar lfy gareka ba don Allah ka rage damuwa da
duk abinda zatayi zai hucce kasan kaima dole zaa fuskanci wannan qalubalen tunda ba ita taga
damar auren nan ba Ni kaina