Showing 96001 words to 99000 words out of 99941 words

Chapter 33 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1514

tayi tana qissima ta yanda zata fara rayuwa cikin zulumi sai ta dauki wayarta kamar
ta kira Kumbo Hami ta fada mata sai Kuma taga kamar bai dace ba haka ta rinqa saqawa da

warwarewa har dare ya fara nisa ta shiga tayi wanka ta dawo ta kwanta abinka da farar fata
idanunta har sun kumbura koda Jummai ta kawo mata Muneefah cewa tayi taje su kwanta tare
ganin kwanciyar bazata kaita bane tasata tashi ta sake alwala ta dauki qur'ani tana karantawa
tana hawaye. Shigowa yayi dakin mamaki ya cikashi jin shassheqarta ya kunna globe din da sauri yaganta
rungume da qur'ani tana rera kukanta ya qarasa gareta ya zare qur'anin ya aje ya dagota ya
mannata da jikinsa yace “meye kikewa kuka Meenah kinsani ko a baya bana qaunar kuka ko?"
Maqalqaleshi tayi tana qarawa kukanta gunji tace “ni don Allah kace ka fasa tafiya kabarni wlh
zanyi maka duk abinda kakeso" dariya tabashi sosai ya shafa kanta yace “to na fasa saime
Kuma?" Rungumeshi tayi tana ajiyar zuciya tace “shikenan idan sun matsa ka bar musu aikin
kawai kaji?"




Daganta kai yayi ta shafa sumarsa tace “na gode Baffa'am...." Janta yayi suka zube a gado ya
fara luguiguiceta ta saki masa jiki kuwa suka raya Daren da wata irin azababbiyar qauna me
narkar da zuciya sun gurji juna sosai tanajin sabuwar qaunarsa na ratsata, tun daga wannan
dare komansu ya fara saituwa cikin ruwan sanyi da dabara ya shawo kanta riritashi takeyi
kamar qwai bata yarda ta tabashi saboda karma yaji yanason tafiya yabarta shima mugun
tattalinta yakeyi Abu daya yaso Basu damuwa tanason zuwa Daura watanni sun fara nisa
tanason taje taga Mom Amma fir yaqi tun tana lallabashi har Saida suka daina mgn ta daina
kulashi da ya matsa mata sai ta kama kuka tace don yaga batada galibi ne batada uwa bata da
uba shiyasa yakeson ya nuna mata Mom ba ita ta haifeta ba.
Sosai ya fahimci Meenah yar sharri ce ta qaro wulaqanci dole ya shiryanta tafiya Katsina
aikuwa tayita murna shikuma yayita kumburi zuciyarsa na basa kawai so take taje taga uwar
mijinta ta tuno da ubar yarta Kareem idan zuciya ta raya masa haka sai kawai yaji koma me
zatayi tayi bazai barta ba ranar data shirya tafi tun asuba take shiri yayi kwanciyarsa yaqi fitowa
harta shirya ta shirya Muneefah ta shiga dakin nasa da sallama ya Amsa mata a ciki ta zauna
tace “Baby na shirya banga kana shiri ba Kuma kace kaine zaka kaimu airport" iska ya furzar
yayi miqa yace “ina zakije ne?" Da sauri ta dubesa tace “Ban fahimta ba Daura Mana" hade rai
yayi yace ba yau ba..." Ai baigama rufe bakinsa ba ta miqe tana cewa “haba don Allah Ya
Rasheed kada kayimin haka wlh na fadawa su Mom dasu Ya'isha yau zanzo har Sarki junior fah
na fadawa yanata murna hatta Amrah da Addah Abulle sunata murna zasuga Muneefah....." A
fusace yace “shut-up Meenah nace bazakije ba yau ki fita ki bani guri dama nasan dokinki kije
kiyi hirar tsohon mijinki kiji dadi ko? To bazaki ba idan kika matsamin ma wlh zan iya cewa keda
Daura har abada muga ta tsiya"




