Showing 24001 words to 27000 words out of 99941 words

Chapter 9 - JUHUD COMPLETE HAUSA NOVELS BY OUM HAIRAN .pdf

17 Nov 2025

1530

lkc qanqani kodon ya tseratar da
ita daga sharrin Muntaz Amma yasan abune ma bame yuwuwa ba tunda bai gama karatunsa
ba a burin irin na Mai Martaba ba mazaba yaransa mata na bayayi musu aure sai sun hada
degree certificate maza kuwa sai sunyi Masters degree ya samawa kowa gwaggwaban aikin yi.




Lumshe idonsa yayi cikin yanayina tausayin kai da Kuma abar qaunar tasa shikam zaiyi
qundunbalar furta mata koda bazaa Basu damar soyayya ba Allah ya jarabceshi da muguwar
qaunarta baiji a ransa zai iya sakacin Bari ta kubce masa ba, da wannan tunanin yaji ana Kiran
sallar magrib ya tashi ya fita domin zuwa masallaci ya jima a masallacin sannan ya tashi ya nufi
cikin gdan a falo ya tarar dasu dukkansu suna kallon wani Indian series gabadaya hankalinsu
ya bayu ga kallon da sukeyi duk cikinsu babu me motsin kirki.
Ya jima tsaye akansu bai gano Juhud ba can ya hangeta kwance a kujera da littafi a hannunta
da alamun nazari takeyi, zuciya yaja ya nufeta inda Momy tabisa da kallo ya tsaya akanta ya
sanya hannu ya zare littafin ta dago idanunta ta saukesu akansa ta kawar dakai, sake jan
numfashi yayi ya zauna a gefenta yace “Ina Ya'isha da Amrah?" Miqewa tayi zaune ta duba
bata gansu ba ta dawo da dubanta gareshi tace “bansan sanda suka fita ba" jinjina kai yayi
yace “wato Addah kun qyale yarannan suna abinda sukeso babu me iya tsawatar musu basuda
aiki saidai suyi wanka su fice su kwaso wannan su kwaso wancan samari saikace budurwar
karya idan anyi mgn Momy tace farin jini ne don Allah wannan wacce rayuwa kuka zaba musu a
matsayinsu na mata da zasu tafi gdan wasu?"
Dubansa Addah tayi tace “nikam bansan da wanne yare zan ganar dakai ka gane ba
Abdulkareem wlh nafika jin ciwon wannan abin da yarannan sukeyi to baka isa kayi mgn bane
kawai sun samu daurin gindi daga Mai Martaba abinda sukaga dama shi sukeyi kayi mgn suje
su fadaka dashi yazo yayita fada shiyasa na tattara na zubansu ido kaima yanzu nemanka
yakeyi sunje sunce masa kaine ka hana Aminatu zuwa chilling"




Jinjina kai yayi ya bude littafin ya fara dubawa ya dubeta yace “ni ba turanci na karanta ba
Amma zanyi bakin qoqarina wajen ganar dake abinda Allah yasa na fahimta ki tsara lkcnki da
safe zanke miki darasin addini da dare Kuma na boko hakan yayi miki?" Rufe fuskarta tayi tana

dariyar jin dadi tace “wlh yayi Ya Kareem na gde Allah yabarmana kai" murmushi yayi yace
“dole saiya kasheni tashi muje ki nunamin assignment dinku na qarshe da Muntaz nagani saina
samu gabar dora miki"