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank

Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/29, 8:00 PM] Oum Hairan: Tsayawa tayi ta zuba masa idanu tanajin ciwon yanda yake
canzawa duk motsinta fassara hadiye wani abu tayi me daci ta juya ta fice daga dakin ta koma
nata ta hade kai da gwiwa tanajin baqin cikin wannan wulaqancin na Rasheed Shi komansa
baya aikatashi da lissafi kawai abinda yayi masa dadi shine yake aikatawa, kwanciya tayi
tanajin Muneefah na buganta qofar taqi budewa tasan abinda zatayi masa kawai ta bata masa
rai kenan.
Ilai kuwa yarinyar ta riqa kuka ya taso ya fito ya isheta a qofar dakin taqi bude mata ya dauketa
ya juya ya shiga dakinsa yasa kayansa suka fice so take y kulata bakuma zai kulata dinba, tun
tana tsammanin dawowarsu harta hqr ta tashi ta shiga kitchen ta dora musu abincin Rana sai
daya da rabi ta gama tayi wanka tayi sallah ta dawo parlour Kiran Mom ya shigo kasa dagawa
tayi saboda takaici meye ma zatace mata? Da wannan tayi qarfin halin daga wayar suka gaisa
tace “munjiku shiru" kukan da take hadiyewa ne ya kwace mata tace “mom zamuzo Amma ba
yau ba" tana fadin haka ta sauke wayar a kunnenta ta kwanta taci gaba da karatunta.
Sai biyu da rabi suka shigo da tarkacen kayan wasansu ya aje yarinyar ya zauna a gefenta
daga kallo daya bata qara kallonsa ba ya sanya hannunsa ya dage rigarta da sigar zolaya yace
“ 4 mouths kinqi karbar ajiyata sai zuba miki vitamin nakeyi kina shanyewa Babu wani good
result" sake dauke kanta tayi daga gareshi tama fara yunqurin miqewa ya saqaleta ta baya ya
miqe ya hadeta da jikinsa yace “meye kuma ya faru My Meenah Baffa'am dinki baison fushinki
kin sani"





Tureshi tayi tace “ai dama nasan bakaso Baffa'am ka rabu dani please kada kasa na fada maka
mgnr da ubangiji zaiyi fushi dani" qwacewa takeson yi yaqi sakinta saima qwalawa Jummai Kira
da yayi yace ta dauki Muneefah, itadai kunya kamar ta nutse shikam Babu kunya ya dagata cak
ya nufi cikin dakin baccinsa da ita ya cillata a gado ya bita ya hade bakinsu tana kuka tana
tureshi yaqi turuwa saima zuge zip na rigarta da yayi ya cafki boobs dinta ta rintse idonta bataso
yake taba mata nono kwana biyunnan zafi sukeyi mata gashi shi Kuma mayensu ne tanaji ya

dora bakinsa a kuncinta yana tsotse hawayen har ya gangaro qasa ya sanya harshensa
tsakiyar qirjinta Yana lasa zuwa kan nipples dinta, takasa qwatar kanta dole ta hqr tanajinsa
yayita karakaina a sassan jikinta Yana bawa kansa nishadi taqi kulashi taqi tayashi sarai yasan
yau dama tunda ya tabata itama saita tabashi shiyasa bai damu ba yayi abinda zaiyi ta kwanta
masa kamar gawa ya gama ya sauka taja bargo ta rufe jikinta, waishi me zuciya ya rinqa jan
tsaki tanajinsa tayi banza dashi yaje yayo wanka ya dawo ya dubeta yace “ki shirya jirgin biyar
zamu bi zuwa Katsina"
Banza tayi masa tama sake gyara kwanciyarta ransa ya sosu sosai yace “wai meye yasa kika
rainani mgn fah nakeyi miki Meenah" dagowa tayi ta watsansa wani matsiyacin kallo tace
“bazani bane nakeso ka gane" murmushi yayi ya juya zai fice Saida yaje bakin qofa yace “ni
nake baki umarni kike cewa bazakiyi ba ko Meenah lallai kin kawo qarfi saura qiris ki fara
dukana" baiyi tunanin zatayi mgn ba yaji tace “idan iyakar dukan ma zan tsaya ai da sauqi"