Miqewa tayi tayi tsalle ta rungume Addah Abulle tace "idan na zama gwamna Ya Kareem zan
fara kaiws makka" dariya sukayi Momy tace “baki rabo da shirme me sunan yaya to Ina kika
baro Baffa'am din naki ni kwana biyu ma banjinsa ko yanayin aikin ne?" Cokalo baki tayi tace
“bayan ya daina sona ko waya ya Kira baya cewa abani" murmushi Mom tayi tace “ai kedin ce
da hayyata kimbi kin damesa yaushe zai dawo naji yace saura wata biyu ya samu hutu ya dawo
gida" tsallen murna ta kamayi tace “na kusa na kwanta a jikin Baffa'am dina me dadi Allah duk
duniya banga Wanda yafi Baffa'am dina iya rarrashina ba sai Ya Kareem da yake
kwatantawa......"
Fuzgarta yayi yace “kin cika surutun banza Amina to shidin muharraminki ne da zakike
kwanciya a jikinsa dan wauta idan kinyi a baya yanzu shima yasan kin wucce wannan shirmen
dubeki fah mace daya da rabi haba wannan ai shirme ne" murguda masa baki tayi tace “eh dai
dan baqin....." Bugu yakai mata suka zuba a guje yana cewa sai kin fadamin waye dan baqin
ciki yarinya itakuma tanayi masa gwalo da haka har bangaren Mai Martaba tana shiga ta shige
bayan Mai Martaba tana dariya shima dariyar yayi ya janyota ta lafe a jikinsa yace “ya akayi ne
Aminatu sarkin wasa kekam kamar ba yar soja ba" tana haki tace “ba Ya Kareem ne yakemin
baqin cikin hawa cinyar Baffa'am dina ba don Mom tace saura wata biyu ya dawo" murmushi
Mai Martaba yayi yace “aifa kaima ka taro March inakai Ina shiga tsakanin ya da ubanta
wannan ai sai Allah" gwalo ta qarayi masa yace “to kagani fah Mai Martaba gwalo takemin"
daquwa ya watsa mata yace “tayi din kaine babban kwabo ai" zama yayi shima suka fara
karatun anan inda batayi daidai ba ya ranqwasheta kafin su gama duk ya tara mata gajiya ta
narke tace ita bacci takeji dakansa ya rakata har qofar falon Muntaz na tsaye a harabar gdan
fuska duk tayi dameji yayi qwafa ya shige dakinsa shikuma ya qarasa rakata ta shiga dakin
nasu sukayi sallama.




Goma da rabi Amma babu kowa a dakin daga Amrah har Ya'isha kayanta ta cire ta daura towel
ta fada wanka tayi wankanta cikin nutsuwa ta bude qofar zata fito taga duhu dakin tace
“subhanallah An dauke wuta Bari na jira a kunna inj....." Mgnr qin qarasa fitowa tayi qirjinta ya
doka da qarfi jin motsi a dakin cikin rawar murya tace “Am...rah.... Ya'isha yaushe kuka daw....."
Nan ma kasa qarasawa tayi jin an rungumeta ta baya a razane tace “please Amrah nace miki
banson wannan wasan ki daina Allah zan fadaki......" Wutar jikinta ce ta dauke jin an Sanya
hannu an janye mata towel din jikinta an dora hannu saman qirjinta ta bude baki tasa ihu
nandanan taji an saketa daidai lkcn da su Ya'isha suka banko qofar da sauri Amrah a lkcn ne
Kuma wutar ta dawo tayi tsaye sangalgal babu komi a jikinta sai rawar baki data jiki takeyi da
sauri Ya'isha ta matsa ta dauki hijjab ta zura mata suka dubeta sukace “yadai Baby meye ya

faru?" Sai lkcn kuzarinta ya dawo ta fara dube² a dakin cikin firgici suma dube²n suka fara suna
tayata ta fara bankada labule itane har qarqashin gado Amma bataga kowa ba suka dubi juna
Ya'isha tace “wai meye kike nema?"




A wahalce tace “mutum" kallon juna sukayi sukace “mutum Kuma?" Jinjina kai tayi sai lkcn taji
hawaye ya qwace mata tace “wanka na fito kawai naga wuta ta dauke Ina tunanin kune naji an
rungumeni ta baya kafin na gama saita natsuwata aka yagemin towel shine inayin ihu naji
kamar an fita da gudu Kuma sai gaku kun shigo don Allah ko kune kuka tsorata Ni?" Numfashi suka sauke a tare Amrah tace “wlh bamu bane muma da muka shigo ihunki ne
yasamu takowa da gudu wannan gdan wani banzan gdane kowa Yana bangarensa sai a
saceka ma baa sani ba"
Zama tayi cikin mugun tashin hankali suma suka zauna Amrah na binta da kallo tace “kece da
shekiyar gardamarki da kin bimu Aida bakiyi gamo ba Kuma ko banza kyaga gari" numfashi ta
sauke tace “to waiko inada Aljanu ne?" Dariya abin yabasu Ya'isha tace “to waye ya sani ni
Amrah fito Mana da qwalam dinmu mu dan lasa Amma wlh yau Shafiq ya wahalar dani shege
inaga magani yaje yasha ya gaji da miyar da nakeyi masa baya qosar dani" Amrah ce ta cafe
da cewa “ke yau ni kinsan sabon kamu nayi wani alhajin birni infada miki quarter million
yasamin a account yace next week zai dawo" tafawa sukayi itadai tana zaune tana kallonsu
suka dauko ledojin da suka shigo dasu suka baje Ya'isha tace “sauko kici rabonki" girgiza kai
tayi suka miqe sukace “aikuwa baki isaba yarinya dole kici" danna mata tsiren sukayi a baki ta
lumshe idonta tana taunawa suka sata a gaba suna dariya saukowa tayi tasa hannu sukaci
sukayi hani'an.



Bayan sun nutsa ne Ya'isha tace “nayiwa Saleem alqawarin gobe zan taho dake yace dubu dari
zaibani tukuici idan Kuma kin amince yazo gda" dagowa tayi tace “aa nidai kar yazo banason
zuwansa wancan zuwan da yayi Ya Kareem kamar zai cinyeni saboda masifa har cewa yayi zai
fadawa Baffa'am" Tsaki sukaja a tare Amrah tace “ke muguwar bahuwa ce waike meye yasa bazaki waye ba koda
yake dama ance sai mutum ya shekara arba'in yake wayewa badon hakaba kawai kita nuqu² da
kayan dadi a jikinki saidai ki wanke kisa masa pant yayi gashi ki aske babu me mora" watsa
mata harara tayi tace “ai cikar mutuncina kenan" wata dariya suka kwashe da ita sukace
“sakarya ita ajiya yanzu haka mijin da kike adanawa ma yana kwance da wata zaa daura masa
aure dake Kinga ta banza kikayi, tabe baki tayi tace “eh shida ubangijinsa nidai nafiso na hadu
da nawa salin alin murmushi sukayi sukace ai saikitayi aikine be isheki ba duk gindin da baayi
masa susa ya zama sorry rayuwar ga ta hutawa daga duniya sai Habuja aljanna tamai rabo"

Da wannan tasa rigar baccinta ta juyansu baya tayi kwanciyarta tanajin kowacce na waya da
saurayinta itakam ko a jikinta washegari da wuri ta tashi tayi wanka tayi sallah ta fito ilai kuwa ta
iske malamin nata a falo yana duba wani littafin addini ta isa gabansa ta zauna suka gaisa cikin
larabci kamar yanda ya sabar mata ya zuba idanunsa akanta yanajin saqon daya dade yanayi
masa yawo a zucci na tasowa hadda take kawo masa shikuma hankalinsa nakanta Saida ta
gama ta dago taga yanda ya kafeta da ido taja numfashi tare dakai hannunta idonsa ya qifta da
sakin wata babbar ajiyar zuciya ya fara Bismillah sannan ya fara yimata qari bayan ya gama
biya mata suka koma Hadith suka sake gangarawa tajweed haka ya rinqa karbar haddarta
mataki mataki yana sake ware injin idonsa akanta gabadaya yau kallon da yakeyi mata yasa ta
kasa sakewa dashi suna gamawa ta miqe ya riqo hannunta yace “na takura miki ko?"
Qasa tayi da kanta tana wasa da yatsunta yaja numfashi ya qara rage sautin muryarsa yace
“wasu fararen kyawawan furanni ne suke sauka saman shararriyar hanyar da babu komai a
samanta sai wasu korayen bishiyu da suka kewayeta gefenta Kuma ruwa ne yake kwaranya ta
saman wani farin dutse a gefen dutsen wata yar bukka ce irin taku ta fulanin asali tsuntsaye
nata shawagi dangin su Kanari Dawisu Jimina Alhuda'huda dadai sauransu"
Gabadaya ya dauke mata hankali da lbrn nasa jin yayi shiru ne yasata dagowa ilai kuwa
idanunta ya fada cikin nasa kwarjini yayi mata irin zaman da yayi saman kilishin dole ne ka
kiyayeshi yayi murmushi yace “ina tafe cikin nutsuwa Amma zuciyata matse take data isa inda
wannan bukkar take wacce ta gefenta ruwa yake gudana take, Ina isa naja na tsaya saboda
wata busar sarewa me kashe jijiyoyin jiki dake tashi ta cikin wannan bukka tare da wata
zazzaqar murya tana rera waqe cikin harshen fullanci" sake tsagaitawa yayi ya hadiyi yawu can
yaci gaba da cewa “bansan wace a ciki ba Amma zuciyata ta kwadaitu dason ganin
mamallakiyar wannan murya me saukar da kasala Kuma me irin suffar matan aljanna, Aminah
ba fadamin akayi ba a Raina naji koma wacece zata kasance haskenta kamar na hurul'ayn, Ina
shiga kinsan wa idona ya ganemin?" Girgiza kai tayi cikin matsuwa dajin qarshen labarin ya
daga hannunsa ya nunata da yatsa yace “kece Aminatuh...." Zaro ido tayi ta dafe qirji tace “ni
Kuma Ya Kareem?" Matsowa yayi numfashinsu na gwamuwa yace “na'am Juhud kene na gani
a dakin Kuma aka mallakamin ke matsayin matata ta sunnah tunda nake bantaba mafarkin da
naji dama ban farka ba kamar wannan naso naga irin rayuwar da zamuyi da rayuwata a
wannan kyakkyawan muhalli Aminatuh Wlh tallahi billahil lazi la'ilaha illahuwa Inasonki sonda
bantaba yiwa kaina ba soyayya ta aure"...............