Tsayawa yayi kamar zai dawo sai Kuma taga yayi gaba taja tsaki ta tashi tayi wanka ta koma ta
kwanta har hudu da rabi Yana jiranta a parlourn baiji motsinta ba ganin lkc nata shudewa Babu
ita yasashi nufar dakin a fusace ya isheta kwance abinta ya tsaya akanta Yana kallonta taji
shigowarsa tayi masa banza takaici ya cikasa yace “kefa nake jira Tun dazu nayiwa Hadi mgn
yanacan yana jiranmu" tabe baki tayi ta miqe tace “Allah ya tsare hanya ku gaishesu" zubanta
ido yayi Yana qanqancesu cike da bala'i yace “kada ki fusata zuciyata ki tashi nace kafin ranki
ya baci" murmushi tayi ta miqe tace “aini Raina ya dade da baci saidai naka ya baci zuwa ne
bazani ba duk abinda zakayi kayi" duk yanda yake tunanin zata sauko taqi saurararsa ya rasa
yanda zaiyi da ita baitaba tunanin kafiyarta takai hakanba ganin wankin hula na neman kaisu
dare ya kira Kumbo Hami ya fada mata abinda yake faruwa ta Kira wayarta tanata yimata fada
kan dole ta fito suka tafi har sukaje Babu me yiwa wani mgn.




Sosai kowa yayi mamakin zuwan nasu musamman Mom da ta gama fidda rai murna gurinsu
baa cewa koma suna hutawa ana gama gaisawa ya dubeta yace su tafi gdansu shi ya gaji da
dawo da safe, Babu yanda ta iya haka suka tafi Mom tanata Sanya musu albarka duk yanda
Meenah taso ta gaisa da Addah Abulle hanata yayi sai Muneefah yabari anan a cewarsa ai
itace dolensu.
Bata tankasa ba saboda ta lura sanadi yake nema suka Isa gdan batasan da ya ginashi ba ya
qawatu sosai iyakar qawa anci uban naira s ginin gdan suna zuwa ta shige dakin da yayi mata
ta kulle ita a dole har yanzu fushi takeyi shikuma gashi da baqin naci hakanan yabita suka
kwana sunajin haushin juna dake yasan tun farko shine ya tabata bai wani damu ba da safe ma
ya fice yabarta da sabuwar motar daya siya mata mahadin lefan da yayi mata na dawowarta
yace idan ta gama abinda takeyi ta tafi shi akwai wani aiki daya bayar akeyi masa zaije ya gani.
Bayan ya fita ta gama abinda zatayi ta shirya ta fice can ta tarar da Amrah da Ya'isha suka baje

sunata hirarsu sunata yimata tsiya waitayi qiba ta zama uwar mata sai shirga qiba takeyi saidai
tayi murmushi kawai.




Rasheed bai shigo gdanba sai dare turakar Mai Martaba ya wucce suka taba hira har goma
sannan ya shigo suka qara gaisawa da mutanen gdan Sarki junior ya maqale yace sai antafi
dashi suka fice dole nan tabar tata motar ta shiga tasa da yaransu biyu suka tafi suna tafe yana
satar kallonta Yana hira da yaransa wai ita fushi takeyi har yanzu, da sukaje ya budewa Sarki
junior dakinsa rakashi yaron ya kwanta bacci ya daukeshi ita Kuma ta shige nata tayi wanka
tayima Muneefah suka kwanta cikin bacci taji wayarta na ring ta wawura ta dauka yayi miqa tare
da cewa “Ina buqatar tea" miqewa tayi tayima Muneefah addu'a ta nufi kitchen din ta hadansa
tea ta nufi dakinsa ta bude Yana kwance bisa kujerar hutawa ta aje masa ta miqe ya riqota ta
fada jikinsa ya matseta yana shaqar qamshinta me ratsa zuciya yace “ya kamata a daina fushin
nan haka please na tuba" turo baki tayi yasa harshensa ya lashi lips dinta yace “kinsan cewa
idan kina fushi kyaunki qaruwa yakeyi idan Kuma kikayi murmushi wane Sarauniyar kyau my
Meenah inasonki saman sosai meye yasa muke yawan samun matsala ne?"




Kwantar da kanta tayi jikinsa tace “idan kana bari zuciyarka na rinjayarka kana fassarani inda
ban nufa ba zankejin ciwo Ya Rasheed naqi samun nutsuwa naqi kwantar da hankalina na kasa
zama lfy da Kareem saboda kai Saida takai ko mgn idan ba taka Ya Kareem zaiyimin ba banida
lkcn hira dashi shi yasani ya zauna dani Kuma a haka a qarshe daka bayyana na dagansa
hankali da taimakon mahaifiyarsa da bata qaunata dashi muka rabu badon yanaso ba, nasan
Ya Kareem yanada yaqinin idan ya matsamin zan iya komawa hannunsa tunda bashi da
haqqina Amma a hankali ya rinqa bina a qarshe ya fadamin ya barni ne saboda yasan kai
nakeso bashi ba kuma bazan iya canza hakan ba saboda son ba shawara yayi ba wajen
shigata, Ya Rasheed sai nake tuhumar kaina meye yasa kaidin Dana zaba Kuma ka kasa yarda
dani kullum rigimarmu akan shudadden abune wanda yariga ya wucce har abada bazai dawo
ba?"
Jikinsa ne yayi sanyi ya shafa dogon gashinta ya hura mata iska a fuskarta ta bude idanunta
akansa ga mamakinta sai taga qwallah nabin kuncinsa tasa hannu ta share yaja numfashi yace
“ina tsananin kishinki ne Meenah wato ubangiji yayi gaskiya daya zartar da wannan hukuncin
tabbas da a gaban idona qaddarar rabon Muneefah yasa na rabu dake Kareem ya aura wlh
tallahi zan kasheshi ne har lahira so sai Allah ya boye al'amarinsa shin waima kinsan cewa
Hajiya Bilki tana gdan yari?"
.

Zaro ido tayi tace "Akan me?" Murmushi yayi yace “saboda ta cutar dani ashe duk abinda ya
faru dani sa hannunta ne kawai don naqi auren yayanta Meenah ta rabani dake bayan ta rabani
dake ta cillani duniya na tafi matsayin mara galibi bayan na bace Kuma rashinki ya sanya
tunanina zama me rauni har takai na samu matsalar data zamemin tambari da bazai goge ba
iyakar cewa da rubutawa cikin files dina na taba ciwon hauka da loosing memories kadai ya isa
cutarwa balle rabanin da tayi dake"
Numfashi ya sauke yace kuma kinsan cewa yarta Khadija itace ta tona musu asiri wai taji suna
qulla zasu farraqa tsakaninmu susa Mana tsanar juna shine tazo ta zayyanewa Mai Martaba
komai shikuma baiyi wata² ba yasa aka kamesu yanzu haka shari'a zaa fara ranar Litinin" sosai
lamarin ya tsuma ta tabbas duniya ta jima da cika da azzalumai da Babu hisabi a lahira da anci
bulus Allah ka tsaremu da imaninmu...........




Juhud is not free read... regular 300 VIP 600 via👉🏼 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank



Then you show ur evidence via WhatsApp 09013718241...



Juhud ba littafin kyauta bane ki biya 300 regular VIP 600 kafin ki karanta ta wannan account
din 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank ko katin MTN pls ban buqatar vtu hoton katin ko
digit number ta WhatsApp number 09013718241.....



*Oum Hairan*
[8/30, 8:55 PM] Oum Hairan: Bai bata damar dogon tunani ba ya miqe ya fara Shan tea dinsa
da biscuits bayan ya gama ya nufi bathroom ya watsa ruwa ya dawo daure da towel ya shafa
mai ya kashensu fitila yaja masu labule suka tsunduma duniyar da duk wani masoyan
ma'aurata suke kasancewa a ciki, tun Daren ta farajin yanayin zazzabi hakanan dai ta rinqa
daurewa har zuwa wayewar gari bata Bari ya fahimta ba ya fice kasancewar zasuje anguwa da
Mai Martaba ita Kuma ta fara hidima da yaranta Saida ta shirya Sarki aka daukeshi zuwa school
sannan ta samu damar sake kwanciya nan sabon zazzabi yayi mata dirar mikiya.
Tananan kwance Allah ya jefo mata Aunty Hamida yanda ta tarar da ita a nade tana rawar sanyi
yasata fahimtar da matsala. Tambayar ta tayi tayi mata bayani ta dubeta sosai tace “kuma ba
cikine dake ba?" Saida gabanta ya Fadi da taji ta ambaci ciki lallai har yanzu da sauranta da
sauri tace da Aunty Hamida “nawa ga watan musulumci?" Duba calendar tayi tace “bakwai ga
sabon wata" dafe kanta tayi tace “ya Salam wlh akwai yuwuwar hakan ne 23 nake period
fah....." Dariya Aunty Hamida tayi tace “banga na biyunki a rashin hankali ba Meenah har yanzu