*Oum Hairan*
[7/19, 9:16 AM] Oum Hairan: *JH012 littafina na kudine idan kinsan baki siya ba don Allah kada
ki karanta, bansanki ba bare na yafe miki haqqina dake kanki*

*Regular group 300 VIP 600 via bank Account 0255526235 Fauziyya Tasiu Umar GTbank or
card for This number 09013718241 only WhatsApp or vtu only for dis 09031307566*

Wata irin zabura tayi ta miqe a hargitse tana waige² kamar ance ta daga kanta sama ta hango
Baffa'am dinta tseye shima ya zubanta ido fuskarsa babu alamun haske ko annuri mamaki ya
cikata a tace “yaushe ya dawo?" Baita samu amsar abinda take nema ba Kareem yasha
gabanta ya tsugunna yace “malaminki yana neman taimakonki Aminatu don Allah kada ki
wofintar dani nasan har yanzu babu kowa cikin zuciyarki shiyasa nayi gaggawa wajen furta miki
abinda Raina ya qunsa"
Sake kallon inda Rasheed yake tsaye tayi har yanzu ita yake kallo ta janye hannunta daga riqon
da Kareem yayi mata ta nufi step din upstairs din da sauri zuciyarta na bugawa da qarfi kafin ta
qarasa taga ya juya ya shige dakinsa ya danno qofar da qarfi daidai lkcn ta qarasa ta shiga
qwanqwasa qofar tana cewa “yau nafi kowacce ya saa Baffa'am ashe idan mutum Yana mafarki
gani yakayi wayyoh dadi baffana ya dawo gareni, please budemin na kwashi tabarraki kasamin
albarka My lovely Dad......"
Yana tsaye jikin qofar yanajinta qirjinsa na harbawa da qarfin dashi kansa baisan dalilinsa ba so
yake ya bude mata ya kasa saboda wani tuquqi da zuciyarsa takeyi masa yayi danasanin fitowa
a daidai wannan lkcn duk da baisan meye Kareem ya fada mata ba Amma yanayinsu ya nuna
wani sashine me muhimmaci sukeson wanzarwa.



Zama yayi saman gadonsa jikinsa Yana wata irin rawa a hankali ya furzar da iska me zafi yace
“meye yake fada miki Meenah?" Miqewa yayi zunbur ya bude qofar har ta hqr ta juya jikinta a
sanyaye abinka da me qoramar hawaye ta fara fitar da qwallah taji ya bude qofar ta juya da
sauri ta nufesa a guje ya bude mata hannu me Kuma ta tuna saitayi turus a gabansa idanunsu
na sarqe cikin na juna hakanan taji sautin bugun zuciyarta yana nunkuwa ta kama hannunsa ta
tsugunna saita rushe da kuka abinda ya qara tashin hankalinsa yasa hannu biyu ya dagota
yasa yatsansa Yana share mata hawayen har zuwa lkcn zuciyarsa tafasa takeyi burinsa kawai
yaji meye Kareem yake fada mata harta bashi attention haka data kasa jin kiransa ta kasa
ganinsa?
A kasalce ya hadata da jikinsa qirjinta ya tokare nasa yaja wata ajiyar zuciya me qarfi yanajin
wata nutsuwa na saukar masa yace “miss ur My Meenah" dagowa tayi hawaye nabin kuncinta
tayi murmushi ta sake saqale bayansa tace “shine Saida ks batamin farin cikina Baffa'am kasan
irin wahalar da nasha kafin na saba da rashinka kuwa meye yasa ka ja zuciyata a qasa harna
fara tunanin ko na bataran haskena?"
Inda kalamanta suka nufa daban inda yakaisu daban janyeta yayi ya zauna a qasa itama ta
zauna yace “meye Kareem yake fada miki me dadi haka da har ya dauke miki hankali kusan 30
minutes Ina tsaye akanku Amma baku sani ba?" Rufe fuskarta tayi tana dariya sokuwar tace
“nifa Baffa'am bansan meye yake nufi ba wai Yana sona kuma son aure hakams Saleem yace
da Ya'isha nikam bana kulasu ma cewa nakeyi suje su sami Baffa'am dina namasan
bazakayimin aure ba ko........."

Wani ihu yayi daya ja hankalin mutanen dake falon qasan gabadaya ya miqe ya shaqeta jikinsa
na tsuma ya kasa mgn sai wani turiri da bakinsa yakeyi haqoransa suna haduwa da gudu Mom
ta nufo saman ta riqeshi tana cewa “na shiga uku ni Aishatu Abdulrasheed meye Kuma yarinyar
nan tayi maka daga dawowarka ko hutawa bakayi ba...." Da ihu yace “So Momy sonta fah yace
yanayi Kuma har take iya fadamin wai yanasonta Nawa take Mom irin riqon amanar taku kenan
har damar soyayya kuka bata injiwa? Waye yabaku wannan damar?" Daqyar suka bambare
Juhud daga hannunsa yayi watsi da ita baijira cewar kowa ba ya fada dakinsa ya doko qofar da
qarfi hada kansa da bango duk wata qofa ta gashi a jikinsa ta miqe idanunsa ya kada yayi jawur
zuciyarsa kuwa kamar ta faso qirjinsa haka yakeji.



Mom ce ta dagota idanunta gabadaya sunyo waje saboda ba shaqar cigaba da rayuwa yayi
mata ba so yayi ya aikata lahira sauka sukayi Addah Abulle ta karbeta hannun Mom tajata
dakinta ta zaunar da ita Ya'isha ta matso tace “kay yau Ina ganin masifa towaishi Big Cele meye
yake nufi dan ance anasonki ya nemi aikaki barzahu?" Iska Addah Abulle ta furzar tace
“Lamarin Rasheed wuyar sha'ani garesa ni yaran nan sun fara gwaramin kai wlh yanzun
Kareem ya fita harda hawayensa wai in taimakeshi ta yarda tanasonsa kafin ya tafi karatu ayi
komai a gama a hada aurensu da Rasheed sai tayi karatunta acan shine nace yaje ya samu
Mai Martaba ya fada masa shikuma wannan kurman yazo Yana neman kasheta kawai don ance
anasonta ko ubanme yake nufi oho"
Shiruce ta ratsa na dan lkc Amrah ta miqe tace “Allah ya kyauta saiki tashi kisa uniform dinki mu
fita ai" tunda suka shigo tana kwance jikin Addah tana aikin kuka daqyar Addah ta rarrasheta ta
miqe tasa uniform din suka fita driver yajasu suka tafi mkrnta duk abinda akeyi akan idon
Muntaz yayi qwafa ya fito ya shiga cikin gidan sukayi clear da Kareem suka harari juna kowa ya
wucce.




Tunda suka fito har sukaje mkrntar kuka takeyi har suka isa kai tsaye office din principal suka
nufa suka gaisheta tare da gabatar mata da Aminah Haroona Moddibo a matsayin sabuwar
dalibar da aka dade dayi mata bayaninta, tambayoyi tayi mata ta bata Amsa duk da batada
nutsuwa Madam Khairat ta Yaba da qwazon yarinyar a mstsayinta na wacce batayi karatu ba. Bayan ta gama mata Interview din tabasu izinin su tafi domin Mai Martaba yace kada a raba
masa yaya abarsu tare, hakance ta faru har aka tashi batada walwala, Muntaz ne yazo
daukarsu baiga fuska a gurinta ba dole yasha jinin jikinsa maimakon ya tafi dasu gda wani park
yakaisu waisu huta tukunna kafin lkcn islamiyya,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login