baki hadu gabadaya ba to ai yanzun saiki fara lissafi" jan numfashi tayi ta koma ta kwanta tace
“banso ba Aunty Hamida har yanzu Muneefah bata shekara biyu ba fah" murmushi tayi tace “ai
kinja lkc kiga fah su Ya'isha da akayi aurensu a bayan naki daga me yara uku sai me hudu
kekam biyu haba Meenah ita haihuwa kayita tunda qarfinka"



Batada yanda zatayi dole ta tattara tayima kanta fatan Alkhairi sukaci gaba da tattaunawarsu
wajen azahar Rasheed ya shigo Aunty Hamida tace “nice zan fara yimaka albishir mun samu
qaruwa Meenah ta kusa sake sunkuto Mana baby kyakkyawa" wani ihu ya saki ya zauna kusa
da Meenah yace “haba don Allah da gaske kike Wai hakane My Meenah" kawar dakai tayi cike
da kunya ya dago kanta ya saukenta kiss a lips dinta yace “naso wannan Allah ya rabaku lfy
Wife kinsan me?" Daga ginin makarantarki nake komai ya kammala primary da Secondary din
an zuba duk wani abu da ake buqata na aiki yanzun sauran diban malamai"
Da rashin fahimta ta dubesa tace “Makarantata Kuma?" Murmushi yayi yace “Oh Sorry na
manta ban fada miki ba diamond dinki da old gold dinki aka siyar diamond din ansai dashi 5.5
million gold din Kuma ansai dashi 2.7 million so sai mukayi shawari da Mom akan meye zaayi
miki da kudin Wanda zai amfaneki ya amfani Al'umma so shine aka Gina masallaci a garinku
kasancewar suna fama da matsalar rashin ruwa da rashin gurin ibada in akayi ruwa saidai suyi
a dakunansu an Gina Bohol guda biyu a farko garin da tsakiyar Wandu masallacin Kuma a
tsakiyar garin aka ginashi da niyyar ubangiji ya rinqa kaiwa iyayenki ladan, so abinda yayi saura
sai aka yanke shawarar Gina makaranta Boko ce hade da islamiyya da Kuma tahfeez yanzu
haka sun kammalu komai da komai kinada rarar 2.9 million a account din Sarki junior yanzu yau
nasa gidan TV na NTA da AIT Da Kuma Arewa24 sunzo sun dauka tallan makarantar zaa fara
tallatata mun Kuma fitar da sanarwar daukan qwararrun malamai domin samun abinda ake
nema am kisan meye sunan makarantar?"





Girgiza kai tayi hawaye na kwarara a idanunta yayi murmushi ya goge mata hawayen yace
“MahfAish academy sunan yayanki Mahfuz Aisha academy....." Rungumeshi tayi ta rushe da
kuka tana kissing dinsa ta ko Ina tace “Banjin akwai wata kalma data saura a duniya da zanyi
maka gdy da ita mijina Allah ya azurtani da mafi qololuwar alkhairin duniya daya hadani da miji
na gari Ina alfahari da samunka matsayin uban yayana Allah yabarmin kai ka dade kayi
qarko...."
Gabaki daya sun shagalce a gurin sun manta da anyi ruwan Aunty Hamida itadai data fahimci
sun manta da ita sumsum ta miqe tabar musu gdansu suka shagalce a gurin dama tunda aka
tafi da Sarki school aka dauke Muneefah
Kwanaki sukayita tafiya komai Yana tafiya cikin nasara rayuwa tanata albarka abubuwa duk
suka rinqa shudewa Mom itane ta takura Meenah akan sai ta ziyarci dangin mahaifinta badon

taso ba haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login